Showing 60001 words to 63000 words out of 69829 words
Chapter 21 - KWANKWASON JIMINA BOOK 2 COMPLETE BOOK 2 hausa novel
shima yana girgiza Kai yace,
"Yaran yanzu kenan. Ubangiji Allah yasa an daura a saa Allah yasa abokan zaman juna ne har gaban abadan"
"Aameen As-sadeeq dina, daya tamkar dadunu"
Murmushi yayi ya saka hannu ya lakuce mata kumatu...
Suka murda kofar dakin suka shiga bakunansu dauke da sallama....
HANSATUWA💜
_K'K'J_
_(M/W/S)_
_BOOK TWO_
_✍️:MX_
_46_
:::::::::
Nawraah ta amsa musu tana kakaro murmushi. Ta mike ta dan sunkuya ta karbi ledar hannun hajia Qibdiyya.
"Sannun ku da dawowa"
"Yauwa Nawraah habibty. Komai dai kalau ko?"
"Eh" Nawraah ta amsa ta
"Sannu Nawraah"
"Yauwa Abba"
Suka nufi gadon da Anees yake akai. Ya karkatar da Kai yana duban su. Ya lumshe idanunsa ya bude yana murmushi
Hajia Qibdiyya da Dr dollars suka nufi kansa suna masa magana. Hajja qibdiyya na shafa kansa. Yayinda Dr dollars ya ke gyarawa Anees din wandok jikinsa daya tattare wajen kafafuwa...
"Kici abinci Nawraah karya huce"
'tohm Mami"
Nawraah taja kujera ta koma gefe can ta bude abincin tana ci. Da farko kamar ta amayo da shi haka takeji. Don wani irin taste ne taji abincin ba irin Wanda ta saba ci ba.
Sai datayi loma ta uku ta fara jin dadin abincin. Ta tuno Amnah da suna tare da tuni da ita zasu cu. Ko hamma ashfeef.
"Wai yau itace a kasar turkiye.... Yayinda ashfeef ke wata kasar shima.? Sun samu kwanciyar hankali da nutsuwa. Abunda Saka rasa shine jigob rayuwar su Wanda har abada duniya ba zata taba musu dadi ba sai dai su bibiyeta a haka... Wato iyayen su... Malama Hindu da Mallam Junaidu. Da Kuma babban wansu Hamma ashfeef..
"Allah ya muku rahama.. ya sa Kuna aljannatul firdaws aameen"
Ta fada ahankali tana goge hawayen daya zubo daga idanun ta ..
Knocking kofar akayi. Nawraah ta mike ta bude kofar. Likitocin ne suka shigo su uku dauke da wani babban silver tray haka da wasu magunguna da allurori akai..
"Sannun ku Dr"
"Yauwa babanmu.. ya jikin nasa da sauki?"
"Da sauki Alhamdulillah har mun fita mun sayo abinci, mun barshi da matarshi tace komai kalau"
"Yayi kyau" likitan ya fada . Dake cikin harshen turanci suke magana.
Wajen Anees suka nufa. Suka dagoshi. Suka sanya wani karfe ta bayansa. Robar bakinsa suka zare sika wullar a shara..
Wani ruwa suka dauka a roba, aka zuba magani cikinsa suka sashi ya kurkura bakinsa da shi..
Sannan sukayi masa allurori aka sanya wani ajikinn wani ruwan yana shiga jikinsa...
Sai magani da suka bashi ya hadiya kala biyu. Sannan sika sake dubawa dinkin nasa komai kalau.
"Yauwa Alhamdulillah... Sai magana ko Anees?" Likitan daya ya fada yana murmushi
Anees ya kada kansa alamar eh. Kansa akan Nawraah yace,
"Naji sauki ai Dr"
"Kana dai kan saukin Anees" Mami ta fada
"Akwai cigaba sosai mashaa Allah. Don haka daga gobe inshaa Allah zai fara cin abinci. Sannan Kuma kada Kumanta mutum daya ne zai zauna dashi. Kafin jikin yakara sauki"
"Toh Dr inshaa Allah. Yadda kache hakan za'ai"
Futa likotocin sukayi daga dakin. Dai dai sanda Nawraah ta karasa cinye abincin nata Tasha ruwa tana hamdalah.
