Showing 72001 words to 75000 words out of 121037 words

Chapter 25 - RUMBUN QAYA COMPLETE hausa Novel

03 Sep 2024

17336

shikenan ba? Tunda kinsan haka sai daina kukan haka nan, suma duk neman rigima ce tasu, ai ba haramun bane ba, kuma kowa ba da KADDARAR sa ba ?"

"Duk yasa kowa yana mun fada, Abby na ma be taba min fada ba sai yau, ga Hamma na Hydar shima tun a kano yake ta min fada, nima duk abinda basa so bana son shi."

"Toh ai shikenan, sai ki tashi kije ki wanko fuskar nan, kizo mu fita yau chan gida zamu,sai dare zamu dawo naga me dafa musu abinci kuma."

"Dadah fushi kikayi dasu?"

"Eh mana, akan me zasu takura miki akan abinda ke ba shine ma a ranki ba? Bar su munyi fushi sai sun zo biko."

"Waye zai kaimu toh?"

"Ba zamu hau motar kowa ba, gwara ma Sadeeq idan yana nan,shi babu ruwan sa da wannan fi'ilin nasu, kira shi ma idan yana kusa yazo ya kaimu yau chan zamu wuni ki shiga cikin yan uwanki kuyi hirar zumunci ba ko da yaushe kina kunshe a daka ba daga ke sai basawan yayyan ki wanda basa son gaskiya, ko wa zai ganki yace yana so suna kaf kaf dake? Yadda suke manyan tuzurai haka suke so ki zauna kema saboda rashin gaskiya"

"Kai Daadah,yau su Hamma sun tsokanawa kansu."

"Dama fa a wuya nake dasu Allah, dole fa sai kin fita wani zai gani ya kyasa, ko a dangi ko a gari, amma duk inda zaki suna biye dake wannan ai kamar ma kashe kasuwa ne."

Dariya ta fashe da, Dadah tayi tsut da fuska dan ita har zuciyar ta da gaske take, dole a sake sabon zama lokaci yana tafiya su bar yarinya ta sarara.

"Bafa wasa nake ba kike dariya, da gaske nake kuma wannan karon dole a sake lissafi, ni da zai yiwu duk a hade ku dasu a sha biki wallahi."

"Ashe kin gaji da gani na Daadah na?"

"Yo ko na gaji dake ko ban gaji dake ba Raihanatu ke fa 'ya mace ce, gidan wani zaki kuma dole."

"Ai shikenan tunda neman head kike dani, dama kin daina so na kwata-kwata."

"Soyayyar ce ta jawo ai, dan haka ki tsaida hankalin ki waje daya kina jina? Ki bawa masu son ki dama ku daidaita, babu wanda lokaci yake jira su bar ganin kina da wannan jar kalar namiji da kin wuce lokacin ki zai daina ta taki."

"Wannan maganar dai a barta sai next time Dadah, bari na wanko fuskar mu tafi."

"Kyaji dashi, yi sauri kafin azahar tayi su shigo neman abinci, sun ga tsiya yau. Shima Abban naku aure ya dace dashi,sai na koma nima cikin yan uwana."

"Ai ko aure Abby zai ba in da zaki Dadah, nan ne gidan ki,."

"Sai dai ki tafi dani naki gidan idan an miki auren ke, amma ba zan zauna ba."

"Ni ai muna jone Dadah, kafata kafarki ba wani da zai raba mu."

"Karya, irin ku ne da an kaiku sai aji luf an samu gidan miji anyi shiru, wata tara a ishemu da kukan jinjiri."

"Bari na dai wanko fuskar tawa Dadah." Tace da sauri ta shige toilet din dan ta lura yau Daadan a sama take neman rikici take da kowa. Fita tayi ta ja mata kofar tana sababi.


***Adam na tsaye a jikin stairs yana jiran fitowar Aryan sai gashi ya fito da dan saurin sa.

"Lafiya?"

"Yes, naji kana waya yau za'a kai mom kotu, so nake naji gaskiyar maganar."

"Eh yanzu haka ma chan zani, kotun dake Normansland."

