Showing 57001 words to 60000 words out of 121037 words

Chapter 20 - RUMBUN QAYA COMPLETE hausa Novel

03 Sep 2024

17358

daina motsi sai sukayi amfani da wukar suka dirza mata a wuyanta.

   Aryan da ya fito cikin magagin bacci yana kiran Mummy ya iso kofar dakin nata kenan daidai lokacin suna dirza mata wukar a makogwaron ta, sandarewa yayi a wajen zai kwalla kara aka yi saurin rufe masa baki da ido sannan yaji an janye shi da sauri.
   Tashin Abby kenan bayan an kira sallar asubah, ya dauki wayarsa zai haska sai yaga alamun sako daga Mummy, fasa tashi yayi ya bude sakon sai dai abinda ya gani yayi mugun daga masa hankali

“Help me, sun san na gansu bansan me zasu iya aikata min ba.”

Da gudu ya duro daga gadon, yayo waje ya shiga gidan su Aryan din, ya wuce kai tsaye saman cike da tsoron abinda zai gani.

“Innalillahi wa inna Ilaihi Raji’un.” Ya furta da karfi kafin yayi kanta yana kwala mata kira, ganin bata motsi ya sashi tallafo ta jikin shi

   Karar jiniya ce ta cika layin kafin su soma shigowa gidan da karfin su, Abby na rik'e da gawar suka shigo dakin suka zagaye shi

"You are under arrest." Ogan ciki yace yana rike da ankwa

"Ban gane ba?"

"Zaka gane a station, arrest him!"

****Firgigit Aryan ya farka daga baccin da yake me cike da mafarkai, a ko da yaushe idan ya kwanta sai yayi mafarkin abinda ya faru hakan ba karamin maida shi baya yake ba, shiyasa ba kasafai ya fiye samun cikakken bacci ba. Tun bayan da ya dawo daga gidan su Raihanan yayi kwanciyar sa bayan ya kashe wayar sa kar ma Kamal ko Ya Nabeela su kira shi, ta fara masa koarafin zuwa gidan su Mummy su gaishe su amma ya zame dan be yi niyya ba idan sun matsu suna son ganin su suzo in da suke amma shi babu in da zai je. Wayar sa ya lalubo a gefen sa ya kunna ta ya duba lokaci sannan ya sake kashe ta ya mike a hankali ya sakko ya nufi toilet ya dauro alwala yazo ya haye saman dadduma ya shiga kai wa Allah kukan sa kamar kowanne lokaci.
   Tunda Kamal ya kirashi yaji wayar a kashe yasan kashe ta yayi, Raihana ya kira a lokacin tana kwance lamo bayan tafiyar Aryan din tana kuka k'asa-k'asa ta kasa tashi ta hada kayan nata ma sai Amina ce ta tayata. Bayan tafin hannun ta, tasa ta goge hawayen sannan ta daga wayar tayi sallama a hankali

"Ba dai kuka kike har yanzu ba kanwata?"

Shiru tayi tana jin wani sabon kukan na sake taso mata

"Please ki daina kar kanki yayi ciwo, nasan Aryan yazo ko?"

"Eh,yazo."

"Ok, hope ba wani abu ya sake fada miki ba."

"A ah, ba komai."

"Ok, ki kwantar da hankalin ki. Duk abinda ya fada ba har zuciyar sa bane ba, ba da gaske yake ba wallahi."

"Ok."

"Yawwa, ki cigaba da normal activities dinki, sannan ki taya mu da addu'a, idan komai ya lafa seat dinki yana nan yana jiran ki a sabon office din ki."

"SABON office?"

"Yes, kujerar oga Aryan, ko bakya so?"

Murmushi ta samu kanta da yi, dan tasan Kamal so yake kawai ya kwantar mata da hankali amma ita kuwa me zata koma yi har da zama a office dinsa? Dama ita ba permanent ma'aikaciya bace ba, kuma dama clearance din karshen wata take so toh tunda ya riga ya bata ba shikenan ba? Sai yaje ya karata da bakar zuciyar sa.

"Da gaske nake miki, zamu zo kafa da kafa har Adamawa mu zo biko mu dauko ki."

"A ah ni ba zan dawo ba."

"Zaki dawo ne, baki ma san sanda zaki biyo mu ba, dan muka tashi zuwa a shiryen mu zamu zo."

"Shikenan, zamu gani."

"Zamu gani kam, Allah dai ya nuna mana, ki yi blocking number Hajiya Zeenat daga wayar ki, sannan ki samu hutu sosai idan kin koma karki yarda ki yi stressing kanki da tunani."

"In sha Allah, thank you so much. Kana da kirki sosai."

