Showing 54001 words to 57000 words out of 69829 words

Chapter 19 - KWANKWASON JIMINA BOOK 2 COMPLETE BOOK 2 hausa novel

24 Aug 2024

8963

badan bappah ba da tuni jin dadin duniya ma kin dena yin sa. Ya Ahmad, Layla ku mun hakuri .Amma mahaifiyar ku lamarin tsanar da take mana yayi tsamari.... Aunty ni da yan waiana kallon ki kawai muke.."

"Dalla can ..wannan wannan wannan yarinyar dama ana cewa sanda kina karama waye waye ba zaki magana nmba da surutu, idanun ki Ina kallon sutun a zamin baya na gano bakida da'aa.."

"Aunty kenan. Me bibiyar mu dik inda muka sanya kafa. Duk wani farin ciki nida yan uwana bakkya so mu samesu. Kokari kike ki dakile komai"

"Ke dallacan.. kinata zuba baki ya bude ana bin maza ko? To ki tsaya kiji dakyau nafi karfin na bi sahun kafafun ku baku Kai matsayi na ba, yan Wahala.. ku Kuma Kun tsaya sakeke yarinya karama tana gasawa mahaifiyar ku magana" ta fada tana dankarawa su Layla harara.

"Me zasu ce?. Ai fadan kine wannan sai yadda zaki karashe kedaya" cewar bappah Auwalu

"Auwalu kenan. Ka gaya mata idan tana cin kasa ta kiyayi ta shuri. Wallahi wallahi yarinyar nan Nawraah naga alama. Tana nan akan wannan tankwararran halin na ta na KWANKWASON JIMINA CE MAI WUYAR SHAFAWA. toh wallahi zan dagargaza kwankwason nata naga bakin da zata dinga magana dashi .. ko hukuma ta shiga tsakanina da ke. Tunda ke din banza ce. Marar da'a. Saboda maza na baki kudi kin kode kin zama fara kina wani fiffika kina iyayi"


"Aunty kenan Ina kyautattan zaton ko ya yanki ba zasu kaini kyakkyawan hali ba, Na biyu anty zaki iya zuwa hukumar ki ce su shiga tsakani na dake. Da ni dake zaa ga Wanda hukuma zata rike. Domin komai nisan dare gari zai waye, Allah zai bayyana mai gaskia"

Tana karasa fadaar abunda za ta fada tana rike da hannun Amnah suka tafi. Ashfeef dama tuni ya fita. Suka jere suka nufi gidan marayun nasu..

Babba Auwalu duk da dare ne ba wajen zuwa. Takaicin Kalaman nusaiba ya sashin sanya slifas dinsa ya futa

Yayinda ahmad da Layla ma kowanne yayi dakinsa suka bar nusiba tanata maganganu..

Yadda Nawraah ke fadan maganganu tabbas tasan wasu abubuwan sun fito ne?

Hannunta na rawa ta dau waya ta na Kiran Dr bintu..Amman Kiran duniya wayar taki shiga batasan ta sanya ta a blocked number ba.


:::


Su Nawraah na futa daga gidan bappah Auwalu ta sauke babban numfashi tana goge hawayen fuskar ta


Ta sanya kanta ta dubi gidan, mallakar su ne a baya. Wanda a yanzu wani mutumi ne gidan ya dawo hannunsa gashinan yana modernizing dinsa ma


Suka karasa gidan na su suka shiga. Su Raudah suka tashi suna rungumeta jin dadin sun dawo

Nawraah ta janyo wayarta dake jaka missed calls rutudu na hajia Qibdiyya dake a silent tasaka baaji. Nan da nan ta kirata back .bayan sun gaysa nawraan ke gaya mata yaddaa akai basu samu tafiyar ba

Hajia Qibdiyya ke sheda mata da zuu Alhaji sambaso yayiwa Mai dakinsa Dr bintu auren bazata. Babban abunda zai sake tsoratata ma shine aminiyarta ya auro Kuma batada masaniyar yana naman auren..to tana dai nanne tasan zuciyarta da gangar jikinta dai ba lafiya dan ance har kwanciyata tayi asibiti bayan ta Suma..

Nawraah tayi mamaki kwarai matuka da maganganun da hajia Qibdiyyata fada mata. Lalle Allah ne ya fara nuna alhakin su akan su.

"Inshaa Allah zuwa da safe ko rana haka. Zaa kawo mota ta dauke su su tafi can yankin su kafin lamura su gyaru. Zaku zauna acan har Sanda Allah zai kawo karshen masifun da suke ciki.....