"Why are you doing this?"

"Wai tambaya ta kake?"

"Yes, menene yasa kake son ganin bayana."

"Bayan ka? Ina bayan? Kasan me kake cewa kuwa? Who are you by the way ma?"

"Ba ta kai nake ba dan Allah Adam, kazo kotu sai kaji duk charges din da yake kanta, sai kasan irin maganar da zakayi."

"Ba zaka taba succeeding ba in sha Allahu, heartless human being."

Murmushi kawai Aryan yayi ya wuce ya bar shi a wajen, yasan ba a hayyacin sa yake ba, shiyasa ma ba zai biye masa ba, dan yana da abun yi, daga kotun wani kauye zai wuce wanda ya samu labarin Hajiya Zeenat din ta taba kai wa wani mutum ziyara garin. Shi zai je ya gani dan yana da yakinin akwai wani abu da ya sani game da ita.

***Sune tsaye a gaban kotun aka shigo da ita, tayi masifar sauyawa tamkar ba ita ba, hayaniya ce ta kaure a cikin kotun kowa yana kokarin tofa albarkacin bakin sa, masu daukar hoto na dauka a boye. Alkaliyar da zata saurari karar ce tayi calling attention din mutane aka samu wajen yayi shiru, sannan aka soma sauraran karar ta bakin lauyan gwamnati tare da Aryan. Bayan an karanto mata dukkan laifukan ta, ta kuma musanta, sai justice Fatima ta bada umarnin aike wa da ita gidan dan kande sannan an d'age sauraran karar zuwa sati biyu masu zuwa in da za'a dawo a fara gabatar da shaidu.
Da sauri Adam ya mike daga in da yake tsaye yayi wajen ta, akayi saurin tare shi ya hau ihu yana zagin Aryan aka samu aka fitar dashi daga kotun sannan itama aka fice da ita ta kofar baya.

Aryan na tsaye tare da wasu manyan barrister message ne ya shigo wayar, tun kafin ya bude yasan waye ya turo message din dan tun jiya ya fara aike masa da sakon akan shari'ar yana kuma kokarin kara masa kwarin guiwa akan abinda yake gaban shi, dan shine ma ya tura masa address din mutumin da kauyan da yake zaune kuma zai je ya ganshi dan so suke a sati biyun nan su karasa tattara duk shaidar da suke bukata

"I'm proud of you.KM."

Murmushi yayi kawai ya kashe wayar ya maida ita aljihu, sannan sukayi sallama ya fito daga cikin kotun. Habeeb ya hanga tsaye jikin motar sa, ya karasa yana duban shi da mamaki

"Barka da rana Sir."

"Ina ka shiga wai Habeeb?"

"Na danyi tafiya ne. Amma na dawo yanzu zamu cigaba in sha Allah."

"Ya akayi kasan ina nan?" Ya tambaye shi da mamaki sosai

"Oga Kamal ne ya sanar dani."

"Kaima cikin su kake ko?"

"Na'am?"

"I know, dama tun farko ban yarda ba, nasan akwai wani abu dole, baka yi mun kama da driver ba, lallai Kamal, akwai tarin abubuwa game dashi da ban sani ba."

"Haka aikin yake sir, mu cigaba da tafiya a yadda muka faro, dan Hajiya Zeenat ba ita kadai bace a wannan tafiyar ba, tana da support kuma suna kokarin duk yadda zasuyi su dakile ka, muna cigaba da bincike a kansu amma dai for now kana bukatar tsaro."

"Allah ya kyauta, muje toh." Ya mika masa key din, ya bud'e masa kofar ya zauna sannan ya zagaya shima ya zauna a mazaunin driver sannan ya kunna motar.

