Showing 33001 words to 36000 words out of 69829 words

Chapter 12 - KWANKWASON JIMINA BOOK 2 COMPLETE BOOK 2 hausa novel

24 Aug 2024

8956

Ko da bayan da suka kammala lectures na rarar Nawraah ta nemi waje ta zauna a wajen kujerun garden dinsu tana jiran marwaan.

Shiru shiru ba marwaan ba alamar sa. Jikinta yayi sanyi ganin bai zo ba, Kuma bai kirata a waya ba.

"Ya tabbata yanada masaniya kenan?" Ta tanbayi kanta tana girgiza Kai

"Yaron dan wanda ya kashe miki iyaye da wa kikeso?" Wata zuciyar ta gaya mata.

"Amma how sure are you da marwaan yasan komai? Kana kallon sa kasan baiyi zubin mugunta ba. Tabbas bashi da masaniya akan wadannan mugayen"

Ta sake kunna wayarta tana refreshing ko network ne. Nan ma shiru kira bai shigo ba. Ta duba sakonnin ta nanma ba text message daya ke tura mata duk safiya da rana da dare da asubah. Ta sake danna Wani madanni tayi restarting wayar baki dayan nanma shiru.

Mikewa tayi daga zaunen da take. Ta fita daga garden din tana kalle kallen makarantar inda zata ganshi. Babban abunda ya sake tayar mata da hankali shine ba motar sa awajen faka motoci.

Ranta duk ba dadi ... Ta dubi wayarta taga lokacin daukar Amnah yayi. Don haka ta fuce daga department din ta dauki hanyar makarantar su Amnah.

Yana zaune daga cikin motar agaba wajen mazanunin driver. Kan motar tasa daman tuni ya setata tun kafin suzo makarantar.

Yana zaune ya kifa kansa akan a steering yana duban ta duk sanda ta nufi wajen ta zauna tamkar ko da yausheml

Yanayin yadda duk ta hargitse ne yasa shi kasa nutsuwa. Kullum yaumin inde zasuyi daukar darasi sai Anees yaje makarantar kawai don ya kalleta yaji dadi a rai da zuciyar sa.

Duk sai yaji bai ji dadin samunta a wannan halin ba. Yaga tanata duba screen din wayarta cike da damuwa ya tabbatar rashin ganin marwaan ne.

Har ta kule bai dena kallonta ba sai data fuce daga cikin makarantar gaba daya. Ya sauke nannauyar ajiyar zuciya. Haka kawai ya samu kansa shima cikin wani irin yanayi mai wuyar fassarawa.

Wayar sa ya dauka ya danna sunan marwaan ya kira shi. Bayan sun gaysa ne yake cewa dashi

"Aboki na ya abubuwan ne?"

"Steady nake gaya maka maza"

"Allah yabar senior man"

"Kai ne senior man Kuma comrade. "

Anees yayi murmushi. Kasan zuciyar sa yana mamakin abunda yasa marwaan baya daukar wayar Nawraah. To ko dai bashi take nema bane? Ya samu kansa da cewa d amarwaan

"Ina mutuniyar ka ne?"

Marwaan na kan kujera a dakin sa dauke da computer dake gaban sa, yana wani bincike yace

"Wa?"

"Yau rabin rai din naka i kake cewa wa?"

"Baba aiki ne agabana Allah. Wai habibty kake nufi,?

"Ohocan ta katse muku. Nawraah dai eh ita"

,Marwaan ya dan yi shiru bai sake cewa komai ba, Anees ya yi murmushi don a zaaton sa fada sukayi na masoya....

