Showing 18001 words to 21000 words out of 69829 words

Chapter 7 - KWANKWASON JIMINA BOOK 2 COMPLETE BOOK 2 hausa novel

24 Aug 2024

8970

sake kamata gaba daya tace,

"Nan tazo itada wannan kanwar tata, Kann dan Allah sunaso su dawo nan gidan marayun basuda kowa su kadai ne nace Ina yan uwan ta tache babu. Sai yayanta daya nace taje ta taho dashi suka cike komai suka zauna anan din. Amman ta shedamun cewar wata mata ta basu tallafinn karatu kyauta a jami'ar nan ta kudi ta naduka. Don haka zasu fara zuwa. Haka din kuwa akayi. Ko masu zuwa musu visiting dinnan ziyarar duk sati ko ta litininn wani mutumine yake zuwa nan din haka ya manyanta shine kadai nasan yake zuwa wajen su su gaysa ya tafi. Allahu Akbar rayuwa kenan. To ubangiji Allah ya jikan musumalmai baki daya. Allah Kuma ya kyauatata namu zuwan amin"

"Aameen Yaa Rabbi. Aameen. Amnah sannu Amnah Ina hamman ku?"

"Hamma ashfeef? Iya gareji"

"Bashi ba dayan hamma"

Nawraah da ta samu nutsuwa kukan da tayi ta sharce da kasan mayafin jikinta ta juya tana duban hajia Qibdiyya tache,

"Ummy ta rasu, abbiey ya rasu, hamma Ashir babban wanmu ko? "

"Eh shi, shi yana Ina? Inata Kiran wayaar sa a akashe"

"Ya rasu shima" ta amsa mata a sanyaye

"Ya rasu?" Hajia Qibdiyya ta tanbayeta dafe da hannuwa a kirji yayinda idanuwanta suka furfito waje. Baki daya al'amarin ya girgiza ta, Ta dubeta tache,

"Meya faru da shi innalillahi Wa inna ilaihi rajiun"

"Ya rasu..."

"Innalillahi Wa inna ilaihi rajiun... Ina kawunan naku suke Nawraah?"

Nawraah tayi murmushin yake tache,

"Suna nan kalau"

"Duk ba Wanda ya dauke ku acikin su?"

"Babu "

"Kai rayuwa. Wato zumunci ya zama sai ana raye ake dakai da iyalan Ka, idan ka rasu kuma mantawa ake da babin ka, yanzu zumunci sai bare ya maka abu na jininka ya guje ka. Rayuwar nan gaba daya sai du'ai ubangiji Allah yasa mu dache kawai"

Baki daya jikin yan wajen sai yayi la'asar. Kwarai matukaa rayuwar su Nawraah abun tausayawa ne. Sai dai kowane dan Adam lullube yake cikin rigar mutuwa. Babu Wanda zai tubeta kuwa duk tsananin mulkinsa ko sarautar sa bare nasabar Sa.

Hajia Qibdiyya ta share hawayen ta da tissue din data zaro daga cikin jakarta ta sake nannado wata ta nufi wajen Nawraah ta kama hannun ta ta sanya tissue din tana goge mata fuska tache,

"Kiyi hakuri kinji? Wannan babban rashi ba ku kadai ya taba ba har da mu baki daya Allah. Mahaifan ki yan albarka ne Kuma da yardar Allah dukkanin su harda hamma Ashir din aljannatul firdaws ce makoma agare su, ki bar kuka kinji? Adduoin ku kawai suke bukata. Kinji Nawraah? Allah ya miki albarka. Kin sheda ni kuwa? Lokacin dana fara ganin ku baki zama yammata haka ba tubark Allah kin tuno wadda kuka sayowa lemo da ruwa kuka kawo mun ummyn ku tasa kuka karbo?"

Nawraah ta daga kai da sauri tana murmushi tache,

"Inda ummy ta fara aiki"

"Kwarai kin tuno.. alhamdulillah! Allah ya karba kukana . Kullum sai na roki Allah ya bayyana mun ku. Gashi alhamdulillah cikin sauki na hadu da ku"

Nawraah tayi murmushi kawai tana sadda kanta kasa.

