Showing 15001 words to 18000 words out of 69829 words
Kuna da iyayen kunada masu son ku"
Magana take sosai da karfi har ta karasa wajen benen barandar karshe daga ita sai Katanga ana hango gidan mutane na unguwar
"Faty dan Allah kiyi hakuri" Nawraah ta shiga nanatawa ganin fatyn na niyar jefaa kanta kasa.
"Kun tsane ni. Badai nice kuke tausayi ba? Nice marar gata acikin ku, ni ce marar asali ko? Banza a wofi, To albishirn ku zan bar muku duniyar sai ku kwadanta ku ci"
"Innalillahi Wa inna ilaihi rajiun faty meye haka? Ina mike da gata? Duk rashin gatar ne ya sa muke anan gidan gaba daya. Yadda baki da iyaye haka dukkanin mu muke.Na sha sanar da ku, musanman ke ba sau daya ba ba sau biyu ba, Ni tsabar rashin usuli ma daga titin da mota ta kade iyaye na nice nayi rai, mutanen wajen sune suka kawo ni nan gidan marayun kasancewar baa san yan ina bane mu , kawai mun taho a titi a motar haya aka samu hatsari kowa ya rasu na motar sai ni da ke da sauran kwana agaba... Toh dukkanin mu Faty, Jirgi daya ne ya debe mu..."Raudah ta fada da karfi tana runtse idanunta
"Faty na dan Allah kiyi hakuri kinji? Wallahi Muna kaunar ki sosai...kamar yadda Raudah ta fada, Dukkanin mu nan baki daya bamu da wani gata sai Allah mahaliccin mu. Zan iya cewa ma kinfini gata, don kuwa ni gidan marayun ne dakansu suka dakkoni suka kawo ni cikin ku, kasancewar mahaifiyata ance ina karama ta rasu batada ishasshen hankali acikin kasuwa muke rayuwa. To faty tsakani da Allah wannene yafi wani gata acikin mu? Na sha gaya miki. Munyi zantukan nan ba sau daya ba tun ma kafin zuwan su Nawraah. Kowa da yadda Allah ya Kadarta masa rayuwar sa. Idan mukayi hakuri sai mu cinma burin da muke fata agaba...
"Abu na biyu, Nawraah ce take cewa yadda bakya kula su abun na mata video tana so ku dinga mutinci kamar yadda kik1e da kowa"
Faty ta juya ta dube su tana girgiza Kai tache,
"Komai ta hada, makarantar yan gayu, kawaye irin ku, kawaye acikin makarantar gayun da suke, ga yan uwa tana dasu na ciki daya dana jinin zumunta. Dole ai taji tausayina saboda ni yar tsintuwa ce banda kowa da komai"
Nawraah na goge hawayen ta tana karasa matsawa wajen Faty tace,
"Wallahi kilama kin fi ni gata, ni da kike gani rayuwata gaba daya data yan uwana acikin hatsari da kunci take, hakika Muna da iyayen a baya. Amman Allah ya karbi abunsa. Ya zama na sai mu da yayan kadai, Shi yake mana komai shine bango majinginar mu. Shine komai namu na rayuwa. Wallahi bashida lokacin kansa sai namu. Mutuwa tazo ta sake mana yankan kauna ta dauke shi. Ya zamana sai ni da Amnah da yayan mu ashfeef. Yan uwa baki daya sun juya mana baya duk wata kadara ta mahaifin mu an kwaceta saboda bamuda arziki. Na takaice miki zance ni da Kai na na kawo mu nan gidan marayun nace zamu zauna saboda bamuda inda zamu zauna. Faty har zaman daki daya tare da tumaki da kiwo mun yi. Ba window a dakin haka muke kwana ba wajen wanka a waje mukeyi, muna karewa da zani, Ba wajen bandaki sai dai muyi a leda mu jefar, Abinci baka samu. Baki daya ba kwanciyar hankali.Yan uwan iyayen mu baki daya ba sayi damu. Dukkan su kowanne yaki amincewa ya dauke mu, mu zauna awajenn sa. Baki daya suka ciremu daga cikin