Showing 66001 words to 69000 words out of 69829 words
Chapter 23 - KWANKWASON JIMINA BOOK 2 COMPLETE BOOK 2 hausa novel
zeyi kukan farin ciki ko dariya yache,
"Nagode sosai. Allah ya biyaku da aljanna."
"Aaaameen jam'an idan Nawraah ta tashi ka ce Muna gaysheta idan mun karasa zamu kira waya inshaaa Aallah"
"Tohm Mami inshaa Allah... Anees ya fada cike da farin ciki ya zube akan gado yanata murmushi yana Murna harda daga kafa... Ya matsa wajen Nawraah tana dubansa tana lunshe ido, yache,
"Wifey da ga ni sai ke muci karanmu ba babbaka. Ya fada yana gyara mata kwanciya a jikinsa...
Ko bayan ta tashi take tanbayar Anees Ina su Mami har yanzu basu zo ba.
Anees yayi murmushi yana gyara zaman rigar sa yace,
"Sun koma su... Mu Kuma zamu bi bayan su"
"Bangane ba Ina sika koma hotel?"
"No can dai gidah. Sun koma.... Sai mu lovebirds"
Nawraah kunya ta isheta. Taja bargon ta rufe har kanta tana tukwikiyewa..
Anees ya sake matsawa dad da itan yache,
"Na baki Kai na, Raina, zuciyata Kai dama gangar jikina Nawraah. Dadin da kika shayar Dani baa magana. Sai dai nace Allah ya Saka miki da alkhairi. Yadda kike gwarzuwa Mai dauke da zumar dadi mai dandanawa, wifey na ma rasa ta Ina zan fara... hakama kedin komai naki daidai ne cute, and sweet Omo yadda zan bayyana miki..
Jin rashin kunyar da yake rada mata ne yasa ta saki yar kara tana rufe fuskarta gam
Anees yayi murmushi ya koma gefe kawai shima yana tunnaninn dadda'daan daren nasu da bazai taba goge masa ba a kansa..
°°°°=°
Sabuwar rayuwa suka shiga yi. Ko da aka sallame su daga asibiti. Daman vvip hotel din da su Mami suka kama baiyi expiring ba.
Don haka akwai sauraron wata uku ragowar zaman su, plus wasu kwanakin da aka biya musu, Anees ya wartsake ragal. Soyayya ba kama hannun yaro haka sukeyinta tamkar cin kwan makauniya...
Wata ukunnan da sukayi agarin Nevsehir dake cappadocia ta yankin Istanbul.
Soyayya ce sun zuba ta fiye da yadda alkalami zai rubuta. Suna Kuma kaunar junan su tamkar zasu cinye juna mashaa Allah...
Sun zaga gari ko'ina sunyi touring na turkiye sosai. Don har Istanbul suka je suka zaazagaya sauran garuruwan irin su Cyprus da sauran su...
Hajia Qibdiyya dake gidah kuwa tanata shirya rantsattsin lefe na Nawraah. Gidan da mahaifin su ya bashi ma shima anata gyarare shi an zuba furnitures da komai..
Bayan sun waiwayo Nigeria ne. Yan uwa tamkar zasu hadiyesu. Ranar da Nawraah taga lefenta sai datayi kuka sosai na farin ciki.
Lefen nan ko gidan shugaban kasa aka kaishi sai anyi santin sa.
Hakama gidan da zasu zauna, komai yayi acancan na masu kudi
Tuni Nawraah ta dakko Amnah ta dawo da ita gabanta. Domin idan ta kalleta fuskar mahaifiyar su marigiyya Hindu kawai take gani ko a baya. Dan zaman da sukayi a cappadocia ma ya sanya ta sake maraicin kanwartata sosai....
Dare ya zama safiya safiya ta zama rana, rana ya zama yammaci lalle Allah qadirun ne aka manyashau..
Rayuwar kowane bangare nata tafiya... Gwanin ban shaawa. Alhamdulillah
Daga Kuma kasar wajen ne inda Anees yayi karatun PhD wato Manchester suka nemi yarjewar sa don ya dawo karkashin kasar su da iyalinsa su fara aiki sun dauke shi aiki da gidah da mota da scholarship na yaransa da dukkanin komai...
Nawraah dai batasan komawar su wata kasar, Tafusn Naduka musaman sabida yanuwa datake dasu, gasu Mami ma.. Amma barin kasar da garin baki daya bataso munsaman da kaburburan iyayen ta Dana dan uwanta yana burnin naduka..ji take kaman tana tare dasu ne Amman sun dan mata nisa...
