Showing 24001 words to 27000 words out of 121037 words
komai.
"Karki damu Hajiya, ba komai duk shirme ne, ba zamu barshi ya dauko mana abin magana ba, yayi kad'an ya bata mana plan."
Kanta ta dafe da sauri, tasan taurin kan Adam da kafiyar sa, tasan kuma da gaske yake tunda ya furta, dan haka ya zama dole ta dau mataki kafin komai ya kwabe mata.
π₯π₯π₯π₯π₯π₯
*_SAK'ON ZAFAFA BIYAR GA AL'UMMAR K'ASAR NIJER_*π³πͺπ³πͺπ³πͺπ³πͺπ³πͺ
_ASSALAMU ALAIKUM MASOYA MAKARANTA LITATTAFAN ZAFAFA BIYAR JAMA'AR NIJER_
_DIMBIN GAISUWA DA FATAN ALKHAIRI A GAREKU_
_MUN FIDDA TALLA MUN BADA NUMBER DA ZAKU TUNTUBA,TO AMMA WANCAN NUMBER DA ZAKU TUNTUBA BA'A SAMUNTA,A HALIN YANZU GA SABUWAR NUMBER DA ZAKU TUNTUBA DON TURA KATI KU SAMU DAMAR SHIGA GROUP NA ZAFAFANKU BIYAR_
+227 90 16 59 91
*Yan jamhuriyyarmu nigeria kumaππ³π¬π³π¬,zaku ci gaba da pyment ne ta account dinmu na*
Maryam sani
0022419171
ACCESS bank
Ku tura shaidar biya ga
+234 903 318 1070
*Katin waya ko VTU zaku tura ta wannan number*
09166221261
Litattafan dai sune kamar haka
RUMBUN KAYA Hafsat rano
A RUBUCE TAKE Huguma
IDON NERA Mamuhghee
KI KULANI Hafsat xoxo
DAUD'AR GORA Billynabdul
*Muna godiya da zabin zafafa biyar*π€π€π€π₯π₯π₯π₯
*RQ*
Β Β Β Page 12
Hafsat Rano
***A kofar gidan ta tsaya ta zaro wayarta ta shiga wajen message ta rubutawa Hajiya Zeenat sako.
_"Na dawo, kuma ya samu sauki."_
Sai ta kashe wayar gaba daya dan bata so ta kirata kwata kwata idan suna tare da yan gidan su. Da sallamar ta, ta shiga gidan da daukin ganin su, ga mamakin ta sai ta tarar basu karaso ba.
"Wai basu karaso ba Adda?" Ta tambayi Addan tana zama a gefen ta
"Eh wallahi, bakuyi waya ba?"
"A ah bamuyi ba, bari na kira su
"Ok kira su muji."
Wayar ta kunna ta kira amma har ta gama ringing ba'a daga ba, dukkansu tabi da kira amma duk basa dagawa, hankalin ta ne ya soma tashi tunda dai babu yadda za'a yi dukkan su ace basu ga kiranta ba. Mikewa tsaye tayi cike da zulumin abinda ya faru ko yake faruwa. Ita kanta Addan jikinta yayi sanyi ganin sai cigaba da kiran Raihana take amma ba ta ma shiga daga baya. Baki daya hankalin su ya gama tashi kusan awa guda kenan da dawowar ta amma duk da haka basu karaso ba, ba kuma su kirata ba. Sam ta kasa zaune ta kasa tsaye haka ta dinga zagaye zuwa chan ta soma kuka dan gaba daya jikinta ya gama bata ba kalaou ba.
***A kofar gidan Lamido yayi parking cikin yanayin gajiya da tafiyar dukkansu suka fito Dadah da jikin ta ya gama laushi sosai saboda tsabar gajiya ta zuro kafafun ta a hankali Hydar ya cicibo intisar da take baccin wahala. Shi da Dadah da intisar din ne a baya sai Lamido da Sadeeq a gaba bayan sun chanja tukin saboda wahala. Awar su kusan biyu a cikin hold up ashe masu manyan motoci ne suke zanga-zanga akan an kashe musu dan uwa, shine suka rufe hanyar gaba daya suka hana kowa bi sai zagaye ta wasu kauyukan suka dinga yi abinda ya saka su dadewar kenan. Sun ga kiran Raihanan sun kuma san tana cike da zulumi amma sanda duk suka ga kiran nata babu service a in da suke balle su iya kiranta.
