Showing 30001 words to 33000 words out of 69829 words

Chapter 11 - KWANKWASON JIMINA BOOK 2 COMPLETE BOOK 2 hausa novel

24 Aug 2024

8971

Alhaji ateeks dai da kuke hulda dashi"

"Okay inde shine babban abokin ne. Ko ince amini ne ga mazajen mu.sannan babban yaro ko ince na hannun daman baban su Anees ne, Kuma abokin huldar cinikayyar su ne. Wani abun ne?"

"Eh to abubuwan ne. So nake na fara sanin su wanene kafin na buda aikin gaba daya. "

"To Allah yasa muji alkhairi. Alhaji ateeks yana daga cikin manyan abokanan baban su Anees. Shima anan naduka crescent yake amman phase 2. "

"Ohh" Nawraah ta fada ahankali tana tariyo abunda ta saurara a kwakwalwarta.

"Ina sauraon ki Nawraah"

Nawraah ta sake muskutawa tana lankwasa hannuwanta tache,

"Mami waye Alhaji sambaso?"

Hajia Qibdiyya ta daga kai ta sauke kallonta akan Nawraah. Tsoro, firgici sun bayyana a atare da Nawraah. Don haka ta saka hannu ta kamo hannun nawraahn acikin nata tana duban ta cikin muryar kwantar da hankali tache da ita,

"Nawraah ki nutsu kinji. Ki sanar mun dukkanin komai kinji? Damuwarki damuwar mu ce Nawraah. Farin cikin ki shine nawa Nawraah. Wallahi Nawraah kunada babban matsaayi a wajena Kai da zuriyata ma gaba daya. Allah ya jikan Hindu. Allah beyi zamuyi dogon zango da ita ba. Yanzun Nawraah kin maye gurbin Hindu kinji? Ki daukeni a matsayin uwa kinji? Saki jikin ki ki kwantar da hankalinki, Nan gidan ku ne. Ki fito ki gayamun dukkanin matsalolin da kuke fuskanta. Idan shawara kike nema zan baki. Dukkanin abunda kike buri in dai bai fin karfin mu ba da iKon rabbi zamu baki shi. kinji?"

Nawraah ta kada Kai sama alamar toh. Hawayen da take ta makalewa ya shiga zurara,

"Nawraah.. Subhan'Allah! Kuka Kuma? Meya faru dan Allah. ?"

Nawraah ta sake fashe wa da wani kukan tana daga kanta sama hadi da saka hannu ta goge hawayen tache,

"Ai shine nace wanene Alhaji sambaso?"

Hajia Qibdiyya ta dubi Nawraah tana cigaba da nazartar ta tache,

"Aminin baban su Anees ne. Alhaji sambaso abokin cinikayyar baban su Anees ne. Alhaji sambaso attajirai ne a wannan garin namu na naduka. Yana daya daga cikin manya masu fada aji na gari da kasa baki daya... Alhaji sambaso miji ne ga aminiyata Dr bintu..."

"Ohkay. Allah sarki.... Lalle akwai zumunta a tsakanin ku sosai"

Mami ta kada Kai alamun eh ta cigaba da cewa,

"Akwai zumunci a tsakanin mu sosai Kam marigayiya Hindu ma ta sansu. Farin sani ma. Ai nan ta koma da girki lokacin da mukayi tafiya. Amman dukkanin wadannan zumunta dana lissafi maki hakan baya nufi don mun sansu mu goyi bayan su akan abu mekyau ko akasin haka. Saboda haka ki kwantar da hankalin ki. Alakar mu dake ta zarce gaban yadda kike tunani kinji Nawraah? Ki cigaba da Sanar damu komai. Alhaji sambaso yana daya daga cikin shareholders na jami'ar Alharamein. Sannan 'yayan su da yayan mu ma tare suke baki daya"

"Allah sarki. Allah yabar zumuncin ku"

"Aameen nawraah Ina sauraron ki cigaba"

Nawraah tayi shiru can ta nisa tace,

"Mami lamarin ne akwai rudani sosai. Ina tunanin ni da yan uwana kawai ya shafa. Don gaskia a yadda nake jina Mami idan ban dau mataki ba bazan taba jin dadi ba."