ATUWA 🥳
[6/8, 9:31 PM] Hafsaat🧕💞: _K'K'J_
_(M/W/S)_


_BOOK TWO_


_✍️:MX_


_41_


:::::::::

WASHE GARI...

  Wasu daga cikin kashe kashen gidajen na cikin farin ciki marar misaltuwa. Saboda haka sun tashi cikin kwanciyar hankali da dadi mai ratsa zukataa

Ya yinda wasu basu runtsa bama saboda bakin ciki da alhini marar misaltuwa..

To haka rayuwar take dama yau dadi gobe akasin haka...

A ranar hajia Qibdiyya ta tura zungureriyar mota ta dauki su Nawraah. Da fari nusaiba Kin yadda tayi ta shiga mota ta Kuma ce bada yaranta ba.

Dakyar dai bayan bappah Auwalu ya kasa hakuri ya zunduma mata mari da karin cewar gida ai nasane don haka sai dai ta zauna a kwararo a titi idan a naduka zata zauna bata zauna agidan ba, su bar garin su..

Dakyar ta hakura harda sharar hawayen bakin ciki ta shiga mota tanayi.

Basu dire ko'ina ba sai yankin bunza garin su na da... Sun samu tarba sosai daga mutanen yankin bunza

Aka sauke su a gidan Mai garin yankin bunza. Waje akaa basu wadatacce Mai dakuna da da bandaki har biyu da dakin girki.

Zasu biya kudin gidan ma Mai gari yace za su zauna har Sanda Allah ya kawo kagshen zaman su. Saboda baya manta alkhairi da zuriyar hamidniyya sukai masa dama ahalin yankin baki daya.

Abinci kuwa haka aka dinga kawo musu shi daga gidaje kala kala. Nusaiba sai yamutsa take. Tana daga Kai Kai kache wata matar mai kudin ce tazo dabatasan kan yankin ba. Bayan tsatson can ce Kuma acan din aka haifeta..

Dakuna hudu ne, don haka bappah Auwalu ya s
Dau daya, nusaiba tana daya, Layla da Nawraah da Amnah suna guda daya. Ragowar daya kuma Ahmad ne da Ashfeef.

Da katuwar rijiyar su a gefen shuri. Sannan abinci Mai gari yacs kar bappah Auwalu ya damu zaa dinga kawo musu abinci har na tsayim watannin uku.

Alummar yankin bunza nada karamci sosai kusan yanzu da shekaru sukaja sun sake sanun abunda duniyakeciki. Tattalin arzukan su na wasu wajen sun dawo. Don Mai gari ma yace zasu zauna da bappah Auwalu acikin duwatsun da aka farfasa an samu gwalagwalai. Sannan shanuwa daya da suka manta ta hayayyafa ta Tara garke .

Akwai makarantu sosai da aka sake bubbudewa. Yanzu har matan garin na zuwa boko sosai. Dama akwai arabi da allo. Komai dai yanzu bunza alhamdulillah. Abu daya ne yankin bunza har yanzu basu sauya shi ba ba Kuma su soke shi ba. Since al'adar su ce bai ibadah ko addini ba. Don haka ba zasu dena ba...

dukkanin Mai karatu dake bibiyar littafin KWANKWASON JIMINA tun da farko zai san, Rafin rau Wato ebo ruwa a kogi rafin rau da mata keyi suna kaiwa godajen angwayen da zasu aura. Sai Kuma mazan dake nome gona baki daya. Amfanin hakan shine ruwan da shi amaryar zata dinga girki suna sha har ya kare..Yayinda amfanin noman da angon yayi Kuma shi zasu dinga girkawa har ya kare. Wannan itace aladar kadai da mutanen bunza suka kasa denawa..

A haka su bappah Auwalu suka cigaba da zama a yankin na bunza. Abinci dai alhamdulillah suna samu. Ruwa Kuma akwai a rijia janyowa kawai zaai.

Amman duk da hakan nusaiba sai dai ta Saka kullum ashfeef ne zai dinga ebo itace a jeji ta tsiri dafa ruwan zafi tace dashi za'ai wanka.

Yayinda Nawraah Kuma itake janyowa ruwa a rijiyar gidan kullum. Sai afakaice ne idan bata kalla Layla zata jawo itama. Yayinda ahmadu ke bin ashfeef su je tare idan sun dawo kofar gidah sai yasa yashiga dashi ciki...

Su bappah sanu suka zo musu ziyara bunza. Shi dai bappah auwalu daga gaisuwa bai sake bi takansu ba yayinda Nawraah ma suna gaysawa suka tashi daga wajen..