"Aryan yafi ni kirki fa."

"Um um, wallahi kafi shi. he's not nice sam."

"Shikenan, zamu gani dai."

Murmushi tayi ta mike zaune sannan sukayi sallama. Ji tayi ta samu dan kwarin guiwa bayan sun yi maganar. Hannunta ta kalla ta tuno sanda ya rike ta, da wani abun da taji ya taho tun daga tsakiyar kanta zuwa tafin hannun nata, damke hannun tayi ta lumshe idon ta wani abu na tsirga mata. Da safe suka bar Kano cike da tunanin abubuwan da zasu kasance bayan tafiyar ta.

   Abby na sane da komai shiyasa ya tura Hydar ya taho da ita dan baya son duk abinda zai faru ya zama tana nan. Sun riga sun gama shirya komai shiyasa ma yace ba sai Kamal da Aryan sun zo ba, dan ya shirya bada abinda suke bukata din dama a wannan lokacin, ya kuma shirya yakar Hajiya Zeenat din ta kowacce siga. A yanzu ba kamar wanchan lokacin bane, dan ya gama tattara duk wasu bayanai a kanta, hadda wanda bata taba tunani ba.



*******Da wani irin sauri yake fitowa daga Office din, kunnensa daya makale da waya dayan kuma bindiga ce irin AK47 din nan, sun riga sun shirya tsaf dama tunda already sun san abinda zata aikata bayan ta samu sakon. A jere ya same su dukkan su cikin shiri suna jiran umarnin sa. Kamewa sukayi dukkan su sanda ya iso in da suke, sannan ya basu umarnin shiga mota su dau hanya. Tun rana matawalle yake kano tare da Lamido da shima yake a shirye cikin shigar kayan nasu na dss shima. A wata mararraba suka hadu, suka dauke su kamal ya gaisa da Matawalle sannan ya gaida Lamido cikin girmamawa.

"Kuna sane da location dinta ko?" Lamido yace yana duba agogon hannun sa

"Yanzu haka tana daf da shiga kaduna, zata je su hadu da Barista.”

“Good.”

Wayar da suke amfani da ita wajen communicating Kamal ya saka a kunne, ya bada umarnin rufe hanyar shiga baki daya sannan ya ajiye wayar.

Drivern ta ne yake tuka motar sai body guard din nan daya a gefe sai ita da Salim a kujerar tsakayi, sai Daddy a kujerar baya an shinfide shi, duk da tashin hankalin da take ciki hakan be saka ta nuna karaya ba, burin ta ta isa kaduna ta samu mafaka sannan tayi amfani da Daddyn wajen tilastawa Aryan ya mallaka mata duk abinda yake hannun sa sannan zata bar musu uban su Ya shaki numfashi. A daf da shiga kadunan suka hangi hold up me tsawon gaske, tsaki taja dan tasan zasu dan bata lokaci sai kawai ta kwantar da kujerar ta jinginar da kanta a jiki ta rufe idon ta. A hankali suka dinga ja motocin na matsawa da kadan kadan har suka kusan zuwa daf da wajen dan suna iya hango gaban sai dai alamu sun nuna kamar yan sanda ne suka tsaida hanyar suna searching. Shiru driver nan yayi be ce komai ba duk kuwa da yaga abinda yake faruwa Ya kuma hango Wasu irin manyan na’urori daga chan gaba da suka tabbatar masa da trackers ne.

“Park!.” Aka daka musu tsawa dai lokacin da suka karaso daidai wajen da sai sun bude maka gate din da suka saka sannan zaka wuce. Sai a lokacin duk hankalin su ya dawo jikin su suka farga da abinda yake faruwa.

“It’s a trap hajiya.” Salim yace yana kokarin bude murfin motar bayan sun yi parking a gefe nan da nan aka saki hanyar kowa ya wuce.

“You are under arrest!” Aka kama hannun hajiya zeenat da tayi mutuwar zaune saboda tsananin gigita aka saka mata ankwa, sannan aka sakawa Salim da bodyguard din nan Amma banda driver da ya koma gefen su ya tsaya.
Motar su Kamal ce ta karaso da wani irin gudu dan ba karamin gudu sukayi ba da suka iso a daidai lokacin, tun kafin motar ta gama tsayawa suka diro cikin kwarewar aiki. Abby ne ya fito daga motar a hankali ya tsaya a gaban ta, akan kafafunsa ba tare da ya jingina da komai ba. Tsayawar da yayi tayi daidai da tsayawar bugun zuciyar hajiya zeenat, tayi luu kamar zata fadi wata cikin su ta buga mata wani abu kamar sanda a gefen kafadarta, saurin Mikewa tayi sai ta fashe da kuka

“Wallahi karya suke mjn, wallahi cuta ta zasuyi, me nayi da zaa min irin wannan kamun wulakacin? Me nayi? Mara lafiya zan kai asibiti, mijina ne zan kaishi asibiti shikenan sai a wulakanta ni?”

