Showing 24001 words to 27000 words out of 69829 words
GIDAH DA KAMSHI SAI KAYAYYAKIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE_
_NAMBAR WAYAR SU: 08095215215, INSTAGRAM/THREADS/TWITTER:yerwaincense_and more_
_YOUR NUMBER ONE STOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS... THEY 'VE GOT YOU AND YOUR HOME COVERED_
[5/5, 11:16 PM] Hafsaat🧕💞: _K'K'J_
_(M/W/S)_
_BOOK TWO_
_✍️:MX_
_20_
:::::::::
Sosai ta shiga nazarin yadda zata bullowa lamarin gaba daya. Wayar ta ta sake yin kukan agajin kira
Wannan shine kira na hudu daya shigo bata dauka ba. Don haka ta janyo wayar tana duban sunan me kiran Layla ce
Baki daya ta manta sunada aikin da aka basu da zasuyi. Wanda library din ya cika , Wanda garin dube dube acikin wayarta nan taci karo da abubuwan da suka daga mata hankali.
Tunani ta shiga yi na yadda zatayi. Kafin ta sanya hannu ta kira laylan ganin Kiran ya katse bata daga ba
Nan take sheda mata gata nan zuwa . Tattara takardun tayi ta chusa acikin yar karamaar jakar dake hannunta
Futa tayi daga dakin ta bar cikin gidan marayun zuwa bakin kofar makarantar tasu ta hadu da Layla.
Tayi kokari ta saita kanta kafin laylan ta gano wani abun. Don sam batason kowa ya gane halin da take ciki gudun kar ta rusa shirin da take kokarin daura damarar sa.
Dakyar ta iya sauya kanta suka hadu suka duba aikin da zasuyi na makarantar. Suka karkare komai tare suka raba yadda zasu bada aikin idan malamin nasu yazo karbar aikin presentation din da zasu yi.
A gurguje ta iya tsayawa suka kammala sauran darussan ranar tana daukar Amnah daga makarantar ta samu kanta da zuwa inda ashfeef yayan su yake aikin kanikanci. Don tuni ya dena zuwa jami'ar sosai yake aiki tukuru a sansanin wajen kanikacin da biyar da goma yake samu ya saya musu wasu abubuwan har ma da katin waya wataran idan ya samu hali.
Yana karkaashin wata mota yana gyaran ta. Suka karasa wajen . Abokanan aikinsa suka shiga kiran sunan sa .
Ya fito daga karkaashin motar yayi butu butu da bakin mai. Neman halak da wuyan baki daya kayan jikinsa rigace mai yankakken hannu shimi da wando sun yayyage. Hannunsa dauke da karafunan kayan gyara.
Yana ganin su ya saki murmushi . Ya dauki ruwaa a buta yana dauraye hannunsa da fuskar sa
"Sannu da aiki" Nawraah ta fada masa tana murmushi
"Sannun mu dai. An tashi ne daga makarantar?"
"Eh an tashi..."
"Hamma"
"Naam Amnah ta.. yauwa ga cheese dinki dana saya dazu a shago rike kici" ya karasa fada yana mikawa karamar kanwar tasu ledar cheese balls guda biyu
Ta karba da hannu biyu tana murmushi. Nan da nan ta yage ledar ta fara ci tana turawa Nawraah wai ta dauka. Nawraah ta girgiza mata Kai tana daga kanta tace
"Na koshi Amnah. Ci kinji?"
"Wani abun kuke so ne?" Ashfeef ya tanbayi Nawraah yana kokarin zaro kudi a aljihunsa
"A'a hamma ashfeef ba wani abun muke so ba magana ce dai nazo na gaya maka ita. Don kada kaji daga baya"
Waiwayawa bayansa yayi ganin abokanan aikinsa daga dan nesa dasu. Yasa ya nuna mata can wajen wata mota suka matsa. Ya dubeta yace,
"Meya faru?"
Nawraah ta nuna masa wayarta tana murmushi hawaye nason futo mata tace,
"Kasan meyasa hamma Ashir yace kar nayi amfani da wayar nan sai na bar aji daya dana biyu da sauran su?"