Hajia Qibdiyya ta dauki sunayen su Raudah gaba daya tace ranar Monday su fara zuwa jami'ar Alharamein din su fara daukar darasi. Komai da komai zata saka a musu kyauta kar su damu ta Kuma ce zaa sauyawa Amnah makaranta a sakata ata kudi dake nan kusada jami'ar.

Sun mata godia sosai. Sun Kuma ji dadin babban abun alkairin da tayi musu. Ta Kuma yi alkawarin kara dakunan kwana a gidan marayun da sauran kayayyakin da ake bukata.

Sai data tabbatar ta kammala komai tukun sannan tabar cikin gidan marayun ta koma nata gidan cike da farin cikin ganin su Nawraah. Sai dai wani bangare na zuciyar ta na mata radadi ciwon rasa rayuwar Ashir. Ta tausaya musu kwarai matuka. Domin ba sau daya ba lokacin da malama Hindu na raye tana gaya mata yadda yaron nata ke tsaya akan yan uwan nasa dukan su .

=====

Sannu ahankali haka rayuwar taci gaba da garawa. Hajia Qibdiyya taso ta dawo da su Nawraah gabanta. Amman Nawraah taki fafur tace zaman su agidan marayun ma yayi Allah ya Saka da alkhairi

Amman duk da haka hajia Qibdiyya bata hakura ba sai data sauya musu gadaje aka Kara ac ta tsaye da fanka.

Kuma kullum sai an kaiwa gidan marayun lafiyayyan abinci mai rai da lafiya, tana basu kulawa sosai ta inda basa zato ..

A haka rayuwar taci gaba da tafiya. Har su Amnah suka kammala level one suka shiga two, two dinma sunyi nisa sosai sun shiga three mashaa Allah sunada matukar kokari da kwazo baki dayan su...

Gefe daya soyayya ce tacacciya marwaan da Nawraah suke ginata akan gaskia da lumana.

Marwaan nata kokarin samun iyayen sa don gaya musu shi fa ya tsayar da matar aure tun da yanzu shi da su Anees suna ajin karshe na kammala jami'ar gaba daya. Dama sun 'dara su Nawraah da aji daya...

:::

Tana zaune bayan ta kammala karanta alQur'anin da ke gabanta ta ajiye shi.

Wayarta ta janyo dake kusa da ita. Tayi murmushi tana tuno sanda hamman su Ashir ya bata ita yana ce mata,

"Ba nisa zanyi ba yanzu zan dawo inshaa Allah. Ungo rike wayar nan taki ce. Ki dinga browsing na assignment da ita idan kin fara jami'a..duk rintsi duk wuya kada ki bari wayar nan ta subule daga hannun ki. Kar ki bawa kowa, Na roke ki da girman Allah kuma recordings din wayar nan kada ki jisu har sai kin shiga aji na biyu zaki shiga na uku, sai na hudun kammala jamia kinji ko? Allah yabada saa"

"Hamma meye haka kamar Wanda zaiyi tafiya ba dawowa? Nagode Allah ya saka da alkhairi Amin"

"Aameen ya Hayyu waayum. Sai na dawo."

Wasu hawaye ne sirara suka shiga kwarara daga idanuwan ta. Ta sanya bayan hannunta tana share su. Zuciyar ta na mata zugi da rada'di...

"Su waye suka kashe ummy........? Da me zan fara?" Ta tanbayi kanta a kasan zuciyar ta tana sauke gwauron numfashi mai tafiyar harshen damo!!!