"Nawraah magana kike Mai harshen damo. Tattare kalaman ki suke cikin rudani da dulmiyar tunani. Wallahi bangane dukkanin abunda kike fada ba. Illa dai sunayen su dana gaya miki da bayanin su a takaice. Ki sanar dani abunda bansani ba Nawraah. Mu taru mu dauki ko wane irin mataki ne. Kinji?"

Nawraah ta kada Kai tana sauke gwauron numfashi tache,

"Mami..."
Sai Kuma tayi shiru.

Hajia Qibdiyya ta mike daga kan kujerar da take ta koma Wadda Nawraah ke Kai ta zauna a kusa da ita tana duban ta sosai tace,

"Wallahi kinji rantsuwar musulmi? Da Allah muka dogara. Da karfin ikonsa zamu taru mu yaye muku damuwar dake damun ku. Amman kafin sannan inason ki yaye ni daga cikin duhun da kika sanya ni Nawraah."

Nawraah ta dan daga Kai tana auna zancen a zuciyar ta...

"Ina sauraron ki Nawraah ..."

"Mami... Su suka kashe ummy da abbiey da hamma Ashir"

Hajia Qibdiyya na zaune sai ta mike. Hannuwanta dafe da kirji cikin tsantsar kidumewa jikinta ya fara rawa tana duban Nawraah cikin zare idanu da tsantsar firgice tace,

"Su waye suka kashe su Nawraah?? Innalillahi Wa inna ilaihi rajiun"


"Alhaji ateeks ya amince.... Plazas dinnan din sun zama mallaki na. Harda estates din mejesa da guzare dana Gpo da na bayan Maduki., shikenan nayiwa Dr abubakhr warwas matsiyaci duk tarin arzikin sa da sannu sai sun zama mallaki na..." Nawraah ta fada tiryan tiryan tana duban hajia Qibdiyya

Jin haka yasa hajiya Qibdiyya ta koma kusada Nawraah ta zauna. Tana duban ta sosai cikin tsantsar tashin hankali tache,

"Nawraah a'ina kikaji wannan zancen? Su waye suke fada? Labari aka baki ko menene? Innalillahi Wa inna ilaihi rajiun "

Nawraah tayi murmushi ta janyo wayarta ta sanya recoding dinnan tiryan tiryan tanayi har ya karashe

Hajia Qibdiyya sai ta nemi bakin magana ta rasa..ta bude baki kawai ta kasa ma rufe shi ko ta furta wani abun. Sai ta zama tamkar mutum mutumii. Sun dan jima a haka. Kafin cikin daurayi da dakewa tace,

"Ina sauraron ki Nawraah. Sai me Kuma?" Ta tanbayeta tana duban ta sosai

Nawraah batai kasa a gwiwa ba. Ta shiga cikin files ta danno bidiyon nan ta kunna mata. Hajia Qibdiyya ta karbi wayar tana gani.

Baki ta bude ta saka hannu ta rufe shi alokacin data karasa kallon bidiyon

"To Mami sai Kuma kisan hamma da akai Wanda nakeda tabbaci shima sune suka kashe shi. Shi tasay a ranar da zai rasu yaban wayar ya ce mun kar na bude recording da wajen bidiyon har sai na kammala aji na biyu zuwa na uku ko na hudu na jami'a. Yanayin da ya mikomin wayar ma yana cikin firgici na lura dariya kawai yakeyi yana yake. "

Mami tayi shiru. Saboda baki daya maganganun sun daureta da jijiyoyin jikinta. Ashe ba zaman Allah da annabi su dr bintu suke zaune dasu ba? Sun dauke su tamkar yan uwa da suka fito ciki daya. Tabbas ba dan Nawraah ta nuna zahiri ba ba zata taba yadda ba.

"Kinyi hakuri Mami dana sani ban gaya miki ba."