Ta Kuma Dan fara damuwa arashin samun ciki dabata dashi, duk da dai ita kadai take damuwa, iyayen mijinta da yan uwansa basu taba mata gori ba. Amman ita tana kokarin son tasamu ciki, Musanman ganin dukkanin yan gidan marayu kawayen su da sukayi aure sun haihu tuni, Su wasila da Raudah da faty... Nawraah ta tsaya akan auren su sanda zasu yi, Ta Kuma sake fadada gidan marayun da gyare gyare da abubuwa. Domin ba zata taba mantawa da gidan marayun da suka karbe su a alokacin da duniya ta juya musu baya. Ciki harda yan uwan mahaifin su da suke gani a matsayin nasu iyayen Amman sun fito since basa kaunar su ba zasu rike su ba. Dukkuwa shekarun baya akai hakan komai ya wuce.... Amman abunda suka musu ba zasu taba mantawa ba!!!
MX🧕💜
*_KWANKWASON JIMINA!!_*
_(MAI WUYAR SHAFAWA)_
🦩🦯🦾
_✍️: MX_
*_ZAFAFA BIYAR 2024_*
_👇_
*_wattpad: mssxoxo00_*
*_arewabooks:mssxoxo_*
*_BOOK ONE: COMPLETED☑️_*
*_BOOK TWO: COMPLETED☑️_*
*_PG :50_*
*_FINALE/KARSHE_*
_*(COMPLETED BOOKS/THE END/AN GAMA LITTAFIN DUKA 1& 2 KAWAI NE DAMA BOOK DIN)☑️*_
____
To haka rayuwar ta cigaba da garawa, yau da dadi gobe akasinta... Kowanne bangare na cikin koshin lafiya.
Farin ciki da kwanciyar hankali hadi da tarin arzuka sun wanzu a gidajen baki daya
Musanman gidan Anees Abubakhar dollars da Mai dakin nasa Nawraah...
To daman komai lokaci ne Kuma sai Allah yaso a sanda yake so yake amincewa da dukkanin kowa da komai..
Nawraah ta takurawa kanta rashin haihuwar da batayi. Gashi sun jajje asibiti ance kalau Allah ne bai kawo ba, Amma itada Anees din komai nasu ma lafiya ba matsala yake..
Damuwar tata ta karu ne alokacin da Layla ta haihu da namiji aka sanya masa sunan marigayi bappah Junaidu suna cewa dashi junior...
Nawraah kwananta biyu agidan Layla suka sadaa zuminci sosai bayan suna ta koma nata gidan dake wata gra...
Ashfeef da Ahmad ma an Kai kudin auren su don har an daura auren ma dake basasan taro a biki. Don haka sukazo kasar bayan wani lokaci Kuma sika koma da matan nasu can kasar wajen da suke ...
Ashfeef ya auro can tsatson su na nesa dinnan dake yankin bunza. Yayinda ahmad ya auro Mai awarar nan dai da Nusaiba tace batasonta.
Nusaiba ta fito daga gidan yari ta koma can Kauyen su dake yankin bunza can garin su. Kowa yace ba zai aureta ba yaji munanan halayen ta...batada aiki sai bin yaran kauye tana duka. Ga bakar sata data keyi. Tana fiffika, zawara yan uwanta mata suka koya mata hankali da ruwan tulu suka zuba mata karatun ta nutsu ko su koreta daga garin...
Bappah Auwalu ya sake samun kwanciyar hankali da nutsuwa... A can gidan sa shida matar sa.
Yayinda Nawraah ta sayi nasu na da Wanda mutumin ya sayar ta sake saya awajen sa..
Ta samo wata mata da basuda matsugunun zama. Tace tabasu har Sanda sika mallaki nasu. Lokaci zuwa lokaci takanje gidan nasu ta zauna tana tuno rayuwar su ta baya ... Komai yanzu ya wuce ya zama labari..
Alhaji sambaso ya samu tabin hankali. Shi kadai yake surutai..An yanke masa zama a kurkuku na shekaru da yawa sannan ga aiki da ake sanya shi na dako a kurkukun da ebo ruwa. Bashida aiki sai yayita zama shi kadai yana cewa,
"Ni na kashe uwa da uban da dan nasu... Na Kuma kashe 'da na marwaan. Marwaan fa. Na kashe marwaan jamaa... Kuma sun sace mun dukiyata dana kwace da kyar...."
Wani lokacin Idan ya hana yan dakin gidan yarin nasu bacci da surutunsa sai su tashi su lakada masa na jaki. Bashida kowa bashi da
yan uwan dake kula dashi ko su kawo masa ziyara, kowa ya rabu dashi.