“Abinda kika aikata ne zaki fara girba daga yanzu, nayi miki alkawarin sai naga down fall din ki zeenatu, baki sani ba duk abinda kike a tafin hannu na kike, wannan da kike gani! Ya nuna Salim da shine yake mata duk kokarin da yake mata yace

“Daga baya mu yake wa aiki.”

“Salim?” Tace, ankwar hannun sa aka cire masa ya matsa yana bubbuge hannun sa.

“Kabir da kika saka yake bibiyar rayuwar iyali na duk da bana tare dasu, dss ne!”

“Salihu da kika dinga bribing sanda ina prison, aiki yake mana.”

“Kinsan mutane nawa ne yanzu zasuyi shari’ah dake?”

Sai yayi murnushi me taushi sannan yace

"Ina Ahmad?"

"Dan Allah karku saurari komai daga bakin wannan mutuncin, mugu ne shine ya kashe min kawata Khadija, shine ya yi Sanadiyyar mutuwar matar sa Aisha, shine yanzu zaizo yana maganar banza, dan Allah karku saurare shi wallahi karya yake mun."

"Abby, ina ganin mu bar wajen nan kawai." Lamido yace

“Ok, muje Lamido.”

"Take her, and lock her up kafin Muzo."

"Ok sir." Suka sara masa.

A mota aka tura ta,ta fara musu ihu da hargowa macen dazu ta dan sassama bakin ta har ya soma jini sannan suka samu tayi shiru.
Kamal da wasu yaran sa su biyu sun wuce da Daddy asibiti tun karasowa su, su kuma sauran Yaran Kamal din sune suka wuce da Hajiya zeenat a daren suka juyo kano. Abby kuma da Lamido suka tsaya a kaduna kafin safiya su dawo Kanon dan Abby yace ba zai iya komawa ba ya gaji.


Direct AKTH suka nufa dashi, Kamal ya kira Aryan yace yazo asibitin Malam yanzu ya same shi, da sauri ya fito ya nufi asibitin yana fatan ya isa kafin wani abun ya samu Daddyn. A hanya yayi ma Ya Nabeela waya ya sanar da ita an samu Daddy amma be san komai akai ba sai ya karasa zai kirata. Be ma san an kama Hajiya Zeenat ba dan Kamal be ce masa komai akai ba. A emergency unit yake dan haka kai tsaye chan ya nufa ya tarar da securities a kofar dakin da Daddyn yake sun tsare wajen rike da bindigun su, tsayawa yayi daga waje ya sake kiran Kamal dan sam be gane abinda yake faruwa ba. Daga dakin Kamal ya fito sanye da uniform dinsa, idanun sa sun yi matukar kadawa kamar wanda ya sha wani abu ko wani abu ya fada masa a ido saboda abinda yake ji, dan zai iya rantsewa yafi kowa cutuwa da wannan abun da ya faru. Da kallo Aryan ya bishi sanda ya nufo shi, yana son gasgata abinda yake gani din, shin Kamal ne da gaske ko dai idanun sa ne?
Tunanin abinda ya faru chan baya ya shiga dawo masa, sanda ya fara haduwa da Kamal a kofar gate din makarantar su ta secondary, sanye da wata riga fara da dogon wando yana rike da waya a kunnen sa.

"Aryan?" Ya kira sunan sa dalilin da ya saka shi tsayawa chak da mamakin ya akayi ya sanshi.

"Ka sanni?" Yace da mamakin sa, gid'a masa kai yayi alamar eh sannan yace

"KAMAL ne da kukayi Montessori tare."

Shiru Aryan yayi yana son tonowa amma ya kasa, fuskar sa ya sake kalla sai yaga kamar ya sanshi amma ya manta

"Ka manta ni Aryan? Ko da yake ni senior dinka ne ko a lokacin, ka manta sanda kake zama kai daya a karkashin wata bishiya nazo na same ka na tayaka zama? Har ma ka sanar dani damuwar ka, ka tuna?"

"Na tuna." Yace a sanyaye

"Boarding school na tafi, amma tun daga lokacin ban manta ka ba, ina tuno ka da damuwar ka, dalilin da yasa na zo ganin ka, na gama secondary school zan tafi karatu."

"Allah sarki, nagode sosai."

"Zan dawo, zan kuma taimaka ma in sha Allah."