"Haba Nawraah ya zaki ce haka? Wannan manya manyan zancen ai sunwa kwakwalwar ki ma yawa Nawraah. Tabbas kedin ba karamar jaruma bace. Sannan yanayin dakikaga na canza tsabar kidimewa ne Nawraah. Ko a mafarki ban taba zato ba. Amman zance na gaskiya a abubuwan da sukafi sanya ni acikin wannan yanayin marar dadi wallahi na kisan gillar su Hindu ne. Wallahi kinji Allah? Na yi matukar mamaki Nawraah tabbas ba dan kunzo da sheda ba wallahi bazan taba yadda ba. Kai ka saki mutum ka kama Allah. Dama akace makashin ka na g!*** Ka. Mun musu rana sun mana dare. Allahu Akbar rayuwa. Wai bintu ce ke Kirana da munafuka da manya manyan zagi da aibatawa. Kai Allah ya kyauta wallahi Nawraah idan nace zan gaya miki yadda alakar mu take dasu zaki sha mamaki. Wallahi yan uwana da muke ciki daya ban aminta da gaya musu surrina ba kamar yadda nakeda bintu. Haka zalika Mlmai gidanta Alhaji sambaso. Ku kashe rayukan har uku Kuma kiyi tunanin kun ci bulus?. Dukkanin wadannan abubuwan daya faru sukai kashe kashen nan tushen sa dai akan Hindu ta ji maganar da suke ne.. Shine sukace bari su kasheta a rufe babin ko Haka zalika mahaifin ku ma da yaje maganar kan kisan da suka mata nanma ya kashe shi. Haka zalika Ashir duk yaddaa akai shima wajen sa yaje suka samu sabani ya saka aka kashe shi .. Tabbas zuriyar Alhaji sambaso ba abun kauna bane., Lalle mutane ne masu fuskoki dubu. Nawraah"

"Naam Mami... Kince dama scholarship aka baki a jami'ar Alharamein ko?"

"Eh"

"Waya baki"

"Ita ce bintu din"

"Daman tasan kin gama sakandire ne tace zata temaka muku ko yaya?"

Nawraah ta zauna ta fara labarta komai tundaga sanda Dr bintu ta fara zuwa tun farko mahaifin su na raye, zuwa ranar da take bawa hajia Qibdiyyan labari ta Karkare da,

"Shysa kawai na yanke shawarar dawowar mu gidan marayun don nan dinn yafi mana kwanciyar hankali akan can din"

"Allah ya muku albarka ya kareku daga dukkanin masu sharri. Tabbas Nawraah kedin KWANKWASON JIMINA ce, MAI WUYAR SHAFAWA. zanu shiga cikin case dinnan da hannuwan mu da kafafun mu."

"Aameen Mami..."

"Kuma iyayen nasa sun san yana kula ki?"

"Wa Mami?"

"Saurayin naki"

"Oh.. eh yace zai tanbayi baban sa yana ta aiki ne na kasuwancin su. Kullum ai tare muke ganinsu a school kafin Su gama. "

"Eh abokin Anees ne sosai ma kuwa..duk da dai marwaan din yadara Anees da shekaru kadan"

"Allah sarki..Masha Allah,"

"To yanzu ya matsayin alakar ku. Kina tunanin zasu yarda ya aure ki?"

Nawraah tayi murmushi kanta a kasa tache,

"Ai ban san su bama Mami..Amma nasan zan san su with time"

Dr Qibdiyyan ta dubeta a razane tache,

"Bangane bakinsa iyayen sa ba. Marwaan fa nake nufi ba wani ba"

"Eh Mami. Bamu hadu ba tukun yace dai idan an kawo kudi zai Kai ni mu gaysa. Ya mana abubuwanda baki ba zai iya ambata karramaawar su ba Mami. Rashin lafiyar Amnah shine akaj komai, cin mu shan mu. Abubuwa da yawa dai. Kyautatawar sa yasa na amince dashi."

