Showing 66001 words to 69000 words out of 121037 words
ba bako bane bare kace zaka ninke ni bai bai, nasan komai har kiran ta da kayi."
"Ya Allah, ita tace na kirata?"
"Ni na sani, kana wasa da aikin detectives ne?"
"Aikin munafukai dai, na ji na kirata kuma saboda kai ne, babu kuma wata doguwar magana da ta hada mu, bayan gaisawa, hakuri kuma na riga na bata sannan na bata abinda take so na monthly clearance din ta, me ya rage kuma?"
"Call her, kace ta dawo you need her."
"Wa? Ina ba dai ni ba."
"Ba in da ego dinka zai kaika, man accept your defeat kawai dan wallahi nasan kana son yarinyar nan, ban taba ganin kayi ma wani irin abinda kayi mata ba, amma ki fadin ka ya hana ka gane."
"Ya Allah, yanzu me ya kawo duk maganar nan? Soyayya CE irin ta yarinta, irin ta yaya da kanwar sa, babu wani abu kuma,."
"Shikenan, zaka ce na fada maka kila a lokacin da bashi da amfani."
"Let's go please."
"Yes muje, dayar girlfriend din taka tana jiranka kar ta gaji da jira."
Fasa abinda Aryan din yake shirin yi yayi, ya tsaya yana kallon Kamal din
"Girlfriend kuma?"
"Zaka ce baka gane duk moves din ta ba?"
"Ya Allah, me ka maida ni me wai Kamal? Huh?"
"Oho, muje madam dita tana jirana kar hakurin ta ya kare."
"Kana da matsala."
Yayi gaba kawai Kamal din ya bishi a baya yana murmushi,duk taurin kansa da ki fadin sa ba zai hana shi fada masa ba, da bakin sa ya furta yana son ta, kila lokacin a rikice yake ne, yayi subutar baki amma dai ko ma menene ya riga ya furta, kuma yaga komai a idon sa, kuma yana da yakinin sune zasu dawo da alakar Abby da Daddy da ta dade da watsewa, hakan yake fata shiyasa kuma ba zai taba hutawa ba sai yaga hakan ya tabbata.
Kamal ne yake driving din, Aryan na gefen sa, ita kuma tana baya daga side din Aryan din, dadi kamar zai kasheta yau gata ga shi a mota suna tafiya. Babu me magana a ciki sai radio da Kamal ya kunna kawai a kalla zata rage shirun motar. Direct gidan sa ya fara kai su, Aryan ya dube shi da sauri
"Baka sauke Zainab ba?"
"Ai nine a hanya oga, ka sauke ta a gida."
Bud'e kofar yayi ya fito da sauri ya tare Kamal din
"Ya zakayi min haka?"
"Me nayi kuma?"
"Ni ba zan iya kaita gida ba, ta sauka ta hau napep daga nan."
"Kasan dai ba'a fiye samu ba anan."
"Toh ka san yadda zakayi da ita ni zan hau napep din kawai."
"A ah Aryan, ka taimaka dan Allah, mace ce fa."
"Ita bata da kamun kai ne da zata zauna tana jira maza su kaita gida?"
"Taimaka dai toh, kar Madam ta leko ta ganta ma ni na shiga uku."
"Ka gama dani wallahi." Ya bud'e motar ya shiga, tayi saurin bud'e kofar bayan ta dawo gaba ta zauna.
"Sai da safe." Kamal yace ya daga musu hannu yana boye dariyar sa
"Ina ne unguwar?"
"Naibawa."
Be ce komai ba, ya maida hankalin sa akan tukin, tana ta satar kallon sa amma ya hade fuskar sa tamau sai uban sharara gudu yake kamar zasu tashi sama.
"Sir hope ban takura maka ba."
"Mm." Yace a gajarce
"Ok thank you so much, nagode sosai."
"Ok."
Shiru tayi jin yadda ya amsa mata, duk sai tasha jinin jikinta bata sake magana ba, sai da aka zo sannan tace yayi, yayi parking ta sauka tana kokarin yi masa godiya ya fizgi motar kawai.