Dr dollars ya dubi agogon dake wutsiyar hannunsa yache,
"Kuje ko kar dare yaja sosai."
"Ah zaka zauna abban su? Da har zan zauna ma tunda Kai ma ba dadi kake jiba"
"No karki damu na wartsake ai. Kuje din Allah ya tashe mu lafiya"
"Auta sai da safe?" Hajia Qibdiyya ta ce da Anees. Tamkar ya fasa kuka haka yaji...
Shi yafuso abar masa Nawraah..
"Ya akai ne auta?" Hajia Qibdiyya ta sake tanbayar shi
Ya sanya hannu a bayan keyarsa yana sosawa yace,
"Na dauka dika... Zaku zauna"
Hajia Qibdiyya tayi murmushi tana girgiza Kai tache,
"A'ah... Sai ka warware duka inshaa Allah. "
Nawraah tayi hanzarin zuwa kofa tasa hannunta akan handle din Anees ya kirata yana wani hade rai,
"Zo nan..."
Nawraah ta juya bayan ta, ta dauka da wata yake. Sai Kuma ta tuna su kadai ne a dakin ta dube shi tana nuna kanta
Ya kada Kai. Alamar eh da ita yake
"Zo kwi sallama Nawraah" cewar hajia Qibdiyya
Nawraah da gaba daya gwiyoyin jikinta sunyi sanyi don ta kara tsorata da lamarin na Anees don da kunya tayi gabas yamma yayi..Ashe..
"Sai da safe" ta fada kanta a kasa
"Gyara dankwalin ki da mayafin...haka" ya karasa fada yana jan dankwalinta ya rufe sumar gashinta data futo
Daman tundazu yake aika mata harara da drs din suka shigo ashe ashe abunda yake Kona masa rai kenan. Yaja mayafin nata ya rufe gaban kirjinta sosai zuwa bayanta...ita bata masan gashin nata ya fito ba. Kuma ya fun mayafin ya sauya .
Nawraah ji take tamkar kasa ta tsage ta fada. Agaban surikai wannan abun kunya.
"Yauwa to muje .. to auta ai da safe"
"Tohm Mami" ya fada yana gyara yadda yake a zaune
Dr dollars yaja kujera gabansa ya zauna yana dubansa
"Sannu kaji"
"Tohm Abba"
Hajia Qibdiyya da Nawraah suka fita zuwa harabar asibitin motoci gasunan jere harda na haya.
Suka kira direba daya ya dauke su. Hotel dinsu ya Kai su. Nawraah Allah Allah take su karasa. Hajia Qibdiyya ta nuna mata dakin da zata zauna
Nawraah ta mata sai da safe ta shige cikin dakin kunya duk ta cinyeta. Tabbas Anees ko kadan bashi da kunyaa
Sam ta kasa hada idanu dasu Mami tun farkon sunbar da ya mata a hannu ya zuwa yanzu daya saka hannuwansa ya gyara mata dankwali da mayafi..
Lalle kishine dashi babba ma kuwa...Tun ba'aje ko'ina ba?
Haka dai tayi alwala tayi wanka tayi sallar nafila tabi lafiyar gado ta kwanta ba jimawa kuwa bacci ya dauketa mai nauyi saboda matukar gajiyar da tayi....
