Showing 9001 words to 12000 words out of 69829 words

Chapter 4 - KWANKWASON JIMINA BOOK 2 COMPLETE BOOK 2 hausa novel

24 Aug 2024

8972

bapoah auwalu.

"Tsaya..meya faru Layla? Nawraah ma bata zuwa? Uhm me yasa ne?"

Layla kanta na kasa tace,

"Baba Amnah ce batada lafiya shine Nawraah ke kula da ita. Kuma makarantar da muke Allah idan ni kadai zani inaga sai daliban sun min duka. Wata iriyar jami!'a ce ta yayan masu kudi dake cin Karen su ba babbaka. Sun raina kowa har malaman saboda yayan masu kudi ne"

"Toh Allah ya rufa asiri. Yanzu Ina su Nawraah suke suna can gidan marayun?"

"Eh inaga suna can"

Bude kofa yayi da sauri ya fuce. Nusaiba tabu bayan sa da harara tana karashe sauran hararar akan laylan tana dogon tsaki tache,

"Sallamamme uban kankanba. Sai kaje ai ka sayar da kanka ka siya musu maganin uban yan tausayi.. maza ke Kuma kafin na Saka gula na hambare ki. " Ta karasa fada kamar zata hau kan Layla ta duka

Layla ta shige daki da sauri tana rufe kofar dakin..

Parlor ya zama sai nusaiba daketa jera tsaki da kananun mita, tana saukewa bappaah auwalu da zuriyar sa kwanduna na kwashewar albarka...

_HGL CHARITY FOUNDATION_

_ASSALAMU ALAIKUM WA RAHAMATULLAH!_
JAMA'A BARKANKU DA _WARHAKA... ALLAH YA SAKA MUKU DA ALKHAIRI YA BADA LADA HADI DA BIYA MUKU DUKKANIN BUKATIN KU DA KUKE FATAN SAMU AAMIN_

GODIA DUBU GA TALLAFIN DA KUKA SAKA NA CIYARWAR AZUMI
INSHAA ALLAHU WANNAN GIDAUNIYAR MAI SUNA A SAMA NA KIRAN MUTANE AL'UMMA MASU SON SAMUN LADAN WANNAN MANYAN AIKI DA MUKE SAKA RAN FARA SHI KAMAR
НАКА

1• DAFA ABINCI A RABA GA MABUKATA RANAR JUMU'AH KO A KAI RUWAN SHA GA MASALLATAI RANAR JUMU'AH

2• HAQA RIJIYOYI ACIKIN KAUYUKA DA UNGUWANNIN DA BASUDA RUWA

3• RABA KAYAN ABINCI KO KUDI GA MABUKATA
MARASA HALI

4•KAI ZIYARA GIDAN MARAYU DA KAI MUSU
ABUBUWAN AMFANI DA SUTURA IDAN DA ME BAYARWA

5• KAI TALLAFI KO ABINCI GA ASIBITOCI WAJEN
MASU JINYA MARASA KARFI..

6•KOKARIN KARASA MASALLACI KO YIN MASALLACI
AWAJEN DA BASUDA SHI...

MAI NERA BIYAR MAI GOMA DiK
YADDA HALI YA KAMA ALLAH YA HADA MU A LADAN DUKA..
JAZAKUM ALLAH BiL JANNAH..
DOMIN SAKA TALLAFI GA ASUSU

9044191709
OPAY
JAZAKUM ALLAH BİL JANNAH💜
[5/1, 1:13 AM] Hafsaat🧕💞: _K'K'J_
_(M/W/S)_


_✍️:MX_


_10_


:::::::::


***Yana* tafe a hanya shi kadai yana surutai. Bai san sanda hawaye suka fara zurara daga idanun sa ba

Ya tsaya a gefen wata Katanga ya jingina yana cigaba da zancen da yake harda daga hannu yana nuni da wani bango. Cike da dimbin damuwar da alkalami yayi kadan wajen bayyana adadinta yaketa nanata,

"Ya'yana .. 'yayan kani na ne fe,. Kanina na jini da muka futo tsatso daya. Wai ache yau ni auwalu ni na kasa rike yayan junaidu? Duka nawa suke gaba daya su uku ne fa? Ache na kasa daukar dawainiyar ahalin sa.? Innalillahi Wa inna ilaihi rajiun Yaa Allah ka kawo mana mafita. Allah ka yafee mana. Ban yiwa zumunta adalci ba hakika nayi babban kuskure. Na tabbatar da junaidu ne a raye ni na rasu iyalina ba zasu tagayyafa haka ba. Allah ka yafe mun Allah ka yafe mun ka kawo kana mafita da zamu bude ni da yaran gaba daya."