***Da farko Aryan ya dauka wasa Kamal yake masa da yace zai yi tafiya kuma yana so ya nemo shi, be dauki maganar tasa da gaske ba sam wallahi, dan be yi tunanin akwai in da Kamal din zai wani je ba. Kwana biyu kenan yana neman wayarsa amma a kashe take, sannan yaje har gidan sa shima baya nan dan gidan ma a datse yake har da padlock a gate din. Abubuwan ne suka tarar masa sosai sukayi masa mugan yawa, ga kula da daddy, ga aikin companyn su da yanzu babu wani tsayayye a wajen sannan ga nasa aikin da ya fara a office dinsa, yana ta kokarin tattare dukkan bayanan kafin ranar da za'a soma shiga kotun amma gani yake komai ya dagule masa musamman matsalar Daddy da rashin wanda zai tsayawa companyn nasu wanda dama shi da Kamal suke karfin aikin toh duk su biyun basa samun shiga ma bare su san ya ake ciki. Haka yake fama tsakanin asibiti da offices din duk ya sauya tamkar bashi ba, yana kuma kara jinjinawa Kamal namijin kokarin sa. He's very strong kuma very hardworking dan sai yanzu ya kara tabbatar wa. Kokari sosai ya dinga yi ganin yayi copying dinsa dan bazai yarda ya bashi kunya ba, zai yi abinda zai yaba yasan taraiyarsu tayi matukar amfani.
***KURA LGA*
Tana zaune a dakin bayan ta gama tattare shi ta gyara yar katifar tata da Malam Audi ya siyo mata bayan iftila'in kofar da ya same su kwanakin baya da ya cinye kusan komai na gidan har da kayan ta da take ta boyo da ajiyar su tsawon lokaci tana fatan watarana suyi mata amfani.
Dago labulen dakin akayi, Atika ce dauke da langa ta shigo ta ajiye a gefen katifar ta gaida ta sannan ta juya ta fita. Jim kad'an sai ga Zuwaira itama da samira a rufe tazo ta ajiye daga gefen wadda Atikan ta ajiye itama ta gaishe ta sannan ta fita. Wannan al'adar su mutanen karkara ce basu da matsala ta rowar abinci duk kuwa da basu da kaloli na abincicikan amma kuma suna dafa shi yadda ya kamata dan haka kuma ko bako akayi yazo ba'a san da zuwan sa ba zaka samu da abincin da za'a bashi ya ci. Tsawon zaman ta dasu basu taba fashin bata abinci ba kuma dukkansu haka suke jere mata abincin ko tace yayi yawa sai sun kawo dole sai dai taci ta rage amma dole ne kowa ta aiko mata idan ta gama daga na safe har na dare abincin har yawa yake mata amma babu fashi, sun dauke ta tamkar itace ta haifi majajen su duk wani girmamawa suna mata suna kuma mutumta ta sosai basu taba yin abinda zai bata mata rai ba. Aminene ce ta shigo daga karshe ita ma da nata kwanon ta ajiye sannan tace
"Yau su zuwai sun riga innarmu sauke tukunya kenan, toh na kulin mu zaki fara shi Inna."
"Na kulin mu dai, ai shine farko." Atika dake kofar dakin ta dago labulen ta fada
"Inna namu zaki fara, yau nice nayi girkin kici kiji dadi."
"Toh aminene, duk zanci ai na kowa, naji girkin Aminatuwa ko da dadi?"
"Wallahi da dadi Inna, taliya ce yar murji wallahi."
Atika ce ta kwashe da dariya
"Yo har wani birgewa ce a dafa taliya yar murji?"
"Ina laifi ko Inna?"
"Ba laifi kam."
"Inna da dai tuwo tayi ko shinkafa da miya ko dafaduka, amma taliya da manja ina wani wahala?"
"Duk da haka dai nayi kokari, ke da kika dafa ranar nan ai chabewa tayi."
"Ai ranar ne kawai shima dan an dan samu akasi ne."
"Toh yanxu dai duk kunyi kokari, ku kara zage dantse kafin bad'i a mika ku gidan majajenku."