_ADVERT👇👇_
_YERWA INCENSE AND MORE_
_(DUNIYAR KAYAYYAKIN KAMSHI MASU MATUKAR DADI DA KAMA JIKI, GIDAH, KAYA DA SAURAN SU)_
_INA MA'ABOTA TURARE? KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE_
_TSAFTA KUMA TANA CIKIN IMANI… TOH KU MAR-MATSO KUSA_
_MUN KUMA ZUWA DA HAJAR KAYAYYAKIN_
_*YERWA INCENSE AND MORE*_
_DOMIN SAMUN ZAFAFAN TURARUKAN WUTA NA GIDA, KAYA, JIKI, TSUGUNNO, GASHI... AKWAI KHUMRAHS MASU DADI YAN BORNU, CHADI, SUDAN DAMA SENEGAL, AKWAI OIL PERFUMES, DA TURARUWAN MOPPING DANA WANKA DANA WANKI DANA GADO DA KUJERU DA BANDAKI DA DRAWER DA MOTOCI.._
_AKWAI MAN GASHI NA FESAWA ME SA KAMSHI DANA KITSO. AKWAI KAYAYYAKIN KAMSHI DANA GYARAN JIKI SOSAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA. •_
_ADIRESHI: KANO.. AMMA SUNA TURA KAYAN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE..._
_INGANCI KYAU RAHUSA DA DADEWA A GIDAH DA KAMSHI SAI KAYAYYAKIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE_
_NAMBAR WAYAR SU: 08095215215, INSTAGRAM/THREADS/TWITTER:yerwaincense_and more_
_YOUR NUMBER ONE STOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS... THEY 'VE GOT YOU AND YOUR HOME COVERED_
_K'K'J_
_(M/W/S)_
_BOOK TWO_
_✍️:MX_
_47_
:::::::::
****Suna idar da sallar asubahi suka yi wanka itada hajia Qibdiyya. Daga nan Kuma maaikatan otel din sika kawo musu na karin kumallo.Bayan sunci sun koshi ne suka nufi asibiti Kai tsaye.
Nawraah ta shirya tsaf cikin wata tsadaddiyar laffaya Mai matukar kyau da tsada.
Abayar na daga daga cikin wadda hajia Qibdiyya ta sassayo mata alokacin da zasuyi tafiyar.
Ba kadan ba Nawraah tayi kyau. Ba kwalliyar da tayi sai kwalli data shafa da Kuma man lebe fari data goga a labbanta.
Hajiya Qibdiyya tayi knocking dakin da Anees yake jinya. Sannan daga bisani sika shiga ciki bakunan su dauke da sallama.
Dr abubukhar da Anees suka hada baki wajen amsa sallamar tasu...
Hajia Qibdiyya ta fara gayshe da mijin nata sannan ta nufi wajen Anees dake kwance idanunsa na bin Nawraah da kallo tun daga kan kafafunta da suka sha lalle ja ta Saka takalmi baki Wanda yayi matukar Mata kyau. Kafafun nata sun karawa takalmin kyau.
Hajia Qibdiyya ta daga kanta tana dubashi.. Anees ya gaysheta yana rike hannunta.
Nawraah ta karasa Dan gefe ta tsugunna ta gaysheta da Dr abubuakhar dollars sirikin ta, ya amsa fuska dauke da murmushi a sake..
Kanta na kasa tache,
"Ina kwana? Ya jiki ? Allah yakara sauki"
Anees yayi kicin kicin da fuskarsa bai amsa ba. Hajia Qibdiyya ta dube shi tana duban Nawraah hadi da nuni da ita,
"Nawraah na gayshe ka tana duban jikin ka bakaji bane?"
Yamutsa fuska yayi yana satar duban Nawraah yace,
"Mami bata ambaci suna na ba fa"
"Toh dole ne sai ta kira sunan ka ta gaysheka ? Haka akeyi ne? Tunda dai kasan a dakin nan Kai kadai ne majinyaci Kuma ta gayshe da abban ku da fari. Ai kasan da Kai take. "
"Hakane, afuwan"
Ya fada yana kokarin mayar da kansa gefe Mami ta sake yin masa magana
"Baka amsa gaysuwa da tambayar jikin naka da tayi ba. "
"Alhamdulillah..."
Ya fada yana karkatar da kan nasa gaba daya... Nawraah ta mike ta koma kujerun dake gefe ta zauna..
"Kina bukatar wani abun ne Nawraah?"
"A'a mami"
"Idan akwai abunda kikeso dai ki magana kinji ko meye"
"Tohm Mami inshaa Allah"
Anees ya sanya hannunsa daya yana girgiza kansa ya ce,
"Abba, Mami"
Suka amsa da
"Naam" a tare... Dr abubuakhar dollars ya Kara da,
"Wani abun kake bukata Anees?"
Anees ya girgiza kansa yace,
"Ina marwaan? Suma suna asibitin nan ko wata kasar?"
