Showing 117001 words to 120000 words out of 121037 words

Chapter 40 - RUMBUN QAYA COMPLETE hausa Novel

03 Sep 2024

17344

da ita baki daya.

Da farko Adam na biye da motar da Hajiya Zeenat din take ciki har aka zo wata danja ta saida su. Waya aka kirashi ya d'aga daga nan Aryan ya bace masa kwata-kwata. Be kawo komai ba, ya chanja hanya dan da gidan zai je amma kuma kiran wayar da ya samu ya sakashi kyale zuwa gidan ya koma baya.
Sai yamma likis sannan ya gama dasu ya dauko hanyar gidan, hold up ne ya rike shi sosai saboda yan siyasar da suka cika garin. Da k'yar ya samu ya yanke ya isa gidan bayan magriba sosai. Falon ya shiga kai tsaye da tunanin ganin ta sai dai yadda falon yake dim an kashe duk wani bulb me haske alamun babu kowa a gidan. Kunna hasken yayi ya nufi bedroom din Hajiya Zeenat din ya murd'a amma sai ya jishi a rufe. Mamaki ne ya kama shi, ya nufi hanyar kitchen yana kwalawa cook din gidan kira wadda yasan tana dadewa a part din nasu kafin ta wuce bq. Shiru bata amsa ba har ya karasa kitchen din ya tarar babu kowa alamun ta dade da kammala aikin ta, ta wuce bq. A kaida idan ace Hajiya Zeenat na nan ya kamata yaga mutane sun kusan cika gidan musamman kawayen ta amma ko a gate be ga alamar ta dawo gidan ba. Da sauri yayi hanyar waje ya fito compound din ya shiga kwalawa gate man din kira da karfi. Yana toilet yana uzurin sa ya jiyo kiran Adam din ya fito a guje dan ko karasa saka wando be yi ba, sai a wajen.

"Sannu da dawowa ranka ya dade." Yace gaba daya ya manta ma shine ya budewa Adam din ya shigo.

"Hajiya bata dawo bane ko ta fita?"

"Hajiya, wacce Hajiyar?"

"Ban sani ba." Ya daka masa tsawa

"Gaskiyar Allah Hajiya bata dawo gidan nan ba."

"Ina driver Daddy?"

"Yaje ganin gida,tun tafiyar Alhaji ya tafi gida shima yaga iyalin sa."

"Waye ya hau Babbar motar Daddyn a dazu?"

"Motar sa? Anya? Gaskiya dama bata gidan nan tun kwanaki aka fita da ita."

"Damn it!" Ya dunkule hannun sa kamar zai nashi gateman din sai kuma ya fasa, ya juya da sauri ya koma cikin gidan ya dauki key din motar sa da ya ajiye a saman kujerar ya sake fitowa yace ya bud'e masa gate ya sake ficewa daga gidan a haukace yana kokarin kiraye kiraye waya.


   ***Abby na zaune a falon sa bayan fitar Sadeeq, Raihana ta kira shi. Tun da aka kaita basu yi magana ba sai yau da ta kira shin yana sane kuma be kirata ba ita kuma nauyin sa ya hana ta kiran shi. Murmushi yayi ya d'aga wayar tata yana jin soyayyar yar tasa tilo a cikin ransa. A kunyace ta gaishe shi ya amsa zuciyar sa fes sannan ya tambaye ta ko akwai wata matsaala. Girgiza kai tayi kamar tana gaban sa sannan tace babu, ya saka mata albarka sosai tayi masa godiya sukayi sallama. Dawowar su kenan daga wajen gyaran jiki tare da Khadija yau Ya Nabeela bata je ba tana da baki a gidan dangin Dr Farouk shiyasa ta hada su kawai da driver tace ya kaisu. Khadijan na falo ta shigo daki ta kara duba wayarta ko Aryan din ya kirata amma be kira ba, gashi ta gwada wayarsa a kashe tun rana. Komawa tayi falon ta zauna suka cigaba da hira da Khadija Amna na zaune a cinyar ta tana wasa da wayar tata har magriba tayi suka tashi don yin sallar magriba.