Domin da a baya daya keda kudi bayayiwa yan uwansa na can kauye . Don haka kowa ya manta dashi. ...
Dr bintu an saketa daga gidan yari ta samu ciwon nakasar hannu daya baya aiki. Sannan idonta daya ma ya shanye da daya take gani .
Batada aiki sai kuka ta koma gidan su wajen
Yan uwanta. Suma basa kulata . Kowa yana kyamatarta tamkar yadda takeyi a baya..
Daki daya aka bata itada yarta lily. Bandaki ma na tsakar gidah Kuma na kasa. Sai hamamin doyi ne yake tashi. Har layin shiga sukeyi. Sannan ba ruwa sai ta ebo Wanda zasuyi amfani dashi a layin borehole na tuka tuka....
Dr bintu kullum sai tayi hawayen dana sanin rayuwar daga girba a baya. Yanzu komai da take kokarin yafaru akan bintu da iyalinta shi ya maye nata gurbin.
Sun rasa dukiya. Mujin datake so ya haukace, An kwace dukiyar tasu dama ta haram ce. Daidai da cokali babu. Amaryar da Alhaji Sambaso ma yayi tuni ta shallare tabar gidan daman batasan kudin damfara bane tarin arzikin na su. Don haka hukuma bata tafu da ita ba..
Acikin 'yaya biyu da Allah yabata jal a duniya.. marwaan babban dansu namiji ya mutu sanadiyyar mijinta Kuma mahaifi ga mamacin akan neman duniya.. gidajen da take takama dasu harda Wanda take ciki da sauran kadarorin an kwace dika Ashe kudin Haram ne ya cinye kwangilolin mutane harda na aminann sa dr dollars...
Rabon dataci kaza ta manta. Ga lily yar tata ta zama mai budadden idanu kullum futa take da dare ta dawo da safe.. rayuwar Dr bintu na cikin wani hali na tausayawa. Amma koma menene itace ta janyowa kanta rayuwa take koya Mata hankali, take girban abunda suka shuka a tun kan aje lahira..
°°°°°°
DR. ANEES ABUBKHAR DOLLARS AVENUE:
Nawraah na zaune tanata tunani ita kadai. Amnah kanwarta tayi bacci a dakin ta dake gidan.
Ta baza turaren wuta na kamfanin tiraren Yerwa incense and more Mai suna mukammaria.
Tiraren wutar nan ya hadu fiye da yadda alkalami zai rubuta. Sunan sa mukammaria ne. Ya bade dika gidan da kamshi..
Gashi ita kanta nawraahn. Kamshi ne yake tashi daga nata jikin da kayanta data turara ta shafa hair khumrahs da kullaccam ta jiki ta Kuma shafa khumrahs na aljaab, tayi tsugunno Dana turaren sa.
Agogo ta kalla ta mike ta dauki turaren parlor na kamfanin Yerwa ta feshe ko'ina. Ta shiga daki nanma ta tarar beedsheet din ya gama turaruwa da turaren kayan gado, nan ma ta shimfide gadon dashi ta feshe turaren bed spray da labulaye.. ko'ina sai kamshi ne ke tashi
Taci kaya cikin doguwar riga bubu ta atamfa gaban rigar an yanka shi v style . Sannan daga karshe ma aabude shi. Dinki yaci sunan dauke hankalin Mai gidah. Hakama ta ci parking tayi dauri gashinta ya tullo ta kasa.
Ga abinci nan akan dinning ta jere komai ta kamalla. Door bell ce tayi kara. Ta mike da sauri tana gyara rigarta da tafiyarta.
Tana bude kofa yayi sallama ta amsa. Ya duaketa Chak bai direba sai kan babbar kujera...
Ta dube shi tana murmushi. Ya sakar mata sumba agefen fuskarta da jan labbanta. Ta dauki brief case dinsa kenan ya hanata ta hanyar rike hannunta ya ajiye brife case din..
"Kinji kamshin da ke tashi daga jikin ki? Gashin ki? Kayan ki? Dama gidan baki daya?"
Nawraah tayi murmushi kanta a kasa Anees ya dago habarta yana tsosan lebanta kamar alawa ahankali cikin kwarewa yace,
"Habibty...Ba zan iya musalta adadin yadda sonki yake lunkuwa a zuciya ta ba a cikin kowace rana. Ina son ki matata. Babu wani abinci da yake yi min dad’i a baki na matu’kar ba ke kika girka shi ba. Ina kaunar ki Ina kaunar ki Ina kau ...