Haka suka karaci zaman su suka tafi. Kudin da suka bawa bappah Auwalu ma kin karba yayi suka bawa nusaiba.

Yace ba ruwansa da su. Tunda dama basa kaunar dan uwan su junaidu da ya rasu ma su kaki rike iyalan nasa. Yafita harkar su baki daya.

Hakama su Nawraah duk hirar da matan su bappah sani suke da su Nusaiba da Layla kanzil bata ce ba tana daga waje tana jan charbi abinta Amnah na gefe tana wasan girki ...


*BIRNIN NADUKA*

Ranaku nata shudewa abubuwa nata faruwa. Yau da dadi gobe akasinta. Dama haka rayuwar baki daya ta ke.

Duk wasu bincike da shedu an kammala su na kashe kashen rayukan da akayiwa iyalan marigayi Junaid da mai dakinsa marigayiya Hindu da babban dansu marigayi Ashir.

Dr Abububakhr ya tsaya tsayin daka wajen ganin komai ya kammala tare da temakon Mai dakinsa hajia Qibdiyya da Anees autan su. ..Kuma bangaren kadarorin Dr dollars din duk an gama bincike an dawo masa da komai har takardun original. Rana kawai aka Saka da zaa damke Alhaji sambaso..

Marwaan da kansa ya samu Anees yana gaya masa komai harda kisan da iyayensa suka yiwa ahalin su Nawraah. Anees ya riko hannun marwaan suka jesu har gaban iyayen su. Marwaan din ya sake nanatawa yana hawaye. Anees na taya shi hawayen yanadafa kafadar marwaan din yana bashi hakuri kan shima dagaa baya sani. Amman saboda gudun kada zumuntar su ta baci Mami (hajia Qibdiyya)tache kar ya nuna masa komai saboda kar su bata.

Nan suka shiga bashi hakuri. Yana basu shima yana Kuma sanar da su komai dangane da abunda ya sani da karin bayani akan irin fatali da mahaifin nasu Alhaji sambaso yayi dasu tunda yayi aure..

Ya futa harkar su Baki daya yanzu. Da su abinci da karsu ci uwar su dayaa awajen sa. Kawai dai suna cikin gidan suna rayuwa ne.kuma ya kwace dukkanin moticin su yace su dena hawa..

Rayuwa ta musu zafi sosai. Mahaifiyar su itace ke dauke dasu yanzu itama bashi ne da ita ba, kullum cikin ciwo take.marwaan na fada yana kuka

Su Dr dollars na bashi hakuri cike da tausayinsa . Don marwaan din shi kadai ya futa zarra agidan nasu tun a baya . Domin lily ma ta dakko izza irinta Dr bintu..

Haka dai suka yita bashi hakuri da baki. A ranar nema Dr dollars din ke fadin zagon kasan da sambason ya masa ya handame kadarorin sa...

Ya Kuma dakko motar sa daya ba Wa marwaan da zai tafi gidah. Ya debi kudi ma ya bashi...

Anees yaja motar ya tafi gidah yana yaba kyawun hali da dattako irin na Dr abubuakhar dollars.....




AFUWAN DA POSTING DIN DARE. WALLAHI BANIDA LAFIYA NE AMMA DA SAUKI. INSHAA ALLAH ZAA CIGABA DA POSTING AKAI AKAI...



HANSAI🥳
[6/8, 11:19 PM] Hafsaat🧕💞: _K'K'J_
_(M/W/S)_


_BOOK TWO_


_✍️:MX_


_42_


:::::::::

A kwana a tashi ba wuya awajen Allah.... Marwaan nata kokarin ganin komai ya saisaita a bangaren mahaifin sa da mahaifiyar sa, Amma lamarin yaki yiwuwa, baki daya ma yanzu inji ma baa kunnawa dasu anyi wiring daban ana kunnawa gidan amarya

Rannan kuwa har cikin gidan nasu kubrah da Alhaji Sambaso suka shiga parlorn na Dr bintu .

Kubrah ta kukkuna voice notes da wayar da su ke da dr bintu akan shiga bokayen da Dr bintu ke aikata.

Gashi agaban su Marwaan da lily. Ga maaikata. Abun kunya, Dr bintu ta hau bori tana maganganu. Alhaji sambaso ya wanketa da mari.

Atakaice dai Dr bintu ta fito ta fara farfadan komai agaban yaran da hajia kubrah. Dukkanin abunda Alhaji sambaso ya aikata ta fada, Da lefukan kubrah data yi da karin cewar kubrahn karuwace ...