***A rana irin ta yau tarihi ya maimaita kansa, kamar yadda a irin wannan ranar Hajiya Zeenat take cike da murnar tura Abby prison sai gashi a yau an nufi gate din da ita. Hankalin ta ne ya tashi ta shiga tuno makamanciyar ranar. Goron dutse prison aka kai ta ita, ana zuwa aka tura ta prison 1 (welcoming prison) In da ake ajiye duk wanda ya shigo prison din a ranar kafin gobe a rarraba kowa prison din da ya dace da shi.
Abby na zaune yana kallon komai da yake faruwa ta cikin wayar sa, duk da akwai sauran zama a shari'ar amma ko a yanzu hakan burin sa ya cika, idan komai ya dawo normal zai yi kokarin sake nesanta kansa da wani abu da zai iya hada su da Alhaji Mukaddas, baya ko bukatar ganin sa shiyasa ma ko zuwa be yi ya duba shi ba, haka ranar da aka kama Hajiya Zeenat din be ko bi ta kansa ba bare ya nemi ganin sa duk kuwa da ya samu labarin yana cikin matukar wahala.
Lamido ne ya shigo ya zaune a gefen sa, ya kalle shi sannan ya ajiye wayar

"Kaga komai Abby?"

"Na gani, ko a yanzu buri na ya gama cika, matsala daya ce nake tsoron ta, Aliyu ya bani labarin alakar kanwarku da Aryan, ni kuma gaskiya ba zan amince ba, ba zan yadda ba, babu wata sauran alaka tsakaninmu da mutanen nan,."

"Hydar din ya fada min nima, kuma in sha Allah babu abinda zai faru, Raihana yarinya ce me biyayya ba zata taba son abinda bama so ba."

"In sha Allahu, ya isa hakan alakar da akayi a baya ta rashin sani ta wadatar,."

"In sha Allah."

"Yaushe zaka tafi wajen aikin ne?"

"Karshen satin nan zan tafi, ina dan karasa hada abubuwan da zan bukata a chan ne."

"Ok Allah ya taimaka ya bada sa'a, dama case din nan da kuke kai ya hana ayi muku transfer din tuntuni."

"Eh shine yasa."

"Ok, Allah yayi riko da hannayen ku, ya taimaka muku ya tsare ku a duk in da kuke."

"Amin Abby."

"Sai a fara maganar saka rana, zaman ya isa haka nan, ni ba mace kuma babu, dan haka dole ayi abinda ya dace."

Sosa kansa yayi

"In sha Allah."

"Madallah. Bari na dan shiga ciki na kishingida ko zan dan samu bacci kafin la'asar, idan Sadeeq ya dawo kace inason ganin shi."

"Ok a huta lafiya."

"Allah yasa."


***

*RQ*

Page 33

©️Hafsat Rano




***Tafiya kilometres hamsin da hudu ta kaisu garin na Rano, karon farko da Aryan ya taba zuwa garin duk da yana samun labarin cigaban da suka samu sosai ta fannoni daban daban musamman bangaren ilimin zamani da kuma kasuwanci da yan garin suka rike na man petrol, gas da kerosene. Sun kafu sosai akan harkar kuma suna samun arziki sosai dan tun daga kofar garin zaka tabbatar da hakan ganin tsarin gine-gine masu matukar kyau da suka zagaye garin ga wasu manyan duwatsu da suke karawa garin kyau da tsari. Akwai abokan Daddy sosai da suke harkar m ai a garin wasu suna haduwa idan an tashi taro ko kuma wani abun ya hada. Rage gudun motar Habeeb yayi sanda suka karaso kofar asibitin garin yayi parking bisa umarnin Aryan din sannan. Da kansa ya fito ya samu wasu mutane a zaune ya gaishe su sannan ya tambaye su in da zasu bi su je layin gidan sarki. Kwatance sukayi masa yadda zai gane yayi musu godiya ya koma mota ya nunawa Habeeb in da zasuyi, suka daga musu hannu suka wuce. Kasancewar karamin gari kowa ya san kowa basu wani sha wahalar gano gidan ba, maimaita sunan mutumin Aryan yayi, yayi daidai da sunan mahaifin Kamal, amma duk da haka be kawo komai ba, ya dauka kawai coincidence ne sunan yazo daya. A kofar gidan sukayi parking ya kalli layin me dan fadi ya hango wani dattijo a zaune a kan wata tabarma gaban wani dan karamin masallaci tare da wasu a zaune a gaban sa kamar suna daukar karatu, bayan su babu kowa a layin sai yan wasu yara suna wasan taya suma daga wani gefen.

