Showing 12001 words to 15000 words out of 69829 words

Chapter 5 - KWANKWASON JIMINA BOOK 2 COMPLETE BOOK 2 hausa novel

24 Aug 2024

8951

masa ba damuwa ay nii maganar ma abarta kawai zan iya hakura"

"Meyasa kache masa haka bayan aminin ka ne?"

Kallonta ya yi, yayi murmushin yake yace,

"A wannan tafiyar da ake ciki. Inshaa Allah daga ke ke sai yaran mu kadai zan aminta dasu. Amman kowa sai naga yadda lamarin zai fito tukunna. Kede muci gabaa da addua kawai"

"Toh Allah ya amince Alhaju Allah yabaka nasara. Amin"

"Aamin ya rabbi. Bari nayi wankan ko?"

Mikewa tayi jikinta a sanyaye. Shima ya mike yana lakuce mata kumatu,

"Haba Mariri. Bansan damuar ki fa, Zan daina gaya miki komai Allah

"Na dai na Alhaji. Kayi hakuri"

Yana rike da hannunta suka nufi bandaki ta tanadar masa komai. Tukun sannan ta koma wajen dinning tana zuzzuba masa dukkanin abunda ya dache Wanda zai iya ci..

Wunin ranar haka suka wuni a atare suna tattauna yadda zasu bullowa lamarin.


:::::::::
_HGL CHARITY FOUNDATION_

_ASSALAMU ALAIKUM WA RAHAMATULLAH!_
JAMA'A BARKANKU DA _WARHAKA... ALLAH YA SAKA MUKU DA ALKHAIRI YA BADA LADA HADI DA BIYA MUKU DUKKANIN BUKATIN KU DA KUKE FATAN SAMU AAMIN_

GODIA DUBU GA TALLAFIN DA KUKA SAKA NA CIYARWAR AZUMI
INSHAA ALLAHU WANNAN GIDAUNIYAR MAI SUNA A SAMA NA KIRAN MUTANE AL'UMMA MASU SON SAMUN LADAN WANNAN MANYAN AIKI DA MUKE SAKA RAN FARA SHI KAMAR
НАКА

1• DAFA ABINCI A RABA GA MABUKATA RANAR JUMU'AH KO A KAI RUWAN SHA GA MASALLATAI RANAR JUMU'AH

2• HAQA RIJIYOYI ACIKIN KAUYUKA DA UNGUWANNIN DA BASUDA RUWA

3• RABA KAYAN ABINCI KO KUDI GA MABUKATA
MARASA HALI

4•KAI ZIYARA GIDAN MARAYU DA KAI MUSU
ABUBUWAN AMFANI DA SUTURA IDAN DA ME BAYARWA

5• KAI TALLAFI KO ABINCI GA ASIBITOCI WAJEN
MASU JINYA MARASA KARFI..

6•KOKARIN KARASA MASALLACI KO YIN MASALLACI
AWAJEN DA BASUDA SHI...

MAI NERA BIYAR MAI GOMA DiK
YADDA HALI YA KAMA ALLAH YA HADA MU A LADAN DUKA..
JAZAKUM ALLAH BiL JANNAH..
DOMIN SAKA TALLAFI GA ASUSU

9044191709
OPAY
JAZAKUM ALLAH BİL JANNAH💜
[5/1, 7:03 PM] Hafsaat🧕💞: _K'K'J_
_(M/W/S)_


_BOOK TWO_


_✍️:MX_


_12_


:::::::::

Yana karasa parker motar sa a wajen adana motoci na dalibai dake department din nasu. Ya fito daga cikin motar tasa. Sanye yake cikin riga da wando na shadda kalar sararin samaniya.

Ya dora pcap akan sa datayi matukar dacewa da aikin dake jikin shaddar. Hannun sa na dama dauke da ruwan roba guda daya da wani littafi da pencil aciki da biro.

Ya murzawa motar key ya nufi cikin department din. Baki daya ya gauraye ko'ina da kamshin turarukan dake tashi daga jiki da kayan sa. Kai kache a kamfanin turaren Tom Ford ne.

