Showing 1 words to 3000 words out of 101092 words

Chapter 1 - Zanyi biyayya COMPLETE HAUSA NOVEL

FEENER   

03 Sep 2024

37716

Zanyi biyayya🌻🌻
*ZANYI BIYAYYA*
🌻🌻



*By FENERH*


*Alhmdulillah masoya na Asali am back nadawo muku da labarin da zai kayatar daku, bazan iya kwatan tamuku mai ya Kunsa ba sai kun biyoni zakuji da kanku, masoya na godiya mara adadi naga kauna a last littafina naga masoya masu kaunar cigaba na Allah ya Kara budi da kauna inyita sambado muku labarai kuna ruwan na data😅, kamar yadda na yi wancan wannan ma hakane masoya is not for free gsky haryanzu bansamu kudin zuwa hajji ba, ina rokon Allah ubangijin kowa da komai, yanda nafara wannan rubutun lafiya Allah ya bani ikon kammala shi lafiya, Hmmm Alhmdulillah masoya masu son karuwata gasky ba Abinda zance muku sai godiya da fatan Rabbi ya bar kauna, tunban furta littafin na kudi bane wasu har Sunfara biya wasu kuwa suna jira infara posting su biya, Allahu yasaka muku da Aljannah ya biya dukkan bukatunku na Alkhairi, one love Real fans*

*BISMILLAHIRRAHMANIRRAHEEM*

1⃣&2⃣

Wani tsoho ne a tsugune ya zubawa wasu Y'an mata guda biyu idanu, dayar zatayi kimanin shekara Ashirin da biyu, sai kuma karamar mai kimanin shekara sha bakwai, gefe daya kuma wani matashi ne wanda kana gani shine Babba a cikin su ga mahaifiyar su na sharar kwalla da gefen zanin ta,
"Hajara yanzu bazaki iya yiwa mahaifinki BIYAYYA ba a rayuwar nan duk da bamuda Arziki amma, yana iya bakin kokarin shi ganin ya kyautata wa rayuwar ku, ya muku duk Abinda uba nagari zaiyi wa ya'yan shi domin ganin rayuwar su ta inganta,


Cikeda rashin kunya da kuma nuna tsantsar rashin tsoro tace " yanzu don girman Allah a rasa wadda za a Aurawa naka sasshe sai ni, saboda uban shi yagan mu talakawa, sai kuma ya lallaba ka kawai ka bashi yarka, wallahi bazan Aure shiba, cikin taushin murya da kwantar da kai yace "haba Ummi yanzu ke bazaki iya taimako na ba ki fitarda ni kunya? Kinsani duk wani cigaban ku da nawa sanadin bawan Allah nan ne ya mun komai a duniya batareda mun hada Alaka ta jini ba, tundaga kan ilimin ku gashi yanzu yayan ku na bautar kasa ke kina 200 level kanwar ki na final year a secondary wallahi Ummi idan ban sharewa bawan Allah nan hawaye ba na zama butulu,

"Wallahi baba tunda Allah ya nufe mu da karatun zamuyi koda taimakon shi ko babu zamuyi, nidai bazan Aure shiba, ka bashi hakuri ya nema wani gidan,

Karamar ce dake kallon Y'ar uwar tata na kelaya rashin mutunci tace "kai yaya Hajara yanzu kina kallon su baba na miki kuka saboda ki rufa musu Asiri fir Amma shedan na miki hudubar tsiya ko,
Hannu ta daga zata masgeta, yayan su namiji dake a fusace yace "wallahi daina ganin baba yace kar in tabaki, Amma kina tabata Saina nakasa ki kema, ba kina kiran wani naka sasshe ba, HAJARA kibi A hankali duniya ce kina ya' mace Y'ar talaka Amma ego dinki yafi karfin ki a rayuwa,
"Wallahi kitabamin ya' kigani yayanku zanba umarni ya lallasa min ke, Malam kaga Y'ar son taka ko kaga diyar da kasha duk wata wahalar rayuwa saboda ita ko?
Tsohon da kana gani kasan rayuwar shi bai dauki komai da zafi ba yace "RAHAMA, ki tayani lallaba Y'ar uwar ki kinji kuje ciki Allah ya ma Rayuwar ku Albarka kinji,