_ADVERT👇👇_

_YERWA INCENSE AND MORE_
_(DUNIYAR KAYAYYAKIN KAMSHI MASU MATUKAR DADI DA KAMA JIKI, GIDAH, KAYA DA SAURAN SU)_


_INA MA'ABOTA TURARE? KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE_
_TSAFTA KUMA TANA CIKIN IMANI… TOH KU MAR-MATSO KUSA_

_MUN KUMA ZUWA DA HAJAR KAYAYYAKIN_

_*YERWA INCENSE AND MORE*_
_DOMIN SAMUN ZAFAFAN TURARUKAN WUTA NA GIDA, KAYA, JIKI, TSUGUNNO, GASHI... AKWAI KHUMRAHS MASU DADI YAN BORNU, CHADI, SUDAN DAMA SENEGAL, AKWAI OIL PERFUMES, DA TURARUWAN MOPPING DANA WANKA DANA WANKI DANA GADO DA KUJERU DA BANDAKI DA DRAWER DA MOTOCI.._

_AKWAI MAN GASHI NA FESAWA ME SA KAMSHI DANA KITSO. AKWAI KAYAYYAKIN KAMSHI DANA GYARAN JIKI SOSAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA. •_

_ADIRESHI: KANO.. AMMA SUNA TURA KAYAN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE..._

_INGANCI KYAU RAHUSA DA DADEWA A GIDAH DA KAMSHI SAI KAYAYYAKIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE_

_NAMBAR WAYAR SU: 08095215215, INSTAGRAM/THREADS/TWITTER:yerwaincense_and more_

_YOUR NUMBER ONE STOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS... THEY 'VE GOT YOU AND YOUR HOME COVERED_
[5/13, 2:00 AM] Hafsaat🧕💞: _K'K'J_
_(M/W/S)_


_BOOK TWO_


_✍️:MX_


_26_


:::::::::

*Marwaan ya dan yi shiru bai sake cewa komai ba, Anees ya yi murmushi don a zaaton sa fada sukayi na masoya.

"Kayi shiru"

"Ba shiru nayi ba baba" marwaan ya amsa shi

"To meya hadu ku,?"

"By Allah bamuyi fada ba Kaman ta har zance munyi a parlorn Mami? Kawai I'm a little tii busy ne. Shysa"

"Kana too busy Kuma ka dau Kirana?"

",Banza... Saboda idan da habibty muke waya Sai mu Kai sama da awa hudu Muna abu daya. Kai kuwa yanzu zamu gama na kashe wayata,"

Anees ya sakeyin murmushi mai taushi. Ya samu kansa da tsokanar da yake masa kullum yace,

"Haba my love, waiting man do man?"

"My love? Kai da Ina kuwa dana zabga maka marf, Banza, Soko, wawa ,Dan wahala"

Anees ya fashe da dariya mai cigaba da tsokanar marwaan. Har ya samu dai ya ragewa marwaan din bacin rai dake cikinsa. Don daga sautin muryar sa Anees ya gano yana cikin damwua.

Yana karasa waya da marwaan ya kunna motar sa ya tasheta a hankali yake tafiya yana tuna zantukan marwaan.

Ya girgiza kai kawai ya wuce gidah. Ya shige can wajen parking lot ya nufi parlorn mamin sa Kai tsaye.

Ya sanya hannu zai tura kofar kenan ya jiyo muryar Nawraah na cewa,

"Yanzu mami ya zanyi? Ina son sa Ina kaunar sa. Munyi wa juna alkawarin aure. Mami anya marwaan yanada masaniya kan iyayen sa sune suka kashe mana Iyaye da babban wan mu?,"

Bude baki Anees yayi alokacin da Nawraah ta karasa zzancen. Ya samu kansa da jingina da bango yana jiyo sautin muryar Nawraah .. yadda take magana kadai mai zai tabbatar maka tana cikin damuwa. Sannan gefe daya jin yadda taake magana ba karamin sanya shi nutsuwa yake ba.

Kunnuwan ba zasu iya jin tsayawa karashen labarin da take bayaraa ba, ta kashe iyayen ta da babban wasu..

Daki ya koma ya shige bandaki ya watsa ruwa. Yayi alwala ya sauya kayansa zuwa marasa nauyi..

Wayar sa ya dauka yana duba hotunan ciki. Rabin hotunan wayar dauke suke da hotunan Nawraah.. ya Saka hannunsa yana shafa fuskar ta a hotan .