Daga wajen wani dan karamin garden dake cikin department din nasu ya hangosu kamar ko da yaushe itada yar uwarta suna zaune a garden din da ake cswa da shi "love garden"

Ya samu kansa da zama a kujerun cikin wajen bana garden din ba. Ya seta su . Kwayar idanun sa baki daya akanta suke kamar koda yahse. Duk wani motsinta yana tare da shi..

Ya janyo gilashin ya Saka ya maze fuska Kai kache wata uwar abun daban yake yi. Littafinsa ya bude ya janyo pencil din yana satar kallon ta yana cigaba da zanata. Koda yaushe cikin zanata yake, a tafe take, a zaune take, a tsaye take, abu take ci ko sha. Komai dai da takeyi akan motsin sa ne.

Ba kadan ba tayi masa kyau cikin wata atamfa me zanen baka da ja na katuwar kujera. Ta yafa wadataccen mayafin daya amshi kalar atamfarr. Tayi kyau sosai duk kuwa da ba kwalliyaa take ba. Zallar natural beauty din da take da shi ya gauraye masa rai, zuciya da Kuma gangar jiki.

Cigaba da zanata yake sosai. Har sanda ta daga biro tana nunawa Layla wani diagram ajikin handout din da suke karatu. Yayi murmushi shi kadai yana gyara wajen tsintsiyar hannun ta da zanen da yake yi.

Ya sake daga idanun sa ta cikin glass ya dora akanta sun tashi tsaye itada Layla da alamar musu sukeyi akan wani abu na daga cikin handout din,

"Taya zan sanar dake abunda ke cikin rai na? Ta yaya?.... " ya sake tambayar kansa ahankali yana runtse idanun sa.

Kamar koda yaushe duk zanen daya mata sai ya rubuta kalamai ajikin sa, sai kache gani zatai ta karanta,

"Nawraah, Tunanin ki na dawainiya da ni a koda yaushe.. Ashe haka so yake? Ya zanyi da rai na ne? Nawraah Ina kaunar ki, kaunar da baki yayi nauyi wajen bayyanawa. Duk da nasan Ina shirirtia ne kawai domin tuni dan uwana ya riga ni shiga wajen ki.. my Nawraah, When thoughts of you cross my mind, my heart races, bakiji yadda bugun zugiyata yake ba and a smile finds its way to my lips. Ganin ki kadai ko da waiwaye ne yana samun nutsuwa sosai, It’s time to confess that you are the reason behind these joyful moments in my life... Hakika kin kawomun babban farin ciki acikin rayuwata. Duk kuwa da bakisan inayi ba. Amman tunanin ki kadai ya gamsar dani farin cikin rayuwata. " yana karasa rubutawa ya sake daga kai ya dora akanta.

Daidai lokacin da marwaan ya karasa waiensa da sauri ya janyo shi ta cikin glass ya rufe littafin.

Marwaan ya dube shi yana tabe baki,

"Uban yan boko, karfe nawa kazo?"

"Ban wani dade ba"

"Ka fara sanaar karatun kenan. Guy ka dinga hutaawa fa. Kullum kanka na kan littafi kana karatu ne oho. Shegen littafin da baa ganin cikinsa" marwaan ya daga hannu ya kaiwa littafin duka

Anees ya janye da sauri yana murmushi. Yana juyawa ya hango Nawraah sun futo daga kofar garden din. Da sauri ya juya ya dubi Anees ya banka masa harara,

"Baka gayamun ga lover ta can aciki ba. Ka barni a tsaye ni dakai, Gardin banza, Uban me zan maka?."

"Wetin man do man? Haba honey"

"Uwar ka, Allah ya isa shege. Na honey wa uban ka. " marwaan ya amsa shi yana kai masa bugu.

Anees ya yi daria ya cigaba da cewa,

"Wa kake nufi kenan?"

"Dalla can aunty zaka dinga Kiran ta Muna yin aure. Kuma ka kusa fara gayshe ta don kaji. Wannan girman kan naka ba zaka ma iyali na ba wallahi"

Anees ya mike daga zaune da yake yana kakaro murmushi hadi da girgiza Kai yace,

"Zaka tsaya kana zubar maganar ko wajenta zaka. Ka takura mun?"