Tana tsakar gidan tsaye taji alamun tsaiwar mota, da mugun gudu ta kwasa tayo waje, bata san sanda ta rungume Lamido ba kasancewar shine a hanya cikin kuka kuka dariya dariya. Tausayi ta basu a lokaci daya duk da sun san zata aikata dama, ta bi su duk ta rungume taki daina kukan da k'yar ta kyale su ta kama hannun Dadah suka soma shiga cikin gidan.
"Raihata kukan na menene kuma?"
Dadah tace ganin still hawayen take, ita kadai tasan yanayin da zuciyar ta ta shiga dan saura kiris ta buga saboda tsabar tsoro. Kin musu magana tayi har aka shiga suka zauna a falon Adda Maimunan da ta taso ta riko mahaifiyar ta.
"Sannun ku da hanya Dadah." Tace ta taimaka mata ta zauna Raihanan ta zauna itama a kujerar ta nanuke mata
"Sannun ku Maimunatu,kun ganmu sai yanzu ko?"
"Eh wallahi, gaba daya hankalin mu ya gama tashi."
"Ku bari kawai, hanya ce tayi mana matsala wallahi, amma alhamdulillah tunda an iso lafiya."
"Alhamdulillah kam."
"Ina wuni Addah?"
Yan mazan suka hada baki wajen gaishe ta.
"Lafiya lou ya hanya?"
"Alhamdulillah."
"Menene wai?"
Hydar yace yana kallon fuskar Raihana da tayi kicin-kicin ita a dole fushi take dasu.
"Tunda dai gamu mun iso ba shikenan ba?"
Lamido yace yana dariya
"Ku kyale min kanwata, kusan ta da saka damuwa a ranta, nasan ta tsorata ne, toh gamu mun zo shikenan ko?"
Daga mishi kai tayi sai hawaye shar-shar
"Naji tsoro sosai."
Tace da muryar kuka
"Babu abinda zai faru damu kinji? Sai Abby ya fito mun yi rayuwar mu, mun aura miki best husband da zai kular mana dake"
"Kai Hammaaa." Tace tana kunshe fuskar ta a jikin Dadah.
"Kaga jaira taji maganar aure har ta murmushi."
Sai aka kwashe da dariya gaba daya.
Abinci da ruwa da lemuka aka kawo musu sannan aka kaiwa Dadah nata daki Raihana da Adda Maimuna suka bita ciki aka bar su Lamido da Muhammad din Adda Maimuna a falon suka fara sallah sannan suka ci abincin.
***Tsaki yaja a karo na ba adadi, sau biyu kenan yana kiran Kamal a waya amma yayi biris dashi. Tashi yayi bayan ya ture system din dake gaban sa ya nufi office din Kamal din da kansa.
Yana zaune yana aiki kansa ya dau zafi sosai dan ya manta ma shaf da kiran da Aryan din yayi masa sai gashi ya shigo. Fuskar sa ya kalla ya tuno da abinda yace masa, ya tuntsure da dariya yana mikewa tsaye
"Yanzu tsakani da Allah fa jiran ka fa nake."
"Bata zo ba fa Aryan, beside kai da kanka kace baka son nata, a gaban ta, kuma yau Friday bata zuwa aiki kasan."
"Call her toh mana.."
"Allah ni ba zan iya kiranta ba, ka kirata da kanka amma ai da kunya nace tazo ta dafa maka tea."
"Ba zaka kirata ba? Ni bani da number ta."
"Waye ya kirata ranar nan? Beside ma ga number ta wajena bari na baka."
"You have problem."
"Ai gaskiya ne,da kunya ai."
"Karka kira ta din."
Ya juya ya barshi yana yi masa dariya.
Dariya sosai Kamal ya dinga yi bayan fitar sa, yayi saurin karasa abinda yake ya bishi office din. Ya same shi yana ta jan tsaki fuskar sa a hade shi a lallai Kamal din ya bata masa rai.
"Bari nasa Zainab ta dafa maka, amma dai kana da bukatar ka shiga daga ciki wallahi, dan rashin yardar ka dole abubuwa da yawa ba kowa zaka yarda yayi maka ba."
"Sai ka sani dole nayi ai, dama ina ta so nayi maka magana, shine kaje kuka hada kai da Ya Nabila ko?"
"A ah hira ce tsakanin ya da kanin ta."
"Munafurci dai,kasan yanzu duk zata bi tasa abun a ranta"
"Ai gaskiya ne."
Chanja zancen yayi zuwa wani daban
"Yarinyar nan ma dole ta zabi ko zuwa duk satin ko naki signing wannan watan."
"Wacce yarinya?"
"Oho."
"Wai Raihana? A ah idan baka mata signing ba ma ni sai nayi mata, tunda dai batayi laifin komai ba, laifin ta daya da bata zo ta dafawa katon gwauro shayi ba."