Ashfeef ya girgiza mata Kai alamar a'ah..
Hawayen da take kokarin mayar da su ne suka bujere mata suka fara zuba a fuskar ta masu dumi sosai
Ashfeef shima lokaci daya yaji hawayen na kwaranyo masa ya dubeta cikin tsantsar damuwa yace
"Menene Nawraah? Wani abun ne ya faru? Dan Allah ki sanar mun ? Menene ki gayamun kinji?"
Nawraah ta girgiza Kai tana sharce hawayen tache,
"Su suka kashe ummy.... Suka kashe abbiey... Kuma suka kashe Hamma Ashir" ta karasa fada tana daga wayarta
Ya dubeta yana duban wayar jikinsa na kyarma yace,
"Su waye eh?"
"Ina kyauatata zato na akan mutanen dana dade Ina tabbatar da sune suka kashe mana gatan mu. "
"Su waye Nawraah?"
"Alhaji sambaso... Alhaji ateeks... Dr bintu. Wadannan mutane uku acikin su akwai Wanda ya kashe mana su ummy. Duba kaga"
Ta karasa fada tana nana masa wayar a kunne yana sauraron maganganun da sukayi sanda ummy ta jefar da plate. Ta Kuma nuna masa fefen bidiyon da aka jefar da mahaifinsu ta baranda
Ashfeef ya sake hannu ya kulle bakisan saboda wata Kara da take son futowa. Idanuwansa suka furfito waje cike da dimuwa yace,
"Yanzu meye abunyi? Kinsan sunfi karfin mu. Bamuda kowa bamu san kowa ba Nawraah"
"Muna da Allah. Shi kadai ya isar mana. Domin shi din mamallakin kowa ne Kuma da komai"
"Hakane Kam kin gama magana. To yanzu da me zamu fara? Ko bappah Auwalu zamu gayawa?"
"Idan muka gayawa bappah Auwalu ai anyi baayi ba kenan. Domin aunty nusaiba sai ta bata mana shirinmu. Don itama Ina tabbatarwa tanada nata kason kwamashon akan kisan da akayiwa iyayen mu"
"Hakane. Amman Nawraah kina ganin ba zamu janyowa kanmu babban abu ba kuwa? Dubafa ba wani babba da ke tare da mu da sauran su"
"Hamma ashfeef nice fa ko ka manta ne?"
Ashfeef yayi murmushi yana girgiza Kai yace,
"Ya za'ai na manta. Nawraah ke din ai KWANKWASON JIMINA ce MAI WUYAR SHAFAWA..."
"yanzu kayi magana. ... To da yardar Allah karshen su ne yazo. Zan samu hajia Qibdiyya muyi maganar. Na tabbatar ita kadai ce yanzu zan iya aminta da ita acikin kowa... Duba da tushen matsalar daga wajen su aka samu"
"Gaskia ne . Toh Allah yasamu dace. Ni yanzu akwai abunda zanyi na daban?"
"A'a hamma. Kawai dai dama nazo na gaya maka ne. Kar na fara koma menene ya zama ba sanin ka aciki, tunda kaga kaine babban mu. Sai da yarjewar ka"
Ashfeef ya kada Kai. Tausayin kannen nasa ya sake lullube shi, rayuwa kenan wai yau shine Nawraah suke kira babban su. Ba iyayen su ba ran hamman su. Baa wani dake tare da su sai Allah.
Hawayen da yake kokarin mayarwa ne suka zubo, Lalle girma ya hau kansa. Ya dube su cike da so da kauna yace,
"Shikenan Nawraah na amince. Allah yasa mu fara a saa. Allah Kuma yayi riko da hannayen mu. Allah yasa karashen kowane mai hannu aciki ne yazo, Allah yasa hakanne yafu alkhairi, Allah ya jikan iyayen mu. Ya bude mana kofofin alkkhairinsa aamin"
"Aameen hamma. aameen"
Kudi ya zaro nera tamanin ya mikawa Nawraah yace su saya wani abun. Suka masa sallama suka tafi yayinda ya koma karkaashin motar ya cigaba da gyaran da yakeyi
Nawraah na rike da hannun Amnah suka tinkari gidan Alhaji Abubakhar dollars.