Marwaan ya Kai masa duka a kafadar sa ya juya da sauri ya nufi wajen su Nawraah. Ya yinda Anees ya wuce cikin theatre din da zasu je class

Gaisawa sukayi da marwaan. Nawraah nata saye fuska. Marwaan ya sunkuyar da Kai yana hango fuskar tata,

"Kyawunki kamar daren goma sha hudu... Kullum kyau kike karawa by Allah."

Ta Saka tafukan hannuwanta tana rufe fuskar ta, ya daga kai yana duban Layla yace,

"Dear sis... Mun kwana lafiya?"

"Alhamxulillaj inlaw..."

"Masha Allah. A'ina zakuyi classes yau?"

"A auditorium ne"

"Okay muje ko?"

Ya basu hanya yana nuna musu da yatsa. Suka wuce sannan yabi bayan Nawraah da sauri.

Suna tafe a hanya yana ta zubar magana kamar yayan kanya. Wani abunma idan ya fada Nawraah murmushi kawai take.

Duk inda suka gitta a school din, sai anyi zunden su. Yammata da yawa na bakin cikin kasancewar Nawraah budurwa agun marwaan, Dan masu kudi. Ita kuwa ba yar kowan kowa bace ya dillalin kashi agidan marayu ma take tsabar rashin gata itada yan uwanta...

_HGL CHARITY FOUNDATION_

_ASSALAMU ALAIKUM WA RAHAMATULLAH!_
JAMA'A BARKANKU DA _WARHAKA... ALLAH YA SAKA MUKU DA ALKHAIRI YA BADA LADA HADI DA BIYA MUKU DUKKANIN BUKATIN KU DA KUKE FATAN SAMU AAMIN_

GODIA DUBU GA TALLAFIN DA KUKA SAKA NA CIYARWAR AZUMI
INSHAA ALLAHU WANNAN GIDAUNIYAR MAI SUNA A SAMA NA KIRAN MUTANE AL'UMMA MASU SON SAMUN LADAN WANNAN MANYAN AIKI DA MUKE SAKA RAN FARA SHI KAMAR
НАКА

1• DAFA ABINCI A RABA GA MABUKATA RANAR JUMU'AH KO A KAI RUWAN SHA GA MASALLATAI RANAR JUMU'AH

2• HAQA RIJIYOYI ACIKIN KAUYUKA DA UNGUWANNIN DA BASUDA RUWA

3• RABA KAYAN ABINCI KO KUDI GA MABUKATA
MARASA HALI

4•KAI ZIYARA GIDAN MARAYU DA KAI MUSU
ABUBUWAN AMFANI DA SUTURA IDAN DA ME BAYARWA

5• KAI TALLAFI KO ABINCI GA ASIBITOCI WAJEN
MASU JINYA MARASA KARFI..

6•KOKARIN KARASA MASALLACI KO YIN MASALLACI
AWAJEN DA BASUDA SHI...

MAI NERA BIYAR MAI GOMA DiK
YADDA HALI YA KAMA ALLAH YA HADA MU A LADAN DUKA..
JAZAKUM ALLAH BiL JANNAH..
DOMIN SAKA TALLAFI GA ASUSU

9044191709
OPAY
JAZAKUM ALLAH BİL JANNAH💜

[5/3, 2:00 PM] Hafsaat🧕💞: _K'K'J_
_(M/W/S)_


_BOOK TWO_


_✍️:MX_


_13_


:::::::::

*Yana* tafe yana ta sake sake akan hanyar sa ta komawa gidah. Ya kan tsaya ya nisa yayi magana shi kadai kamar zaucacce sannan kuma ya cigaba da tafiya a haka har ya karasa gidah cikin sa na ta murdawa tsananin yunwar dake yasar yan hanjin cikin sa ..

Bakin sa dauke da sallama ya shiga parlorn na su. An kawo wuta TV dinsu yar karama tanata nuna faifon bidiyon wani dadaddan tsohon shirin film din hausa.