"Ok." Yace ya daga masa hannu, ya nufi mota lokacin driver yana tsaye yana jiran sa.

Bayan nan be sake ganin sa ba, sai bayan shekara hudu, a lokacin ya dawo rayuwar sa,tun daga lokacin ya zama garkuwar sa, yake kare shi da dukkan iyawar sa. Ko da wasa Aryan be taba kawo shi a wannan layin ba, ya kan yi mamaki sosai idan Kamal din yayi wasu intelligence abubuwan, amma be taba hasaso shi a wannan yanayin ba. A gabansa ya tsaya ya karkada masa hannun sa ganin hankalin sa ya tafi tunani

"Kamal?" Ya nuna shi da hannu sannan ya kalle shi tun daga sama har k'asa

"Ka kara da Sir Kamal a gaba." Yayi murmushi. Girgiza kai Aryan yayi, sannan yace

"Babu wanda yake zaune dani da gaskiya kenan? Kowa sai ya boye min ainahin waye shi?"

"Karka fara, please." Kamal yace

"Why? Me yasa?"

"Kawai, kar muje nan, akwai abubuwan da suke gabanmu yanzu, dan haka ba yanzu bane lokacin."

"Kasan yadda ake ji? After all this years? You pretend to be under me,it's like bansan ka ba, bansan komai akan ka ba, who are you?"

"Aryan, is this the right time?"

" I don't know, ban sani ba."

Ya matsa baya

"Please kar kayi complicating komai, yanzu ba lokacin fushi bane ba, Daddy yana bukatar ka a yanzu, kayi hakuri zan maka bayanin komai."

"It's ok, bana son ji please."

Sai ya juya kawai yayi ficewar sa, kwala masa kira Kamal ya shiga yi amma kamar be ji ba ya karasa sauka daga wajen ya shiga motar sa.