"Mu karasa wajen mutanen chan Habeeb."

"Ok." Yace ya kashe motar suka fito suka nufi masallacin. Zuwan su wajen ya saka dattijon katse karatun da yake na littafin sunanin nabiy da yake karantar da manyan unguwar duk bayan sallar la'asar har zuwa magriba sannan suyi karatun alkurani me girma bayan magriba din zuwa Isha, daga nan sai su hadu suci tuwon dare har zuwa karfe taran dare sai kowa ya shige gida sai kuma asubah idan da rai da lafiya. Durkusawa sukayi har k'asa suka gaishe su dukka, suka amsa a sake sannan ya tambaye su daga ina dan be gane su ba.

"Daga kano muke, munzo wajen Malam Hassan sarki ne, daga chan titi aka kwatanto mana wanchan gidan."

"Ni ne nan Hassan sarki, sannun ku da zuwa."

Kallon juna sukayi shi da Habeeb sai Aryan yayi murmushi ya kara gaishe shi sannan yace magana ce take tafe dasu. Tashi yayi bayan ya nemi afuwar wanda suke tare yace su taso su biyo shi, suka nufi gidan da suka yi parking. A jikin motar Habeeb ya tsaya shi kuma Aryan yabi bayansa zuwa cikin zauren gidan, me dauke da wani dan madaidacin daki.

"Bismillah shigo."

Yace masa bayan ya shiga ya zauna, shiga Aryan yayi ya zauna a ladafce sannan ya shiga yi masa bayanin dalilin zuwansa,

"Yanzu haka an soma shari'ar tata, kuma ana bukatar samun hujjojin da zasu bada damar yanke mata hukunci."

Ya karkare yana duban Malam Hassan din

"Tabbas lokaci yayi da azzulumar matar nan zata girbi duk abinda ta shuka, naji dadi matuka kuma zan bada gudunmawa ta dari bisa dari, zan zo har kotun na bada shaidar duk abinda ya faru ranar, amma kafin nan inaso na sanar da kai yadda komai ya kasance. Gyara zama Aryan yayi cikin zakuwar son jin labarin duk da kuwa baya duniya a sanda abun ya faru amma ya samu labari daga baya, kuma yasan yana daga cikin abin da har Mummy ta koma ga Allah be bar zuciyar ta ba, ta kan tuna tayi kuka sosai dan ba karamin tashin hankali bane a raba ka da dan ka tun yana jinjiri.