Fuuuu HAJARA ta mike ta wuce d'an karamin dakin su dake tsakiyar gidan,
Kanwar ta ce ta kalli baban su" baba kayi hakuri zata Amince insha Allahu, zan tayaka rokonta, "To RAHAMA, Allah ya Albarkace ku kinji, Ameen ta Amsa ta wuce cikin dakin itama,
Kafin ya juya cikin natsuwa ya kalli D'anshi namiji da yayi shiru kana ganin shi kasan a zuciye yake,
"Gadanga kusar yaki, kayi hakuri kaji da halin Y'ar uwar ku, ka zama uba kazamo namiji ako da yaushe da zai tsaya akan Y'an Uwan shi, kaine Babba kaine gatansu,
Ko bana raye kaine zaka zamo jigo a rayuwar gidan nan, don haka tashi kaje Allah ya maka Albarka kaji,

Wasu irin hawayen tausayin mahaifin shi ne ya lullube shi, ganin yanda yake fama dasu tsawon rayuwar su ya tsaya musu akan komai da wahalar neman shi har zuwa yau, ji yake dama shi mace ne da yau ya rufawa Mahaifin su Asiri ya Auri zabin shi, mikewa kawai yayi yabar gidan,
Bai iya kara cewa komai ba, Amma Addu'a yake Allah ya sa baban ya fita sai ya lallasa ta a gidan ko ya rage takaici,


Mikewa inna ma tayi zata wuce, yace " zauna matar Aljannah uwargidana ta gari, komawa tayi ta zauna domin bata iya yimai gardama ko kadan,
Share sauran kwallar tayi "malam sanyin ka yayi yawa,
Dariya yayi kamar bakomai a ranshi yace " so kike inrika daukar zafi a cikin rayuwar da bamai dorewa bace larai, ki taya ya'yan ki da Addu'a ko mutuncin su kawai da suke tsarewa wani Abu ne bakya ganin tsananin mu zai iya janyo fadawar ta cikin hadari? Banason ta yi tunanin zanyi mata Auren dole, larai so nake ta yarda, yanda hankalina zai kwanta ko bayan Auren, Amma in mun tilasta ta
Anyi wane riba zamu samu yaron da baida lafiya tun tashin shi,

"Malam tuntuni nakejin kana maganar rashin lafiyar shi, wai Meke damun shi ne? Larai Addinin mu yayi hani ga tsananin bincike, kada musulmi ya tsawaita bincike, Allah yagani tun yaron na karami mahaifin shi yafada min yasamu nak'asu suka fitar dashi kasar waje, bankuma taba binciken komai akai ba, yasha fadamin har yanzu yaron bawai ya samu lafiya bane, kuma kanin shi ma yayi Aure tuntuni harda yara biyu shine dai ya rage saboda lalurar dake damun shi,

Rokona yayi a karon farko, yace min "malam bala ina neman Alfarmar ka bani Y'ar ka Babba domin nasan ta mallaki hankalin ta zata iya rayuwa da shi, bazan iya watsa mai kasa a idoba tsawon shekaru yana min hidima bai taba gajiyawa ba sai yanzu kawai rana daya ya roki Abu guda daya kacal a wurina in kasa yimai, bazan iya ba larai,
"Gaskiya Alhaji Shu'ibu mutum ne mai karamci da mutunci ya fi karfin komai kam a wurinka,
"Kingani don haka ki tayani lallaba Y'ar ki larai, yafada cikin barkwanci, " zan yi iya bakin kokari na insha Allahu malam,