Ya Kai bakinsa kan ababen dayafu kauna ajikinta. Nawraah tashiga sauke numfashi tana shafa kansa...ahankali tache
"Zakaci abinci ko wanka Wanne zaka fara? Sannu da dawowa habiby.. fatan kaje kalau ka dawo kalau? Allah yabada albarka akan abunda akaje nema. Allah Kuma ya cigaba da shiga lamuran ka ya iya maka..."
Anees ya daga kansa yana dubanta yana murmushi tache,
"Aameen baby tah, Bari na gama wannan tukunna sai na dora da sauran ..".
Nawraah bata Kara cewa komai ba saboda jitayi yana kokarin mayarda
Ita wata duniya sai surutai yake shi kadai yache,
"Da zaki iya ganin irin halittar da ubangiji yayi maki, da kin gane cewa ke ta daban ce a cikin mata hadaddu. Kyawun ki ba irin nasu ba ne habibty"
Ya Kai sumba gefen kunnenta da kofar kunnenta... Yana dubanta idanuwa a shanye yache,
"Gobe ne tafiyar mu fa "
"Haba dai?" Nawraah ta fada cikeda mamaki
Ya kada kai alamun eh cikin tabbatarwa yace da ita,
'idan na gaya miki caza kiyina sake bada lokaci. Ni Kuma so nake mu tafi"
"Ina alfahari da samun ka Habibi. Allah yasa komawar mu can dinne mafi alkhairi.. hasken idanu na, annurin rai na. Miji na, uban ‘ya’ya na inshaa Allah...Tabbas samun miji irinka shi ne abun da mata da yawa suke fata. Na same ka hakan ya sanya nake jin tamkar na fi kowace mace sa’a a duniya. Ina kaunar ka sosai"
Anees ya sake sumbatar labbanta yana rungumeta tsam a jikinsa sai daya rungumeta sosai sannan ya sake kissing goshinta. Ya daga fuskarta yana dubanta yache,
"Ina abincin?"
"Yana dinning ko a kawo nan?"
"No muje..." Ya daga ta yakai dinning din yaja kujera ya ajiyeta akan kujera. Sannan yaja shima tasa ya zauna
Nawraah tayi murmushi kawai tana kallonsa tache,
"Habjby ka bude ciki sosai zakaci abinci yau baka isa ba"
"Komai naki ai bana kin yi habibty tuni dankwali yaja hula...."
Abinciin ta zuba masa mandi rice da chicken sai patoosh salad da mango juice. Sai cake da milkshake daga gefe da dabino....
Anees ya gyara zama. Taja kujera ta koma kusa dashi. Ya matsar da tasa kamar zasu shiga cikin juna...
Tana diba tana bashi a baki da cokali. Kazar ma tana gutsira tana Saka masa a baki haka dai sai daya cinye komai tas.
Daga nan ta debe kwanukan takai kitchen nan da nan ta tattare komai . Kafin ta koma tuni har Anees ya shige dakinsa.
Ta nufi dakin tana sallama. Yana bandaki ta kwankwasa tana tanbayarsa ko da akwai wani abun da yake bukata?
Hannunta ya janyo cikin bandakin . Daman tasan wayo ze mata. A dole yasata sake sabon wani wankan..
Don a bandakin suka baza sharholiyar su Anees yasa ta masa wankan shima ya mata suka dauro tsarki. Sannan suka fito ..
Daman tuni kowannen su yayi sallah..don haka Anees ya sanya hannu ya kashe futulin dakin
Ya sunkuci Nawraah bai dureta ba sai tsakiyar gadon. nan labari ya canza. Tanata kokarin kwacewa ya hanata
"Yarinya kullum ciki matsi da dadi kike meye sirrin?" Ya tambayeta yana dubanta
"Nima bansani ba Habibi. Istighfari ne. "
"Lalle fa malamata kenan. To sai me Kuma dan akwai wani lamarin gaskia. Ki gaya mun "
"Ai ba wani abu bane kayan turaren matar nanne"
"Wai wannan ne dai Yerwa incense..Kai Mami nasan turaren ta..."
"Ya sunan su?...uhm" ya sake magana ya na yawo da harshen sa kan cibiyarta
Nawraah da baki daya ya burkita Mata lissafi har wani zillo take tache,
"Na tsugunno ne turaren da na shafawarsa...
"
"Uhm.lalle fa..dadi kan dadi..Allah daiili ya kara albarka Nawraah"
'amiin"
Haka suka sha soyayyar su kamar cin kwan makauniya.