Yaran basa parlorn. Sai ita kadai tana kallo tana murmushi. Gabanta kuwa wata tasa ce dauke da ragowar fura tasha ta isheta ne da alama...

Ta daga kai jin tamkar an tsaya akanta ta sauke idanunta akan sa yana tsaye shima duban ta yake yi,

"Ya akai ne Auwalu?"

"Ya akai kuwa? Yanzu saboda Allah shikenan ke kinfi kaunar wannan rayuwar da muke cikinta mai tsananin sarqaqiya da wahala? "

"Ah kaji ka da wani zance can daya . To ni me zanyi akan rayuwar da muke ciki? Ba Allah ne ya Kadarta mana hakan ba? Kawai dai saboda ka kwaso fushi da bacin rai shine kake son ka zazzage shi akai na? Gaskia karka sake mun irin wadannan abubuwan ka Kai ni karshe"

"Lalle ma Nusaiba. Wallahi wannan rayuwar da muke ciki har da tagomashin kason lefin ki aciki "

Dogon tsaki taja, Ta dube shi shakeke tana watsa masa harara hadi da saka hannu ta tura masa kwanon furar gaban sa,

"Bismillah dauki kasha, Na tabbatar yunwa ce take dawainiya da Kai wannan zubar zancen da kakeyi wanda bashida Kai"

Ya dubi kwanon furar ya dubeta ya saka kafa ya hambare kwanon sauran kadan ya zube tayi saurin rike kwanon tana duban mijin nata,

"Menene haka auwalu? Nace menene haka?"

"Ni kike mayarwa karamin mutum? Tamkar wani Wanda bashida ishasshen hankali. Ina miki magana ta gaskiya zaki wani kawo kwanon gaba na nayi meye dashi? An gaya miki zakara ne ni sai da tsaba? To ki bude kunnuwan ki dakyau kiji abunda zan gaya miki. Ni ba mutumin banza bane. Kuma ke a matsayin ki na matata wallahi tamkar riga ce zan zare na saka wata. Amman 'yaya fa? 'ya'yana ne wannan alakar ba zata taba goguwa ba. Yadda su Layla suke awaje na hakan matsayina iyalan kanina junaidu suke awaje na."

"Okay yanzu na gano sigar inda zancen ka ya dosa auwalu ah yanzu na gano. Kawai so kake Kaci mitinci na Kaci zarafina. Su 'ya'yan da kake tunkaho na Kane. Kai ka dau cikin su ka haife su ne? Sai ka dinga baje hanci kana wani bubbudawa 'yaya na ne ya ya na ne. Akwai Wanda yace ba yayan ka bane? Allah yabani hakuri ni da na tsugunna na haife su ai bakai ka haifa mun su ba. Haka zalika naka yayan yan uwan ma dai da kaketa fada ba dagaa tsatson kaba bane, komai abunka wannan jalli biyun da Allah yabamu sune yayan ka na gaskia. Don haka banason naji wata magana ta daban auwalu Kai bakasan zaman hakuri nake ba zaman 'yaya nake da Kai ba? Wallahi ba dan yarana ba da tuni na dade da bar maka wannan kangon gidan naka, tunda Kai har abada bazan taba burgeka ba dukkanin abunda zanyi. Wannan tsana da kake mun ina sane da ita a burnin zuciya ta . Na fada na Kara fada yara ne dai bazan rike ba wallahi. Mu kanmu gidan bai ishemu ba Bare wasu a waje, yau da ace Kai me hali ne sosai ka rika tutiya haka. Amman muna zaune Muna rufawa juna asiri kullum banida kima a idanunka sai kawo suka sukaa. Kai Allah ya kyauta. Kowa dai ka nemi ka rabu dashi. Haka yan uwan ka da kuka fito ciki daya wadanda suke rage baki daya ka yanke huldar zumunci da su. Kana fushi da su akan wadanda basa duniyar ma gaba daya. Kaki naka duniya ta so shine dama ai. Su 'yayan cikin naka da baka ta tasu. Da yardar Allah sune zasu rufa maka asiri da yardar Allah , wadanda ka dauka ka fifitaa fiye da yaran da ka haifa da yardar Allah ba zasu zama wasu ba. Tunda kowa kansa yasani ,aikin kawai, Dan Allah daga yau ka sauya musu suna su koma Nawraah auwalu, Amnah Auwalu da ashfeef Auwalu. Aikin kawai"

Ta karasa fada hadi da mikewa ta sauke masa harara da dogon tsaki ta juya ta shige daki da sauri.