Ya karasa maganar yana sharce hawayen dake zuba masa ya cigaba da tafiya ya karasa naduka crescent har bakin gate din gidan marayun Mai gadi ya tsaya yana duban sa bayan sunyi musaba ta sallama.

"Ranks ya dade menene?"

"Baka sheda ni bane? Ai ina zuwa nan, kwana biyu ne dai ban leko ba"

Mai gadin ya dube shi tun daga yatsun kafafunsa zuwa fuskar sa yana girgiza Kai,

"Ban sheda ka ba gaskia"

"Allah sarki to babu damuwa. Dama nazo ganin 'yaya na ne anan din"

"Yayan ka kuma anan din?"

"Eh"

"Nan gidan marayun ne fa ranka ya dade..."

"To bawan Allah yayan dan uwanka ai yayan ka ne ko?"

Mai gadi ya daga kai cikin tabbatarwa. Ya nisa kafin ya janyo wani liytafi a kusa dashi dake kan desk yace,

"Ya sunan ka?"

"Auwalu Hamidniyya Lebanon"

Mai gadin ya daga kai da sauri ya dubee shi,

"Bawan Allah...." Ya karasa fada yana nuni da bappah Auwallu da kasan biron sa.

Bappah Auwalu yayi murmushi yace

"Ka sheda ni yanzu"

"Sai da ka fadi sunan wallahi. Na tuna kana zuwa Kar mu tsaya ma wani lokacin muyita hira, kayi hakuri dan Allah wallahi baki daya ka canza mun ne"

Bappah Auwalu u ya sosa keyar sa yana murmushi yace

"Kasan rayuwar sai a hankali Kam"

"Hakane Kam wallahi ya'yana. Allah dai yasa mu dache yayi mana maganib abunda yake damun mu..

"Aameen Yaa Rabbi"

"To ka shigo ka zauna a waien zaman ko. Bari a kirawo su"

"To godia nake. "

Ya shiga cikin wani babban daki da kujeru aciki. Nanne inde baki sukazo suke zuwa, suke gaisawa da yan uwansu na ciki, Wasu Kuma suke daukar yaro wato adopting da foster parents keyi... Wasu kuma kawai suna zuwa su dan kakkawo tallafi ga marayun. Na daga abunda hali ya kama. Irin su kayan abinci, ko surutu. Ko raba maganin sauro da gidan net din..

Bapoa auwalu yana zaune yana matsa yatsun hannun sa sai ga shigowar Nawraah rike da hannun Amnah data fiye ta zama yar karama itama

Bakinsu dauke da sallama suka shiga. Mai gidan ya dubi agogon hannunsa ya saita lokaci acikin wani babban abu me buga kararrarwar lokacin magana ya kare.

"Nawraah, Amnah..." Bappa awualu ya kira sunayen su yana karasawa kusa da su ya riko hannun Amnah ya rungumeta yana hawaye,

"Amnah..."

"Naam.m bappah"

"Ina wuni bapoah?" Nawraah ta gayshe shi tana gyara tsayuwar ta

"Lafiya kalau. Nawraah Ashe Amnah ce bataji dadi ba har kika dene zuwa makarantar? Wallahi bansani har sai da nake tanbayar Layla ba dadewa nace su Ahmad kuwa sun fara zuwa jami'ar tache kwana biyu bakwa zauwa batasn ko sunje ba. Take cewa kina jinyar Amnah bakyaa lillahi Wa inna ilaihi rajiun "

Nawraah ta kakaro murmushi don ta kwanta masa da hankali tace,

"Ai dake ba wani ciwo bane bapoah"

Ya girgiza Kai yana daya duban Amnah,

"Haba Kalli ba. Kalli Amnah fa. Da haka take? Dubi yadda ta dawo fa. ? Nawraah nan gidan marayun ba waien zaman ku bane. Ku dawo gidah dan Allah kinji?"