_HGL CHARITY FOUNDATION_

_ASSALAMU ALAIKUM WA RAHAMATULLAH!_
JAMA'A BARKANKU DA _WARHAKA... ALLAH YA SAKA MUKU DA ALKHAIRI YA BADA LADA HADI DA BIYA MUKU DUKKANIN BUKATIN KU DA KUKE FATAN SAMU AAMIN_

GODIA DUBU GA TALLAFIN DA KUKA SAKA NA CIYARWAR AZUMI
INSHAA ALLAHU WANNAN GIDAUNIYAR MAI SUNA A SAMA NA KIRAN MUTANE AL'UMMA MASU SON SAMUN LADAN WANNAN MANYAN AIKI DA MUKE SAKA RAN FARA SHI KAMAR
НАКА

1• DAFA ABINCI A RABA GA MABUKATA RANAR JUMU'AH KO A KAI RUWAN SHA GA MASALLATAI RANAR JUMU'AH

2• HAQA RIJIYOYI ACIKIN KAUYUKA DA UNGUWANNIN DA BASUDA RUWA

3• RABA KAYAN ABINCI KO KUDI GA MABUKATA
MARASA HALI

4•KAI ZIYARA GIDAN MARAYU DA KAI MUSU
ABUBUWAN AMFANI DA SUTURA IDAN DA ME BAYARWA

5• KAI TALLAFI KO ABINCI GA ASIBITOCI WAJEN
MASU JINYA MARASA KARFI..

6•KOKARIN KARASA MASALLACI KO YIN MASALLACI
AWAJEN DA BASUDA SHI...

MAI NERA BIYAR MAI GOMA DiK
YADDA HALI YA KAMA ALLAH YA HADA MU A LADAN DUKA..
JAZAKUM ALLAH BiL JANNAH..
DOMIN SAKA TALLAFI GA ASUSU

9044191709
OPAY
JAZAKUM ALLAH BİL JANNAH💜
[5/4, 8:55 PM] Hafsaat🧕💞: _K'K'J_
_(M/W/S)_


_BOOK TWO_


_✍️:MX_


_17_


:::::::::

Agogon wayar ta ta kalla. Ranar ne bikin 'yayan hajia Qibdiyya mace da namiji da zata aurar.

Baki daya batason halartar taron, sai dai kuma hajia Qibdiyya ta taka muhimmiyar rawa acikin rayuwar su.
Su Raudah tuni sukayi gaba su da Amnah. Itace kawai tace zata zo daga baya kanta na dan sara mata.

Badan taso ba ta mike tsaye tana rage kayan jikinta hadi da daura zani ta shige bandaki bakin ta dauke da addua.

Wanka tayo ta durje jikinta sosai, sannan ta daura alwala ta fito ta fara shafa mai ta gama komai dai ta zura wata doguwar rigar abaya ja da suka saya a gwanjo kwanakin baya itada su Wasila...

Ba tai wata kwalliyaa ba. Don ba mai san kwalliyar bace daman, Ta dai shafa farar hoda da kwalli. Ta kuma zizara jan jambaki a bakinta kadan. Duba da dama labban nata jajaye ne...

Ta yane kanta da mayafin rigar ta rike yar wayarta a hannun ta da purse mai dari shida aciki kudin ta.

Kai tsaye ta futa daga gidan marayun zuwa bakin titi tana tafe tana karanta Invitation card din bikin da ke rubuce da manyan baki na,

"Biki buduri burede... Hajia Mariyatul Qibdiyya (Mrs Abubakhar dollars) na gayyatar ki zuwa shagalin bikin yayanta: Abubakhar Abubakhar dollars (junior) da kanwar sa Hayfa Abububakhr dollars. Ranar juma'ah karfe hudu na yamma idan Allah ya kai mu a grand marquee na naduka apple crescent...."

"Okay bama nisa kenan?" Nawraah ta fada tana mayar da katin cikin jakarta. Ta janyo face mask dinta tana kokarin saka shi.

Daman futowar ta yake jiran yana ganin ta futo ya sauke ajiyar zuciya yana lunshe idanun sa. Ya samu kansa da dukan sitiyarin da ya jingiran da kansa yace,

"Alhamdulillah...."

Ba kadan ba tayi masa kyawu, tafiya ya shiga yi ahankali da motar tasa. Ji yake inama halaliyar sa ya karasa ya dakkota cak ya zura ta a mota su tafi. Amman yasan ko kallo bai isheta ba saboda ta riga ta san yashi acikin sahun mutanen da bata kauna.