*_ZAFAFA BIYAR COMPLETE DOCUMENTS_*


*ZAFAFA BIYAR BACTH A*


1.. _WUTSIYAR RAƘUMI_ 350
*(Bilyn Abdul)*


2.. _KAI MIN HALACCI_ 350
*(Miss xoxo)*


3.. _BURI DAYA_ 350
*(Mamu gee)*

4... _DAURIN BOYE_ 350
*(Huguma)*

5... _SAUYIN KADDARA_ 350
*(Hafsat Rano)*

_Duka biyar 1500_

*___________________________*


*_ZAFAFA BIYAR BATCH B_*


1... _DAURIN GORO_ 350
*(Hafsat Rano)*

2... _ALKAWARIN ALLAH_ 350
*(Huguma)*

3... _QAUNAR MU_ 350
*(Mamu gee)*

4... _IGIYAR ZATO_ 350
*(Miss xoxo)*

5... _GUDU DA WAIWAYE_ 350
*(Bilyn Abdull)*


_Duk biyar 1500_

*_____________________________*

*_ZAFAFA BIYAR BATCH C_*

1... _MIN QALB_ 350
*(Mamu gee)*

2... _SARAN ƁOYE_ 350
*(Bilyn Abdull)*

3... _KIBIYAR AJALI_. 350
*(Miss xoxo)*

4... _ABINDA KE CIKIN ZUCIYA_ 350
*(Hafsat Rano)*

5... _SIRADIN RAYUWAR BILKISU_ 350
*(Huguma)*

_Duk biyar 1500_

*____________________________*


*_ZAFAFA BIYAR BACTH D_*

1... _ALKIBLA_ 350
*(Huguma)*

2... _DALAAL_ 350
*(Miss xoxo)*

3... _UBAYD MALEEK_ 350
*(Mamu gee)*

4... _MABUDIN ZUCIYA_ 350
*(Hafsat Rano)*

5... _MAKAUNIYAR KADDARA_ 350
*(Bilyn Abdull)*


_Duk biyar 1500_

*____________________________*

*_ZAFAFA BIYAR BATCH E_*

1... _SO DA ZUCIYA_ 350
*(Mss xoxo)*

2... _TAKUN SAAKA_ 350
*(Bilyn Abdull)*

3... _HALIN GIRMA_ 350
*(Hafsat Rano)*

4... _DAB'IZAR ZUCIYA_ 350
*(Huguma)*

5... _DEEN MARSHALL_ 350
*(Mamu gee)*


_Duk biyar 1500_

*______________________________*


*_ZAFAFA BIYAR BACTH F_*

1... _BAKAR INUWA_ 350
*(Bilyn Abdull)*

2... _RAYUWAR MACE_ 350
*(Hafsat Rano)*

3... _NOOR ALB_ 350
*(Mamu gee)*

4... _MASARAUTA_ 350
*(Mss xoxo)*

5... _KUFAN WUTA_ 350
*(Huguma)*

_Duk biyar 1500_

*_____________________________*

*_ZAFAFA BIYAR BATCH G (COMPLETED)_*

1... _FARHATAL QALB_
*(mss xoxo)* 400

2... _GURBIN IDO_
*(Huguma)* 400

3... _SANADIN LABARINA_
*(Hafsat Rano)* 400

4... _INAYAH_
*(Mamu gee)* 400

5... _BABU SO_
*(Bilyn Abdull)* 400

_Kuɗinsu a yanzu 2K duk biyar_




*_ZAFAFA BIYAR 2023_*🔥🔥🔥
_*Sabuwar shekara sabon salo sabon taku,*_
_*Makaranta littafan hausa kuma masoya marubutan zafafa kuzo ga sabuwar tafiya zazzafa tazo karku bari ayi babuku *_

_*Zafafan alkaluman haziqan maruban zafafa biyar kowa yasan na daban ne,wannan karon ma sunzo da sababbin salo me kama zuciya.*_
_*ZAFAFAN MARUBUTAN SUNZO DA SABABBIN LITATTAFANSU NA 2023 Kamar haka,*_

1 _*IDON NERA*_
Mamuhgee

2 _*DAUDAR GORA*_ ciki ka shata
Billyn Abdul

3 _*RUMBUN QAYA*_
Hafsat Rano

4 _*KI KULANI*_ mallakin zuciyata
Hafsat Miss Xoxo

5 _*A RUBUCE TAKE*_ qaddarata
Safiya Huguma


_DUKA GUDA BIYAR DIN ZAKA SAMESU A FARASHIN 1200_

Guda 5 1200
Guda 4 1000
Guda 3 800
Guda 2 600
Guda 1 400

_*zaku saka kudin a wannan account din👇*_

_*0022419171 Access Bank Maryam sani*_

Saiku tura shedar ta👇

_*09033181070*_

Idan kuma katin Waya ne zaku tura katin MTN ta wannan layin👇

09166221261



TEAM ZAFAFA BIYAR🔥🔥
MUNGODE🙏🙏❤️
*RQ*
 
      27

****Murza gefen goshin sa yayi ya juya kawai ya koma ciki dan yana so ya tabbatar da lafiyar Daddyn. Ya Nabeela ce ta karaso da maigidan ta, ta tarar da Daddyn ana kan yi masa gwaje-gwaje domin gano ainahin matsalar sa, domin akwai wasu allurai da Hajiya Zeenat tasa aka dinga yi masa a spinal cord dinsa wanda zai yi wuya idan basu yi effecting dinsa ba. Hankalin ta yayi matukar tashi da taga halin da Daddyn yake ciki, ta dinga kuka suna rarrashin ta dole ta dawo reception ta zauna saboda ta kasa yin shiru kwata-kwata. Babu kowa a ciki da ya rage sai Kamal wanda yake tsaye a kofar cikin jin zafin abinda Hajiya Zeenat ta aikata. Waje  ya fito bayan kiran Lamido ya shigo wayar sa, ya daga daga chan kofa sukayi magana sannan ya koma ciki suka cigaba da tsaiwa da jiran tsammani.
   Driving Aryan yake amma ya kasa controlling fushin sa, sosai ya zama baya ganin gaban sa saboda yadda yake ji tamkar zuciyar sa zata yi bindiga, me yasa kowa sai ya dinga boye masa komai akan me? Zai iya rantsewa a yanzu be san waye Kamal ba, be kuma san komai a kanshi ba duk kuwa da tsawon lokacin da suka dauka a tare suna tare da juna. A dan lokacin da be gaza kwana uku ba ya zama heartbroke, daga wajen mutane masu matukar muhimmaci a wajen sa, duk kuwa da ya gano komai da sukayi sun yi shi saboda farin cikin sa amma me yasa sai an boye masa? Me yasa yake zama na karshe da zai san komai akan abinda ya shafe shi? Gefe ya samu yayi parking ya dora kansa a saman steering motar kawai dan ya tabbatar idan ya cigaba da tukin zai iya yi wa kansa mummunar illah. Ya dade a haka har sai da wani me wucewa ya zo ya kwankwasa masa glass din motar, ya dago ya kalle shi sai ya tuno a in da yake wanda shaf ya manta ma. Kunna motar yayi kawai ya bar wajen ya juya zuwa asibitin dan be wani yi nisa da chan din ba. A reception ya hadu da su Ya Nabeela taci kuka ta koshi kawai sai ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login