Showing 42001 words to 45000 words out of 69829 words

Chapter 15 - KWANKWASON JIMINA BOOK 2 COMPLETE BOOK 2 hausa novel

24 Aug 2024

8957

mike sun tafi. tache,

"Bakina ba zai gaji ba dai da maimaita maganar nan ba. Yanzu Kafi son mu zauna a wannan rayuwar Muna yunwa da wahalar rayuwar juna..bansan wace iriyar zuciya bace da Kai wallahi. Ace ga sauki yazo mana baki daya amman ka kasa fuskanta"

"Idan maganar nan zaki sake maimaitawa zan tashi na bar miki wajen baki daya.... Bana hango abunda yayi mun nisa na gaba dani, Abunda Allah ya horemun ya isheni rayuwar duniya.."

"Naji, ajiye shi gefe. Yanzu saboda Allah a wannan kangin zamu cigaba da zama. Kana zuwa dakyar ba kawo dari ko dari biyu kana tafiya dakyar haka kake so muci gaba da rayuwa eh?"

"Sai Kuma kiyi. Na gaya miki, kwadayi mabudin wahala.. wannan zuriyar da kike bi kibi a hankali. Kwarai zasu Kai ki su baro ki. Ato"

"Gaskia Kam. Kai naga saboda zuciya da rashin son abu wasu ,da kake dashi ka zama wani abu yau rayuwa, ah sannu Wanda ya tara yayan kudi a banki....Mashahuri.."

Bappah Auwalu ya dauki carbinsa yafuce daga gidan,. Yabar nusaiba nata kunduma mita

"Wahalle uban yan fadin rai" ta fada tana hararar sa bayan ya futa.

Haka ta zauna a parlorn tanata sakin tsaki ta mike ta shige dakinsu tanata kunduma ashariya tana durewa a zuriyar hamidniyya lebanon...





*Nagode da addu'oi Allah ya jikan musulmai ya bamu lafiya Mai dorewa amin*









HANSATUWA🧕







VIP PAGES NA
: AREWABOOK:MSSXOXO

_KKJ_

_32_



***



Kwance take akan gadon ta. Baki daya bacci ya kauracewa idanun ta. Ta sanya kasan rigar ta tana goge hawayen dake zurara daga idanun ta..

Baki daya ji take duniyar ta mata nauyi. Rayuwa ta mata zafi. Shin Ina madafa? Su Wa zata duba ta gayawa tarin dakon dimbin damuwar dake addabar zuciya, ruhi da Kuma gangar jikin ta?

Ta tuno yadda suke zaune a baya taree da iyayan su da babban wan su kula dasu kamar Wanda ya haifee su?

Ta sauke ajiyar zuciya ahankali tana girgiza Kai ita daya. Tunani dankare cikin ranta. Tayi wannan ya kauce ta dakko wannan shima ta gama haka da haka dai.

Baki daya yan dakin nasu tuni sunyi bacci. Don wasunsu har da sakin minshari. Alamun baccin yayi nauyi tuni sun dade da lulawa duniyar bacci.

Mikewa tayi a hankali. Hannunta rike da wayarta ta shiga bndaki bakinta dauke da addua

Fitsari tyi hadi da tsarki ta Kuma dauro alwala. Kan sallaya ta nufa ta tsaya ta janyo hijabin ta ta tada iqama. Sallolin nafilfili tayi hadi dayin adduar istikhara don neman zabin Allah acikin lamuran data Saka agaba.

Ta jima tana kwarara addua tana rokon Allah ya dube su ya dubi halin da suke ciki ya musu tallafi ya dorasu akan makiyan su..

Tayi istigfari da sauran adduoi ta shafa. Ta dade a zaune abakin gado bayan ta idar bacci sam yaki daukar ta

Dakyar dai bacci barawo ya dauketa zuciyar ta fal da sake sake abubuwan kan yadda zata bullowa lamarin da suke ciki da Wanda zai doso su..

Haka ta cigaba da addu'oin neman zabin Allah..tana istikhara har ya zuwa kwanaki hudu. Tuni tafara jin ranta na mata sauki daga matsayin da take ciki.