Wani kallo Aryan yayi masa, be sake magana ba ya ja system dinsa ya shiga motsa mouse din dan ya lura Kamal din so yake ya kure shi, shi be ma san yadda akayi har ya biye masa haka ba
π₯π₯π₯π₯π₯π₯
*_SAK'ON ZAFAFA BIYAR GA AL'UMMAR K'ASAR NIJER_*π³πͺπ³πͺπ³πͺπ³πͺπ³πͺ
_ASSALAMU ALAIKUM MASOYA MAKARANTA LITATTAFAN ZAFAFA BIYAR JAMA'AR NIJER_
_DIMBIN GAISUWA DA FATAN ALKHAIRI A GAREKU_
_MUN FIDDA TALLA MUN BADA NUMBER DA ZAKU TUNTUBA,TO AMMA WANCAN NUMBER DA ZAKU TUNTUBA BA'A SAMUNTA,A HALIN YANZU GA SABUWAR NUMBER DA ZAKU TUNTUBA DON TURA KATI KU SAMU DAMAR SHIGA GROUP NA ZAFAFANKU BIYAR_
+227 90 16 59 91
*Yan jamhuriyyarmu nigeria kumaππ³π¬π³π¬,zaku ci gaba da pyment ne ta account dinmu na*
Maryam sani
0022419171
ACCESS bank
Ku tura shaidar biya ga
+234 903 318 1070
*Katin waya ko VTU zaku tura ta wannan number*
09166221261
Litattafan dai sune kamar haka
RUMBUN KAYA Hafsat rano
A RUBUCE TAKE Huguma
IDON NERA Mamuhghee
KI KULANI Hafsat xoxo
DAUD'AR GORA Billynabdul
*Muna godiya da zabin zafafa biyar*π€π€π€π₯π₯π₯π₯
*RQ*
Β Β Β Page 13
Hafsat Rano
Β Β Da weekend suka shirya gaba dayan su a karo na farko suka nufi prison din. Hajiya Zeenat na kwance akan tafkeken gadon ta kira ya shigo wayarta, sai data fara kallon number kafin ta daga da dan sauri dan bata wasa da duk wani information akan sa
"Hajiya barka da safiya."
"Barka dai Malam Salihu, ya aiki?"
"Alhamdulillah, kina da labarin zuwan iyalan Barrister kuwa?"
Wani irin wantsalawa tayi daga kwanciyar da tayi cikin yanayin tashin hankali tace
"Iyalai kamar ya? Ban gane ba."
"Toh dai gasu nan baki dayan su, mahaifiyar sa, da Yayan dukkan su."
"Kan balai! Yaushe har suka shigo garin amma bani da labari?'
"Toh gaskiya sai dai ki bincika, nima mamakin ganin su yasa ni kiran ki, bayan kuma naga baki sanar dani zuwan nasu ba."
"Ka kyauta, ka sake ajiye min account details dinka ta whatspp, ko da yake, bana harkalla da account, zan aiko driver da cash sai kasha ruwa."
"Godiya nake Hajjaju, bari na koma na bibiyar miki yadda ake ciki."
"Toh sai na jika Salihu."
Mikewa tayi tsaye ta hau safa da marwa a tsakanin dakin nata, ko da wasa bata ji zuwan nasu ba kamar yadda take bibiye da duk wani motsin su. Wayar ta, ta dauka da sauri ta yi dialing number sa. Ta cigaba da zagayen har zuwa sanda ya daga daf da katse
"Ya akayi baka fada min zuwan su ba?"
"Kano suka zo?'
"Auw baka sani ba?"
"Ban sani ba wallahi, Kaduna mukayi dasu zasu biki bansan me ya kawo su nan ba kuma, ko Raihana suka zo dubawa?"
"Itace ma." Tace tana zame dankwalin kanta, idan ta bud'e baki ta fada musu komai fa? Tabbas tana fadan sunan ta da bayanin zasu gane, shikenan komai zai koma baya kenan.
"Yanzu menene abun yi?" Yace jin tayi shiru
"Ka kira Hydar kaji yaushe ne dawowar su, a cikin satin nan nake da bukatar key din nan, idan yayi dadewar duniya sati biyu,kai ba ma zan iya jira ba."
"Shikenan, zan kira."
Kashe wayar tayi da sauri ta sake kiran Salihu, yana daga tsaye a dakin da suke zaune suna jiran fitowar Abbyn, dukkan su cike suke da zumudi musamman da suka samu wani dadadan labari da ya saka su kusan sumewa dan dadi, signal yayi wa Lamido kafin ya matsa daga wajen ya daga wayar
"Me yake faruwa Salihu?"