"Taya zaki gane ba kiayyyar ki nake ba Nawraah?" Ya tanbayi kansa yana girgiza Kai kawai ya sake cewa a kasan makoshi,

"Kaunar ki ce sanadi .... Kaunar ki ta gama gauraye ilahiran jikinta da tsohon Nawraah. Ina miki kaunar da ban taba yiwa wata ya maceba. Bansan meye so ba sai akan ki. Bansan meye kauna ha sai akan ki zuciyata da gangar jikina sun rigada sun dauki ragamar kaunar ki baki daya, ya zanyi kisan Ina cikin wani hali Nawraah...?" Ya karasa jan sunan nata cikin wata iriyar muryar dake bayyana tsantsar damuwar da yake ciki na son kasancewar ta a tare da shi, a matsayin sahibar masoyiyar zuciyar sa...

Yana daga gaba ya dan tsaya yaga ta tare dan adaidaita sahu ta fito da katin bikin gidan nasu tana nunawa dan sahun da alama kwatance take masa. Dan sahun ya karba ya karanta yana nuna titi . Suka gama ciniki ta shiga,

Anees na jin inama shine suke magana haka ba dan adaidata sahun ba. Ya sake sauke katuwar ajiyar zuciya. Yabi bayan su da motar tasa.

Sannu ahankali haka suka karasa wajen taron. Taciro kudin sa ta mika masa ta shiga wajen taron bayan security/bouncers sun karba katin bikin a hannun ta. Sun Kuma scanning jakarta kar ashigar da wani abun saboda tsaron duk Wanda zai shiga sai da aka masa haka. Ciki harda Anees daya fita ya mika nasa katin shima ya shiga bayan sun gama chaje shi.

Wajen taron ya hadu fiye da yaddaa baki zai fada. Hakama yafi karfin girman yadda alkalami zai rubuta. Mai karatu dakin wurin taron bikin ya kai koluluwar karashen kyau tamkar a kasashen turai.

An sake kawata shi da uban su decorations da sukayi matukar karawa wajen kyau..

Nawraah nata wulkita idanu inda zata hango su Raudah, can ta hango su bayan sun kira ta a waya suna daga mata hannu. Tayi murmushi ta karasa wajen su tana daria.

"Jirgin dankaro" cewar wasila ta na yiwa Nawraah harara da wasa

"Tuba nake mutane na" Nawraah ta rausayar da Kai tana murmushi

Amnah ta nufeta da sauri ta rungumeta tsam ajikin ta. Nawraahn itama ta sake kankameta tana sakejin dumin jikin yar uwar tata

"Kinsan gwara da sai yanzu kikazo. Wallahi mu da muka zo da wuri mune farko sai dj dayazo ba dadewa" faty ta fada tana daria

Nawraah ta fashe da daria itama tana jan kujera ta zauna tace,

"Ai nida nasan halin bukukuwan mu kullum cha ake no African time. Amman ko yaya dai sai kinga an bada lokaci. Shysa na tsaya na shirya da wuri...

"Kije ki gayshe da hajia. Tun dazu take zuwa wajen nan tana Ina kike? Muka ce baki karaso ba"

"Haba dai?" Nawraah ta fada tana waiwaya wa.

"Allah kuwa gata can daga can a tsaye tare da wasu"

"Bari na je na gayshe ta. Zo ki rakani Amnah"

Nawraah ta rike hannun Amnah suka karasa har inda hajia Qibdiyya take a tsaye itada wasu mata da suke wajen. Sai data bari sun kammala sannan suka karasa

Tana ganin su ta nufe su da sauri ta rungume Nawraah ajikinta ta daga ta dubeta tanata murmushi

Nawraah kunya duk ta kamata. Sam matar batada kyama irin na me kudin ko daga kai da dagawa.

"Ina wuni Mami?" Ta gayshe ta tana sunkuyar da kanta kasa.

Hajia Qibdiyya tayi murmushi itama tana rike da hannun su tache,

"Alhamdulillah Nawraah. Ai har nayi fushi inata zuwa ana cemun baki karaso ba "

"Yi hakuri Mami. Na dan tsaya ne na gama kintsawa"

"Allah sarki mashaa Allah... Kun samu wajen zama?"