Ys kunshe idanu ya bude su akan labbanta masu taushi, gashi labbanta jajayene kamar ta sanya jambaki..

Ya samu kansa da rungume wayar tamkar ita ya dora a kirjinsa haka yake ji.

"Ina son ki, Ina son ki Ina son ki, . na kaunar ki Nawraah. Kaunar ki Allah ne ya dasamuni Nawraah. Kaunar da nake miki zatamun illa Nawraah. Ina cikin yanayin da baki ba zai iya furtawa ba haka ma alkalamii. Ki sanii har gaban abadan ba zan taba mantawa dake ba. "

Ganin tunanin da yake da zubar da yake shi daya kamar sabon mahaukaci.
Mikewa yayi ya dauki charbin sa ya nufi masallin da ke cikin gidan na su. Shiga yayi ya zauna kafin a kira, Suka idar ya zauna yanayin lazumi har.....

_ADVERT👇👇_

_YERWA INCENSE AND MORE_
_(DUNIYAR KAYAYYAKIN KAMSHI MASU MATUKAR DADI DA KAMA JIKI, GIDAH, KAYA DA SAURAN SU)_


_INA MA'ABOTA TURARE? KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE_
_TSAFTA KUMA TANA CIKIN IMANI… TOH KU MAR-MATSO KUSA_

_MUN KUMA ZUWA DA HAJAR KAYAYYAKIN_

_*YERWA INCENSE AND MORE*_
_DOMIN SAMUN ZAFAFAN TURARUKAN WUTA NA GIDA, KAYA, JIKI, TSUGUNNO, GASHI... AKWAI KHUMRAHS MASU DADI YAN BORNU, CHADI, SUDAN DAMA SENEGAL, AKWAI OIL PERFUMES, DA TURARUWAN MOPPING DANA WANKA DANA WANKI DANA GADO DA KUJERU DA BANDAKI DA DRAWER DA MOTOCI.._

_AKWAI MAN GASHI NA FESAWA ME SA KAMSHI DANA KITSO. AKWAI KAYAYYAKIN KAMSHI DANA GYARAN JIKI SOSAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA. •_

_ADIRESHI: KANO.. AMMA SUNA TURA KAYAN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE..._

_INGANCI KYAU RAHUSA DA DADEWA A GIDAH DA KAMSHI SAI KAYAYYAKIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE_

_NAMBAR WAYAR SU: 08095215215, INSTAGRAM/THREADS/TWITTER:yerwaincense_and more_

_YOUR NUMBER ONE STOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS... THEY 'VE GOT YOU AND YOUR HOME COVERED_
[5/15, 8:41 PM] Hafsaat🧕💞: _K'K'J_
_(M/W/S)_


_BOOK TWO_


_✍️:MX_


_27_


:::::::::
   Har ya zuwa sanda aka fara kiraye kirayen sallar isha'i. Bayan sun idar ne ya tashi ya fita daga cikin masallaci..

Hanyar sashen hajia Qibdiyya mahaifiyarta su yayi. Daga can nesa ya hango futar su Nawraah da Amnah kanwarta.

Ya tsaya yana duban su har suka kulewa ganinsa suka fita daga gidan zuwa gidan marayun da suke rayuwa acikin sa.

Katon numfashi yaja ya sauke yana mai Saka hannu akan goshinsa. Yaa dan runtse idanunsa sabdoay tsananin yadda kansa ke masa ciwo yana barazanar fadowa kasa.

A daddafe ya karasa bangaren mahaifiyar su, Sanyayyan turaren wutar keci a parlorn kamar koda yaushe ya sanya shi lunshe idanu ya baje hanci yana shakar ni'mantaccen turaren wutar sandal munawwara exclusive na kamfanin turaren yerwa incense and more. Ta ke yaji wani kaso na daga bacin ran da yake cikinsa ya rage.

"Anees..."

"Mami" ya fada yana juyawa wajenta. Don baki daya ma hankalinsa ya tattare kan nimattaccen turaren dake ci ahankali mai musulmin kamshi..