Tana zaune lamarin nata jujjuya mata. Ta saki wayarta tana duban number marwaan yau kwanaki kusan nawa basa waya. Ba message ba chat. Zuciyarta na mata zugi da rada'di..

Ta samu kwarin gwiwar danna masa kira a waya. Marwaan na zaune akan kujera a dakinsa. Baki daya har ramewa yayi ya zabge saboda tashin hankalin da yake ciki

Wayartsacetafara kara. Dajin ringtune din yagano Nawraah ce. Don ita kadai ya sakawa ringtune daban saboda ita din special one ce, a duk inda yake idan ta kira zai gane itada ce.

Gabansa ya tsanants bugawa. Hannunsa na rawa, ji yake anya zai iya daukar kiranta kuwa? Baki daya kwanakin daya sauke mata wuta baya nemanta baya amsa Kiran da sakon da take yi masa duk saboda matsayin da yake cikine. Sam bayason ya sanyata a damuwa acewar sa ga abunda iyayensa sukace akanta. Sannan ba babbar matsalar da take gabansa

Ya samu kansa da daga wayar yana duban screen din. Har wayar ta tsinke bai dauka ba. Ta sake kira. Ya danne kirjinsa da hannunsa daya yana cije lebe ya dauka.

'hello..."

"Assalamu alaikum " ta fada cikin sanyayyar muryarta.

Kana jin muryoyin nasu kasan dukkanin su na cikin matsalar rayuwa, Dubada yadda kowanne muyarrsa ke a cunkushe dake lullube cikin radadi da zugi na tashin hankalin da take ciki.

"Wa alaykm Salam" ya amsa yana sauke numfashi.

Duban screen din wayar tayi bayan ta zare daga kunnenta. Ta mayar cikin kunnen nata tana mai sake cewa da shi,

"Ina wuni?"

"Alhamdulillah" ya amsa yana sake jan kasan lebensa, shi yana rasa me zai ce mata

"Marwaan" ta kira sunansa cikin wata iriyar muryar dake nuna tana cikin damuwa

"Uhm"

"Kana jina?"

"Uhm"

"Kazo inason magana da Kai"

Samun kansa yayi da zunkudawa daga zaunen da yake a kujera yana sosa kasan keyarsa yace,

"Ba.."

"A'a ... Yau nakeso nanda anjima kadan kazo muyi magana da Kai"

"Nawraah please"

"Yau please marwaN... Kazo inason muyi magana"

"Nawraah ki sake hakuri, har yanzu Ina kokarin tausasar zukatan su ne. Kinji?"

"Ba damuwa kazo dai muyi magana"
Kit ta katse kiran tana ajiye wayar a gefe

"Nawraah kina ji? Please give me some time, like I'm battling with .....hello?"

Jin tayi shiru kamar shi daya yake magana yasa ya daga wayar yana kallon screen, Ashe ta katse kira.

Ya sauke gwauron numfashi. Hadi da saka hannu yashafi fuskar sa yana tallabe ta.

"Innalillahi Wa inna ilaihi rajiun " ya fada yana sake suake numfashi

Mikewa yayi ya shiga bandaki ya watsa ruwa. Closet dinsa ya nufa ya dakko jallabiya da singlet ya Saka. Ya faffesa turare ya dauki mukullin motar sa ya fita.

Yana shiga ya tasheta ya nufi unguwar su Kai tsaye. A bakin kofar gate din gidan su Anees ya tsaya da motar sa. Ya kutsa daga ciki ya shiga gidan

Kai tsaye ya nufi sashen Anees din. Ya shige har zuwa kofar dakin Anees din ya murda kofar ya jita a rufe.

Yadda saitin karatun qurani da kiraar maheer mueqly ke tashi ya tabbatar masa da Anees din na ciki.

Anees na cikin dakin nasa a kwance akan gadi. Ya daga wayar sa saitin fuskar sa yana duban hotan Nawraah. Kallontaa yake kamar ita din yake gani a gaske. A tsaye take a cafeteria sanye cikin wasu kaya riga da skirt da mayafi da sukayi matukar amsar surar jikinta.

Gashi yanayin yadda ya dau hoton komai da komai nata ya fito tayi kyau sosai tana daria.