"Babu abinda yake faruwa Hajjaju, kamar ma ba zasu samu ganin sa ba gaskiya"
Ajiyar zuciya ta sauke da karfi hankalin ta,na dan kwanciya
"Shikenan, ka kirani duk abinda ake ciki."
"An gama hajjaju."
Komawa yayi ciki, ya sake kallon Lamido da shima shi yake kallo, yayi masa alama da hannu ya jingina masa kai kawai.
Β A hankali ya zuro kafafun sa a karo na farko bayan shekaru masu yawan gaske, kansa ya d'aga kad'an ya kalli sararin samaniya sannan ya sauke a hankali yana cigaba da shak'ar iskar yanci, bayan tsawon lokacin da ya dauka a rufe.
_"babu abinda yafi yanci dadi."_ ya furta a kan labban sa
Β Β Idanun su na kan kofar kyam ko kiftawa basayi, cikin yanayin farin ciki suke dukkannin su, hannun Raihana na sarke da na Haydar ta kasa nutsuwa ko kadan. Ita ce ta fara gano shi sanda ya fito, ta kwace a guje suka rufa mata baya, idonsa a kanta har ta karaso ta rungume shi kafin ta fashe da wani irin kukan na farin ciki.
"Abby...". Suka kira sunan sa a kusan tare cikin yanayin nuna tsantsar farin ciki, jinjina kansa kawai yake ya kasa furta kalma daya saboda tsabar farin cikin da yake ciki, da k'yar Raihana ta cikashi tana share hawayen dake kwance a fuskarta tana had'awa da dariya.
"Alhamdulillah Ya Allah."
Ya furta bayan ya rungume yan mazan daya bayan daya banda Lamido dake tsaye hannun sa zube a cikin aljihun sa, fuskar sa a sake sai dai yanayin sa be sakashi furta kowacce kalma ba sai jinjina kansa da yake kawai. Kokarin dukawa yake ya gaida Dadah tayi saurin hanashi tana rufe fuskar ta da mayafin ta. Girma sosai ya kamashi duk kuwa da askin da yayi fuskar sa tayi fayau yayi matukar ramewa. Dukkan gandurobobin suka zagaye su cike da farin ciki, shi kansa Abby be san wanne irin yanayi yake ciki ba, tun bayan da ya samu labarin fitar sa a jiya da daddare, wanda ya rasa dalili tunda babu wanda ya sanar dashi dalilin sauyin lokacin da aka samu, shi dai kawai an ce ya shirya yau zai fita daga gidan, hakan kawai ya sani shikenan babu kuma wani bayani da ya biyo baya amma tabbas yasan akwai dalili me girman gaske, da har zai saka a chanja komai cikin dan kankanin lokaci.
Β Β Dukkan abinda ya kamata ayi an gama, haka suka rako shi har mota suna daga masa hannu, a hankali ya saka hannu ya share hawayen da ya biyo gefen kuncin sa a boye dan kar ma su gani, ya daga musu hannun suka fita daga harabar wajen. Idanun sa akan titi tunda suka fara tafiya yana mamakin sauye-sauyen da ya gani, yana tuna ganin sa na karshe sanda suka tabbatar sun tura shi prison bayan bashi da shakikai aminai sama dasu.idanun sa ya runtse ranar ta shiga dawo masa akan sa.
****KURMAWA PRISON,KANO.
Β Β Karar motar prison din ce ta sasu dagowa suka bi ta da kallo har zuwa sanda ta isa gate din, gandurobobin dake kula da kofar suka tashi da sauri daya daga cikin ya bud'e gate din motar ta saka kanta a ciki, a hankali gate din ya rufe ruf bayan shigar motar. Kallon ta yayi itama a lokacin ta kalle shi sukayi wa juna murmushi
"Munyi nasara!"
Tace cikin yanayin da yake nuna tsantsar farin cikin ta
Β Β
"Yes we won!"
Yace yana mika mata hannu. Kallon hannu tayi kad'an sai kuma ta zuge zip din jakarta ta ciro envelop me fadi ta dora masa a saman hannun sa
"Na cika alkawari."
Gid'a kansa yayi cikin yanayin jin dadi yace
"Of course."
Sai ya tura envelope din a aljihu ya murd'a handle din motar yana kokarin fita
"Sai yaushe Barrister?" Tace tana dan karyar da kanta
"Sai sanda kika neme ni Hajjaju, for now dai aci duniya da tsinke."
Dariya ta kwashe da ita sosai yana tayata kafin ta ware yan yatsun hannun ta, ta kada su tana girgiza kanta
"Sai ka ji ni."