ahalin su. Mutum daya ne zakka acikin su, yana zuwa shi wannan bayada halin rike mune da tuni ya rikemu sai dai Kash, baiyi sa'ar matar aure ba, Faty, Cikin kankanin lokacin da baifi shekara ba da kwanaki. A kub'i a kub'i Allah ya amshi ran iyayen mu da yayan mu baki daya ni da kike gani dawowa nan muksi daga baya lokacin iyayen mu na darai. Asalin mu yan yankin bunza ne...... Zuriyar hamidniyya lebanon. Idan kina raayi Kuma kina bukata. Ni Nawraah zan zamar miki kanwa agare ki da yardar Allahzakuma ki same ni me cikar alkawari. Wallahi summa tallahi bantaba ji na tsaneki ba a raina faty, Alkhairi ne kawai ya hada jini na da naki. Don naki jinin a tsaneni ko a tsameni ace baaso. Nafuson na zauna da kowa lafiya domin baki daya duniyar kankanin lokaci ne mai wucewa cikin yan kalilan dakikai "
Faty ta sharce hawayen ta da bayan hannunta tana duban Nawraah. Ta girgiza Kai tana hawaye sosai tace,
"Ban tsane ki ba nima haka zalika... Kawai banason na sake sabawa da wani ne azo a rabamu daga karshe... Kinganni nan banda saa. Dani aka dawo wannan gidan marayun da sauran yaran dika aka dinga dauki dauki daya daya aka Barni ba Wanda yake so na. Ba Wanda yake son hada zuriyar da son daukata, gaba daya kan baa so na, an dauke ni ma an dawo da ni haka kawai. Wannan abun yasa na tsani komai. Baki daya dukkanin lamurana suka fita da Kai na. Babban abunda yafu damuna ma irin nidin yar tsintuwa ce da batada usuli gaba daya kowanne acikin ku maraya ne. Amman ni fa? Bansan kowa ba. Kilama cikin she....
"Shhh karki karasa Faty. Kedin cikakkiyar mace ce me cikar albarka da alkhairi Wanda Allah ya halitta da so da kauna... Yadda kowa yake haka kike. Kilama kin fimu kusanci wajen Allah. Wallahi faty. Da ace kana iya tsara rayuwar ka daban kayo rayuwar ka smoothly ba wani matsala lokaci daya masifu suka dinga faruwa kinji Allah! Da irin rayuwata a baya. Wallahi zon fison ace irin rayuwar ki ce dani. Banda kowa bansan komai ba. Wallahi sai yafu mun Amman astagfirullah ni da kike gani Ina cikin wata irin rayuwata da yan uwana biyu da suka raye, Amman nasan da yardar Allah. Allah bazai bar mu dukan mu da ku haka ba, inshaa Allah nan da kankanin lokaci komai namu zai zama tarihi Kuma zaku zama yan gata kamar kowane 'da dake gaban iyayen sa."
Faty ta yi murmushi tana girgiza Kai. Nawraah ta dubeta itama tana murmushin taci gaba da cewa,
"Saboda ana gani a films suna fadawa daga dogon gini su mutu sunyi commiting suicide, saboda depression, shine kike son gwadawa. ? Karki sake sudin basuda imani ne tunda ba musalmai bane. Amman kowane tsanani yana tare da sauki inshaa Allahu wannan rayuwar komai zai wuce Allah daya san damuwar mu shi zai yaye mana ita. Amman da ache yanzu kin fada kinga kin mutu kafura kenan. Wadda bata yadda da kaddara ba. Amman idan kika hakura kika fawwalawa Allah lamuran ki to zaki sha mamaki Allah, ki rike karatun alQur'ani, Sallar nafila data farilla, azumi, addu'oi, da istigfari, ki rike 'suratul Duha' surah ce mainly da akayita akan yaye damuwa... Khairan inshaa Allah"
Da sauri faty ta sauka daga kan yar karfwn katangar ta nufe su da sauri. Suka rungumeta gaba daya suka koma barke da kuka alokaci guda.