A can cikin dakin kuwa RAHAMA ce ta dauki Quranin ta ta zauna gefen Y'ar uwar ta kan y'ar madai daiciyar katifar su dake kasan dakin, cikin kwantar da murya tace " yaya HAJARA don soyayyar ki da manzon tsira kiyi BIYAYYA, zaburowa tayi, a fusace, "wallahi kar inkuma jin muryar ki a dakin nan da sunan waike kina min zancen Auren da bazan taba yarda da shiba, zan naka d'a miki na jaki wallahi, "shegiya mai kirar takand'a ke kije ki Aure shi mana,
"Haba yaya ai bazai yuwu ace kina gida ni inyi Aure ba,
Shekara nawa ke tsakanin mu? Kusan Biyar fa, kuma kinsani kece kikafi cancantar Auren yanzu you are not getting younger everyday,
Jifarta tayi da wani robar cream ta kauce tareda kara rungumar Qur'an nin ta da kyau, tace " uwarki ce ta ke tsufa baniba shegiya Y'ar iya yi iyami masu kunu da ruwan sanyi,



" keni yanzu da ajina da ilimi na inkare a Auren naka sasshe Wallahi ni ko ubanshi dakeda kudin bazan Aureshi ba, d'an kudin su da bai wuce cikin cokali ba, wane Arziki gare su wa yasan da su a duk fadin garin nan ma,
Ke baby mijin HAJARA na nan zuwa zanba kowa mamaki mijina sai an share titin layin nan motar shi zata shigo,
Kallon kanki ya tabu kawai RAHAMA ke mata, ganin yayar tata ta zauce kar itama ta biye mata su zama daya yasa ta bude Qur anin ta fara tilawa cikin natsuwa,


WAYE MALAM BALA?

D'an Asalin garin jega ne dake jahar kebbi, neman kudi ya shigo dashi cikin babban birnin na sokoto, ta sanadiyar sana'ar Albasa, tun yana saurayi har ya samu jari yayi Aure da wahalar neman shi domin Almajirine tun yana karami iyayen shi suka kawo shi karatu wurin malamin shi, sai kuma Allah ya dauki ransu, malamin ya rikeshi tareda bashi kulawa har ya koyamai yanda zaiyi sana'a tun yana saro Albasa a cikin garin Alero yana siyar aa jega har ya fara zuwa sokoto da sana'ar ta mike,
Sanadiyar shigar shi sokoto ya bashi damar koyan karatun Boko kadan bamai zurfi ba domin ya lura komai na rayuwa saida ilimin nasara kake samun cigaba, koda kanada na Addini, a harkar kasuwanci kana bukatar na zamani,


Yayi Aure da uwar ya'yan shi larai da ta kasance Y'ar uban rikon shi wato malamin shi, a lokacin ya dawo da zama cikin garin na sokoto, ya kama gidan haya a cikin Unguwar mabera gidane na kasa madaidaici,
Suna tafiyarda rayuwar su cikin sauki kasancewar itama larai macece mai biyayya da hakuri, har lokacin da ta haifi d'an su na farko Aliyu, rayuwa ta fara musu zafi lokacin da ta kuma haihuwar Y'ar su ta biyu, domin rayuwar HAJARA daban ce tun tana karama komai ta gani sai ta damu baban ta tanaso, haka yake fafutuka ya nemo mata, domin Allah ya dora mai kaunar HAJARA wadda yasakawa sunan mahaifiyar shi,

Lokacin da ta isa shiga school kuwa tana shekara shida aka fara kokarin sakata makarantar gwamnati kamar yanda d'an uwanta ke zuwa, Amma fur taki tace wata makarantar kudi dake Unguwar su ita take so wanda a lokacin gaba daya sai ya Tara cinikin wata biyu na Albasar shi zai hada kudin makarantar, kuma ga hidimar gida gata sutura,

Dole ya fara fafutukar neman canjin sana'a domin cikawa Y'ar shi burinta,
Amma Abu ya gagara, ranar yana zaune a bakin titin da yake kasa Albasar shi , wata katuwar crv ta faka,
Ya tashi da Sauri ya nufi motar don ya saba da mutumin yana mai ciniki sosai don sai yasai kwando ma wata rana, mutumin kuma yana mai kyauta,


