Showing 6001 words to 9000 words out of 69829 words

Chapter 3 - KWANKWASON JIMINA BOOK 2 COMPLETE BOOK 2 hausa novel

24 Aug 2024

8950

ce. Aka bata maganguna. Ranar Nawraah bata je.. makarantar ba.

Wasa wasa sai datayi kwana uku bataje makarantar ba. Kullun idan Layla ta biyo mata taga jikin Amnan ne dai har yanzu. Itama sahoda tsoron rashin Nawraah a kusa yasa take komawa gidah taki zuwa makarantar.

Ciwon Amnaah meyakwan yayi sauki sai gaba ya sake yi ma. Tayita ramewa a tsaye kamar zaa hureta ta fadi. Asibitkn cikin gidan marayun sunyi iyakar abunda zasu iya since yafu karfin su don haka su dangana da specialist hospital wato asibitin babban na kwararrun likitoci.

Duk inda Nawraah da Ashfeef suka zaga babu way out. Basuda wata madafa da zasu kama suce zasu samu sauki ta bangaren. Ko zaa yaye musu matsalar lalurar da Amnah ke cikin ta rashi lafiya domin kusan cuwonta na baya da aka mata aiki ne yake dawowa

Dakyar take iya cin abinci ruwa ma sai anyi dagaske take iya sha.

Zaune suke a zauren gidan marayun. Amnah na jikin Nawraah dake jingine da bango. Yayinda ashfeef yake daga can gefe ya saka hannu ya tallabe habarsa yana tagumi.

"Nawraah me kikaci karshe cikin naki ya fara miki ciwo. Likita nata tanbayer ki kinki fada ko?"

Amnah tayi rau rau da idanun tana lankwasa yatsun hannuwanta tace,

"Kiyi hakuri Adda.... Hamma ashfeef kayi hakuri Kai ma"

"Hakurin me? Muna sauraron ki..."

Ta Saka hannunta dakyar tana katse hawayen dake zuba mata tache,

"Irin wannan abunda Ammi take kawomun kafin ta mutu dinnan"

Nawraah ta dubi ashfeef shima yana duban ta muryar Nawraah na rawa tace,

"Wane abu eh Amnah? Me kikaci"

"Wannan abun da ake cin su chakulet acikinsa ko Madara me kwakwa"

"Innalillahi Wa inna ilaihi rajiun. Filled doughnut Amnah..ain kika ci?"

"A cikin sharar can suka Saka suna gama ci fa basu cinye ba suka wullar dashi to shine... Shine na dauka na karkade na ci"

Salati Nawraah da Ashfeef suka kamayi. Amnah ta fashe da kuka tana basu hakuri. Da sauri ashfeef ya sungumi Amnah suka nufi asibitkn cikin gidan marayun.

Sunata haki suka sanar da likitan yadda ake ciki. Likitan yayi dube duben sa sai sunje anyi mata scanning awani asibiyin nan baayi acikin saanan zaa gane inda lamarin ya dosa...

Suka dai durkawa amnah allurar bacci akan gadon marasa lafiya daker acikin asibiyin..

Ashfeef da Nawraah suka futa daga ciki suna tunanin yadda zasu samu kudin da zaa yiwa Amnah scanning.

"Kache su bapoah sani kowanne bai ce komai ba ko?"

"Wallahi Nawraah ba abunda kowanne ya ce. Bappah salisu fa cayayi yana meeting ya katse kawai"

"Subhan Allah ya Allah ka kawo kana dauki"

"Aameen Yaa Rabbi"

"Nawraah..."

Da sauri ta juya jin muryoyin su wasila. Daga mata hannu sukayi suka karasa wajen suna tanbayar ya jikin Amnah.

Nawraah ta gaya musu Duk yadda ake cikin. Nan suka yanke shawarar shiga cikin makarantar Alharamein ko zsu dache da wani liititan da zai musu sauki. Ko ayi amfni da record din Nawraah na medical issues.