"Naam Mami" ya amsa yana juya Kai zuwa inda take a zaune. Ya nemi kujerar gefenta ya zauna yana dubanta

Sai kuma ya juyar da kansa wajen turaren wutar dake ci ya ce,

"Mami wannan scent din ya mun dadi sosai"

"Mashaa Allah.. na kamfanin turaren wutar yerwa incense and more ne. Kasan turaruwan ta gaskia ba na banza Kuma kowa zai iya saya mai kudi da talaka, Abun sake burgewar Kuma kasan menene?"

Anees ya girgiza Kai alamar a'ah tache,

"Tiraren ta top notch ne. Sannan sunada matukar kama guri ko kaya ko mota da sauran su"

"Mashaa Allah" cewar Anees. Ya dan saci kallon mahaifiyar tasa yagsabaki daya yanayinta ya sauya kana dubanta kasan tanada abunda ke damun ta.

"Meya faru mami?"

"Me kwa fa auta?"

"Mami naga face dinki ba yadda na saba gani bane, Da alamar akwai tabbacin abunda ke damun ki. Mami please? Ki gayamun abunda ke damun ki..ko wadannan yaran da suka futa ne yanzu daga nan?"

Hajia Qibdiyya tayi hanzarin girgiza Kai tana cewa dashi,

"Wayyo karka dau hakkin su..... Kasan su waye su?"

"Mami kin fada several times ai. Maman su itace wadda ta fara mana abinci dinnan me dadi"

"Eh anyi haka... To wadannan yaran kusan ince amana ne a agurin mu. Dubada Allah yace kada abari maraya ya zubar da hawaye..kar a zalinci maraya. Musanman ma sudin na gaba gaban farko ne a marayun . Nawraah, Amnah, Ashfeef. Ka ji su su uku "

"Okay Allah sarki. Allah ya musu rahama Amin. Su Kuna Allah ya raya su Amin... Nagansu ai da zanzo nan din itada kanwar su sun tafi"

"Eh nan tazo muke magana ne"

"Mami akan marwaan dai?"

"Eh akansa ne. "

"Wai meya faru?"

"Ba sai ka saji ba Anees. " ta fada tana kauda kanta gefe

Zuciyar sa ta shiga yi masa zugi. So yake ya sanarwa mahaifiyar tasu abunda yakd game da Nawraah acikin zuciyar sa. Ba kadan ba ya kamu da sonta. Kaunar da zata iya masa illa. Ta masan ma illa ,don ko sunanta aka kama wani abu yake ji babba game da ita.

"Mami dan Allah... Kakki manta nasan abunda ke tsakanin su da marwaan."

Hajia Qibdiyya ta dube shi tana sauke ajiyar zuciya tache,

"Wani irin alamarinne mai sarkakiya yake faruwa Anees. Abune da mu kanmu da ku muke cikin sa, lamarine babba dake tunkarar mu..sai dai fatan samun nasara kawai. Allah yasa mu dache Amin"

"Aameen Mami. Amma dan Allah Mami ki sanar mun ko menene Dan Allah ba nutsuwa atare da ni"

"Anees.... Kayi alkawarin ba zaka gayawa wani abun da zan fada maka ba? Dik kuwa da nasan halin ka bakada dibar zance da sauran su. Amman wannan maganar da zan gaya maka me sammatsi ce dake bukatar sirri"

Anees ya daga Kai, Don ya dauki maganar dazun dayaji sunayi da Mami daya kabe ajikin Kofa ya sauararai a matsayin kuskuren suna Nawraah ta kamo ta fada., Ko Kuma kunnuwan sa basu ji masa sosai ba, Sam ma zuciyar sa ta ki amincewa da maganar da kunnuwan sa suka saurara. Ya samu kansa da ce mata

"Nayi alkawari Mami inshaa Allah bazan fada ba. "

Hajia Qibdiyya ta danyi shiru na dan wani lokaci kafin tache,

"Anees... Ina kadarorin baban ku da muka ce ku dinga taya mu da addua Allah ya tona wadanda suke da hannu aciki. Allah Kuma ya kwato masa hakkin sa ko?"