Fitowa mutumin yayi cikin shigar Alfarma irin ta wa inda suka jik'a da naira ya gyara madubin idanun shi ya mikawa malam bala hannu ba kyama, cikin ladabi ya rusuna sukayi musabaha, tareda tanbayar shi yau kwando za akawo ko rabi?
"Muje inuwarka muyi magana malam bala taimako nake nema Allah yasa ka Amince,
"Bismillah Alhaji, ya bashi bencin da yake zama, ya ko zauna, tareda fuskantar shi,

"Dama Alfarmar itace, ina son ka Ajiye wannan sana'ar kazo muyi aiki tare idan Badamuwa ka zamo driver na akoda yaushe, zan rika biyanka Albashi mai tsoka,shiru malam bala yayi, Alhaji shuaibu yace" nawa ne ribar Albasar ka a kullum?
Shiru yayi nadan lokaci yana nazari kafin yace a kullum ina iya samun ribar dubu biyu, idan na siyarda ta dubu goma inkuma kasuwar tayi kasa bai wuce ma insamu Dari Biyar a rana wata rana har Dari biyu,
Kaga in za ayi cefane ma wata rana sai mun shiga cikin uwar kudin ma,

"Toh karka damu, yanzu dai zan hadaka da wani yaro na ya koya maka mota nan da sati biyu in kana da kai zaka kware da Y'ar dar Allah, ya ciro katin address din shi ya bashi yace ya same shi a gidan shi dake tamaje quarters,
Yayi godiya sosai, domin yana matukar bukatar canjin sana'ar domin wata rana ma Albasar tafka hasara yake musamman lokacin zafi taita rubewa,
Suka rabu A ranar da tsantsar farin ciki ya koma gidan shi, ya fadawa inna larai,
Tace "malam zaka iya kuwa? "Insha Allahu larai ki tayani Addu'a kinga HAJARA nakeso insaka ta makarantar da takeso HAJARA ta nason hutu larai ina son ta huta,
Murmushi tayi tareda kallon Y'ar karamar yarta RAHAMA dake wasan ta a lokacin, bata wuce shekara daya ba, tace to "ya' tafa? "Dukan su in Allah ya Y'ar da zasuji dadi, to Allah ya bamu Alkhairi malam Allah ya taimaka ya kuma bada sa'a, ya Amsa da Ameen,


Alhmdulillah cikin watanni kadan rayuwar su ta canja domin
Domin Alhaji shuaibu mutum ne mai dattako da sanin darajar d'an Adam bayan Albashi harda hidimar kayan Abinci yi musu yakeyi,,
Don haka har Account malam bala ya bude yana adana kudin shi, domin siyan gidan kanshi, ana haka mai gidan da suke ciki yanemi su tashi zai siyar da gidan, Hankalin malam bala ya tashi domin ko rabin kudin gidan baida da ya siya don haka, dole yafara neman gidan haya domin tashi su bashi gidan ya siyar,
Ranar yaje wurin aikin shi yake neman izinin Alhaji shuaibu domin komawa gida da wuri ya nemi haya domin notice din da aka bashi ya kusa cika,
Anan Alhaji shuaibu ya nemi yafada mai waye mai gidan?

Ya fadamai yace ko yanada number shi ya Bashi, yace eh ya ciro Y'ar karamar Nokia dinshi ya duba ya bashi, atake ya kirashi yace mai Alhaji shuaibu ne mai dala yabo ai kuwa cikin tsananin girmamawa ya gaida shi, ya tanbaye shi ina yake yana son ganin shi, cikin rawar jiki yace Alhaji lafiya? "No akan gidan kane da kakeson ka siyar na mabera so ina son siya,
Cikin rawar jiki yace ansiyar maka Alhaji duk da wani ya taya Amma kai nasiyar maka, domin duk garin sokoto yasan waye Alhaji shuaibu Mai dala yabo, domin ya shahara ta fagen daukaka da taimakon Al Umma,