Ashfeef kuwa ya zagaya wajen gyaran mota shima ko zai samu wani dan kudin da zasu rage

Baki dayan hankulan su baya jikin su. Nawraah tamkar itace marar lafiya yadda baki daya ta zabge ta fice daga hayyacinta. Hakama ashfeef da yaketa kaikawo ganin ya kawo musu dauki ganin shine namiji. Kuma babban yaya daya rage tilo agare su.


***" Yana daga zaune a kujerun waiting sessions yana jiran futowar abokin nasa. Sanye yake cikin kananun kayan da sukayi matukar karbar zatin haibar halittar jikin sa.

Idanuwan sa suka sauka akan kyakkyawar fuskar da ba zai tabe mancewa da itaba a rayuwarsa.

Ya samu kansa da yin kasa da idanu yana binta da wani irin kallo tamkar zai hadiyeta.

Hango su yayi sun nufi kantar wajen neman karin bayanin bude file ko ganin likita da biyan consultation fees. Ya dan matsa gaba dasu yana jiyo abunda suke fada.

Take yaji wani taisayin ga ya sake kama shi. Amma saboda tsoron abunda zai wargaza amintar tsakanin su...

Hakan yasa ya koma ya shiga ta kofar da yake. Ya same shi yana masa bayanin komai.

Bai gama sauraron saba ya futa da sauri yana hangosu ya karasa dauke hannunsa yake da handkerchief din abokin nasa daya kwace da ruwan roba guda day cira a ofishin likitan daya shiga....

_HGL CHARITY FOUNDATION_

_ASSALAMU ALAIKUM WA RAHAMATULLAH!_
JAMA'A BARKANKU DA _WARHAKA... ALLAH YA SAKA MUKU DA ALKHAIRI YA BADA LADA HADI DA BIYA MUKU DUKKANIN BUKATIN KU DA KUKE FATAN SAMU AAMIN_

GODIA DUBU GA TALLAFIN DA KUKA SAKA NA CIYARWAR AZUMI
INSHAA ALLAHU WANNAN GIDAUNIYAR MAI SUNA A SAMA NA KIRAN MUTANE AL'UMMA MASU SON SAMUN LADAN WANNAN MANYAN AIKI DA MUKE SAKA RAN FARA SHI KAMAR
НАКА

1• DAFA ABINCI A RABA GA MABUKATA RANAR JUMU'AH KO A KAI RUWAN SHA GA MASALLATAI RANAR JUMU'AH

2• HAQA RIJIYOYI ACIKIN KAUYUKA DA UNGUWANNIN DA BASUDA RUWA

3• RABA KAYAN ABINCI KO KUDI GA MABUKATA
MARASA HALI

4•KAI ZIYARA GIDAN MARAYU DA KAI MUSU
ABUBUWAN AMFANI DA SUTURA IDAN DA ME BAYARWA

5• KAI TALLAFI KO ABINCI GA ASIBITOCI WAJEN
MASU JINYA MARASA KARFI..

6•KOKARIN KARASA MASALLACI KO YIN MASALLACI
AWAJEN DA BASUDA SHI...

MAI NERA BIYAR MAI GOMA DiK
YADDA HALI YA KAMA ALLAH YA HADA MU A LADAN DUKA..
JAZAKUM ALLAH BiL JANNAH..
DOMIN SAKA TALLAFI GA ASUSU

9044191709
OPAY
JAZAKUM ALLAH BİL JANNAH💜
[4/28, 11:32 PM] Hafsaat🧕💞: _K'K'J_
_(M/W/S)_


_✍️:MX_


_8_


:::::::::

   Suna tsattsaye dukkan su itada su Raudah. Nawraah ta sadda kanta a kasa hawaye masu dumi na diga a kasa. Jijiyar goshin ta ta sake fitowa radau. Ranta baki daya ba dadi. Sun rasa madafa. Sun rasa yadda zasu bullowa lamarin. Da tuni da abbiey da Ammiey dinsu da hamma Ashir na raye da duk wadannan abubuwan ba zasu faru ba.

Katuwar ajiyar zuciya ta sauke tana goge hawayen dake tsigaya da kasan mayafin ta ... Kowa ne bawa da irin tasa kaddarar. Cikin kankanin lokaci Allah sai ya sauya maka rayuwar ka. Wadda kayi a baya ta zama tarihi...