Duk abunnan da suke yi, hajia Qibdiyya data futo daga gidanta tana tsaye tana jinsu tiryan tiryan. Hawayen data makale ne ya zurara daga idanunta. Ta nufi kofar shiga gidan marayun bakinta dauke da sallama. Mai gadi ya mata bayani ya rubuta komai ta shiga ciki har ofishin mai kula da wajen baki daya.
Bayan sun gaysa ne hajia Qibdiyya ta fadi abunda ya kawota daga karshe ta Karkare da....
_ADVERT👇👇_
_YERWA INCENSE AND MORE_
_(DUNIYAR KAYAYYAKIN KAMSHI MASU MATUKAR DADI DA KAMA JIKI, GIDAH, KAYA DA SAURAN SU)_
_INA MA'ABOTA TURARE? KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE_
_TSAFTA KUMA TANA CIKIN IMANI… TOH KU MAR-MATSO KUSA_
_MUN KUMA ZUWA DA HAJAR KAYAYYAKIN_
_*YERWA INCENSE AND MORE*_
_DOMIN SAMUN ZAFAFAN TURARUKAN WUTA NA GIDA, KAYA, JIKI, TSUGUNNO, GASHI... AKWAI KHUMRAHS MASU DADI YAN BORNU, CHADI, SUDAN DAMA SENEGAL, AKWAI OIL PERFUMES, DA TURARUWAN MOPPING DANA WANKA DANA WANKI DANA GADO DA KUJERU DA BANDAKI DA DRAWER DA MOTOCI.._
_AKWAI MAN GASHI NA FESAWA ME SA KAMSHI DANA KITSO. AKWAI KAYAYYAKIN KAMSHI DANA GYARAN JIKI SOSAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA. •_
_ADIRESHI: KANO.. AMMA SUNA TURA KAYAN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE..._
_INGANCI KYAU RAHUSA DA DADEWA A GIDAH DA KAMSHI SAI KAYAYYAKIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE_
_NAMBAR WAYAR SU: 08095215215, INSTAGRAM/THREADS/TWITTER:yerwaincense_and more_
_YOUR NUMBER ONE STOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS... THEY 'VE GOT YOU AND YOUR HOME COVERED_
[5/3, 9:35 PM] Hafsaat🧕💞: _K'K'J_
_(M/W/S)_
_BOOK TWO_
_✍️:MX_
_15_
:::::::::
"Ina son idan har ba takura, Zan dauki nauyin karatun wadannan yaran yammata har ya zuwa lokacin da zasu kammala inshaa'Allahu."
Mai kula da gidan marayun ta kada kai tana murmushi tace,
"Mashaa Allahu! Allah yabaki ladan temako Aameen. Muna godia sosai kina aiko mana da kayayyaki da gudunmuwa kala kala kama daga abinci, suturu, da sauran su duk kuwa da bamu taba ganin juna ba sai dai afadi sunan ki ko na mai gidan ki. Allah ya saaka muku da mafificin alkhairin sa Aameen"
"Aameen Yaa Rabbi...Aaameen"
"Yaran dai ina tunanin su Raudah ne.. su biyar ne a dakin. Raudah, Wasila, Faty, Nawraah da kuma karamar kanwar ta Amnah. "
Hajia Qibdiyya tayi shiru tana nanata sunayen su akan labbanta. Nawraah? Amnah? Tabbas yayi shige da sunayen yaran marigayiya malama Hindu. Matsalar daya bata san su a fuska ba yanzu. Tayi tayi tagan su Allah baiyi ba. Malama Hindu na cewa zata kawo mata su da yardar Allah. Zuwanta na farko ne dai ta taba ganin su lokacin data je sayan awara suna kanana...
"Toh shikenan. Koma su nawa ne dai. Ba zai gagara ba inshaa Allah. Ina fatan sun kammala sakandire ko?"