"Kuma sai naje har gaban Marwaan na basu hakuri na fadi komai"

"Ki fadi me? Yo ai na a'ika da mutane na garin kije kuyi abunda zaki. Motar kamfanin shareholders Dr dollars yana waya da matar sa ta aika musu sun koma can yankin su ko. Zaku sha mamaki da ke da y
'yayan ki munafikai"

"Alhaji yayan cikin naaka kake cewa munafikai?"

Marwaan bai jira jin karashen ba ya rike hannun lily suka yi hanyar mota. Lily ta riko uwar tasu

Mita suka bude suka shiga marwaan yaja ta da karfin gaske.

Alhaji sambaso ya shiga motar shima yana biye dasu a baya yana waya..

Sannan a hanya marwaan ya kira Anees yake sheda masa halin da ake ciki. Anees ya sanarwa nasa iyayen suka dau hanya suma

Baki daya sai suka nufi yankin bunza dukan su. Alhaji sambaso yanata waya da wadanda ya aikata.

Yayinda Dr dollars da hajia Qibdiyya da Anees Suma sun tafi cike da motocin maaikata na uniform da marasa kaki..

YANKIN BUNZAA

ahalin da ake ciki Kuma ayankin bunza ahalin hamdniyya Lebanon mai unguwa ya zauna da bappah Auwalu an fito da dukiya fal ta dutse mallakin su.

An raba gadon kowanne aka bashi. Sauran bappan duk sun zo. An babbawa kowanne.

Na marigayi junaid aka bawa iyalinsa. Sannan saniyar data Tara garke ma Ashe mallakin junaidu ce don haka aka sake rabawa su Nawraah gadon su.

A Kuma ranar ne Mai gari yasa maza biyu acikin yaran sa su nome dandagi. Yayinda ya roki alfamar ma wajen bappah Auwalu yace ya aurawa yayaansa mata mazansa biyu sunyi karatu a jami'a Kuma ga kudi nan sun samu zasu koma birni. Don haka sun yafee ma basai su Nawraah sun ebo ruwa daga rafin rau ba...

Koda bappah Auwalu ya gayawa nusaiba taki amincewa tana cewa saidai Nawraah Amma Layla bazata auri Dan kauye ba

Bappah Auwalu ya sharara mata mari da furucin saki har biyu Daman ta kaishi karshe .

Ya Kuma amincdwamai vairi saboda karamin da ya musu Kuma ya zauna da Layla da Nawraah duk since sun amince baza suki bin maganar su ba

Musanman Nawraah da hakan yafi mata tunda har abadah ta rantse bataza auri marwaan ba...

Layla da Nawraah suka roki bappah Auwalu kan sama suna shaawar ebo ruwan rafinrau tun suna kanan, tun da su alaadr su da hamaiddniya basayi. Amma ya amince musu suyi

Hakan kuwa akayi. Suka damara suka dauki randuna suka tafi rafinrau...

****


Ashe yan daba masu bindigu da adduna da wukake Alhaji sambaso ya turawa yankin bunza don a hallaka Nawraah da yan uwanta.

Motocin yan daban suka dira a yankin da adduna sunata sare bishiyu suna shelar akaisu wajen Nawraah ko su kone yankin baki daya..

Gari anata budurin bikin su Nawraah sai ya rude gaba daya da ife ife daguje guje....


Dai dai lokacin da motar marwaan takarasa dasu Anees . Can Kuma sai ga Alhaji sambaso

Amma Ina yan daban sun riga sun tafi can dandalin da aketa hidima da rafi. Sunata sare sare suna harba bindiga a iska...

Marwaan ya tafi da sauri yana tanbayar mutanen me ake sukace auren su Nawraah da yaran Mai gari. Aladar shine nome gonaa.

Ya dauki abubuwa ya nufi gonar shima ya shiga nomewa gumi sai zuba masa yakeyi.

Yayinda Anees ya nufi bingi wajeen Nawraah

Can ya hangesu da tulu itada Layla sun debo ruwa ya tafi da sauri

"Nawraah"

Ta juya da sauri ganin sa. Idanunwansu suka sarqe. Zuciyar sa na bugawa. Bata taba jin wani aabu game dashi ba sai aranar ko cika mata ido yayi oho

"Naam Anees... Ta samu kanta da amsa masa"

Ya tafi da sauri har yana tuntube ya sauke tulun Nawraah da Layla.ya riko hannun Nawraah yana janye Layla tabu bayansa. Nawraah sai turjewa take tana kiransa ya kyaleta.