   Ya Nabeela ce ta shigo dakin tana zaune akan sallaya ta idar da sallah tana istigfari. Zama tayi a gefen gadon ita kuma ta gyara zaman ta tana duban ta.

"Wai kuwa kunyi magana yau da Aryan?" Tace cike da kulawa dan rashin zuwan nasa ya fara damunta sosai

"Wayar sa a kashe take."

"Toh, yau ma? Dan sake gwadawa ko lafiya. Na kirashi dazu ma switch off. Bakin da nayi ne suka sa na sha'afa wallahi."

Daukar wayar tayi ta yi dialing switch off har lokacin, karbar wayar Ya Nabeela tayi ta kira Kamal sai dai har ta gama ringing be dauka ba. Tashi tayi taje ta dauko wayar ta, ta kira chan main house Malam Yahya yace mata ya fita tun sassafe. Duk da tasan Aryan ba wai karamin yaro bane da za'a yi ta neman sa amma kuma sam hankalin ta ya kasa kwanciya, tana jin kamar ba kalou ba yawan shirun nasa. Ganin yadda Ya Nabeelan ta damu sosai yasa Raihana sanar da ita yazo jiya da daddare wanda ita a tunanin ta ko tun ranar nan be sake zuwa ba. Hankalin ta ne ya dan kwanta tayi mata sallama ta tafi. Shiru shiru tana saka ran zaizo amma har ukun dare babu labarin sa. Da k'yar bacci ya dauke ta cikin tunanin abinda ya hanashi zuwa da abinda ya saka shi kashe wayar. Gashi yana ta rokon ta da kar ta barshi duk runtsi duk wuya.

Kauye ne sosai wanda ya amsa sunan sa kauyen kayau a shekaru biyu baya da suka shige, babu wani jin dadi ko more rayuwa a wajen sai dai kawai ana rayuwa ne gaba gadi ba tare da sun san wani abu wai shi cigaba ba, ballantana su samu arzikin more wasu cikin alfanun gwamnatin. Aryan ne mutum na farko da ya fara shigowa cikin su sannan yayi musu abinda basu taba tunani ko tsammani ba. Duk da bashi da wata alaka ta kusa ko ta nesa dasu illa iyakar wata mai-aiki da suka taba yi bayan mutuwar mummy din wadda ta kula da Aryan din ta damu da damuwar sa sosai a karshe Hajiya Zeenat ta kore ta saboda yadda take saka ido sosai akan sa.
Duk da ya dade rabon sa da zuwa amma ya kan yi musu aike ta lokaci zuwa lokaci sai gashi a yau yazo da uzurin sa da yake ganin anan ne kawai zai samu abinda yake so. Na farko shine Hajiya Zeenat tayi confessing dukka laifukanta da bakin ta sannan ya samu in da Ammy take, daga nan ne zai yi duk abinda zai yi ganin ta karbi hukunci daidai da ita, tunda sun bi duk matakan da ya kamata su bi wajen ganin anyi adalci amma ya gagara.
Waigawa yayi baya sanda ya karaso kofar gidan da k'yar saboda lalacewar hanya da rashin bin ta da mota ba tayi. Baccin Hajiya Zeenat take har a lokacin irin baccin da ake cin karfin mutum ba tare da ya shirya ba. Parking yayi sosai sanda suka fito daga gidan jin tsayuyar mota. Sun riga sun san da zuwan sa dama chan dan haka ma yana zuwa suka fito. Hannu ya mika musu maimakon su bashi hannun sai suka dan duka cike da girmamawa suka gaishe shi ya amsa a sake yana jin nauyin yadda suke masan. Bashi da niyya ko cutar da Hajiya Zeenat amma kuma yana ganin wannan itace hanya mafi sauki wajen samun cikar burin sa, zai barta tayi rayuwa a cikin irin mutanen da take ganin har abadah su din kaskantattu ne a wajenta sannan ya tabbatar bata samu kofar sanin komai akai ba. Wayar ta dake tare da ita dama ya zare ta tun a hanya ya cire SIM card din ya jefa shi wani ruwa da suka gani a hanya. Mata biyu ne suka fito bayan sun gama gaisawa da Aryan din wanda ya kasance gidansu ne kadai a gaba daya rukunin main cikin garin sai kayi yar tafiya me nisa kafin ka shiga. Dalilin shi yasa suka dawo wannan gidan nasu saboda idanun mutane. Matan nan ne suka rirrike Hajiya Zeenat wadda har lokacin take shakar bacci suka shiga da ita cikin gidan zuwa wani daki da ya yi matukar lalacewa babu komai a cikin sa sai wata lalatacciyar tabarma da ta gama jin jiki sosai. Zaunar da ita sukayi amma sai ta bingire daga zaunen tana kiran sunan Aryan din cikin sumbatu. Sai da ya gama komai sannan ya sake dauko hanya a daren ya juyo Kanon.