"Eh mun samu Mami. Ina tare da su Raudah."

"Eh eh eh haka fa. To zaa kawo muku komai inshaa Allah. Dan Allah ku tsaya kuci abinci kinji?"

"Tohm Mami inshaa Allah"

"Eh anjima idan an tashi zan sa a mayar da ku da yardar Allah"

"Kai Mami ba sai kin wahala ba"

"Wahala? Haba Nawraah ai ba abun wahala anan. Shi da ai na kowanne. Kuje ku zauna Allah ya muku albarka " ta karasa fada tana sake rungume su tsam ajikin ta.

Ta yi saurin mayar da hawayen dake neman zubo mata. Duba da Nawraah yadda ta Kara girman itada Amnah sai suka sake juye wa sak mahaifiyar su malama Hindu. Kamar har ta baci.

Duk abunnan da sukeyi akan idanun Anees daya seta su ya mayar da su tamkar tv din kallon sa. Yayinda kwayar idanun sa na motsawa ne kadai akan mutum daya wato Nawraah.

Wani irin kallo yake mata tamkar zai mayar da ita cikin sa. Ta sake kyau kamar wata baturiya. Doguwa ce sosai tubarkAllah. Sannan halittar kirar jikinta ma mashaa Allah sai sam barka kawai.

Tanada manyan gabbai sosai tubarkAllah. Ga yalwataccen gashin ta nan fam. Domin bayan hodar data saka ta dora mayafi sai da gashin nata ya sake tullowa ta kasa baki kanannade na larabawan usul. Itada Amnah sake lallabawa suka dakko wato zuriyar su ta hamidniyya Lebanon

Kai kache renon gidan carpet ne masu shan cornflakes, Har ta fatar jikin su ma Kai kache yayan wasu manyan ne.

Bugu da Kari Nawraah akwai tsafta. Da iya daukar wanka da kwalliya. Komai nata abun burgewane. Batada fada kowa nata ne. Ga darajta dan Adam ko mai kankantar sa.

Tabbas wasu tun kan su rasa rayukan su a doran duniya ake fadan halayen su na kwarai ko akasin haka. To hakan take akan iyalan marigayi junaidu da marigayiya Hindu. Hakika Allah ya jarbi addu'oin su na yara nagari. Domin tundaga kan Ashfeef da Nawraah zuwa Amnah dukkanin su nutsattsu ne masu dimbin ladabi da biyayya, wajen ibadah ma kuwa Alhamdulillah. Suna farko farko. Basuda wasu halaye gurbatattu yau da zaa ce Allah wadaran su. Kowa yabon su yake lungu da sako dukkanin inda suka shiga.

Anees ne ya shiga da su. Yayan sa junior da yayar sa haifaa itama da angonta. Mashaa Allah. Suka shigo atare cikin wata waka mai take ahankali ba sauri.

Hajia Qibdiyya da kanta takira su Raudah tace suzo su dau hoto da yaran nata. Gwanin ban sha'awa. Haka da akazo rabon abinci ma ta kan teburin su tasa afara raba komai harda tabo savouneirs na bikin.

Sunci sun sha sun gyatse, mashaa Allah. Da lokaci yaja kuma tache Anees ya mayar da su Nawraah gidah....

_HGL CHARITY FOUNDATION_

_ASSALAMU ALAIKUM WA RAHAMATULLAH!_
JAMA'A BARKANKU DA _WARHAKA... ALLAH YA SAKA MUKU DA ALKHAIRI YA BADA LADA HADI DA BIYA MUKU DUKKANIN BUKATIN KU DA KUKE FATAN SAMU AAMIN_

GODIA DUBU GA TALLAFIN DA KUKA SAKA NA CIYARWAR AZUMI
INSHAA ALLAHU WANNAN GIDAUNIYAR MAI SUNA A SAMA NA KIRAN MUTANE AL'UMMA MASU SON SAMUN LADAN WANNAN MANYAN AIKI DA MUKE SAKA RAN FARA SHI KAMAR
НАКА