Nawraah ta sake kakaro murmushi tana girgiza Kai tafe,

"Bappah auwalu nanma ya isa Allah. Akwai wajen kwana mai kyau, akwai bandaki , akwai wuta. Kuma ana bamu abinci daidai gwargrwado. Duk wadanda mike tare da su kowanne da irin tasa kaddarar jarabawar ta rayuwa... Rashin lafiyar Amnah Kuma abu ta dauka taci a shara. Amma kalau muke Allah Kuma Allah cikin ikonsa wani dalibi shine yayi mana fafituka wajen tsayawa aka Wa Amnah komai da komai bappaah. Dan Allah ka ragee damuwaa da kake akan mu, Kai nema naga ka fada bappah. Bakada lafiya ne?"

Bappah auwalu ya sauke zuciya. Daman yasan ba zata amice ta dawo ba don idan sun koma nusaiba sasu zatayi agaba

"To yanzu ya jikin nata? Amnah ba inda yake miki ciwo?" Ya karasa fada yana Kai hannunsa kan goshin Amnah da cikinta dake shafe kamar marar tueo. Duk ta jeme sai kashi

"Da sauki sosai ma. Jijjuya fa ta dingayi ta suke. Allah ne yayi da kwanata agaba"

"Amma Nawraah menene dalilin da zaki nemoni ba ko a waya ne?"

"Bappah Banda waya . Baka.haka ba gaba daya hakulan mu a tashe suke. Banason Kuma na daga maka naka hanalokin bapoah"

"Karki sake wannan gangancin kinji ko Nawraah? Zaku iya yanke hulda da nusaiba ita kadai. Amman banda su Laye. Itace Bare. Zan iya sauya mata yanzu Amma ku yayan ciki na ne abunda yayi junaidu shi yayi ni Nawraah. Kisa a ranki. Wannan abubuwan da zasu zam tarihi inshaa Allah. Sannan ki tsaya ku cigaba da karatu kinji?"

"Inshaa Allah bappah.."

"Ina ashfeef?"

"Yana garejin mota"

"Shine me waya ahannun sa ko?"

"Eh shinemmm, nima inada wadda hamma Ashir yabani Amma yace sai na shiga level two inshaa Allah"

"Mashaa Allah to duka abunda yake faruwa kafin na bullo ko Kuna bukatar wani abun Ashfeef ya dinga Kirana kinji?"

"Toh inshaa Allah bappah. Amma ba komai ba kakka damu

"Banason musu kice to kawai"

"Toh bappah." Tana rufe baki kararrarawar karashen zancen su ta buga

Bappah Auwalu, ya mike yana lalubo aljihunsa yan nera tamanin ya dakko yan ashirin guda hudu ya mika mata,

"Rike wannan kwa sayi wani abun"

"Bappah daka barshi ba abunda mukebukata Allah"

"Ki karba dai yaushe muka fara yar haka"

Hannu biyu ta Saka ta karba tana rissinaawa

"Angode bappahh Allah yakara arziki aamin

"Aameen aamin. Allah ya muku albarka. Ya tsare kuryciyar ku har girman ku kinji! Layla tache jami'ar taku gatanan ce. kudai kuje da tsarin da iyayen ku suka horeku akai. Ba ruwan ku da shiga harkar kowa.

"Inshaa Allah bappah"

"Yauwa Allah yayi albarka sai na sake bullowa"

Toh bappah"

Har bakin gate suka raka shi Yana daga musu hannu suna daga masan ko da ya juya sai daya goge hawaye wai yau iyalan junaidu ne agidan marayu basuda gata kwata kwata, Allah mubuwayi ne gagaraa misali...