***Da duku-duku ko gama tashi basuyi ba Adam ya fara bubbuga musu gate kamar zai karya shi, a firgice maigadin ya fito haka ma Dr Farouk. Shigowa yayi gidan bayan ya je gidan Aryan din ya tarar baya nan ya kira wayarsa a kashe kuma.

"Lafiya Adam?"

Dr Farouk yace yana kallon shi ganin yadda yake a hargitsa

"Ina dan iskan yaron nan."

"Wa? Ban gane ba?"

"Aryan, yana ina ya fito ya gaya min in da ya kai min uwata, bana son rashin mutunci."

"Yaushe Hajiyan ta fito?"

Ya Nabeela tace tana karasowa wajen sanye da Hijab akan doguwar rigar baccin ta

"Duk abinda yaron nan yake kece kike daure masa gindi, idan banda rashin mutunci bayan rufe ta da yasa akayi a prison har dadewa haka jiya court ta bada belin ta amma bata koma gida ba, wayarta a kashe haka ma tasa a kashe, ban kuma ganshi a zaman ba sam, ina ya kaita?"

"Yanzu belin Hajiyar aka bayar Adam? Bayan laifin da ake tuhumar ta dashi?"

"Malam ba ruwanka da wannan maganar, kaja girman ka."

"Lallai Adam, toh Aryan baya nan kuma na tabbatar babu in da Aryan zai kai ta sai dai idan wani wajen taje."

"Zai dawo ne, koma ina yaje ina nan ina jiran sa wallahi, yayi kad'an."

Ya juya fuu ya fice. Cikin jimamin abinda yake faruwa suka koma ciki. Hankalin Ya Nabeela a tashe ta kira Kamal tana komawa cikin ta sanar dashi abinda yake faruwa. Yayi matukar mamaki da kaduwa jin court ta bata belin Hajiya Zeenat din wanda yake kyautata zaton duk cikin shirun su ne yasa akayi masa transfer a daidai wannan lokacin. Dakin Raihanan ta shiga ta samu ta tashi suka gaisa ta tambaye ta ko Aryan din ya kira.

Dare sosai ya shigo ya wuce office dinsa kai tsaye ya shiga ya kwanta saboda yadda kansa yake masa wani irin sarawa. Be tashi farkawa ba sai wajen shida da rabi ya tashi da salati a bakin sa yayi saurin shiga toilet yayo alwala yazo yayi sallah ya roki gafarar Allah delay din da ya samu wajen tashi sannan ya koma saman gadon ya zauna yana tunanin abinda ya kamata yayi next. Kusan minti arbain ya dauka yana chaja brain dinsa kafin ya tsaya a matsaya daya ya tashi ya fito ya rufe ya nufi gidan sa yana cigaba da jin kan nasa na kara daure masa amma ya daure. Wanka ya farayi a tsanake ya shirya ya dawo falon ya ajiye tab dinsa da zai fita da ita da wayoyin sa da suka a kashe ya wuce kitchen ya samarwa kansa tea da short bread ya dawo falon ya zauna yana kurba a hankalin zafin na ratsa mokoshin sa zuwa lungs dinsa. Sai da ya gama sannan ya dauki wayar da yasan zaa neme shi ya kunna ta. Kamar jira Kamal yake kiran sa ya shigo. Cikin calmness dinsa ya d'aga wayar yana sakata a handfree dan baya jin zai iya riketa a kunne sa sannan airpod dinsa na mota bare yayi connecting.

"Aryan? Kana ina?"

"Oga sir, kai da kake officer, kawai tracing dina zakayi sai dai naga ka turo mota an yi min daukar kaza."