"Eh daya daga ciki ma tana jami'ar dake daga baya tazo. Su dinne dai basa yi su ukun. Sai karamar kanwar ita Nawraah din. Tana yin primary din dake cikin nan gidan marayun wato "home school"
"Mashaa'Allahu... Idan ba damuwa ko zan san abunda suka karanta bangaren science ne ko art ko accounting"
"Okay to ranki ya dade. Bari na kirawo su ko?"
"Toh shikenan ba damuwa.."
Matar ta tashi daga kan kujerar ta tana gyaran zaman hijabin jikinta ta futa zuwa dakin su Raudah.
A hangar dakin na su ta hango su zasu shiga ciki.
"Kuzo nan"
Jikin su ya dau kyarma dika suna tunanin ta jiyo abubuwan da sukayi,
"Ma dan Allah kiyi hakuri"
"Da akayi me? Alkhairi ne yazo kuzo office yanzu. Ah tsaya kafin sannan ku nawane a terrace din sama kuke magana?"
"Iya mu kadai ne Ma. Ni sai wasila da Nawraah mu hudu ne kawai. Don Amnah tana daki muka bar ta"
"Okay kuzo office yanzu harda Amnah din" tana karasawa ta juya ta nufi ofishin ta
Suka tsaya suna kallon juna. Faty da jikinta baki daya yadau kyarma ta dube su tache,
"Allah sa ban janyo muku wani babban lefin ba. Amma me Amnah zatayi acikin mu? Kar dai"
Wasila ta katse ta tana daga hannu.
"Karma ki kawo wannan maganar"
"Me kike nufi wata magana?" Nawraah ta tanbaye su itama jikinta ba dadi
"No wai ko tana tunanin an samu me daukar mune ko Amnah akeson ayi adopting"
"Me? Ina bazai yiwu ba ai" Nawraah ta fada da karfin gaske ta shiga daki ta riko hannun Amnah ta zura mata hijabi
"Ina zaki?" Wasila ta tambaye ta
"Zuwa zanyi nace daga yau munbar gidan marayun don ba zaa rabamu da yan uwana ha. Dan bamuda matsugnin zama ne daman muka zo nan din, Amman bamu zo dan mu raba kawunan mu ba"
"Chill. Ba abunda zai faru inshaa Allah. Maybe wani abun ne na daban"
"Koma menene dai kuje muji ko"
Gyada Kai sukayi atare suka nufi office din bakunan su dauke da sallama.
Hajia Qibdiyya na zaune tana danna wayar dake hannunta. Sanye take cikin wata rantsattsiyar abaya data sha ruwan stones da sukayi matukar Kara mata kyau .
"Assalamu alaikum..." Suka hada baki wajen yin sallama alokacin da suka karasa shiga ciki
"Waalykm Salam" hajia Qibdiyya ta amsa musu tana ajiye wayar da take dannawa akan cinyar ta
"Ina wuni? " Suka shiga gayshe da ita daya bayan daya.
Ta amsa Wa kowanne da fuska a sake tana murmushi tache,
"Sannuku yammata adon gari. Allah ya muku albarka"
"Aameen " suka hada baki wajen amsa ta..
"Ranki ya dade gasu nan. Da farko dai kusan dukkanin kayan masarufi dana suturu da magungna Kai harda furnitures na cikin wannan gidah na mu na marayu me albarka. Wannan baiwar Allah na cikin mutanen da sukafi bada gudunmuwa aciki, Kuma ko sau daya bata taba zuwa da kanta ba sai dai aike itada mai gidanta. Ubangiji Allah ya Saka musu da allhairinsa. Wannan gidan Mai kallon mu shine gidan su. Ta futo tana shawagi ta saurari abubuwan da kuke fada. Ta Kuma yaba da hankulan ku sosai. Don haka ku sake mata godia zata dau nauyin karatun ku na jami'a tundaga ranar da zaku fara har ya zuwa sanda zaku kammala "
"Mashaa Allah. Allah ya Saka da alkhairi"
"Mungode Allah yasa kudi haka"
"Allah ya biyaki da gidan aljanna"
"Allah ya kara arziki Amin"
Suka shiga yi mata godia daya bayan daya. Hajia Qibdiyya tayi murmushi kawai tana duban Amnah ta mika mata hannu ta rikota,
"Ya sunan ki?"