Ta dora hannu akan gate din gidan zata bude kenan wayarta ta fara Kara. Ganin me Kiran yasa tayi murmushi, ta juya ta dau wayar a kunnenta suka koma bakin gate din gidan marayun .
Marwaan ne ya kirawota suka fara waya. Yake sheda mata gashinan zai zo su gaysa.
Don haka ta fasa shiga gidan Alhaji Abubakhar dollars din suka shiga gidan su na marayun tana tafe da wayar a kunnenta suna waya. Hannunta na dama rike da hannun Amnah suka karasa shiga ciki....
*NADUKA ZONE*
Da kanta ta ke tukin motar, Bayan motar shake yake da kayayyakin abinci da manya manyan ledoji....
_ADVERT👇👇_
_YERWA INCENSE AND MORE_
_(DUNIYAR KAYAYYAKIN KAMSHI MASU MATUKAR DADI DA KAMA JIKI, GIDAH, KAYA DA SAURAN SU)_
_INA MA'ABOTA TURARE? KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE_
_TSAFTA KUMA TANA CIKIN IMANI… TOH KU MAR-MATSO KUSA_
_MUN KUMA ZUWA DA HAJAR KAYAYYAKIN_
_*YERWA INCENSE AND MORE*_
_DOMIN SAMUN ZAFAFAN TURARUKAN WUTA NA GIDA, KAYA, JIKI, TSUGUNNO, GASHI... AKWAI KHUMRAHS MASU DADI YAN BORNU, CHADI, SUDAN DAMA SENEGAL, AKWAI OIL PERFUMES, DA TURARUWAN MOPPING DANA WANKA DANA WANKI DANA GADO DA KUJERU DA BANDAKI DA DRAWER DA MOTOCI.._
_AKWAI MAN GASHI NA FESAWA ME SA KAMSHI DANA KITSO. AKWAI KAYAYYAKIN KAMSHI DANA GYARAN JIKI SOSAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA. •_
_ADIRESHI: KANO.. AMMA SUNA TURA KAYAN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE..._
_INGANCI KYAU RAHUSA DA DADEWA A GIDAH DA KAMSHI SAI KAYAYYAKIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE_
_NAMBAR WAYAR SU: 08095215215, INSTAGRAM/THREADS/TWITTER:yerwaincense_and more_
_YOUR NUMBER ONE STOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS... THEY 'VE GOT YOU AND YOUR HOME COVERED_
[5/7, 6:54 PM] Hafsaat🧕💞: _K'K'J_
_(M/W/S)_
_BOOK TWO_
_✍️:MX_
_21_
:::::::::
A haka ta karasa unguwar Naduka zone. Tana juya kan sitiyarin motar ta faka a daidai kofar gidan da zata shiga.
Fitowa tayi daga ciki motar ta ta bayan ta karasa parking din a inda ya dace. Sanye taa ke cikin doguwar riga ta atamfa. Tayi daurin channel o.
Sai mayafi da ke dabaibaye da manyan stones da aka bi da shi da design din flowers.
Hango Ahmad tayi yana tahowa daga cikin gidan su.
"Ka ga" ta daga hannu tana kiran sa...
Karasawa yayi wajenta ya gayshe ta ta amsa tana nuna masa bayan motar ta ta,
"Dan dakko kaya anan. Idan zaka iya hadawa akwai wasu a booth ma."
"Tohm" ta fada tana bude murfin baya... Ya dakko wasu manyan ledoji ya rike.
Ya zagaya wajen booth din nanma bayan ta bude ya dakko wasu ledoji ya dora akan sa. Sauran kuma ay rike su da hannuwan sa.
"Ina za'a Kai?"
Ya tambaye ta yana rike da kayan
"Muje gidan ku" ta amsa shi tana yin gaba.
Ahmad na biye da ita, suka karasa har kofar parlorn su..