"Allah sarki... Nawraah! Marwaan dayazo dazu nake miki magana fa"

"Eh shi din ne dai Mami"

"To ai dan bintu ne, Babban 'da ga Alhaji sambaso"

Dimmm Nawraah taji kirjin ta ya buga da matukar karfi a razane ta daga kai tana duban Mami cikin karin bayani ..

Mami ta jijjiga mata Kai cikin tabbatarwa tace,

"Shine babban dan su sai lily,"

Nawraah ta sakeyin shiru tana lulawa duniyar tunani. Ji take tamkar mafarki take..

Kakwalwarta ta shiga tariyo mata komai da komai game da marwaan ciki harda sanda suka fara zuwa makarantar da Layla taje ta tanbayi sunayen su, tabbas Anees Abubakhar dollars da marwaan sambaso.

Shin marwaan nada masaniya akan abunda iyayen su suka mata, ta girgiza Kai ita kadai tana magaba acikin zuriyar ta

"Ina marwaan ba zai mun haka ba, tabbas dayana da masaniya ,ai zai gaya mata. Wasu siraraan hawaye suka shiga zuba a fuskar ta. Data kasa gane na menene

Hajia Qibdiyya ta zaro tissue akan center table ta mikawa Nawraah dake hawaye sosai...

Bayan hannunta ta ta Saka tana katse sauran hawayen bayan ta kammala kukan tana ajiyar zuciya. Mikewa tayi tana layi kamar wadda tasha maganin bacci. Tuni jijiyoyin kanta sun murde kanta ya fara ciwo sosai.

"Tashi muje Amnah .."

Amnat ta kike daga zaunen da take. Hajia Qibdiyya ta dube su cike da damuwa tace,

"Zauna mana Nawraah"

"Mami zan je na kwanta ne. "

"Kalli condition din da kike ciki mana. Ki bari zuwa jimawa ko kwana mana yau dai daya"

"Akwai aiki da aka bamu a makaranta. Amnah ma batai homework dinta ba . Sai da safe Mami"

"Shikenan sai da safen mu Nawraah. Inshaa Allah idan baban su ya dawo daga wajen aiki zamuyi magana. Zan gaya miki yadda mukai dashi"

"Tohm sai da safe." Ta riko hannun Amnah suka fita zuwa gidan marayun da suke....

Dakyar Nawraah ta iya karasawa saboda yadda gabobin jikinta suka saki baki daya ba karfi ajikin ta. Ga kanta dake mata ciwo sosai , yayi nauyi yana yi kamar zai fado ..

_ADVERT👇👇_

_YERWA INCENSE AND MORE_
_(DUNIYAR KAYAYYAKIN KAMSHI MASU MATUKAR DADI DA KAMA JIKI, GIDAH, KAYA DA SAURAN SU)_


_INA MA'ABOTA TURARE? KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE_
_TSAFTA KUMA TANA CIKIN IMANI… TOH KU MAR-MATSO KUSA_

_MUN KUMA ZUWA DA HAJAR KAYAYYAKIN_

_*YERWA INCENSE AND MORE*_
_DOMIN SAMUN ZAFAFAN TURARUKAN WUTA NA GIDA, KAYA, JIKI, TSUGUNNO, GASHI... AKWAI KHUMRAHS MASU DADI YAN BORNU, CHADI, SUDAN DAMA SENEGAL, AKWAI OIL PERFUMES, DA TURARUWAN MOPPING DANA WANKA DANA WANKI DANA GADO DA KUJERU DA BANDAKI DA DRAWER DA MOTOCI.._

_AKWAI MAN GASHI NA FESAWA ME SA KAMSHI DANA KITSO. AKWAI KAYAYYAKIN KAMSHI DANA GYARAN JIKI SOSAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA. •_

_ADIRESHI: KANO.. AMMA SUNA TURA KAYAN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE..._

_INGANCI KYAU RAHUSA DA DADEWA A GIDAH DA KAMSHI SAI KAYAYYAKIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE_

_NAMBAR WAYAR SU: 08095215215, INSTAGRAM/THREADS/TWITTER:yerwaincense_and more_

_YOUR NUMBER ONE STOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS... THEY 'VE GOT YOU AND YOUR HOME COVERED_
[5/13, 1:55 AM] Hafsaat🧕💞: _K'K'J_
_(M/W/S)_


_BOOK TWO_


_✍️:MX_


_25_


:::::::::

    Bakin su dauke da sallama suka shiga dakin na su. Kusan sallamar Amnah ce ma ta fito fili sosai. Ya yin da Nawraah tayi kasa kasa.