Wunin ranar baki daya bappah Auwalu a tunanin Ina ya nufa ya dosa baki daya hankalinsa yanzu kacokam ya koma kan yadda zai karbo su Nawraah daga gidan marayun su dawo gabansa

Tunda sauran yan uwan nasu suma sunyi fatali dashi saboda yana goyan bayan iyalan marigayi junaidu. Shikenan sika daina shiga harkar sa shima ya dena shiga tasu. Da sukan aikowa da yaran nasa hatsin abinci ya hana yace kar a sake kawo masa ko da dai da kwayar zarra ne. Allahn daya basu bai manta dasu ba, Kuma inshaa Allah 'yayan junaidu ba zasu tagayyara ba inde yana da saurin numfashi a kasa.

Ranar a parlor ya kwana yanata Kai adduar gurin Allah kan ya zabar masa dukkanin abunda yafu alkhairi akan kankin kansa da iyalan sa da Kuma iyalan dan uwansa junaidu dama sauran musalmai da ke cikin jalin qaqanikayi....


*********

Kasancewar karashen sati ne na weekends ba makaranta. Zaune suke dukkanin su a dakin su, sun kammala wankin su sun shanya sauran kwasa kawai

Hira suke baki dayan su akan tabarmar dake malale a tsakiyar dakin na su. dakin su. Yayinda Amnah ke tsakiyar su akwance akan pillow. Wasila na yarfa mata kananun kalba style din bob Marley..

_ADVERT👇👇_

_YERWA INCENSE AND MORE_
_(DUNIYAR KAYAYYAKIN KAMSHI MASU MATUKAR DADI DA KAMA JIKI, GIDAH, KAYA DA SAURAN SU)_


_INA MA'ABOTA TURARE? KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE_
_TSAFTA KUMA TANA CIKIN IMANI… TOH KU MAR-MATSO KUSA_

_MUN KUMA ZUWA DA HAJAR KAYAYYAKIN_

_*YERWA INCENSE AND MORE*_
_DOMIN SAMUN ZAFAFAN TURARUKAN WUTA NA GIDA, KAYA, JIKI, TSUGUNNO, GASHI... AKWAI KHUMRAHS MASU DADI YAN BORNU, CHADI, SUDAN DAMA SENEGAL, AKWAI OIL PERFUMES, DA TURARUWAN MOPPING DANA WANKA DANA WANKI DANA GADO DA KUJERU DA BANDAKI DA DRAWER DA MOTOCI.._

_AKWAI MAN GASHI NA FESAWA ME SA KAMSHI DANA KITSO. AKWAI KAYAYYAKIN KAMSHI DANA GYARAN JIKI SOSAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA. •_

_ADIRESHI: KANO.. AMMA SUNA TURA KAYAN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE..._

_INGANCI KYAU RAHUSA DA DADEWA A GIDAH DA KAMSHI SAI KAYAYYAKIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE_

_NAMBAR WAYAR SU: 08095215215, INSTAGRAM/THREADS/TWITTER:yerwaincense_and more_

_YOUR NUMBER ONE STOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS... THEY 'VE GOT YOU AND YOUR HOME COVERED_
[5/3, 2:53 PM] Hafsaat🧕💞: _K'K'J_
_(M/W/S)_


_BOOK TWO_


_✍️:MX_


_14_


:::::::::

Hirar duniya suke , labarai kashi kashi wani na ban tausayi, wani bandariya wani Kuma ban haushi.