"Eh Mami anyi haka"

Hajia Qibdiyya ta sake nisawa kafin tache,

"Naga sheda a azahiri da idanu na. Naji da kunnena ganau ce ni da jiyau. Evidence sosai dai Anees. Kasan waye ne behind duk wadannan abubuwan daya danganci kadarorin baban ku? "

"Mami waye?"
Anees ya tanbayeta yana zare idanu

Hajia Qibdiyya ta danyi murmushin yak'e tache,

"Alhaji sambaso, mahaifin su Marwaan, da temakon Alhaji ateeks shima abokin ga mahaifin ku"

Anees sai ya hangame baki yakasa cewa komai cikin tsananin mamakin sunayen da ta ambata, Wanda ko a mafarki bai taba zato ko tsammani ba. Duniya Ina zaki damu? Dama ance makashin na g**ka.

Gaba daya gabobin jikinsa sai suka saki. Ko wani rassa na jikinsa ya shiga tsuma na daga labari mai tsoratarwa da suka ji.

Hajia Qibdiyya ta sake sauke katuwar ajiyar zuciya ta cigaba da cewa,

"Sannan mahaifan yarinyar nan da babban wan su. Suma kashe su aka yi da daya daya. Ban gayawa baban ku ba saboda ranar daya dawo daga aiki a ranar mukayi maganar da Nawraah. To Kuma nache zan sanar masa. Sai kuma ya dawo baya jin dadin jikin nasa dinnan har ya rubuta maka magani yace kasayo masa? To ganin jikin nasa ba dadi hakan yasa ban yi masa zancen ba. Dubada bayada lafiya kar na Kara tayar masa da hankali."

Anees yayi shiru yanata jujjuya zancen a zuciyar sa. Duk tsananin amintar dake tsakanin iyayen nasu? Baban su da baban marwaan aminai ne. Haka zalika Dr bintu mahaifiyar su Marwaan ma aminiyar Mami ce.

"Mami Kuma an tabbatar su ne?" Ya samu kansa da tambayar ta hakan.

"Kwarai ma kuwa Anees. Akwai shedar komai na recoding muryar su da Kuma faifan bidiyon"

Anees ya sauke gwauron numfashi cikin sanyin jiki mai dauke da damuwa yace,

"Yanzu ya ake ciki Mami?"

"Sai yau zan wa baban ku maganar tunda har ya samu sauki yaje asibiti. Yace mun ba ze biya ganin patients ba na private consultations yau ba, gidah zai wuto kawai. So zamuyi zancen da yardar Allah..Amman kafin sannan Anees kada ka bari maganar nan ta fita, Kuma ba wai hakan na nufin zaka daina hulda da marwaan ba..tunda bamuda tabbacin yasan abunda iyayen sa suka aikata"

"Hasbun Allahu Wa ni'imal wakil ..." Anees ya furta yana jujjuya kansa cikin alhinin maganganun da sukayi

"Sai addua kawai Allah yasa mu dace".
.
"Amin .. to Mami kashe iyayen nasu da wan nasu. Shima iyayen su Marwan dinne an tabbatar?"

"Hmm Anees kenan. Ba zanyi mamakin tambayoyin da kake ba sabida ni Kai na ba dan naga sheda ba wallahi bazan yadda ba. Amman komai nagani Kuma naji. Kusan ince Dr bintu ma tasan komai game da lamarin amman kaga Koda nake gaya mata rasuwar malama hindun nunawa tayi batada masaniya Anees. What a cruel world. Wannan rayuwar da ba abakin komai take ba yau ga naka gobe ga ka waninka. Amman wai ace musulmi yan uwan musulmi sune suke kashe kashen rayuka kamar cinnaka? Saboda mahaifiyar su Nawraah malama Hindu marigayiya kasan da zamuyi tafiya sai Dr bintu face dan Allah ta dinga zuwa tana mata abinci cuz taji yadda nake kuranta abincin ta, na taba aikenta karbo sako ma to harta taya su abinci Alhaju sambaso wai yayi ta Santi, to sai take neman alfarma. Na roki Hindu tace ba damuwa sai tayi,