Su Raudah suka amsa sallamar tasu suna musu maraba. Kowacce na kan gadon ta sunata hirar duniya.

"Nawraah. Meye faru ne?" Raudah ta tanbayi Nawraah ganin ta nufi gadonta ta kwanta ta dora fulo akan fuskar ta

"Gaskia ni ma naga yanayinta da sanyi sanyi ta shigo" wasila ta fada tana duban Raudah.

Faty ta mike ta nufi gadon Nawraah ta zauna a gefe tana leka fuskar Nawraah data tukwikwaye da fulo.

"Nawraah... Dan Allah menene kin saka zukatan mu acikin rudani. Dan Allah menene kinji?" Faty ta mata magana cikin lafazi na ban hakuri da rarrashi.

"Nawraah... Nawraah. Amnah meya faru ne eh?"

Amnah ta girgiza kai tana duban Nawraah tache

"Nima bansani ba.. bansan ko uncle marwaan bane ya mata fada"

"Marwaan ? A'ina kuka hadu da shi?"

"A gidan Mami"

Su faty suka dubi junan su da kallon karin bayani. Raudah ta riko hannun Amnah tace,

"Ai munata neman ku. Ganin Nawraah bata school. Kema muka biya zamu dakko ki. Me gadin makarantar ku yace ai tun dazu dayar yayar taki ta dauke ki. Muka zazzaga dakunan dake gidan nan. Nanma bakwana kan..don faty har ta cewa mu ku shiga gidan Mami ko kuna can. Wasila tache ba lalle Kuna canba sai dai ko Kuna gidan bappann nan naku. Mu kuma.bamu san gidan ba. Yanzu shi uncle Marwan din dukanta yayi ko fada ya mata?"

"Nima.bansani ba Saboda ni da Mami mun koma dayan parlorn muka bar musu wannan shi da ita"

"Okay tohm, maza yi sauri kije ki wanka kinji? Kici abinci sai ki aiki in an baku homework?"

'eh an bamu suna cikin jaka"

"Yauwa Amnah..maza jeki wankan bari na duba homework din kafin ki fito"

"Tohm Aunty Raudah"

Raudah ta janyo jakar ta duba aikin gidan ganin Amnah zata iya yasa tabar mata su a gefe. Ta juya wajen Nawraah tana fuzge fulon. Abin mamaki sai suka ga ta sake fashe wa da wani irin kuka mai tsuma zuciyar duk Wanda ya saurara.

"Dan girman Allah Nawraah ki sanar mana abunda ke damun ki kinji? Dan Allah"

Nawraah ta girgiza Kai tana runtse hawayen idanunta. Dake zuba tace,

"Ba bu komai"

"Kinsan ko duk jikina kunne ne ba yadda zan ba. Malama meke damun ki?.damuwar ku tamu ce. Nawraah kada ki manta idan muka shiga irin wannan yanayin kece me karffafa mana gwiwa kita rokonmu har sai mun gaya miki damuwar mu. Amman ke saboda Allah ace kina cikin damuwar da har ta saki zubar da hawaye amma ki kasa sanar mana. Shin baki aminta da mu din bane ko kuwa?"

"Gaskia hakane sai dai idan baki dauke mu tsintsiya madaukin ki daya ba."

"Nawraah dan Allah ki gaya mana abunda yasa kike zubar da kwalla haka. Kinji?"

Baki daya haka suka shiga tofa tasu suna bata baki ta gaya musu damuwar data sanyata shararar hawaye haka.