====



Sannu ahankali haka rayuwar taci gaba da garawa. Yau da dadi gobe akasin haka, kwanaki nata shudewa, safiya ta koma rana, ranata ta koma yammaci , yammaci ya koma dare

Su Nawraah suka cigaba da zuwa jami'ar Alharamein university. A satin ma su ashfeef suka fara zuwa, Ahmad da Shareef accounting suke karanta, Layla da Nawraah kuma criminology.



Mai karatu alkalmi yayi kadan wajen rubuya muku yadda zazzafar shakuwa ta shiga tsakanin marwan da nawraah. Sunyi matukar saho da juna Wanda duk sanda ka Dora idanun ka akan su sai kaha tamkar mata da mini ne sahoda yadda suka dache da juna. Duk inta ta Saka jafa yana biye da ita.... Duk inda ka
_HGL CHARITY FOUNDATION_

_ASSALAMU ALAIKUM WA RAHAMATULLAH!_
JAMA'A BARKANKU DA _WARHAKA... ALLAH YA SAKA MUKU DA ALKHAIRI YA BADA LADA HADI DA BIYA MUKU DUKKANIN BUKATIN KU DA KUKE FATAN SAMU AAMIN_

GODIA DUBU GA TALLAFIN DA KUKA SAKA NA CIYARWAR AZUMI
INSHAA ALLAHU WANNAN GIDAUNIYAR MAI SUNA A SAMA NA KIRAN MUTANE AL'UMMA MASU SON SAMUN LADAN WANNAN MANYAN AIKI DA MUKE SAKA RAN FARA SHI KAMAR
НАКА

1• DAFA ABINCI A RABA GA MABUKATA RANAR JUMU'AH KO A KAI RUWAN SHA GA MASALLATAI RANAR JUMU'AH

2• HAQA RIJIYOYI ACIKIN KAUYUKA DA UNGUWANNIN DA BASUDA RUWA

3• RABA KAYAN ABINCI KO KUDI GA MABUKATA
MARASA HALI

4•KAI ZIYARA GIDAN MARAYU DA KAI MUSU
ABUBUWAN AMFANI DA SUTURA IDAN DA ME BAYARWA

5• KAI TALLAFI KO ABINCI GA ASIBITOCI WAJEN
MASU JINYA MARASA KARFI..

6•KOKARIN KARASA MASALLACI KO YIN MASALLACI
AWAJEN DA BASUDA SHI...

MAI NERA BIYAR MAI GOMA DiK
YADDA HALI YA KAMA ALLAH YA HADA MU A LADAN DUKA..
JAZAKUM ALLAH BiL JANNAH..
DOMIN SAKA TALLAFI GA ASUSU

9044191709
OPAY

[5/1, 6:47 PM] Hafsaat🧕💞: _K'K'J_
_(M/W/S)_


_BOOK TWO_


_✍️:MX_


_11_

*Zaune* ta ke, A babban parlorn da ke gidan na su... Ta daura kafar ta daya kan daya. Gabanta wani teburi ne cike da kayan motsa baki... Da sanyayyen robar ruwa da kwalin lemo na 'ya'yan itatuwa.

Idanunta saqale cikin gilashi ta sake duban number a karo na uku na cikin screen din dake wayar hannun ta. Sau uku tana kira not reachable a iya zaman da tayi na lokacin..

Dawowar su kuwa ko da yaushe sai ta kira duka numbers din nasu bata samu. Ta sauke katuwar ajiyar zuciyar mai cunkushe da damuwa.

Baki daya bata jin dadin kiran da take musu bata samu. Zuciyar ta nata kawo mata labarai marasa dadi..

Ta sake sauke wani gwauron numfashi tana runtse idanun ta hadi da furta,

"Inna Lil Laahi Wa Inna Ilaihi raji'un... Allah ya jikan ki Hindu, Allah ya gafarta miki. Allah ubangiji ya bamu iKon kula da iyalan da kika bari. Kai rayuwa, Mai rai ba a bakin komai yake ba. Allah kasa muyi kyakkyawan karshe Aameen"

Ta yunkura zata tashi sai ga shigowar mai gidanta parlorn bakin sa dauke da sallama...