"Dan Allah ku temaka.  .. yar makarantar nan ce fa. a madadin ta na student file tunda health issue da komai free ne. Dan Allah muke son aga kanwar ta emergency case ne.. Dan Allah ku ceci rai. Bamu da yadda zamu yi ba muda wata madafa data rage mana" wasila ta shiga rokon maaikatan wajen..

Dai dai lokacin da marwaan ya karasa gare su yana sun kuyawa inda Nawraah ta saukar da kan nata kasa...

"Mekyau.." ya kira ta a hankali cikin wata iriyar siga...

Ta daga kanta da sauri tana katse hawayen dake zubowa.

"Kuka? Oh no ... Haba precious ya zaki dinga Zubar da hawayen ki Mai tsada haka. Ungo handkerchief rike ki goge hawayen kinji? Ga Kuma ruwan sanyi ki sha ki sanyaya ranki.....me yake faruwa?" Ya karasa fada yana mika mata robar ruwan.

Taki karba ya sake nana mata a dole ta karba ganin har ya since murfin robar daga ruwan.. Tayi baya tana basmala ta nemi kujera ta zauna tana sha harda ajiyar zuciya. Ba kadan ba ya temaka mata dan baki daya kishiruwar take ji da yunwa sosai. Amman tafi bukatar ruwan inda taci saa Kuma ruwan Mai sanyi..

"Meya faru ne?" Marwaan ya sake tanbayar su Raudah yana kallo Nawraah ta wutsiyar idanun sa..

Suka shiga labarta masa komai suka karkare da,

"Yanzu kanwar tata tana can asibitin gidan marayun rai ahannun Allah batada lafiya sosai. Ana bukatar ayi scanning din yanzu. "

Marwaan ya kada kansa yana duban maaikatan asibitin da sukayi kasa da kan su..

'wane in duty wane likitan ne eh?" Ya fada a tsawance yana duban maaikatan da dukan jikin su ya yake kyarma ..

*Dr Felix ne..."

"Emergency ward nake magana"

"Dr. Gloria ce"

"Tana Ina yanzu?"

"Ranks ya Dade tana cikin emergency ward din tun safe"

"Je kace a shirya komai akwai patient da take bukatar kulawa yanzu zaa kawo ta. "

Da sauri ma'aikacin ya tafi yana waiwayon su ya nufi emergency ward din. Nan da nan kuwa aka fara hallara komai.

Nawraah ta rasa bakin godia alokacin dasu wasila suke fada mata yadda sukayi dashi.

Ta shiga yi masa godia harda hawaye. Marwaan murmushi kawai yake yana dashare hakora.

Da sauri suka nufi can asibitin gidan Marayun suka dakko Amnah data fara sankamewa saboda tsananin azabar ciwon dake addabarta..."

Ashfeef daya dawo daga zagayen da yayi. Ko'ina ya rasa Mai bashii ko dubu daya ce. Dakyar yan garejin motar suka harhada masa Mai ashirin Mai hamsin kudi suka hadu dari biyu da tamanin. Da su ya tsaya ya sayi cincin da lemo guda daya da nufin idan Amnah ta tashi abata ta ci.

Hangosu yayi sunata sauri da Amnah a hannun su sun shiga cikin jami'ar ta Alharamein.

Ya bi bayan su da sauri yana katse hawayen da yake zuba masa. Zuciyar sa na Masa zafi da radadi. Ba ran iyayen su ba ran babban wansu daya zamar musu kamar uba. Shi yana amatsayin namiji babba daya zama shine mahaifi gare su yanzu Amman ya kasa tabuka komai? To yaya zeyi? Wane dalilin zai samu. Ta Ina zai bullowa lamarin?

He failed his sister's... Ya samu kansu da tsayawa yana bubbuga hannunsa abango hawaye daya na bun daya akan kyakkyawar fuskar sa.

Yabi bayan su . Manyan likitoci da nurses da sauran yan agaji tuni sun gyara inda zaa fara duba lafiyar Amnah.