Nawraah na insu..ta cigaba da rusgar kukan ta kafin ahankali ta mike ta jingina da jikin gadon

Amnah ta fito daga bandaki ta sauya kaya zuwa na bacci, Ta ja littafan aikin gidan da aka basu tayi, taci abinci sama sama, sannan ta nufi wajen yar uwarta ta zauna. Nawraah ta janyota jikinta tana shafa bayanta. Sosai taji ta samu nutsuwa da salaama. Ta dubu Amnah dake malale da ita tana hawaye.. Da sauri ta saka kasan dankwalin ta fara goge mata fuskar ta

'kukan me kike uhm?"

Amnah ta girgiza Kai bata ce komai ba. Raudah ta dubi Nawraah itama idanunta sun ciko da hawaye. Taceh,

"Nawraah ai dole Amnah tayi kuka.. haka kawai ba ita kadai ba Kuma kinsaka hankulan mu shiga cikin wani yanayin mara dadi. Mun rokeki ki fadi koma menene mu taru mu magance ki mu baki shawara kinki. Sai Amnah ce ke cewa Kuna gidan Mami har Kun hadu da marwaan. "

Nawraah ta saki gwauron numfashi mai tattare da tarin radadi na santsin rayuwa tache

"Ba zaku gane ba... Faty, Raudah... Wasila. Rayuwata da yan uwana tana cikin wata sarkakiya da bazan iya fayyace muku ita ba. Lamarin ne daya ke da matukar firgici da razana fiye da yadda Luke zato.. wannan babban lamarin ya shafi rasuwar iiyayen mu da babban wanmu. Abu ne dake dunkulalle sai an since shi daya bayan daya. Duk yadda kwalkwalwa zata ayyana muku ba zaku taba ganewa ba, Kai ko da fayyace muku komai..Kun tambaye ni menene ko da yadda zan a magance, Alfarma daya nake roka a wajen ku kawai. Dan Allah ku sanyamu cikin addu'oin ku. Kuma na adduar Allah yabamu nasara. Allah ya dora mu akan su. Ku.mana addua kan Allah yasa karashen sune suka zo, Ku tayamu rokon Allah ya amsa bukatin mu. Wannan shine boyayyen al'amarin da rayukan mu ke ciki. Abunda zaku mana kawai a matsayin ku na abokan zaman rayuwar mu shine ku kana addu'a'

Nawraah na karasa fada ta juya ta kwanta hadi da jan zaninn gado ta rufe kanta.

Jikin su yayi sanyi kan maganganun da tayi, Da tsananin tashin hankali dake fuskar ta zaa ka gane lamarin abun babbane ....

Shiru sukayi jugum jugum. Amnah tuni bacci ya dauke ta tana minshari ahankali.

Su Raudah suka hada idanu sun rasa bakin cewa komai. Dakyar suka iya babbata baki.

Sannan daya bayan daya sukayi alwala dukan su har Nawraah. Suka dan kwanta dare naja sosai tsakar dare suka tashi yin sallar tahajjud wurin neman temakon Allah akan lamarin su Nawraah.

  ::;;;;;

WASHE-GARI..

   Da wuri suka tashi dukkan su. Daga sallar asubah basu koma ba kasancewar sunada test da zasuyi a ranar Kuma jarabawar su ta gabato.

Nan da nan gari na fara haske lokacin makaranta Nawraah ta zura hijabi ta riko hannun Amnah da dan lunchbox dinta da hajia Qibdiyya ta saya mata...

Kuma ta hada mata da cartoons da biscuit da capri- sun, su cakes da Kuma warfer da ruwan roba da apple.

Bayan ta Kai Amnah ta dawo. Ta ci abincin da bata ci ba. Ta sake watsa ruwa ta gina abubuwan da zata saka ta mayar da julbab dinta. Suka nufi jami'ar su su hudu.

Amman baki daya zuciyar Nawraah sam batada nutsuwa. Tunani ne dankare cikin ranta. Da abubuwan da zasu biyo baya.

Allah ne ya temaka ta karasa iya rubuta test da aka basu.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login