Da sauri suka tashi suka fice cike da kunyar maganar Innan, murmushin tayi itama kawai dan tasan dama maganin musun nasu da anyi maganar aure sai su gudu. Abincin ta jawo gabanta ta bud'e sannan ta tashi ta wanko hannun ta ta dawo ta zauna tayi bismillah ta soma ci a hankali.
*RQ*
Page 30
****Yana tsaye gaban mirror yana feshe jikinsa da turare yana dan duba gefen wuyan sa da yake ganin kamar ya fada sosai a yan kwanakin nan saboda rashin nutsuwa. Adam ne ya turo kofar ya shigo kamar me jan kafa sai dai yanayin sa ya nuna alamun yasha wani abun. Wani kallo Aryan ya bishi dashi har ya karaso ya tsaya daga gefen sa yana yage baki yayi wata doguwar hamma idanun sa da suka yi mugun kadawa sukayi ja ya zube su akan Aryan din. Saurin ja baya yayi jin warin giya sannan ya zaro ido cike da mamakin Adam din yace
"Giya Adam?"
"Manta da wannan, alfarma nazo nema a wajenki."
"Alfarma?"
Gid'a kan sa yayi
"Kwarai, ka taimaka ka kaini naje naga Mom please, ka yi mun wannan alfarmar kwaya daya tak, nayi maka alkawarin baka wani bayani me matukar amfani a gareka."
Murmushi Aryan yayi kawai, yayi masa kallon mara hankali sannan yace
"Yanzu Adam akwai wani taimako da kake ganin zaka iya yi min kuma ba amince maka?"
"Ka gane? Ka ajiye duk wannan aside muyi magana ta fahimta nayi alkawarin taimaka maka amma ina son sanin in da uwata take mana, haba mana ka tausaya mun ita kadai gareni."
"Kai kana da ita ma, ni fa? Ina tawa? Wannan abinda kake nema a wajena ba hurumin ka bane ba, ka jira mu hadu a kotu kawai."
"Ba zaka dai taimaka min ba kenan ko?"
"Ba zan iya ba , babu wani abu wai shi taimako tsakani na dakai."
"Shikenan, shikenan zamu gani."
"Babu abinda zamu gani sai alkhairi. Na riga nayi latti already kazo kuma ka kara sani yin wani,."
"Shikenan, ba damuwa zamu gamu ne."
Jakar sa Aryan ya dauka ya saba a kafad'a ya nuna masa hanya alamar ya fita, yayi kwafa sannan ya fita shi kuma ya rufe kofar sa ya jefa key din a cikin aljihun sa yayi gaba da saurin sa dan abinda yake gaban sa yau yayi yawa gashi har lokacin na neman kubuce masa.
***Ana i gobe zatayi monthly clearance dinta ta shigo Kanon ita da Hamma Hydar. Gidan Addah Maimuna ta wuce shi kuma ya shiga sabgar gaban sa saboda dama akwai abinda yake da niyyar yi a Kanon gashi kuma dama Abby yace dole duk karshen wata su dinga rakota shi da Bobbo Sadeeq wanda dai yake available a lokacin. Kayan ta kawai ta ajiye suka fito tare da Amina ta rakata cafe tayi printing schedule dinta sannan tayi photocopy na clearance letter din ta hade su waje daya sannan suka dawo gida. Sake gwada dialing number Oga Kamal tayi amma still a kashe, tun kwana uku da suka wuce take kiran shi amma bata shiga a kashe, da farko ta dauko ko bashi da charge ne ko wani abun dai haka sai ta share kawai, amma ganin ta cigaba da kiran kuma still a kashen sai taji duk babu dadi, taga missed calls dinsa a ranar amma ko sanda taga missed calls din bayan wajen awa biyu da kiranta ne dan tana chan falo tare da Abbyn ta ranar ya dawo daga tafiyar da sukayi shi da Lamido da bata san ina ba, shiyasa ta makale masa ta ki barin sa hatta abinci tare suka ci. Dalilin da yasa ta damu ta cigaba da kiran nasa taji ko lafiya amma shiru. Yanke shawarar kawai ta biya gobe ta office din ta duba shi daga I'd card dinta yana chan ta barshi idan yaso sai ta dauka daga nan ta wuce kumbotson. Da wannan shawarar ta kwanta ta kuma tashi ta shirya cikin NYSC khaki dinta da suka sha guga ta saka wani farin sneakers me adon stones ta bar jacket din a bud'e ba tare da ta saka buttons din ba sa saboda ta dan matse ta, tayi rolling da white medium veil da ya kara haske farar fatarta sannan ta fito. Sune zaune dukkan su a falon lokacin karfe tara daidai Muhammad ya kura mata ido yana kallon ta cike da yabawa sai dai be yi magana ba, Amina ce ta hau yi mata tafi dan yau ne karon farko da taga tayi complete dressing din dan last month da taje clearance din bata san
"Kin ganki kuwa Adda Raihana, wow."