"Joke apart, kana ina? Me ya faru da baka sanar da ni ba?"

"Nothing much, kawai abinda kaji labari shi ya faru."

"Are you serious? Amma shine ba zaka kira ka sanar dani ba?"

"Naga babu amfanin hakan ne kawai, beside maganar ma bata min rai take."

"Naji, yanzu ina Hajiya Zeenat?"

"I don't know, ban sani b."

"Adam yaje ya samu Ya Nabeela yana wasu maganganu, hankalin ta ya tashi sosai, ka sanar dani idan akwai wani abu."

"Babu komai, zan je yanzu gidan. Please ka kirata kace ta bani matata dan Allah."

"Muna maganar serious kana wata magana daban, please Aryan ka sanar dashi idan akwai abinda ya kamata na sani din."

"Babu fa, karka damu shirmen sa kawai ne."

"You are not telling the truth, zan gano da kai na."

Yace ya kashe wayar. Tabe baki Aryan din yayi ya mike yana kakkabe jikinsa kamar wanda abu ya hau masa. Ya kwashi sauran gadgets din nasa yayi waje.

**RQ**

     Page 52


****Tun da Adam ya tafi Ya Nabeela take tsaye tana kaiwa da komowa, tana jiran jin yadda Kamal sukayi da Aryan akan maganar domin tasan halin Aryan idan har suka yi kokarin danne shari'ar nan toh fa zai dauki doka a hannun sa ne wanda ba zata taba so ya shiga matsalaa ba. Kiran Kamal ne ya shigo tayi wajen wayar da sauri ta daga

"Ya akayi Kamal? Ka same shi?"

"Eh na same shi, munyi magana amma kinsan taurin kan Aryan, be bani damar ma da zamuyi magana sosai ba, dan haka yanzu ma ina hanyar office zan kiraki da na samu kan labarin in sha Allah, karki damu babu abinda zai faru shima yace yana hanyar zuwa gidan."

"Nan zai zo? Gwara yazo ai ni zan masa maganar, ni ko visa za'a yiwa Aryan ne ya dauki matar sa su tafi? Wallahi bana son tashin hankali kwata-kwata."

"Babu abinda zai faru fa, karki damu gaskiya ce zatayi halin ta, nasan waye Aryan nasan kuma ba zai yi abinda yasan zai bata shi ba"

"Toh shikenan, bari ya karaso naji ko ni zai fada min abinda yake faruwa."

"Ok, yadda kukayi let me know."

"I will! kaima sai ka sanar dani."

"In sha Allah."

Ajiye wayar tayi Dr Farouk ya kalle ta sai ya mika mata hannun sa yace tazo ta zauna, zama tayi a gefen sa jikin ta duk a sanyaye kalou.

"Calm down Maman Aryan, kinsan fa halin yaron naki, da kin bashi matar sa ma da duk hakan bata faru ba, ko da rike shin nan honeymoon kawai kika tura shi shikenan fa."

"Ai wallahi ban san za'a yi haka ba, da ban fara ba ma wallahi, wai ni dai muyi biki a kai lefe da komai nake so ayi, ashe yace bari ya samu wani aikin yayi."

"Toh wai kin yarda da maganar Adam ne? Kila ma Hajiyan wani wajen ta tafi ta huta "

"Hmm, nasan waye Aryan, tsaf zai aikata wani abu wallahi. Dama Daddy ke hanashi dani wasu abubuwan, sai Kamal kuma. Toh babu ni babu daddy Kamal din ma ya tafi, kana ganin zai bari abinda ya dade yana tanadi ya salwanta a kankanin lokaci?"

"Gashi nan naji an shigo da mota."

Mikewa tayi da sauri tayi compound din dan ba zata bari ma ya shigo ciki ba saboda yadda ta matsu. Parking yayi ya hangi fitowar ta tana kallon side din da yake. Murmushi yayi kad'an yasan halin rikicewar ta, ya sake tattaro calmness dinsa ya balle murfin motar ya fito ya nufe ta hannun sa zube a cikin aljihun wandon sa. Fuskar sa ta ke kallo tana son gano wani abun amma sam ya hana mata duk wani clue da zata iya gani a tattare dashi. He looks so calm da ya hana mata gano ainahin abinda yake sussukar zuciyar shi. Tafiyar sa ta maida hankali har ya karaso ya tsaya a gabanta cikin sigar zolaya yace

"Ya Nabeela yau tara ta kika fito yi haka?"