Tun daga kan kafarta yake zooming ya zuwa kan kirjin ta data rike handout awajen ya zuwa fuskar ta.

Ya samu kansa da dan kasa da yin hannunsa yana zoomo wajen mayafin ta data rufe saman kirjin da handout

Bai San meya same shi ba, ya sake zooming yana duban ko'ina na jikinta kamar ita yake gani ba hoto ba

Sosai surar jikin Nawraah ta sake sanya Anees acikin wani yanayi da bai zata ba. Daman yadda takeda kyan hali da kyawun fuska hakama jikinta yake dama ?

Lalle tsarki ya tabbata ga Allah daya halicci wannan halittar Mai halittin abubuwa masu ingiza zuciyar dukkanin wani namijin da zai dora idanunsa akanta sai ya ji wani abu game da ita..

Ya samu kansa da Kai hannunsa ya sake zooming hoton zuwa wajen labbanta. Ya sanya yatsunsa yana zage labban. Ji yake dama halaliyar sa ce. Ba abunda zai hanashi lasar labbanta a wannan yanayin. Amman ya zeyi? Ba tasan yanayi ba ballentama ace zata iya zama halaliyar tasa ta hanyar auren sunnah

"Ya Rabb kszhihs cikin lamuran." Ya fada hsmjsmj yana sake gysts kwnaviyat san ahdj da kwantar da wayar tasa akan kirjinsa yana shafa wayar. Da alamar.hogon naku ya sauka Nawraah ce ajikinsa yadda yake shafa wayar cikin wani irin salo.

Vibrating din datayi ne yssashi mikewa da Sauri yana janye wayar .

"Marwaan sambaso" shine sunandaya a fito daga screen din wayar tasa.

Kamar ba zai dauka ba sai Kuma ya dauka ya dora akan kunnen sa....



_ADVERT👇👇_

_YERWA INCENSE AND MORE_
_(DUNIYAR KAYAYYAKIN KAMSHI MASU MATUKAR DADI DA KAMA JIKI, GIDAH, KAYA DA SAURAN SU)_


_INA MA'ABOTA TURARE? KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE_
_TSAFTA KUMA TANA CIKIN IMANI… TOH KU MAR-MATSO KUSA_

_MUN KUMA ZUWA DA HAJAR KAYAYYAKIN_

_*YERWA INCENSE AND MORE*_
_DOMIN SAMUN ZAFAFAN TURARUKAN WUTA NA GIDA, KAYA, JIKI, TSUGUNNO, GASHI... AKWAI KHUMRAHS MASU DADI YAN BORNU, CHADI, SUDAN DAMA SENEGAL, AKWAI OIL PERFUMES, DA TURARUWAN MOPPING DANA WANKA DANA WANKI DANA GADO DA KUJERU DA BANDAKI DA DRAWER DA MOTOCI.._

_AKWAI MAN GASHI NA FESAWA ME SA KAMSHI DANA KITSO. AKWAI KAYAYYAKIN KAMSHI DANA GYARAN JIKI SOSAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA. •_

_ADIRESHI: KANO.. AMMA SUNA TURA KAYAN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE..._

_INGANCI KYAU RAHUSA DA DADEWA A GIDAH DA KAMSHI SAI KAYAYYAKIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE_

_NAMBAR WAYAR SU: 08095215215, INSTAGRAM/THREADS/TWITTER:yerwaincense_and more_

_YOUR NUMBER ONE STOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS... THEY 'VE GOT YOU AND YOUR HOME COVERED_

_K'K'J_
_(M/W/S)_


_BOOK TWO_


_✍️:MX_


_33_


:::::::::

Kamar ba zai dauka ba sai Kuma ya dauka ya dora akan kunnen sa,

"Speak"

"Dalla malam! fito ka mun rakiyaa it's urgent"

"Akan wani dalilin zaka kirani Ina hutawa ta?"

"An kira din, Dan wahala. Wawa"

"Sai ka bada hakuri"

"Naji to, Afuwan. Dan Allah kaji maza? Zo ka mun rakiya pls"

"Rakiyar uban Ina?."

"Wajen Nawraah pls."

Anees na kwance sai ya mike yana gyara zaman rigar sa dake jikinsa.