Faty na daga can nesa dasu kanta na kan ceiling tana kallo. Baki dayan tunaninta Kuma baya nan yayi wani wajen. Gangar jikinta ce kawai.

Nawraah ta daga kai ta dube ta ta sunkuyar da shi kasa da sauri. Yadda faty bata aminta da su ba kawai take jin ba dadi

Kowa na cikin gidan marayun tana mutinci da shi suna magana. Amman itada Amnah ne kawai ta tsana. Ta rasa wani dalilin ne oho.

"Menene Nawraah?"
Raudah ta tanbayeta cike da damuwa.

Wasila dake kitse kan Amnah ma ta daga kai ta dubi Nawraah tana tanbayar ta itama,

"Yanayinta ya canza kam wani abun ne Nawraah?"

Nawraah ta girgiza Kai da sauri tana mayar da hawayen dake son bijere mata ya zuba tace,

"Ko daya.... Kawai dai Ina mamakin abunda yasa faty bata son shiga harkata ni da Amnah abun yana damuna bansan ko mun mata wani lefin bane amma gaskia banajin dadi"

Wasila da Raudah suka Kalli juna suna girgiza Kai

"Ki ma dai na bari wannan abun yana damun ki. Normally Faty ta saba haka. Mu kara bata wani lokacin zatai adjusting don kanta" cewar Raudah

"Toh Allah ya amince ", Nawraah ta amsa mata

"Amin inshaa Allah.. kinsan yanayinne sai a hankali. Kuma kunzo Kun sameta alokacin da take kunci na zuciya. "

"Subhan Allah meya faru wasila? "

Wasila ta daga kai ta sauke cike da tu'ajjabi tache

"Tun tana karama take gidan marayunnan, Don ta rigamu zuwa ma kusan ance sune fist set na wadanda aka bude gidan marayun da su. Duk Wanda suke tare yara alokacin haka aka dinga dauki 'dai 'dai dasu kowanne mutane sikace sunaso suka dauka Amman banda ita.... Labari yazo mana cewa koda yake ta gaya mana Muma alokacin da aka kawo mu. Take cewa batada saa . Ba Wanda ke kaunar ta da zai dubi maraicinta ya dauketa itama akai ta gidah tashiga ciki itama yau gashi ace tanada yan uwa. "

"Innalillahi Wa inna ilaihi rajiun..." Nawraah ta fada tana girgiza Kai.

"Ai abun akwai damuwa sosai. To haka shekarun sikai ta shudewa... Zuwanmu ba dadewa wasu zuriah suka zo haka kaman yare kaman yan kudu kudu dinnan dai. Amman musulmai ne Kuma suna jin hausa sosai suka ce suna so suyi adopting dinta suna son su mayar da ita yar su tunda basu taba haihuwa ba. Faty nata murna suka dauketa. To abu dai kamar almara washe gari Kiran sallar asubah na fari sai gashi sun dawo ita wai basa sonta gaskia, anan take suka dauki wasu yaran har biyu har yanzu Kuma suna wajen su. Babban abunda yafu damun ta ma shine cewar wai ita din yar tsintuwa ce baa san daga Ina zuriyar ta suke ba baasan daga inda ta fito ba. Kawai an ce an ganta acikin shawul tana jaririya..."

"Hasbun Allahu Wa ni'imal wakil...Allah sarki Faty. Gaskia gaskia lamarinta akwai tausayi sosai..."

Tamkar ance ta bude idanunta ta bude da sauri tana duban su. Ta mike daga kwancen da suke tayi kan Nawraah tana nunata da yatsa,

"Ya akai? Gulmar me kike? Magana ta kuke ko? Wato ke har kin isa kin Kai kina zance na ko? Har tausayi na kike. Wacece ke? "

Nawraah ta yi kokarin riko hannun faty , Faty ta fuzge da karfi ta fita.. suka bi bayanta da sauri dukan su banda Amnah dake wasa da kayan wasanta na mota da yartsana..

Can barandar sama faty tayi tana hawaye sosai,

"Gwara ma na mutu kowa ya huta. Gwara ka na mutu na bar muku duniyar kune yayan da ake so.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login