Akan gado Mai Taya aka sakata suka turata zuwa cikin emergency unit. Su Nawraah suka koma baya suka jingina da bango wasila da Raudah Kuma suka zauna akan kujera. Baki daya jikin su yayi sanyi Suma.

Domin sun shaku kwarai matukaa da Amnah ta zama tamkar kanwar su, yarinyar akwai ladabi gata batada hayaniya ko rashin ji irin na yara shekarunta. .

Zirga zirga ya farayi ya kasa tsaye ya kasa zaune. Yaje ya dawo ya shiga yi ta corridor dinnan yana dafe goshinsa. A haka marwan ya same shi yana sanar dashi yadda sukayi.

An debi lokuta masu tsawo don har suka tattashi sukayi sallah kafin a futo da Amnah daga emergency unit zuwa wani daki na kudi wato aminety room.

Tayi fayau tamkar ba ita ba. An mata aiki ancire wasu kwalabe dataci acikin donut din Allah ya rufa asiri basu taba ko yanka wani sassa ba cikin cikinta ba. Tuni ta samu bacci tana sauke numfashi ahankali.

Don farin ciki Nawraah da Ashfeef suka rungume juna suna murna.nawraah ta sake rungumo su Raudah tana musu godia suma...

Sannan ta samu Marwaan dake tsaye shi da Anees tayi sallama tana sadda kanta kasa.

Marwwan yayi murmushi yana shafa kasan gemunsa,

"Ya akai habibty?"

"Nagode sosai...Allah ya Saka maka da mafificin alkhairi. mungode Allah ya biyaka"

Kada kansa yayi yana Jan kasan lebensa hadi da saka hannu ya sosa gashin keyar sa. Ya dubi Anees zaiyi magana. Anees ya dakatar dashi ta hangar bubbuga kafadarsa yabar wajen

"Ba damuwa ... Ai yiwa Kai ne... Allah zai bata lafiya inshaa Allah.."

"Aameen Yaa Rabbi. Mungode kwarai"

"Akwai wani abu da kuke bukata?"

"A'a ba komai. Mungode sosai . "

"Mashaa allagu. Toh Allah yakara mata lafiya Amin"

"Aamin Yaa Rabbi"

Barin wajen yayi yana gyara zaman Bluetooth din dake kunnen sa waya aka Kira shi Mai muhinmanci dan haka da sauri ya fuce daga makarantar gaba daya.

Nawraah ta koma daki waien Amnah dasu ashfeef da ke gefe suna duban gadon da Amnah ke kwance tayi fayau rana daya duk ta zabge ta fita hayyacinta.

"Gashi Nawraah. Abunda na iya samu kenan. Naji Kuma since katta ci abu ne nauyi ko?"

Nawraah ta Saka hannu ta rike ledar tana duban jikinta. Mirinda ce da cincin manya guda uku

"Ayyah hamma ashfeef ance sai zuwa jibi inshaa Allah. Sannu da kokari"

"Rike kuci mana...bari naje na dan zagaya"

"Toh shikenan. Allah ya Kara arziki sannu da kokari"

Fucewa yayi daga cikin asibitin ya koma can naduka zone inda ake wankin mota. Ko zai samu motar dazai wanke abiyashi.

A haka suka kara har kwanaki uku acikin asibitin kafin a sallame su suka koma gidan marayun da suke. Cikin kwanaki ukun nan kullum sai an Aiko musu da hadadden abinci na safe zuwa na dare da ruwan roba da lemo. Kaya dai himili guda. Dan aiken da yake kawowa. Nawraah tayi tayi taji sunan Wanda yake Aiko shin yaki fada. Nan ta sake tabbatar wa kanta tabbss ba kowa bane fyace Marwaan.. Ta shiga yi masa adduar samun nasarar Allah a dukkanin abunda ya Saka agaba. Take ta fara jin shaukin kasancewar sa acikin rayuwar ta. Tabbss yadda yake kyautata mata itada yan uwanta. Ya samu wani babban Kaso na daga cikin wasu rassa a burnin zuciyar tah...

Kullun wasila da Raudah anan suke wuni tun safe har dare. Yayinda Nawraah ke kwana da Amnah. Ashfeef Kuma yakan yi yar buga bugansa ya kawo musu wasu abubuwan har Allah ya anince Amnah ta wartsake aka sallame su.