"Anees baiwar Allah nan tagama musu abinci ta Kai. Ita da Nawraah dinnan ne kuwa sukaje . Yarinyar ta saka recoding a waya tana recording wakar Maher Zain da ake a tv din parlorn. Sai ita marigayiya taje takai abinci sai ta jiyo suna maganar kadarorin mahaifin ku Alhaji ateeks ya amince da sauran shareholders komai ya koma mallakin Alhaji sambaso. Anees wai har bintu ce zata dinga zagina tana fadan sunaye akai na da mugun alkaba'i . To sai ita marigayi Hindu taji, hannunta rike da kwanukan abinci a tray sai ta zubar a kasa. Saboda dimaucewa na abunda ta saurara. Sai bintu tayi kanta. Marigayiya Hindu ta shiga magiya tana cewa ba abunda taji ita daga rajat ma tabar aiki. Bintu tace tadama kunnu. To annanne Nawraah taje daukar wayar mahaifiyar tasu. Na karkare maka zance dai Alhaji sambaso shi ya kashe marigayiya Hindu hit and run case ne. Ya bigeta ya gudu abins a,a then later bayan abubuwa sun faru mijin ya gano Alhaji sambaso ne ya kasheta cikin fushi kagane sunata mayarda magana wa juna. Sai Alhaji sambaso ya tura shi mahaifin Nawraah malam Junaid. Ya fadi ya mutu"

"Sai kache film Mami? Innalillahi Wa inna ilaihi rajiun "

"Hmm Anees rayuwar nan,kaji tsoron mutum kaji sai babban wansu bayan rasuwar uban. Yana amfani da wayar itamalama Hindu marigayiya nan yan gano recodings din ya saurara sai yaje wajen Alhaji sambaso din. Kai Inna lillahi Wa inna Ilaihi raji'un "

"Meya faru Mami?" Anees ya tanbayeta cike da damuwa

"Long story short ... Alhaji sambaso ne ya sa aka raba shi da ran sa. Kasan ta yaya?"

"Yadda muke maganar da Nawraah tace mun cause of death din shi yayan nasu...saboda tace a ranar da wan nasu zaa kashe shi ne yabata wannan wayar da komai yake ciki. Yache ta yi amfani da ita idan ta fara school amman karta ta bude media and files sai tana ajin uku zuwa na karshen gama jami'a. Tache yanayin sa ya sauya cikin firgici yake..."

"Eh eh Mami"

"Katuwar mota ce tazo ta bige su acikin motar yake taxi, komai da komai nasa ya kone. Subhan'Allah . Yaa Allah ka rabamu da zama ajalin wasu. Ka Kuma raba wasu da zama ajalin mu. "

"Gaskia dai astagfirullah. Innalillahi Wa inna ilaihi rajiun..."

"And you know the most funny and cruel part?"

"No Mami. I'm all ears"

"Wai tsabar mugunta sune suke aika musu food stuffs irin suna claiming saint and caring, sannan bintu taba yaran scholarship a alhaaramein har su gama jami'a irin ga masu tausayin nan. Kai wasu abubuwan ma ba dadin fada ,Ga matar bappann su hates them plus sauran dangi sunki karbar su. Wato Anees sai kana raye ake yi da kai da iyalan Ka idan ka rasu bawon albasa ma yafi ka da iyalan ka daraja da matsayi awajen su. Allah ya sa mu dace"

Ameen Mami"

"Ga fate ya hada 'ya'yan su soyayyah. Har zancen aure ya shiga tsakanin su sunason juna. Iyayensa sunki saboda ba dangin kudi bane plus wadannan abubuwan Subhan'Allah

"Allah ya shiga lamarin su"

",Ameen"

Door bell ce ta fara Kara. Anees ya mike zai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login