"Whr u?"

" gani a kofar dakin ka. "

"Alright"

Kan mudubi ya nufa ya dauki turare ya fashe jikinsa da su. Ya bude kofar dakin ,

Marwaan na ganinsa ya riko hannun Anees yana jansa. Anees ya janye hannun nasa yana dankara masa lafiyayyar harara,

"Akan me zaka wani rike mun hannu? Banza gardi"

Marwaan da rabonsa yayi dariya sai alokacin yayi dariya yana duban Anees yace,

"Wetin man do man? Mace kake so ta rike ka? Munafikin banza"

"Oho maka. Akan wani dalilin zaka rike ni sai kache wasu yara"

"Wawa. Dalla Nawraah ce wallahi take fushi Dani. Nasan quite alrigjh ni ne me lefi but guy Ina cikin situation ne. Like su Maa basu amince da auren mu ba. I'm trying it way too hard to convince them. Ita Kuma ta kasa ganewa ko da yake nace mata matsalan daga busy dinsu ne nace since zasu nemeni dai for now aiki ya musu yawa. But guy ba zaka gane ba. Nawraah gaba daya ta cazamin lissafi"

Anees yayi murmushin yake yana duban marwaan . Gaba daya ma ya rasa ma Mai zai ce. Wai mahaifan marwaan ne suka kwace kadarorin baban su Alhaji Abubakhar dollars. Bayaga haka sune silar kashe iyayan Nawraah da babban wan su Nawraah. Kallon marwaan kawai yake abubuwan nata masa yawo a kwakwalwar sa. Shi kansan zuciyar sa ta kasa daukar tarin lamuran masu kama da tatsuniyar gizo da koki. ..

Marwaan ganin Anees yayi tsuru yana dubansa tun dazu ya Saka hannu yana waving dinsa (bye bye)

"Hello. Guy? Bakace komai ba"

Anees yayi gyaran murya yana sosa keyar sa tunowa da Mami datace masa kar ya soma canzawa marwaan fuska kar yana nuna masa yasan abunda suke faruwa

"Bari kawai baba, na tafi tunanin laliga din anjima da zaa kalla"

"Dan wahala..anata soyayya kanata ball. Zo muje ka rakani. Kaji abubuwan dana fada kuwa? "

Anees ya kada Kai suna tafiya zuwa hangar fita yace,

"Lefin kane abokina..shi lack of communication yana taba alakar dake tsakanin masoya. Baa waya ba message ba chat ba komai a hakan zata dore? Sannan kai yarinyar nan ko kiranka tayi ba dauka kake ba. Kai da kanka ka gayamun kana ignoring dinta ne kafin kayi figuring out abubuwan "

"Eh nasani. Kawai dai ta kasa ganewa ne"

"Taya zata gane baka mata bayani ba? Kawai budurwa ce saurayi zai ce mata yawa iyayensa maganar auren su, sun shiga busy ne sosai Amma zasuyi magana ta kwantar da hankali. Kuma Kawai sai a dena yin wata hulda dake a baya ba Sako na kira ba komai. Ka zauna kayi tunani"

"Gaskia ne, wani lokacin idan ka fadi abu kamar Wanda yake soyayya ko ya taba soyayya.

Anees yayi murmushi jin abunda marwaan ya fada. Tabbas dayasan tarin kalamai da soyayya me dauke da tacacciyar kauna da yake yiwa mallakin zuciyar sa nawraah abat kaunar sa to da bazai iya gane kwatan kwatankwacin mecece soyayya ba, don ko kadan bai Kai shi ba..

Marwaan ya janyo wayarsa ya kira Nawraah yana shedaa mata dayazo yana waje

Ba jimawa kuwa ta sakko daga gidan marayun sanye cikin wasu kaya doguwar riga ta atamfa ta rufe jikinta, Hannunta rike da wayarta ta nufe su

Tunda ta shiga takawa zuwa wajen Anees ya fara jin numfashin sa ma na son daukewa saboda zillo da tsananin son kasancewar atare da iya acikin soyayya. Amman Ina? Ta riga ta masa nisan da bazai taba samunta ba.