Suka koma gidan marayun da suke. Nawraah ta gyara ko'ina na dakin da gadon Amnah ta kunna musu tiraren wutan tsinke data saya nera goma tun kwanaki

Nan suka zazzauna akan tabarna itada su Raudah kowanne yana bada labarin tarihin rayuwar sa da irin maraicin sa.

Faty dake can kan gadonta sun cika mata kunne sai jera tsaki take kamar tsaka ta tashi fuuu ta fuce daga dakin tana banka musu harara...

*NADUKA ZONE*

_HGL CHARITY FOUNDATION_

_ASSALAMU ALAIKUM WA RAHAMATULLAH!_
JAMA'A BARKANKU DA _WARHAKA... ALLAH YA SAKA MUKU DA ALKHAIRI YA BADA LADA HADI DA BIYA MUKU DUKKANIN BUKATIN KU DA KUKE FATAN SAMU AAMIN_

GODIA DUBU GA TALLAFIN DA KUKA SAKA NA CIYARWAR AZUMI
INSHAA ALLAHU WANNAN GIDAUNIYAR MAI SUNA A SAMA NA KIRAN MUTANE AL'UMMA MASU SON SAMUN LADAN WANNAN MANYAN AIKI DA MUKE SAKA RAN FARA SHI KAMAR
НАКА

1• DAFA ABINCI A RABA GA MABUKATA RANAR JUMU'AH KO A KAI RUWAN SHA GA MASALLATAI RANAR JUMU'AH

2• HAQA RIJIYOYI ACIKIN KAUYUKA DA UNGUWANNIN DA BASUDA RUWA

3• RABA KAYAN ABINCI KO KUDI GA MABUKATA
MARASA HALI

4•KAI ZIYARA GIDAN MARAYU DA KAI MUSU
ABUBUWAN AMFANI DA SUTURA IDAN DA ME BAYARWA

5• KAI TALLAFI KO ABINCI GA ASIBITOCI WAJEN
MASU JINYA MARASA KARFI..

6•KOKARIN KARASA MASALLACI KO YIN MASALLACI
AWAJEN DA BASUDA SHI...

MAI NERA BIYAR MAI GOMA DiK
YADDA HALI YA KAMA ALLAH YA HADA MU A LADAN DUKA..
JAZAKUM ALLAH BiL JANNAH..
DOMIN SAKA TALLAFI GA ASUSU

9044191709
OPAY
JAZAKUM ALLAH BİL JANNAH💜
[5/1, 12:29 AM] Hafsaat🧕💞: _K'K'J_
_(M/W/S)_


_✍️:MX_


_9_


:::::::::

*NADUKA ZONE*


A tafe yake lahai lahai... Wata kodaddiyar riga ce a jikin sa ta shadda koriya. Duk ta futa hayyacin ta shaddar ta zama tamkar abun tatar Koko.

Yayinda hular kansa tashi ka fiya naci dinnan ce duk ta jeme itama. Takalman da ke kafafunsa irin dan madinan nanne da dadde duk ya cinye ta dunduniyar. Wajen yatsun kuma ga alamar nanewa ta kunar wuta nan... Ya tsinke an nane shi da gaushi.

Ya saka hannu ya rufe bakinsa daya sake sakin wata hammar a karo na ba adadi. Ya rame ya zabge baki daya har wani manyanta ya sakeyi fiye da shekarun sa.

Kallo daya zakai masa ka tabbatar yana cikin ha'ula'in rayuwa. Rike hannunsa yake da leda fara dauke da gari baifi gwangwani biyu ba.

Yana tafe sharaf sharaf, tsaf idan akayi iska mai kadawa sosai sai ta jefeshi ta wancakalar da shi gefe.

Karasawa yayi cikin harabar gidan nasu. Ya daga kai ya sauke a gidan farko mai tarin tunatarwa kan rayuwar su ta baya shi da dan uwansa da iyalan dan uwan nasa.