Nusaiba ce a zaune akan kujera . Tanata girgiza kafa. Ta jiyo motsi, idanunta a rufe saboda masifa ta shiga cewa,
"Wallahi wallahi zan surfa maka rashin mutinci Ahmad. Dan iskanci nace maka kaje kayi sauri ka gaya masa ko ya bada wani abun ko ya kwan a waje ni ba baiwar gidan su bace. Aikin kawai"
Ahmad da ke rike da kaya ,Nike Niki kunya duk ta mamaye shi hi na maganganun da mahaifiyar tasu nusaiba ke fada,
Aiken sa tayi wajen bappah Auwalu mahaifin su, kan yaje ya nemo shi duk inda yake ya sanar masa inde ba zai bada kudin abincin da zaa dafa ba ko ya bada abincin da zaa ci, lalle kar ya dawo mata gidah zai kwana, ya nemi waje kwana daban..
"Assalamu alaikum Wa rahamatullah" Dr bintu ta yi sallama tana kutsa Kai ciki
Nusaiba na zaune sai ta mike tana dashare hakora hadi da saka hannu ta gyara dankwalin kanta.
"Waalykm Salam hajia. "
Ahmad ya karasa shiga da kayayyakin ya ajiye yana komawa gefe
"Yauwa yaron kikri nagode. Ungo wannan kasha ruwa" ta zaro yan dubu daya guda biyar ta mikawa Ahmad
Ahmad ya girgiza Kai yana murmushi,
"A'a nagode"
"Rike mana baka nayi ai ba roka kayi ba" cewar Dr bintu
"Karbi mana " nusaiba ta dankara masa harara tana kifta masa idanu ya karba
Ahmad ya mika hannu ya karba yana mata godia
"Nagode sosai. "
"Bakomai"
"Umma naje kenan ko kuwa?"
"Kaje ka sanar mai, kaji dai na gaya maka"
Ahmad ya girgiza Kai kawai ya futa daga cikin gidan yana kambama irin halayen nusaiba. Kiri kiri gashi nan an kawo kayan abinci amman ta tilasta yaje ya gayawa mahaifin nasu ya kawo cefane ko ya kwana awaje.
Yana tafe ransa duk ba dadi saboda ko kadan bayasan halayen nata. Duba da wasu halaye ne marasa kyawu. Wanda kasancewar sa babban da agare su yake ganin bai dace ba.
Ya karasa bakin kasuwa a inda mahaifin nasu ke zama yana lodin bus.
Bappah Auwalu yana ganinsa ya mike . Ahmad ya karasa suka gaysa,
"Ya akai Ahmadu?"
Ahmad ya sauke ajiyar zuciya yana sake sadda kansa akasa yace,
"Umma ce"
"Yau kuma me tache?"
Ahmad ya Kai hannunsa kan keyarsa yana sosawa. Saboda maganar ta yiwa harshen sa nauyi
"Ina sauraon ka Ahmad me tace?"
"Baba ca tayi wai la bada kudin cefene ko cefenen. Wai idan ba haka ba..."
"Uhm Ina sauraon ka"
"Wai kakka dawo gidah"
Bappah Auwalu ya girgiza Kai yana murmushin da yafi kuka ciwo yace,
"Nusaiba kenan, Allah ya shirya. " Ya ka rasa fada yana taba alijun gabansa ya zaro wata dari biyu duk ta jeme ya mikawa Ahmad
"Ai ka barshi kawai, kaga wannan matar yanzu tazo da kayayyakin abinci kala kala. Ta kirani na shigar mata su shine ta bani dubu biyar ga su" ya karasa yana mikawa bappah Auwalu
Bappah Auwalu ya girgiza Kai yana janye hannun Ahmad dake tura masa kudin yace,
"Allah sarki. Angode, Amman ba zan karba kudin nan ba Ahmad. Kaje ka dinga taru gaba kayi wani abun amfanin dashi. "
Ahmad ya girgiza Kai da sauri yace,
"Ba abunda zanyi dasu Allah. Ka rike ka bayar a kudin kayan abincin"
Bappah Auwalu yayi shiru yana yaba kyan Kai irin na babban dan sa Ahmad.