"Kai Aminatu banda sharri."
"Dan Allah Mama batayi kyau ba."
"Tayi mana, amma wannan mayafin be yi karami ba Raihana?"
"A ah be yi ba Mama, haka ake sawa fa." Amina tace da sauri
"Ko da yake jacket din da tsawon ta kuma." Adda Maimunan tace
"Yawwa, Allah muma ya nuna mana sanda zamu saka kayan nan wai za'a ga yanga."
"Sai kace kyau zasuyi miki."
Muhammad yace yana hararar ya
"Ai dama ko kowa zai ce nayi kyau ai banda kai Hamma, amma wallahi ni na san zan yi kyau."
"Tafi chan, wata mummuna dake."
Dariya suka kwashe dukka, ta zumburi baki tana hararar sa ta gefe, ita dai Raihana dariya kawai take yi
"Adda na tafi, zan fara biyawa ta office dinmu na dauki I'd card dina sai na wuce,."
"Toh sai kin dawo Raihana."
"Muje na sauke ki kanwata."
"Nagode Hamma."
Gwalo Amina tayi masa ya jefa mata pillow da yake kan kujerar ta chafe tana dariya
"Zan dawo zan kamaki ne yarinya. Da kanki kamar goriba a wajen."
"Irin kanmu daya." Tace ta gudu da sauri ta shige ciki. Girgiza kai kawai yayi, yabi bayan Raihana da tuni ta fita yana jin sa ontop of za world. Da sauri ya karasa ya bud'e mata motar ta shiga ta zauna sannan ya dawo wajen zaman driver ya shiga ya zauna yana shak'ar kamshin turaren me sanyin kamshi. Kusan minti biyu suka dauka ya kasa tada motar dan wani irin feeling ne yaji yana shigar sa akanta, karo na farko da yaji wani abu ya darsu a ransa game da ita. Sai da ya daidaita nutsuwar sa sannan ya kunna motar bayan ya sakar mata murmushi, ya saita radio din motar ya kamo cool FM ya dan rage volume din sannan suka bar layin.
Duk da saurin da Aryan yake yi sai da ya makara sosai, bacci ne be yi da wuri ba jiya yana wani bincike shiyasa ya makara gashi akwai meeting din da zasuyi anjima da directocin companyn su dake wasu states din sannan zasu je su duba Daddy da jikinsa dan sai jiya suka samu labarin abinda ya faru daga bakin Aryan din dan duk kiran da suka yi masa bayan labarin ya bazu be dauka ba, dan bashi da nutsuwar da zai iya yi musu magana a lokacin. Har ya hau sama ya zauna a office ya manta da important files din na cikin mota, tsaki ya dan ja kad'an ya tashi da sauri ya sake fitowa ya sakko kasan daidai lokacin da motar Muhammad ta shigo compound din tayi parking a opposite motar sa. Da farko be lura da wadda ke cikin motar ba, sai bayan ya bud'e tasa motar ya dauki abinda zai dauka ya fito kawai idanun sa suka hango masa ita a gaban motar tana magana da wani handsome saurayi suna ta faman zabga murmushi. Wani das yaji gaban sa ya fadi, maganganun da Kamal ya fada masa suka shiga yi masa bita aka
_"Tana da saurayi."_
yaji muryar Kamal din kamar tayi masa rada a kunnen sa. Tsayawa yayi chak yana kallon su ya ma manta shaf da abinda ya kawo shi wajen, Muhammad ne ya fito da sauri ya zagayo ya bud'e mata kofar sannan ya ware hannuwan sa alamun bismillah sukayi dariya a tare, muryar ta, ta shiga cikin kansa sanda tace
"Kana da abin dariya Hamma."