"Amnah"
"Mashaa Allah... Sunan yan gayu"
"Ranki ya dade itace karamar da nake gaya miki. Ga yayarta nam. Sunan ta Nawraah, wannan Kuma sunanta Raudah, wannan itace wasila. Ga Kuma faty nan daga gefen ki"
"Mashaa Allah. Duk gasunan nagansu. Allah ya muku albarka ya raya ku, ya tsare kuruciyar ku har girman ku Aameen"
"Aameen Aameen" suka hada baki wajen amsata
"Allah ya jikan mahaifan ku. Allah yabamu iKon cigaba da kulawa da ku"
"Aameen Yaa Rabbi"
"Me kika karanta ke... Raudah ko?"
"Eh nice Raudah. Art na karanta"
"Mashaa Allah! Sai ke wasila ko?"
"Eh sunana wasila. Nima art din na karanta"
"Mashaa Allah ga Kuma faty ko?"
"Eh sunana faty. Nima art dinne"
"Mashaa Allahu. Ke Kuma Nawraah ko, kece kike jami'ar ? Wacce?"
"Eh Nawraah. Nan jami'ar Alharamein university nida wata yar uwarta aka bamu scholarship da yayyan mu maza biyu"
"Mashaa Allahu. Waye ya dauki nauyin karatun naki?"
"Wata mata ce... Kaman tanada babban matsaayi a makarantar haka. "
"Okay to alhamdulillah.. inshaa Allah Kuma sauran ku ukun inshaa Allah zamu muku gurbin karatu daga Monday dinnan ma sai ku fara zuwa. Idan tazo Nawraah art kike ko science course ne?"
"Criminology ne. Social sciences. Art kenan "
"Yauwa ai shikenan sai a Saka su a department dinku tunda dama first semester kuke ba?"
"Eh"
". Sai Amnah Kuma akwai private schools masu kyau dake nan naduka crescent inshaa Allah sai a sakata aciki...."
"Mungode Allah ya Saka da alkhairi...." Nawraah ta shiga mata godia. Sauran ma sukayita kara godia
Hajia Qibdiyya nata kallon Nawraah baki daya kaman malama Hindu take gani ta kasa hakuri ta dubeta tace,
"Nawraah su wanene mahaifan ki? Shin anan naduka kuke Kuma?"
Nawraah ta sauke zuciya tana duban kasa tace,
"Allah ya musu rasuwa dukan su, eh a naduka zone muke Amma"
"Okay mashaa Allah. Naduka zone? Kinsan gidan da ake awara ?"
Nawraah ta daga kai da sauri ta dubi hajia Qibdiyya tache,
"A baya ko yanzu?"
"No a baya ... Awarar tayi tashe sosai. Daga unguwanni kala kala ake zuwa har layi akeyi"
Hawaye ya taho mata idanuwata suka ciku taf ta gyada Kai tana katse shi kar ya zuba tache
"Eh na sani.... Gidan mu ne"
Hajia Qibdiyya ta mike daga zaunen da take ta taka gaban Nawraah tana dago da fuskar ta tace,
"Nawraah! Nawraahn malama Hindu?....