1• DAFA ABINCI A RABA GA MABUKATA RANAR JUMU'AH KO A KAI RUWAN SHA GA MASALLATAI RANAR JUMU'AH

2• HAQA RIJIYOYI ACIKIN KAUYUKA DA UNGUWANNIN DA BASUDA RUWA

3• RABA KAYAN ABINCI KO KUDI GA MABUKATA
MARASA HALI

4•KAI ZIYARA GIDAN MARAYU DA KAI MUSU
ABUBUWAN AMFANI DA SUTURA IDAN DA ME BAYARWA

5• KAI TALLAFI KO ABINCI GA ASIBITOCI WAJEN
MASU JINYA MARASA KARFI..

6•KOKARIN KARASA MASALLACI KO YIN MASALLACI
AWAJEN DA BASUDA SHI...

MAI NERA BIYAR MAI GOMA DiK
YADDA HALI YA KAMA ALLAH YA HADA MU A LADAN DUKA..
JAZAKUM ALLAH BiL JANNAH..
DOMIN SAKA TALLAFI GA ASUSU

9044191709
OPAY
JAZAKUM ALLAH BİL JANNAH💜
[5/4, 10:24 PM] Hafsaat🧕💞: _K'K'J_
_(M/W/S)_


_BOOK TWO_


_✍️:MX_


_18_


:::::::::

Sallama sukaje suka yi mata. Ta sake rungume su daya bayan daya tana shi musu albarka kowanne tana Kiran sunan sa. Taji dadi sosai da suka karbi katin gayyatar da tayi musu na bikin 'ya'yan nata.

Domin dukkanin su basuda wani hali marar kyau. Kowanne acikin su tun daga kan wasila zuwa Amnah sunada kyawawan dabiuu nagartattu masu kyau sosai.

"Anees yana waje shi zai Kai ku. Ai kunsan Anees ko?"

Suka daga kai gaba daya. Nawraah kamar ta fashe da kuka. Wannan dan wulakancin da baya magana ? Idan sukazo wuri ya tashi yabar gun, Koda tare su ke da marwaan. Gani take tsana ce kawai ko kyama suke masa, batasan so ne sanadin buyar da yake ba.

"Eh mun san shi" ta fada dakyar tana duban Raudah.

"Yauwa to yana waje. Wait Ina wayar ki. ?"

Nawraah ta mika mata wayar. Hajia Qibdiyya ta zuba nambobin Anees aciki ta danna Kiran sa ringing biyu ya dauka tache,

"Ga yaran da nace ka Kai su har kofar gidah nan banda gudu da mota please. Idan ka Kai su ka duba agidah akwai sauran motoci? Idan akwai akawo hudu nan please mutanen da yawa asamu a rage Wa mutane wahalar abun hawa"

"Toh.... Ma... Mi" ya fada a rarrabe yana zare wayar daga kunnen sa.

Tunda ta kira da lambar sunan Nawraah ya bayyana ta Truecaller da tayi saving da 'Nawraah Junaid' Nanata sunan yayi a saman labbansa yana murmushi. Kafin ya Kai hannun sa yana shafa rubutun dake dauke da sunanta ta a jikin screen din wayar tasa.

Nan da nan yayi saving lambar tata da N ya kara emoji na zuciya da kwado❣️🔐. Ya langabar da kansa ajikin sitiyarin yana murmushi. Ji yake tamkar an amsa dukkanin bukatin sa da burikan sa, wai yau number Nawraah ce awayar sa? Kuma gashi Nawraah Zata shiga motars sa ya Kai su gidah?

Wani murmushi mai taushi ya sake kufce masa. Ya murmusa kawai yana ajiye wayar akan saitin zuciyar sa. Daga kansa da zeyi kenan yaga futowar su

Itace agaba itada Amnah kanwarta. Ta zare facemask din hannunta tana tafiya tana gyara zaman mayafin jikinta.

Dama gashi akwai haske sosai awajen duk kuwa da dare ne Amman wasu irin fitulu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login