"Ok..." Yace ya karasa fita daga motar.Β Motar sa ya nufa da take dayan side din. Ta zuba masa ido tana kallon sa ya shiga motarΒ ya kunna ta, yayi horn sannan ya bar wajen. Ajiyar zuciya ta sauke sannanΒ ta daga waya ta kira driver ta da yake tsaye daga chan gefe tace
"Mu tafi."
"Ok Ma."Β Ya karaso da sauri ya kunna motar suka bar wajen suma.
Β Β
Kallon daidaikun motocin dake kai kawo a tsakanin titunan garin take har suka kusa isa gida, wayar tace tayi yar kara ta ciro ta, murmushi ya subce mata, a yangace ta daga tana kara ta a kunne kafin ta dan yi baya yadda zata fi jin dadin amsa wayar
"Kin kusa karasowa?" Aka fada daga cikin wayar bayan ta yi masa bayanin nasarar su.
"Yes muna daf da shigowa, ya kayi da mutanen?"
"Nasa aje a tashe su yanzu, sai dai kin karaso zaki ji komai."
"Ok..." Tace tana zare wayar. Ba yau ne karo na farko da ta fara samun nasara a duk abinda tasa a gaba ba, haka nan take jin ta sakayau tamkar ta cire wani gagarumin abu daga birnin zuciyar ta, tayi fatali dashi, a yanzu ne zata mike kafarta sosai taci duniyar ta da tsinke! Babu wanda ya taba shiga gonar ta face ta saka kafa tayi fatali dashi daga cikin rayuwar ta, koma duniyar baki daya. Shi yafi komai sauki a wajenta. Barrister NASIR MATAWALLE! Kayi kad'an kace zaka tozartani, ta ja tsaki tayi cilli da wayar akan kujerar.
"Abby na!"
Muryar Raihana ta dawo dashi daga tunanin bakar ranar, ranar da ya fara kwanan bakin ciki, ranar da yayi kwanan tsaye saboda kwarkwasar da ta cika dakin da aka kira shi da nasa. Ido ya zuba mata dan bata da maraba da mahaifiyar ta zamanin kuruciyar ta, hatta dimple din da take dashi irin nata ne sak. Murmushi yayi mata yana riko hannun ta yana tunawa da rikon da yayi mata na karshe a wanchan lokacin
"Raihana."
Jinjina kai tayi dan dama tunanin da ya tafi ya sakata yi masa magana dan ta hangi damuwa shinfide a fuskar sa. Daidai lokacin suka isa asibitin Al-ihsan dake titin karkasara,tun suna hanya Babbo Sadeeq ya kira Dr Karaye a waya yace gasu nan, kafin ma su isa shi ya rigasu suna zuwa aka karbi Abby aka bashi gado domin a bashi kulawa ta musamman.
Da Magriba Hydar ya maida Dadah da Raihana gidan Addah Maimuna ba dan sun so ba, Raihana har da kukan ta akan ba zata tafi ba. Kayan jikinta ta rage ta shiga wanka dan zafi take ji sosai, tana fitowa Hajiya Zeenat na kiran ta, taga kiran dazu ma amma bata daga ba dan tana tare da yan gidan su kuma tsaf zasu gano ta tunda sun san ita ba wai wasu kawaye ne da ita ba. Abinda ya faru da taje ne ya fado mata,sai kunya ta sake kamata, kamar ta bud'e kasa ta shige dan gani take shikenan a marar kamun kai zai dauke ta. Sake kira tayi dan yau baki daya ba'a nutsuwar ta take ba duk da Salihu yace mata ba'a barsu ma sun gansh ba amma dai tana son duk yadda za'a yi Monday Raihana ta dauko mata key din nan daga nan kuma duk ma abinda yaran suke shiryawa da sauki tunda ta samu abinda take nema a hannun ta.
"Wai ba kiran ki ake bane Raihana?"
"Dadah wata bakuwar number ce, idan ma na daga shiru akeyi."
"Ko dai saurayi kikayi da bakya so mu sani ba. Amma ina ji dazu ma ana ta kiran ki."
"A ah ai duk number ce fa."
"Toh ai shikenan, idan ma hakan ne ai zamu sani ko ba dade ko ba jima."
Wayar ta dauka tayi waje tana wa Dadan dariya, sai da ta zagaya bayan dakunan sannan ta bi kiran aikuwa ko ringing bata ji ba sai ji tayi an daga.
"Ina kika shiga daughter ina ta kiran ki."
"Ina tare da yan gidan mu ne Anty, ba zasu yarda ba idan suka ji muna waya