Amsawa tayi ta nufe shi da sauri tana masa sannu da zuwa. Suka rungume juna. Ta harde hannuwanta a ruwan cikin sa. Kasancewar ya fita tsayi. Rumfa ya mata da faffadan kirjinsa. Ya Kai hancin sa kan dankwalin kanta daya dan zame ana hango gashinta batai kitso ba. Sai kamshin turaren man gashin Yerwa incense and more ne ke tashi. Sunba ya kaiwa gashin yana lunshe idanun sa. Ko'ina na jikinta kamshin yake yi.

"Sannu da zuwa Habibi...." Ya jiyo sanyayyar muryarta ta daki kofar kunnen sa.

Ya daga kanta yana duban idanunta hadi da saka hannu ya tallabo bakin ta da sauri ya kai mata sumba. Ta kallo baya da sauri tana murmushi. Shima murmushin yayi..

Ya riko hannun ta suka zauna akan kujera. Kallonta yake cike da zallar so da kauna tamkar zai mayar da ita cikin sa.

"Kinyi kyau Mariri na... "

Murmushi tayi tana rufe bakinta tache,

"Yau Kuma da wannan sunan ka tashi?"

Daria yayi yana cigaba da kallonta ya riko hannun ta cikin nasa yace,

"Ya za'ai na manta sunan da nake Kiran ki dashi muna saurayi da budurwa uhm? Shaukin so na dawainiya da ni. Idan kika kirani da As-sadeeq dinnan har cikin bargon 'kashi na nake jin ki Mariyatul Qibdiyya ta" ya karasa fada yana sinsinar gefen wuyan ta

Murmushi tayi tana duban sa hadi da damtse nasa hannun cikin nata tache,

"Kafi kyawu kyau... As-sadeeq dina daya tamkar da dubu. Yadda kake faran ta wa duban mutane ubangiji Allah ya cigaba da duban ka da idanun rahama ya nunka ma ka dukiyar Ka, Allah yakara maka hakuri da juriya, lafiya ingatacciya ya hobbasa dik wani samun ka ya yaye maka damuwar ka... Har gaban abadan kai ne mamallakin zuciya da gangar jiki Kai da ilahiran rai da jijiyoyi na gaba daya... Ni din taka ce kayi yadda kaga dama dan gata na.. abun alfahari na a koda yaushe" ta karasa fada tana sunkuyar da Kai kasa hadi da wulkita idanu kar wani ya gano su.

Alhaji abubukhar dollars yayi murmushin dake karawa fuskar sa kyawu duk da shekarun sa Amma tamkar dan karamin matashi haka yake da kyawu da cikar zatin haibar halittar ta fulanij usul..

"Allah ya miki albarka matata uwar yaya na. Allah ya cigaba da faranta miki kinji?"

"Tare da kai nawan.."

"Uhm uhm dan Kara fada banji ba?" Ya Kai hannun sa kan kunnen sa yana karasawa da kunen dede saitin bakin ta .

Ta Saka labbanta ta kamo kasan kunnen nasa, Ta cize shi ya janye da sauri suka saka dariya gaba daya

"A kawo abinci ko wanka ne farko?"

"Toh dika biyun ciki dai sai zuwa anjima inshaa Allah..."

Duban sa tayi taga ya nata lankwasa yatsun sa ya hade su waje daya. Hakan yake yi idan yanada damuwar da bayaso ya bayyana ko ta masa nauyi a harshen sa.

Saka hannu tayi ta juyar da fuskar sa gareta tana duban sa sosai.

"Baban su .... Meke faruwa? Dan Allah kada ka boye mun. Wani abun ne ya faru?"

Duban ta yayi sai Kuma ya juya gefe yana sauke numfashi yace,

"Ba wai wani abun damuwa bane can. Kawai dai lamarin ne na kasa ganewa. "

"Ina sauraon ka. Matsalar ka tawa ce. Damuwar ka damuwa tache. Ina sauraron ka. Idan shawarace sai na baka idan yadda zamu bullowa lamarin ne nanma sai muyi. Nima daka ganni anan inata sake sake ne kan iyalan marigayiya Hindu Mai aikin nan namu data rasu ne. Na kikkira wayar dan nata da nake samun su bata shiga gaba daya. Dan Allah kada ka bari koma menene ya dake ka. Ka sanar dani abunda ya shige maka duhu"

Alhaji abubukhar dollars ya daga kansa saman pop kafin ya sauke yana duban ta sosai yace,

"Kawai kira na gani daga share holders .. Plazas dinnan nawa na kudi na hakki na fa, kinji wai an duba accounts whatsoever dai wai banawa bane sun futa daga cikin kadarori na. Harda estates din mejesa da guzare dana Gpo da na bayan Maduki."