"Me yake faruwa? Fada min maza maza."

"Aina fa?"

"Gama da case din Hajiya, abinda Adam yazo yana magana akai gaskiya ne?"

"Ohh, Kamal ya fada min dazu, kawai shirmen sa ne dan Allah karki biye masa, matar da ta iya tserewa hukunci daga hukuma ni ne zan iya dauke ta? Na kaita ina ma toh?"

"Are you telling me the truth?" Ta kalle kwayar idon sa.

"Ku shigo ciki Maman Aryan, wannan tsarewa tun a waje."

Dr Farouk yace yana tsaye jikin kofar shiga ciki. Juyawa tayi ta shiga ciki Aryan din ya bi bayanta. Ko zama bata yi ba ta sake watso masa tambayar, ya gid'a mata kai yace

"Bansan komai akai ba."

Wata katotuwar ajiyar zuciya ta sauke sannan ta zauna.

"Barka da gida Dr?"

"Barka dai kanina, ya angonci?"

Murmushi Aryan yayi tunowar da yayi ya ganshi ranar ya kuma san da biyu ya tambaye shi angoncin dan a karshen muryar sa ta nuna sigar tsokana.

"Ango kasha kamshi, gashi dai wannan yayar taka ta hanaka matar ka, bansan me take nufi damu ba, idan kuma sai mun kai kara wajen Daddy ne toh."

"Ko zaku kai sai na gama shirya kanwata, shima Daddyn ba zai ce komai ba."

"A ah, zai fada fa, ai ba haka ake ba, ke haka aka miki da aka aura miki ni?"

"Aka aura maka ni dai." Tace tana dariya

"A ah dai, kin ga handsome guy kika nace kika ce idan bani ba sai rijiya."

"Ahaap, ai kullum aka tashi maganar haka kake cewa, bayan kowa yasan ba haka bane ba."

"Haka ne ai ko Aryan?"

"Haka ne."

Yace yana murmushin jin dadin yanayin rayuwar su. Dr simple mutum ne me raha da iya tafi da iyali ba tare da cin mutunci ba. Zaman su lafiya lou babu wata matsala. Hakan yana bashi sha'awa wani lokacin shi kadai sai yayi ta hasashen dama hakan ce ta kasance tsakanin su daddy.

"Aryan?" Ya Nabeela ta kira sunan sa jin ana magana be ce komai ba. Ya tafi duniyar tunanin har be ji tambayar da Dr Farouk din ya sake jeho masa ba.

"Dr ne yake maka magana,."

"Sorry sir, banji bane ba wallahi, na tafi wani tunani."

"Cewa nayi yanzu shikenan haka zaka zuba ido a hanaka matar ka, ko dan kewayowa ai yakamata ka dinga yi."

Shiru yayi yana dariya kasa k'asa, be san yaa Nabeela ta riga tasan da zuwam da yayi ba, wanda ta zata shine kawai.

"Duk yadda akayi Dr ni bani da matsala."

"Auw haka kace?"

"Wai me ya faru ne? Ko dai Aryan kana dan lekowa ne?"

"Ba ya lekowa, kanina ba haka yake ba."

"Anya?"

"Toh yaushe yazo? Kin hana shi kince kar yazo."

"Toh shikenan."

"Shiga ku gaisa Aryan, karka biye ta yayar nan taka kaje ka sake kafa gwamnatin ka."

"Kai kake zuga shi ko?"

"Laifi nayi?"

"Emana, nace fa sai ne neme shi."

"Sai kisa a toshe kofar baya." Dr yace yana mikewa

"Na'am?"

"No bance wani Abu ba, muje ki tayani shiryawa na wuce office kar na makara."

"Ok, Aryan ga hanya ne, sai anjima." Tace tana mikewa tabi bayan Dr da yake dariya.

Dan jim yayi a zaune kafin ya mike ya nufi dakin da take. Kansa tsaye ba tare

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login