"Dan Allah ka karba" Ahmad ya sake tura masa kudin
Bappah Auwalu ya karbi kudin ya zari guda biyu yan dari biyar na dubu daya ya ninke sauran ya zura a aljihunAhmad. Ahmad zai sake magana, bappah Auwalu ya daga masa hannu alamar ya dakata yace,
"Dubu dayan ma ta isa Ahmad. Allah ya maka albarka kaji?"
"Aamin, Amman daka Kara"
"Ta isa haka Allah. Yanzu ungo rike dari biyu nan dana baka da wannan dari biyar din. Dari bakwai kenan ka bata"
"Toh shikenan. Bari na kai mata"
"Yauwa sai na dawo"
"Sai ka dawo"
Ahmad ya juya ya nufi gidah. Yayinda bappah Auwalu ya koma kan bencin da yake ya zauna . Tunani sosai ya fara akan iyalan Alhaji sambaso dake musu abubuwan arziki kama daga kayan abinci ya zuwa suturu da tsabar kudade..
Ya sauke ajiyar zuciya yana sake zurfafa bicike na tunani akan su. Shin meyasa wannan kyautata wa har yanzu bata yanke ba?
Ganin ya kasa samun amsar tanbayar da yakewa kansa. Ya mike ya nufi bakin titi yana taro mutanen da zasuyi tafiya zuwa motar dake kan lodi a layi.
:::::
Dr. Bintu tayi shiru tana duban nusaiba dake zuba tana bata labarai. Ta saki ta kama wani ta saki ta kama wani. Baki daya ta hanata fadar abunda ya kawo ta.
A haka Ahmad ya shiga ciki bayan yayi sallama. Nusaiba nata hangen sa. Ya mika mata kudin ta karba tana wani yamutsa fuska tace dashi,
"Je ka anjima ka dawo"
'Tohm" fita yayi da sauri
Dr bintu ta dubi Ahmad daya futa tache,
"Shine babba?"
Nusaiba tayi murmushi tache,
"Eh. Daga shi dai kanwar sa Layla. Allah beyi ........
Nan ta fara ratattako zance tun farkon auren su da komai da komai. Tun Dr bintu na fuskanta har ta fara yake kawai tanayi kamar tana sauran Nusaiban
Sai daga can karshe ta jiyo Nusaiban na cewa,
"Shine fa daga baya sai Allah ya azurta su din suka tsaya. Shi da Layla. Shikenan kuma haihuwar ta dakata. Alhamdulillah"
Dr bintu ta kada kai kamar irin ta gane komai da komai dinnan jin karshen yasa tace,
"Allah ya jikansu da rahaama su kuma wadannan biyun Allah ya raya miki su aamin"
"Aameen. Ameen nagode" nusaiba ta amsa tana matsa hannuwa.
Ta sake bude baki zatayi magana. Dr bintu tayi hanzarin katse ta. Sanin idan ta barta kara dakko wani labarin zatayi sai su kwana a haka. Don taga alamar batasan tsayawa ba. Ko gajiya batayi. Tache,
"Kafin komai dai ga kayayyakin abinci nan da sauran su ayi hakuri ba yawa"
Nusaiba ta dubi manyan ledojin tana murmushi tace,
"Kamar kinsan ba ko kwayar tsaba agidan kam , inata kiranki ai bakya dauka ko sako na turo ma ba reply"
Dr bintu ta kakaro murmushin yake yayi. Tana kambama karfin hali irin na nusaiba. Wato sune zasu dinga ciyae dasu kamar wani dolen su akan su yake? Tayi kokarin mazewa tace,
"Abubuwan ne sai a slow. Inata samun patients haka plus akwai projects dana keyi ne kwana biyu"
"Allah sarki. Daman jiya nake cewa ko gidah zan zo kinga Kuma sai ga ki"
Dr bintu ta sake yin murmushin tana sosa kasan idonta tache,
"Abu na biyu. Insso ki sanar mun idan akwai business haka ko wani abu daki ke fatan ko burin yi sai mu ga abunda za'a tallafa miki da shi"
Nusaiba na zaune sai ta mike ta koma kusada Dr bintu sauran kadan ta take mata yan yatsun kafarta tace,
"Ni kwa nakeda burika. Ciki harda barin wannan ukubar gidan. Na biyu ina son sauya waya zuwa babba. Na uku mota, mota ta dade tana burgeni inason na mallaki mota. Na hudu sai aban jari inason na fara sarin kaya a kasashen waje. Tamkar dai yadda matan masu kudi sukeyi"
Dr bintu tayi shiru tamkar ruwa ya cinye ta yau ta sake tabbatarwa da Nusaiba matar wani mashahurin mai kudinnce to tabbas zaa sha gayu da fi'ili. Wadannan burika data zayyano sai kache kudaden a bishiya suke suna tsinkowa.