Yaki cikata sunata lulawa cikin jeji suna Kai tsakiyar sa ta kwace tana tsinka masa Mari ya dafe wajen da sauri ,

Layla ta rike mata hannu tana girgiza mata Kai,


"Mai yasa zai rike min Hannu ?"

"Narwah please..Kikasan meyasa? Bai saki ba Kam yayi lefi Kuma haramun ne Amma be kamata ki mareshi ba"

Anees ya bude baki zaiyi magana yan daba uku suka karasa da makamai, daya bindiga daya da Adda da ya da wuka katuwa.

"Innalillahi Wa inna ilaihi rajiun" suka fada baki daya

"Wacece Nawraah?" Wani ya fada acikinsu

"Ba Nawraah anan "

"Karya kake matsiyaci "

"Kece Nawraah" dayan ya sakawa Layla bindiga akai

"Nice nawraah wallahi ni ce Nawraah" Nawraah ta matsa wajensu tana hawaye

Anees ya fusgota da karfi ya hankadata gefe yashatale Layla itama ya buge dan daban.

Suka shiga dukansa da Adda da wuka.
Can saiga marwaan da yan sanda kafin su karasa wajen tuni dayan ya harbawa maarwan harbi uku ajere. Yayinda sauran suka hau saran Anees a kirjinsa.

Dukan su suka fada kasa . Nawraah tasaka kara itada Layla..

Maiaaikata masu kaya da sauran suka kame yan daban da suka rage dama sauran dake cikin garin duk sun Kame ukun ne baa kame ba suka kame su.. aka kame Alhaji sambaso da wurin aka nuna masa arrest paper na cinye kudi da kashe kashen da yayi. Yayinda Suka kama Dr bintu na temakawa Alhaji sambaso da shawarar kwace kadarorin. Da Kuma rufa masa asiri bata fadawa hukuma yayi kashe kashe kashe. Aka hada harda Alhaji ateeks shima kan saka hannu a yarjejeniyar bawa Alhaji sambaso kadararorin Dr dollars.

Basu tsaya anan harda ba Hannafi shima sunansa na nan Wanda ke gyaran gonakin Alhaji sambaso. Suka sake tasa keyar nusaiba da itama kedaa lefin yin karya kan cewar ai tasan wani boyayyan lamari akan gidan na Alhaji Abubakhar ,a kason kudaden data karba a hannun su Alhaji sambaso. Da Kuma cin zarafi na marayu da tayi duk aka kame su wadanda ke wajen . Wanda sunansu ke a paper yan burnin naduka hukuma dake can burnin ta tura motoci an kame su an Saka a cell...

Guri sai ya maye da koke koke. Tuni dama ambulance ta kwashi marwaan da Anees. Akai babban asibitin kudi dake garin dasu

Dr abubuakhar dollars ya shiga cikin liktocin. Ana dubawa aka tarar Allah ya amshi ran marwaan. Yayinda Anees Kuma bai farfado ba ya shiga coma..

Tirkashi..

Wuri sai ya Kara rudewa. Aka tafi da motocin zuwa burnin naduka duka. Daman kafin sannan a masallaci an fara daurin auren Layla. Baa zo kan na Nawraah ba kasancewar waya da aka kira waliiyan madauran kan gari fa a hautsine ba lafiya. yan daurin aure tuni kowa yayi ta kansa wasu suka nufi wajen iyalan su...

*BIRNIN NADUKA*

sai da aka sake tabbatarwa fa marwaan ya rasu sannan aka cire rai, don bayan sun iso naduka sai da aka Kai shi asibitin da ake ji dashi a kasa dake nahiyar naduka. Wanda turawa nema liktocin duk sunyi gwaje gwaje marwaan ya rasu. Harsashi uku aka cire masa.

Ahalin sai koke koke sukeyi.dakyar hukuma ta amince ayi bakwai din marwaan sannan su mayar da su Alhaji sambaso da Dr bintu cell.

Tabbas marwaan yasamu mutane. Ya Kuma samu sheda. Aka kaishi gidansa na gaskiya aka birne.


.****


Tsayawa gaya muku yadda alhinin rasuwar marwaan ta kasance ma sai muyi kwanaki munayi.

Amma anyi alhini.rayuwa ba zata taba zama kamar ta baya ba sai addua kawai. Domin marwaan jigo ne bawan

Sannan abubuwa na dadi da akasin haka sun faru..

Alhaji sambaso ya samu tabuwar hankali tun ranar da aka kwace kadarorinsa da rashin babban dan sa Wanda shine ta hanyar sa aka kashe shi shin. . Aka Kuma sanya shi a kurkuku na tsawon sati biyu bayan ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login