Dr abubuakhar dollars ya juya ya dubi Mami dake kusada Anees.yayinda itama kallon nasa tayi sai Kuma ta juya ta kallo Nawraah da kanta ke a kasa"
Anees ya sake numfasawa yace,
"Na tuno sanda muka hango tahowar su shida jamian tsaro. Ciwon dayaji da yawa ne? "
Nanma hajia Qibdiyya da Dr abubuakhar sukayi shiru. Kowannen Su tunanin da yadda zai gaya masa komai s. Gashi bashida lafiya basaso a tayar masa da hankali..
Shirun da sukayi ne gaba daya basu ce komai ba ya sashi sake tanbayar su da,
"Taya akai marwaan ya bari aka aura mun Abar kaunar sa Nawraah ? Bayan kowa yasan irin kauna da burin dayaci akanta na aurenta, Meya faru? What's happening ?"
Dr dollars ya mike ya nufi gaban gadon yana duban Anees dake kwance ya riko hannunsa yana yace,
"Meya faru ne kaketa wadannan maganganun haka?"
Anee ya dube su zaiyi magana hajia Qibdiyya tache,
"Haka gaisuwar matarsa ma bai amsa ba. Wani sabon atitude ne ga yana bayarwa . Ko magani ne ko allurori ne sike sashi"
"Definitely. Baari a kira doctor din yazo ya sake duban shi"
Anees yayi murmushi jin maganganun da suke fada. Ya daga Kai ya sauke akan Mami yace,
"Mami"
"Naam Anees"
"Abba" ya fada yana duban Dr abubukhar
"Naam Anees. Wani abun ne? Ko kan kane yake ciwo"
Anees ya sake sakin tattausan murmushi kafin yace,
"Ba sai Kun kira likita ba Mami kalau nake... So nake nasan dalilin dayasa aka hada aure na da Nawraah. Da babban dalilin dayasa marwaan ya amince aka aura mun, sannan Taya akai Nawraah ta amince aka daura auremu. Bayan tarin kiyayyar da take mun. Inason nasan meysaa. Kar ku boyemun komai. Domin rashin maganar shike sakawa zuciyata radadi. Na rokeki da girman Allah kada ku boyemun.."
Hajia Qibdiyya ta sauke nannauyar ajiyar zuciya mai dauke da tarin amsar tambayoyin da Anees yayi musu. Amman bakinta Sam ya gazaa furta bayyana komai. Ya mata nauyi matuka.
Don haka ta Dan kallo Mai gidanta Dr dollars da suka hada idanu
"Anees ka rufe ido kayi bacci Dan Allah. Da alama wani side effect din maganin ne yake damunka ko allura. Bari dai akera su. Ina wayar ne kira likitan"
Ya daga wayar da ake kiran doctors din idan emergency issues ya taso. Anees ya daga hannu ya riko na Dr dollars yana girgiza Kai. Hawaye masu matukar dumi na zuba daga idanunta.