Murmushi kawai tayi ta dubi nusaiba tache,
"Shikenan ba zasu gagara ba. Amma da wani hanzari ba gudu ba, Amman akwai sharadi. Inde zakibi sharadin shikenan"
Nusaiba ta wulkita idanu ta hango kofa rufe ko'ina an datse. Don kada wani ya jiyo su tache,
"Na amince. Idan akwai gaban amincewa ma nayi. Menene?"
Dr bintu ta dubi Nusaiba cikin idanunta tache,
"Zaku tattara naku ya naku ke da iyalan ki duka dasu nawraah ku bar naduka da zama.......
_ADVERT👇👇_
_YERWA INCENSE AND MORE_
_(DUNIYAR KAYAYYAKIN KAMSHI MASU MATUKAR DADI DA KAMA JIKI, GIDAH, KAYA DA SAURAN SU)_
_INA MA'ABOTA TURARE? KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE_
_TSAFTA KUMA TANA CIKIN IMANI… TOH KU MAR-MATSO KUSA_
_MUN KUMA ZUWA DA HAJAR KAYAYYAKIN_
_*YERWA INCENSE AND MORE*_
_DOMIN SAMUN ZAFAFAN TURARUKAN WUTA NA GIDA, KAYA, JIKI, TSUGUNNO, GASHI... AKWAI KHUMRAHS MASU DADI YAN BORNU, CHADI, SUDAN DAMA SENEGAL, AKWAI OIL PERFUMES, DA TURARUWAN MOPPING DANA WANKA DANA WANKI DANA GADO DA KUJERU DA BANDAKI DA DRAWER DA MOTOCI.._
_AKWAI MAN GASHI NA FESAWA ME SA KAMSHI DANA KITSO. AKWAI KAYAYYAKIN KAMSHI DANA GYARAN JIKI SOSAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA. •_
_ADIRESHI: KANO.. AMMA SUNA TURA KAYAN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE..._
_INGANCI KYAU RAHUSA DA DADEWA A GIDAH DA KAMSHI SAI KAYAYYAKIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE_
_NAMBAR WAYAR SU: 08095215215, INSTAGRAM/THREADS/TWITTER:yerwaincense_and more_
_YOUR NUMBER ONE STOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS... THEY 'VE GOT YOU AND YOUR HOME COVERED_
[5/7, 7:29 PM] Hafsaat🧕💞: _K'K'J_
_(M/W/S)_
_BOOK TWO_
_✍️:MX_
_22_
:::::::::
Nusaiba ta kikkifta idanuwa tana saka dan yatsan ta cikin hudar kunnenta na dama tace,
"Me kika ce hajia?"
Dr bintu tayi murmushi tana duban Nusaiba tace,
"Cha nayi idan kinaso wadancan burikan naki su tabbatarl daya bayan daya.. To sai dai idan kin aminta zaki yarda da sharadin da zan fada... Kuma kince kin amince. Amman dubada yanzu kin nuna baki jiba zan sake maimaita miki su. Kinasan wadannan burikan da kika zayyano su tabbata?"
Nusaiba da jikinta baki daya yayi laushi ta kada Kai tache,
"Ina sauraron ki hajia. Tabbas abubuwan dana zayyano kowanne Ina son naga na yi ."
Dr bintu ta sake yin wani murmushin irin na gefen bakin nan tache,
"To sharadin shine. Sai dai ku bar zamann naduka. Ba zaku waiwayo ba har gaban abada kun tafi