A ranar ya biya kudin gidan tareda mallakawa malam bala takardum yace mishi nashine halak malak, kuka malam bala yayi sosai saboda jin dadin yadda Allah ya kawo Alhaji shuaibu cikin rayuwar su, gaba daya rayuwar iyalin shi ta inganta sutura Abinci Abin batarwa, ga inna larai ma tana sana'oin ta a Unguwar ya gyare gidan tsab ya zama na zamani da ajiyar da yakeyi, gini ne mai tsakar gida dakuna guda hudu ne a tsakar gidan ciki daya daya, sai kitchen da bayan gida sai kuma bandaki na bayan gida dana wanka,
Tsakar gidan fes yake ya lailayu da suminti wanda suke wanke shi kaida kai kasan cewar inna larai mace mai tsafta,
Ba Abinda zasuce sai hamdala,

HAJARA na makarantar da takeso, har lokacin da RAHAMA ma ta isa itama aka jefata, rayuwar su sai hamdala, Aliyu har ya kammala secondary ya shiga d'an fodio university sokoto,
Shekaru na tafiya cikin fik'irar ubangiji da kuma Y'ar dar shi, har Hajara ta shiga itama d'an fodio wanda da taimakon Alhaji shuaibu duk karatun su ke tafiya ba tangarda don kowa yasan karatun jami'a ba Abu ne mai sauki ba,
While RAHAMA na Ajin karshe a secondary,

HAJARA yarinya ce mai mugun girman kai da rashin kunya ga sangarta sam bata taba Ajiye kanta kusa ba don komai tagani duniya sai tasa malam bala ya siyeshi, shikuwa Allah ya dora mai sonta fiyeda Y'an Uwan ta yace MAMAN shi ce ita gata da sunan mahaifiyar shi gata suna kama, domin fara ce tas irin farin fulanin Asali tanada jikinta mulmule kamar mai rayuwa cikin kankara,
Kyakkyawar gaske ce tanada kyau a fuskar ta da laushin fata saidai batada cikar halittar ya mace ta gefen sura kirjin tama saitaga dama takesa musu brah a gida inzata fitane dai take Amfani da mai soso domin karawa halittar ta Armashi, sumar kanta kuwa batada tsawo sosai saidai inka kalleta zakayi tunanin tanada shi saboda yanda suma ke kwance saman goshinta,
Tana rikita Maza gida da school domin HAJARA akwai daukar wanka da gayu,
Akwai wulakanci domin har yau taki tsaida kwakkwaran saurayi saboda dogon buri a rayuwar ta don ita bama ta hango kanta a gidan gwamna tafi hangota a president Villa, tana ikirarin ita fa matar manya ce, inna tayi tayi ta rage mugun hali taki,
While RAHAMA kuwa she is very cool girl bata cika magana ba gata chocolate color ce ita mai haske ba mai duhu ba irin color din nan mai wuyar samu, kallo daya idan kayi mata idan tana tareda HAJARA zakace she is ugly but wanda duk yasan ainihin sirrin kyau yasan tafi HAJARA sinadaran kyau, eye lashes dinta is natural gira lips everything about her is unique she is very cam girl and simple,
Fagen jiki kuwa she is slim but akwai body figure ainihin coca cola shape akwai k,asa dai dai jikinta haka kirjinta a full da har suna damunta kuma irin masu bajewar nan ne saman kirji, that's why she is always in hijab to hide her body,

A fagen aikin gidan ma itace kan gaba duk aikin gidan shara girki wanke wanke har wankin kayan su da na HAJARA gata bata taba damuwa da rashin yin HAJARA ba,
Tasan duk yanda zata tafiyarda rayuwar ta tundaga boko har islamiyya,
Bata wasa domin tayi sauka yanzuma takai izu talatin a hadda,

Gashi yanzu Ana fama da zancen Auren HAJARA da d'an gidan Alhaji shuaibu,


*******************
Kamar koda yaushe ta tashi da wuri ta gyara ko ina tareda taya innar su hada Abin kari, ita ta dauki na yayan su ta kaimai dakin shi dake farkon shigowar sai ta dauki nasu, inna tace " Y'ar uwar ki taki tashi ko? "Eh inna nayi ta tashin ta taki,
"Allah

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login