"Honey?"
Kunnen sa kawai yaji tace ba Hamma ba, ji yayi kamar ya karasa ya same su ya faffalla musu mari a wajen da suke tsaye. Daga masa hannu tayi yayi reverse ya fice sannan ta sauke ajiyar zuciya tana jin kamar be dace ace tazo ba, kamar bata da zuciya ita kuwa? Korar kare fa Aryan yayi mata Amma shine ta zo? Wata zuciyar ce tace mata ai bashi kika zo gani ba, kuma Kamal yayi miki halacci babu laifi dan kin tabbatar da lafiyar sa. Da wannan shawarar ta amince ta nufi building din kanta tsaye duk kuwa da wani abu me kamar tsoro tsoro yana neman dakushe ta. Bayanta yabi kawai ganin ta wuce ba tare da ta lura dashi ba. Tana shiga su Zainab suka yo mata cha da ido, ta gaishe su normal kamar babu komai sannan ta yi hanyar office dinsu dan ta fara daukar I'd card din nata kar ta manta. Babu kowa a office din nasu ta bud'e drawer ta, ta hau duba I'd card din a in da take zaton ta ajiye shi, sai dai baya nan ta sake dubawa sosai tana cikin dubawa Abdulhakeem ya shigo suka gaisa sannan ta tambaye shi ko sun ga I'd card din ta
"Kamar yana wajen oga Aryan gaskiya, saboda ranar Abdallah ya ganshi sai ya dauka ya kai masa."
"Innalillahi, ai da kun ajiye min a wajen KU."
"Ai yazo ma, kije kawai ki karba a wajen sa"
"Ba karbar bace ba ai, ta ina ma zan fara shiga office dinsa?"
"Ba zaki iya zuwa ki karba ba wai?"
"Gaskia, gashi LGI dinmu idan babu I'd card din nan ba zai maka clearance ba"
"Ba dai Tanko bani ba? Shine LGI din naku ko?"
"Shine."
"Wai, ai kuwa idan kina son kanki da arziki kije ki karba gaskiya, in ba haka ba zaki samu matsala."
"Toh ka taimaka ka karbo min dan Allah, zanje na gaishe da Oga KAMAL idan na fito sai na karba na tafi."
"Oga Kamal ai yayi tafiya, baya nan wallahi."
"Haba dai? Ina ta neman wayar sa bata shiga."
"Wallahi baya nan kuwa.'
"Toh ko baya k'asar ne?"
"Eh toh, watakila dai, babu wanda yasan ina yaje a cikin mu gaskiya."
"Toh da sauki ai, dama na dauka ko ba lafiya ne naga ina ta kiran sa switch off, tunda tafiya yayi toh alhamdulillah, yanzu ka taimaka ka karbo min I'd card din ina jiranka dan Allah."
"Ok bari naje."
"Yawwa nagode." Ta zauna sosai shi kuma ya fita. Aryan na zaune yaji an kwankwasa yayi saurin kallon kofar a tunanin sa itace, come in yace yana sauke kansa sai kuma ya sake dagowa jin Abdulhakeem ne
"Ya akayi?"
"Sir dama sister Raihana ce tace nazo na karbar mata I'd card dinta."
"Wacece?" Ya fada kamar be gane ba
"Wannan corper din sir."
"Kace tazo ta karba da kanta."
Ya maida kansa kan aikin da yake yi.
Juyawa Abdulhakeem din yayi ya sameta a office din ya fada mata abinda Aryan din yace
"Na shiga uku, dan Allah yanzu be baka ba? Wallahi bana son zuwa."
"Wai laifi kika yi masa ne hala?"
"Ba komai, ba zaka gane ba."
"Gwara kije da kanki, ba zai bayar ba wallahi."
"Kai innalillahi." Ta mike jiki a sanyaye ta fito. Da sauri Zainab ta tashi ta tare ta.
"Karki shiga office din Oga Aryan."
"Akan me?"
"Saboda yace kar wanda