_ADVERT👇👇_
_YERWA INCENSE AND MORE_
_(DUNIYAR KAYAYYAKIN KAMSHI MASU MATUKAR DADI DA KAMA JIKI, GIDAH, KAYA DA SAURAN SU)_
_INA MA'ABOTA TURARE? KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE_
_TSAFTA KUMA TANA CIKIN IMANI… TOH KU MAR-MATSO KUSA_
_MUN KUMA ZUWA DA HAJAR KAYAYYAKIN_
_*YERWA INCENSE AND MORE*_
_DOMIN SAMUN ZAFAFAN TURARUKAN WUTA NA GIDA, KAYA, JIKI, TSUGUNNO, GASHI... AKWAI KHUMRAHS MASU DADI YAN BORNU, CHADI, SUDAN DAMA SENEGAL, AKWAI OIL PERFUMES, DA TURARUWAN MOPPING DANA WANKA DANA WANKI DANA GADO DA KUJERU DA BANDAKI DA DRAWER DA MOTOCI.._
_AKWAI MAN GASHI NA FESAWA ME SA KAMSHI DANA KITSO. AKWAI KAYAYYAKIN KAMSHI DANA GYARAN JIKI SOSAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA. •_
_ADIRESHI: KANO.. AMMA SUNA TURA KAYAN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE..._
_INGANCI KYAU RAHUSA DA DADEWA A GIDAH DA KAMSHI SAI KAYAYYAKIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE_
_NAMBAR WAYAR SU: 08095215215, INSTAGRAM/THREADS/TWITTER:yerwaincense_and more_
_YOUR NUMBER ONE STOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS... THEY 'VE GOT YOU AND YOUR HOME COVERED_
[5/3, 10:46 PM] Hafsaat🧕💞: _K'K'J_
_(M/W/S)_
_BOOK TWO_
_✍️:MX_
_16_
:::::::::
*Dimmmm* naura taji baki daya rassan jikinta sun amsa, Idanuwanta suka dauke ganin su na yan wasu dak'ik'ai. Yayinda jinta ma ya dauke dif. Kafafunta suka gaza daukar nauyin gangar jikin ta.
Sunan marigayiya ummy su data kira yasa kwakwalwarta tuno mata baya. Alokacin da suke zuri'ah daya suna raye dukkanin su. Abbieyn su marigayi junaidu da ummyn dinsu malama Hindu. Da babban wansu mai kaunar su marigayi Hamma Ashir.
Wasu hawaye ne masu dumi suka shiga yi mata reto akan kyakkyawar fuskar ta. Hajia Qibdiyya ta sanya hannu ta janyo Nawraah jikinta ta rungumeta tana bubbuga bayanta,
"Kuka? Dan Allah kibar kuka Nawraah. Wallahi kullum Allah ne shahidi cikin neman ku nake. Na rasa samun lambar wayar ku. Idan na kira akashe. Na tura ance mun kunbar gidan nan. Yanzu Ina yayyun ki biyun? Ashir da ...
"Hamma Ashfeef" Amnah ta karasa mata itama tana duban yayarta Nawraah
"Eh Ashir da Ashfeef suna Ina? Mahaifin ku da baki daya dai ina kowa yake? Meya sa kuka dawo gidan marayu Nawraah? " ta daga fuskar Nawraah dake zubar da hawaye sosai. Jijiyoyin kanta sun futo radau radau agaban goshin ta..
"Eh Nawraah? Meyasa? Kiyi magana kinji?"
Nawraah ta shiga girgiza Kai tana janye jikinta daga na hajia Qibdiyya ta kifa kanta a bango tana kuka sosai
Hajia Qibdiyya ta dubi su Raudah da shugabar gidan marayun tache,
"Nasan su. Mahaufiyar su munyi zaman mutinci da ita sosai. Tafiyar da mukai kasar waje lokacin Banda lafiya naje haihuwa. Allah beyi zan dawo mu ganaa ba d'an dana haifa ya rasu acan na hadu da cuta babba. Sai da muka kara sabon zama na wartsake tukun sannan muka dawo ake shedamun ta rasu. Daga haka Kuma dif nadaina jun komai, ko yaushe da tunanin yaran nan nake kwana nake tashi. Kai subhan Allah. Mai rai ba abakin komai yake ba. Alhamdulillah babban burin da nake fata ya cika. Yau gani ga iyalan marigayiya Hindu. Allah ubangiji ya jikan mahaifiyar ku. Allah ya baku hakurin rashinta Allah ya muku albarka ya buda muku kofofin alkkhairinsa Amin"
"Aameen Aameen" suka amsa baki daya
Shugabar orphanage din ta kada kai cike da rudani da tausayin Nawraah ya