Jikinsa har wani rawa ya farayi yana zillo yace,
"Kada ka kida kowa Abba. Dukkan ku boyemun kawai kukeyi... Amma marwaan ya rasu ko? Marwaan ya rasu ne shysa aka aurawa Nawraah ni. Marwaan ya rasu ne shysa naga banganshi Tare da ku ha. Marwaan ya rasu tabbas shi yasaa kuka kasa cewa komai duk tanbayar da nake. Yanzu sun kashe min marwaan? Innalillahi Wa inna ilaihi rajiun "
"Dena kuka Anees. Wayace maka marwaan ya rasu uhm? "
Anees ya kadaa kansa hawayen nata zuba daga idanun sa yace,
"Bakwaso ku gayamun ne don kada na tada hankali na. Saboda halin da nake ciki .. Amma tabbass marwaan ya rasu. Innalillahi Wa inna ilaihi rajiun. Subhan'Allah. "
"Kayi hakuri Anees ... Ba Dan wani abun aka boye maka ba. Sai Dan halin da kake ciki. Tunda Kai ma coma ka shiga baka farfado ba sai bayan munzo nan kasar ta turkiye...sun sassare ka yayinda shi Kuma sika harbe shi. Tun Muna yankin bunza ma da aka kaiku aisibti shi ya cika... Batun aurenka da Nawraah Kuma zamu iya kiran sa daga Allah ne. Dubada bamu taba sanin kana kaunar taba sai da muka dauki wani littafin ka da wayarka da hirar chatting dinku da marwaan din. Sannan itama a tata wayar ta bamu voice notes mun saurara ne daga maganar auren ku da kaunar ta da marwaan din yayi yace ko bayan ransa da sauran su. Sannan kana dauke da cuwon damuwa ya fara maka illa ma Wanda daga bisani likitoci ma suka sake fadar damuwar taka,sai muka nefi Nawraah. Muka roki alfama awajenta . Ta Kuma amince zata aureka.. sai Kuma abun farinn ciki shine an kama Alhaji sambaso don yanzu hakama ancemun surutai kawai yake na daga abubuwan daya aikata, donya samu tabin hankali ma yana gidan yari. Sannan matar sa itama tana gidan yarrin Amma da Tara zaa saketa, yayinda mata ga bappan Nawraah da ta fada hada Kai dasu .itama tana Tara da zaman kurkurku na Dan wani lokaci. Kai na karkare maka zance dai duk wani Mai hannu da ruwa da tsaki acikin lamarin hukuma ta cafke su. "
Anees ya kasa ceaa komai. Bayan wani lokaci kankani Kuma ya fashe da wani irin Kuka Mai dauke tarin damuwa. Yanayi yana jijjiga Kai yace muryarsa na rawa yace,
"Innalillahi Wa inna ilaihi rajiun. Marwaan fa. . Marwaan fa Mami. Na shiga uku. Marwaan fa amini na, abokin shawarata, dan uwana Subhan'Allah "
Su hajia Qibdiyya da Dr abubuakhar na bashi baki suna ce masa addua zai yi masa ba kuka ba...
Anees ya dade yana kuka yana maganganu , har lokacin shigar likotociin sa yayi, suka shiga suka duba abunda zasu masa. Kuma suka sarqafa masa allurar bacci nan da nan kuwa yayi baccin
Hajia Qibdiyya da dr dollars na maimaitaa zantukan. Nawraah na jinsu a gefe . Hawaye ne ke zurara mata na tunowa da tayi da marwaan....
::;;;
Hakika lamarin ya daki Anees sosai, don sai da ya yi doguwar suma bayan ya tashi daga allurar da suka masa ta bacci...
Yayita surutai gwanin ban tausayi. Ya dau tsawon lokaci na sati biyu kafin komai ya lafa masa. Don har yana iya tashi ma da sandunan karfe ya tsaya...
Hajia Qibdiyya da Dr dollars su biyu suka zauna awajen sa suna jinyar sa . Nawraah ce Mai sayo abinci yanzu tasan kan gari tana Kuma rage wasu abubuwan. Da daddare take tafiya can hotel dinsu ta kwana.
Yayin da bayan asubah daga gama kintsa komai sai ta koma hotel din nasu...
Anees dai daren ranar ya badewa idanunsa kasa. Yana muza yatsu ya dubi Mami yace,
"Mami..."
"Naam auta"
"Bacci kikeji Kalli idanuwan ki. Hakama Abba"
"Ba wani bacci ai Muna samun bacci Anees.."
"Amma ai da wahala"
"Wadannan maganganun da kakeyi na meye?"
Ya dan sauke zuciya yana satar kallon Nawraah da tayi kicin kicin da idanu yace,
"Yarinyar nan yau ta zauna itama ta kwana. Ku kuje ku huta"
Hajia Qibdiyya ta bude baki zatai magana Dr abubuakhar dollars yace,
"Hakane ya kamata Kam. Daughter yau sai kiyi hakuri ki kwana kinji?"
"Tohm Abba inshaa Allah" Nawraah ta fada kanta a kasa.
Hajia Qibdiyya ta dankarawa Anees harara tana duban Nawraah tace,
"Zaki kwana din habibty?"