Hajia Qibdiyya na zaune sai ta mike dauke da hannuwanta ta Kara a kirji idanuwanta a waje sun firfito cikin tsabar dimbin mamakin ta dube shi cike da fargaba Mai tartare da tsoron ban mamakin dauke da tu'ajjabi da karsashin muryar da ke nuna ta hau mizanin damuwa sosai tace da shi,

"What? Ban ban bangane me kake nufi ba Abubakhar?" Ta karasa cikin in'ina da karin fadin sunansa cikin dimuwa..

Duban ta yayi ya girgiza Kai ya janyo hannunta ya dawo da ita kusa da shi ya zaunar da ita yana tallabe habar sa yace,

"Akwai Wanda ke cin dunduniya ta Mariyah... Akwai wadanda ke bibiyar al'amurana ta karkaashin kasa Mariyah. Ina tare da makiyan dana kewa kallon masoyane. A zagayen nake cikin kuraye masu son ganin bayana Mariya. To Amma matsalar itace, wanene? Su wanene daga Ina suke? Taya zan bullowa lamarin? Shin menene zai biyo baya? Ya lamarin ya ke ne? Duka wadannan dama wasu tarin tambayoyin baki daya bansan yadda zan ba. Baki daya komai ya dawo square one. Sai na biyo ta baya na gane komai sannan zan iya cinma nasara ta na dawo da hakkokina, Amma ta yaya? Kai hasbun Allahu Wa ni'imal wakil. Allah kasa mu dace"

"Aameen Alhaji. Tabbss akwai wadanda suke maka zagon kasan masu cin dunduniyar ka ko suwa nene Allahu a'alam. Amma dik wani dan Adam daya bi bayan wannan makirci aka salwantar da wadannan kadarori da yardar Allah tasu tazo karshe. Inshaa Allahu komai naka zai dawo hannun ka da izinin rabbana. To bakasan su waye ba kenan ba wani dan hint da zaka gane?"

Daga kai yayi sama yana jijigawa kafin ya sunkuyar dashi kasa yana duban ta yace,

"Yanzu zan fara Saka ido akan komai. Amman zan nuna ni baibai ne, Kuma kurma ne, Sannan makaho ne kuma soko ne gaula da baya gane komai ..Kingane?"

"Ban fahince ka ba Alhaji?"

"Ina nufin zan zama baibai ko kurma maana zan nuna maganganun duk basu tabani ba, Bana tasu, Na shafe su ko ana yin zancen bazansa baki ba."

"Meyasa kace haka?"

"Sai ka taka sahun barowa kake zama daidai dashi Mariyah. Idan na nuna na fito da makaman yaki na to hawa Kai na zasiyi kila su illata nima. Maso abin ka ya fika dabara Mariyah, Amma idan nayi biris da zancen na shafe shi tamkar na manta na nuna baya damuna. To sannu ahankali gaskia zata biyo baya"

"Dakace zaka nuna baka gani fa?"

"Magana ce hausa cikin hausa..abun nufi ba zan nuna inabganin su ba ko Ina Saka ido ganin na gano su wanene aciki ba, Zan nuna tamkar makaho maana zanyi watsi da lamarin bana ganinsa bana sauraron sa"

"Mashaa Allah. Kana ganin hakan mafita ce?"

"Da yardar Allah komai zai bayyana kansa. Amman sai munyi hakuri. Sai Kun lura sosai. Muna nan dake gaskiya zata fito Kuma koma wajen ko su waye Allah bazai bar su haka ba"

"Kayi magana da Alhaji sambaso?"

"Eh yakirani dazun har yake cewa zai zo office ya same ni nace

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login