Wasu zafafan hawaye ne suka ciko idanun sa taf suka kawo ruwa dakyar ya iya sanya kasan hannun rigar sa ya katse hawayen.

Gani yake tamkar zasu futo daga cikin gidan. Ya juya ya dubi titi yana girgiza kai kawai, ya karasa shigewa can cikin bangaren nasa muhalin.

Bakinsa dauken da sallama ya shiga gidan nasa. Tana zaune akan kujera kafa daya kan daya hannunta rike da wayar ta tana dannawa tana murmushi.

Sai da ya yayi sallama a karo na uku bata amsa ba, ya dauki wata hula daya gani a gefe ya jefeta dashi. Sai a saman ta fuskar ta ta juya da sauri tana hade rai,

"Meye haka auwalu saboda Allah kamar wani karamin yaro ?"

Dogon tsaki yaja yana karkada mata hannu yace,

"Baki daya da ma'aunar tace hankalin ki tayi gabas yamma kikayi. Sam idan kina rike da shegiyar wayar nan a hannun ki to baki dayan tunanin ki gushewa yake. Sai ki zama wata sullutuwa ache wayar hannu salula ta mayar da mutum tamkar wani sabon tabi? Kai Allah ya kyauta"

Nusaiba ta daga kai ta hararo shi tana duban sa shekeke dinnan tace,

"Wai har kura ce zata ce da kare maye. ? Dan Allah bakaji kunyar wannan maganganun naka da Kake ba?"

"Kunyar me zanji? Yau kika fara ana miki magana hankalii na kan waya? Ke gaba daya baki da lokacin kowa da komai sai aikin danna waya? Wannan wace irin gurbatacciyar rayuwa kika daurawa kanki ne? Kai Allah wadaran naka ya lalace"

Nusaiba ta sake duban sa tana mikewa tsaye ta gallara masa harara tana zunbura baki gaba tace,

"Irin wadannan maganganun da kakeyi sai wani ya rantse da Allah Kai din kasan me kakeyi. Wai auwalu ni kake budewa baki kake gayawa wadannan maganganun? Allah na tuba astagfirullah Kai acikin jerin mazan aure masu iyali da sukasan abunda sukeyi suke bawa iyalan su hakkokin dake kansu kaji nace Allah? Wallahi baka ciki. Saboda Kai gaba daya gakanan gakanan ne. Hakkokin mu iyalan ka da suke kanka ma ba saukewa kake ba. Saboda zuciyar ka tagama mutuwa. Wayar da muke cin albarkacin ta? Naga da wayar nake rufa mana asiri a abubuwa da dama. Amman shine zakazo kana hankado kirji gashi kana warin rana kana gasamun maganganu. Aikin kawai"

Bappah Auwalu wani malolon bacin rai ya dunkule masa a wuyan sa, ya daga hannu kamar zai mareta ya sauke shi kasa kawai yana girgiza Kai.

"Baba sannu da zuwa" cewar Layla data futo daga bandaki tayi wanka

"Yauwa layla.. ungo rike kusha wannan kafin zuwa annema muga abunda Allah zaiyi" ya karasa fada yana mika mata ledar hannun sa.

Nusaiba tabu ledar da kallo tana hararar ta hadi da tsaki ta koma ta zauna tana girgiza Kai,

"Kullum dai aikin kenan. Gari gwangwani biyu. Su bai ishesu ba mu bamu samu ha. Kai Allah ka yaye mana wannan kaddarar Amin"

Bai ce komai ba ya juya zai shige daki sai Kuma ya fasa yana kiran sunan Layla,

"Naam baba"

"Sh Ahmad na zuwa makarantar kuwa?"

Girgiza Kai tayi tana lankwasa yatsunta,

"Gaskia bansani ba. Ko sanda bama zusa sunje"

"Ke ko bari na gama abunda nake Allah kirbar dukan da zan miki sai kin yabawa aya zaiijta. Shashasha, sakara sullutuwa. Saboda ita bata zuwa makarantar shine kema kika dena zuwa. Kanki kike cuta ai. Maza kafin na hambare ki" nusaiba ta fusata kan Layla tamkar zata mata dukan tsiya

Layla ta guya abayan mahaifin ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login