"Eh Mami ba komai"
"Allah ya miki albarka... Kinji"
"Nagode Mami"
Anees ya daga hannu ya sosa keyarsa yana gyara kwanciyar sa sosai akan gado .
"Mariyah muje ko?"
"Tohm Abban su"
Hajia Qibdiyya ta mike ta sakala jakarta. Ta matsa wajen Nawraah tana sake sanar mata komai idan emergency ya tashi.
Nawraah ta musu sallama har bakin kofa suka tafi. Yayinda ta koma ta zauna akan kujera tana danna wayarta...
Anees ya sauke nannauyar ajiyar zuciya yana gyara saitin kwnaciyarsa. Idanunsa na kanta yace,
"Naw.....Rahhh..........
KUZO MU HADA KARFI DA KARFE MU DANDALI KUDI A TELEGRAM... WANDA NOTCOIN TA FASHE DASU ZASU BAMU LABARI. YANZU KUMA GA HAMSTER KOMBAT YAR UWA KINA ZAUNE IDAN BAKYA AIKI KI RIKA TAPPING NAN DA NAN KIGA KIN TARA COINS DIN KI. IDAN TA FASHE KEMA KI DANDALA...
https://t.me/hamster_komBat_bot/start?startapp=kentId5210987055
Play with me, become cryptoexchange CEO and get a token airdrop!
💸 2k Coins as a first-time gift
🔥 25k Coins if you have Telegram Premium
KWANKWASON JIMINA!!!
(MAI WUYAR SHAFAWA)
💞
MX🧕
PG:48.
°°°
Nawraah tamkar zatayi shiru ta kyaleshi. Ta fasa, inda ta daga kanta ta saukar akansa.
Idanuwan su suka sarke da kallon juna. Tayi azamar janye nata idanun ganin yadda yake wani lumshe idanu yana bude su akanta .
"Naam" ta amsa shi..
"Ki kiramun Drs kinji ...?"
Mikewa tayi da sauri ta nufi inda yake taja kujera ta zauna. Gaba daya agigice take. Idanuwanta sun furfito cikin firgici harda in Ina tache,
"Wani. ... Wa... Wan.... Wani abunne ta faru? Inna ne. Ina ne ke maka ciwo?" Hankalin ta duk ya tashi..
Anees ya saki tattausan murmushi ya kamo hannunta ya sanya akan kirjinsa yace,
"Nan dina ne ke mun zugi... Yana mun radadi... Yana mun zafi .. yana wata iriyar buguwa tamkar zai fado kasa... Raina ba dadi Nawraah, Raina na yin wani iri Nawraah... Numfashi na...iskar Numfashi na yana sauka wata iri Nawraah... Yanamun tamkar zai janye Nawraah.... Gangar jikina rawa take saboda rashin kyautatawa ta.. Gabobi na sun min nauyi Nawraah...nauyin da Kai na yake yana barazanar fadowa.. idanuwana na zubar da hawayen rashin kyautatawa, yayinda kunnena ke radamun ni din ban kyauta ba... Bakina yana nauyi Nawraah. Labbana sun gaza furtawa.. Ina cikin wani yanayi,,,Ina cikin wani hali Mai wuyar fada. Inaso ki kiramin likita don yazo da kansa ya kira su Mami. Domin halin da nake ciki yanzu Allah ne kadai zai iya yafemun. Sannan sai na nemi yafiya awajen ku. Domin bazan iya sake hada idanuwa da ku haka ba. So nake lamarin ya wuce... Kinji?" Ya karasa yana zubar da hawaye masu matukar dumi da ban tausayi
Nawraah itama jikinga sai yayi sanyi ta bi ilahirin gangar jikinsa da kallo tana saukewa akan idanunsa dake tsiyayar da hawaye.
"Menene? Inane yake maka ciwo?wadannan maganganun dakake ta fada meya kawo su? Meke damun ka? Ka gayamun Dan Allah... Kaga amanar ka su Mami suka ban"
Anees ya goge hawayensa da dayan hannunsa yace
"Ni Mai laifi ne Nawraah. Wadanda nake bukatar likitoci suzo yanzu su kira iyaye na su sanar dasu. Suma na nemi yafiyar su"
"Bangane ba. Ni bare ce da