_"Kana jina yaro? Watarana bayan Magriba daf da ishai na fito daga gida ina kokarin karasawa masallaci a lokacin ni ne ladanin masallacin ni ke kiran sallah, a daidai wata kwalbati dake da dan tazara da masallacin na ji kamar kukan jinjiri, matsawa nayi domin tabbatarwa cikin tsananin mamaki na ga jariri babu ko riga a jikin sa sai pampers ya cure waje daya yana kuka sosai, waigawa nayi da tunanin zan ga wani amma babu kowa kasancewar layin babu mutane ba kuma kasafai aka fiya bin sa ba idan dare saboda masu kwacen waya da yan iska. Ni kaina a lokacin saurin da nake yasa ni yankewa nabi ta lungun saboda yafi kusa da masallacin akan ta chan titi. Jaririn ne ya cigaba da kuka na juya da nufin tafiya ta amma sai naji chak na tsaya, ba zan iya ba, rashin tausayi na be kai haka ba, dawowa nayi na duka nasa hannu na dauko shi ya kara chanyarewa da kuka, hawaye ne suka biyo gefen kunci na, na share ina rike shi kam kam kar ya sullube dan ba iya daukar jarirai nayi ba ko haihuwa akayi a gidana bana iya dauka har sai sunyi kwari. Lungun na sake bi da nufin na shiga cikin mutane sosai sannan na nemi taimakon su mu mika jaririn gidan mai gari ina shigowa wani dan lungu sai na hadu da wasu maza su biyu suna tsaye a dan wani lungu. Ina zuwa daidai in da suke tsaye dan da fari ban ma lura dasu ba, sai da na matso daf naji kuma sun min magana sannan na ankare."Malam Hassan barka da wannan lokaci." Gudan yace min yana kallon na. Amsawa nayi ina kallon yanayin suturar da take jikin su ta rashin d'a da wata uwar suma da suka tara akan nasu babu kyawun gani. Kallon hannu na sukayi nayi saurin cewa "jariri ne aka yar dashi a cikin kwata, ko su waye suka yar dashi basuyi adalci ba, basu kyauta ba kuma basu da imani, gidan me gari zan mika shi nasan in sha Allah za'a iya samun iyayen sa in da anan kusa suke." Babu wanda ya ce uffan a cikin su, sai cigaba da kallon na da sukayi , ganin haka kawai yasa nA juya da nufin yin tafiyar ta,sai ji nayi an fisgoni kamar wani karamin yaro, nayi baya kamar zan fadi suka shataloni sannan suka shaka min wani abu me warin gaske, Allah ne ya kiyaye ban yada jinjirin hannu na ba. Tun daga nan na rasa hankali na, bansan ina nake ba. Tsawon awoyi na dauka a hakan kafin na farfado na ganni a wani daki me duhun gaske. Kukan karamin jariri ne ya karade dakin a hankali sai haske ya maye gurbin duhun da ya mamaye dakin. Matata Rabi na hango a zaune a kuryar dakin rike da jaririn sai lokacin na tuna abinda ya faru, na yinkura da sauri zan mike naji an daure min kafa ta da hannu na. Rabi? na kira sunan ta, kanta a kasa tana kuka bata san na farfado ba sai da nayi magana ta dago a zabura. "malam." Tace cikin muryar kuka, "me muke anan Rabi?" Na tambaye ta ina kallon jaririn hannun nata da har lokacin kuka yake. "Wasu maza ne suka je har gida suka dauko mu ni, suka kawo ni nan sannan suka ce wai kashe mu zasuyi." Subhanallah, me mukayi musu." Ban sani ba, amma koma menene Malam akan jaririn nan ne, naji suna maganar kashe shi zasuyi ma, wallahi Malam inason shi, lokaci daya son shi ya shiga zuciya ta, dan Allah kar mu bari su kashe shi, ina son shi." Menene alakar su da jaririn toh? Tabbas shine dalilin da yasa su kawo mu nan, kuma ina kyautata zaton akwai wani abu da suke boyewa." Jin ana taba kofar ya saka mu yin shiru, samarin nan ne tare da wata mace wadda sai daga baya na gane wacece, itace Hajiya Zeenatu Mukaddas, itace kuma ta sace jaririn ta sa aka jefar dashi, mu kuma muka tsince shi, bamu taba haihuwa ba tsawon lokacin nan, dalilin da yace muka gudu da jaririn kenan muka raine shi, bayan mun gudun da safe a hanyar barin garin muka samu labarin batan dan gidan Alhaji Ibrahim Mukaddas, tabbas a lokacin mun so juyawa mu maida musu dansu, amma bamu samu dama ba saboda biyo mu da sukayi suka kuma yi yinkurin sake kwace shi, mun riga mun san idan har muka barsu suka tafi dashi kashe shi zasuyi, shine muka roke su, su bar mana shi da alkawarin ba zamu bari ya san su waye iyayen sa ba, zamuyi nisa da garin kano ba zamu sake waiwayowa ba. Kaji abinda ya faru a lokacin muka bar gari muka tafi chan Kaduna muka soma sabuwar rayuwa, muka raini jariri har ya kai munzalin saurayi daga nan muka tattaro muka dawo Kano mahaifar mu, daga nan ne kuma muka sanar dashi komai game da rayuwar sa, sannan muka bashi damar neman iyayen sa da kansa saboda a lokacin ya kai matakin da babu wanda zai iya takashi. Yanzu haka a cikin Kanon yake zaune da matar sa tunda da ma daga bayan dawowar mu nan gidan dan uwana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login