Washegari suka kintsaa, Kai tsaye suka nufi gidan mami, da bappah Auwalu da gidan Layla... Ko'ina dai..
Mami kamar zatayi kuka bataso tayi nesa dasu. Dakyar aka iya banbareta daga jikin su..
Suka shiga mota suka daga airport sai kasar england wato garin Manchester..
ENGLAND/MANCHESTER
Abun shaawa dama already Anees yasan garin. Don haka yasan komai na kasar
Ya kaisu gidan su nacan . Amnah sai farin ciki take tana duban koina..
A ranar da suka koma meyakwan su huta sai da Anees ya faki idanun Amnah sannan yaja nawraahn suka nufi daki. Ya samu nutsuwa yanata murmushi. Nawraahn ta girgiza Kai kawai tana mamakin Anees sam ba zakace yanada halaye haka ba.... Soyayya ma tsaf zakace baisan tana amfani ba..
Haka rayuwata cigaba da garawa Anees ya samu babban aiki anan kasar Manchester na architectures, yayinda Nawraah ta samu a wani company kusa da gidah..
Rayuwar tasu gwanin ban shaawa... Rayuwa taci gaba da tafiya yadda take. Lamarin sai hamdalah kawai ..
°°°°°
Nawraah ta fara wani azabbban zazzabi kullum rashin lafiya. Anees yayi yayi suje asibiti taki.. Tache ai da yamma yana lafawa.
Dayaga abun nata bana kare ba shi kuwa ya kira babban likita tazo gidan. Likitan tayi gwaje gwajenta tatafi tace zata dawo, bayan awanni ta dawo dauke da murmushi tache ai Nawraah na dauke da juna biyu
Sheda muku yadda lamarin ya kasance ma sai mu kwana ana labari. Anees yayi farin cikin dabai tabayi ba. Harda kuka, Nawraah na tayai kukan..
Ya kira gidah ya gaya musu, da sauran yan uwan yanata fada harda su ashfeef su Layla su bappah Auwalu kowa sai da ya sani
Nawraah nata mamaki. Tundaga ranar ya dena bari ko wanke kofi tayi. Maaikata ya dakko har biyu suke musu komai.
Amnah na zuwa makaranta idan lokacin tashi yayi ya dakkota ya dawo da ita.
Bayan cikin ya tsufa nema. Mami tazo itada Layla. Da suka mata passport itama da komai suka zauna da Nawraah
Nawraah ta sha wahalar nakuda kafin ta haihu. Don da zaa mata cs ma acire cikin. Dakyar cikin qudurar Allah ta haife yayan ta biyu mace da namiji..
Alhamdulillah nan da nan aka musu huduba.. Anees yanata kuka yasanya musu sunan namijin yaci marwaan macen taci sunan marigayiya Hindu.
Dan da bappah junaid zai sakama Mami tache asa bappah Auwalu tunda an Saka junaid layla tayi. Sai bappah Auwalu da sukayi waya yace a'a asaka dai mahaifin Anees din wato Abubakhar. Dr dollars yace a'a a sanya sunan marigayi marwaan. Hakan kuwa akayi.
tubarkAllah gata iya gata don su Mami basu har kasar ba sai da Nawraah tayi wata biyu da haihuwan abbiey da ummy. Don haka take Kiran su shine nicknames dinsu takance tana tuno mahaifanta. Sunan kuwa ya bi su.
Babbar babysitter aka dakko personal ta babies din take kula dasu..jin dadi na duniya sun samu Alhamdulillah
Shekarar su daya tif kafin sukaje hutu gidah. Mami ta dauki yan biyu tatafi dasu gidanta.
Anees daman abunda yake so kenan daga shi sai Nawraah don Amnah ma tana gidan ashfeef sun kammala karatu sun yi kamfani shida Ahmad sun dawo gidah..
Ahmad ya ginawa bappah Auwalu babban gidah shida matarsa. Ya Kuma yi wani babban a yankin bunza ya sanya nusaiba . Wadda ta sakko Kai ta nemi gafarar su Nawraah da bappah Auwalu .. da ahmad din kansa da layla data kyamaci wadanda suka aura a baya...
Ashfeef ya sayi katon shago anayin abinci ana kaiwa gidajen marayu. Ya Kuma yi rijiyiyo da masallatai kan Allah yakai ladan wajen mahaifan su marigayi junaidu (abbiey) da marigayiya Hindu (ummy).
Matar sa na haihuwa ta samu da namiji ya sanya masa suna ashfeef suna Kiran sa da Hamma...
Rayuwa tayi dadi....