Ya janye idanunsa da sauri don kallo daya yayi mata bisa qa'ida .. Don idan ya cigaba da kallonta to ba makawa zai iya barin bakin gaya mata zuciyarsa ko Kuma yayi azamar sanyata cikin kirjinna sa don share mata hawayen dayaa tana fitar daga shi daga idanun ta.

Ta matsa kusada su tana duban marwaan dake matsa yatsunsa tache,

"Ina wunin ku?"

"Lafiyaa kalau" Anees ya amsa mata

Marwaan bai samu damar magana ba. Bayaga bugun zuciyar sa daya canza saboda tsoro..

Nawraah tayi mamaki kwarai matukaa da Anees din shi kadai ya amsa sallamar/ gayshe su da tayi

Ta dubi marwaan tana sake hade rai tache,

"Ba zaka amsa ba ko me?"

Marwaan ya girgiza Kai yana duban Anees yace,

"Kiyi hakuri mind dina ya ya tafi wani wajen ne"


"Lalle fa. To a'ina agaban sa zamuyi magana ?"

Ta tambaya tana nuna sa Anees da yatsa.

Marwaan da jikinsa gaba daya ba kwari ya daga Kai,

"Eh eh."

"Okay ba damuwa.
Tanbayoyi ne uku zuwa hudu zan maka dama. Ina Kuma bukatar ka bani amsa dalla dalla"

"To..." Marwaan ya amsata yana satar kallon Anees

"Tanbaya ta farko shine...dama Kai ne marwaan sambaso . Dan gidan attajirin nan Alhaji yusuf sambaso? Tanbaya na biyu..menene dalilin boyemun Kai ko wannen su waye mahaifan ka akan me?" Ta tambaye shi tana tsare shi da idanu

Marwaan ya samu kansa da sakin zuciya dan mamakin tambayoyin.

"Kiyi hakuri nayi lefi, Kawai bansan rashin nuna ni din wanine ko nuna fahariya da su din iyayena ne da akeji dasu agari da kasa. Kuma nayi lefi da ban sanar miki ba kiyi hakuri"

Nawraah ta saki murmushin nan na gefen baki tache,

"Lalle fa... Amma meyasa zaka ce mahaifan ka since ka basu lokaci zasuyi magana ayanzun aiki ya sha musu Kai? Menene dalilinr? Shin zanyi wani abune na daban ko na matsa akan lalle kazo ka aureni?. Kai ma kasan iyayen ka ba tsaran iyaye na marigayu bane. Kwarya tabi kwarya ake. Kudin dangin masu kudi sai yaran masu dashi."

"Nawraah kiyi mun afuwa nayi lefi. Please. Kinji?. Bamaso na rasaki shysa ban gaya miki yadda mukai ba. Kuma bazan iya hakuri dake na barwa wani ke ba. Ni nake son ki Kuma nizan aureki. Babu Wanda zai hana inshaa Allah. Ki sake bani time"

"Sai tanbaya ta karshe. "

"Ina sauraron ki"

"Amma tambayar karshe. inaso ta zama kan tsarin lalle zaka gayamun meyasa da Kuma amsar, Sannan wannan tambayar ta karshe da zan maka marwaan. Ita ce kamar fate zance ne ko destiny. Marwaan I'm afraid idan har amsar tanbayar nan da zaka bani bame hujjaa bace. To daga yau ba bu hulda tsakanin mi "

"Ishas Allah ". Ya ambata cike da kwarin gwiwa, don yasan ba zato ko tsammanin zata fado wasu tambayoyin da zata raba tsakanin su ba kenan a ranar

"Tambayar karshen itace. Marwaan. Daman kanada masaniya akan abunda iyayen ka suka aikata akan nawa iyayen? Ina nufin kisan da sukayi wa iyaye na da babban wa na..a eh ko a'a"

Marwaan bakinsa har kasa ya fara yana duban Anees . Anees dashi kansa yayi mamakin tambayar da tayi a karshe yace,

"Nawraah please, dan Allah kiyi hakuri abar maganar nan. Dan Allah ki hakuri . Kar kiyi cutting relationship dinmu Nawraah. "

"Marwaan tambayar da nake maka zaka ban amsa"

Marwaan ya hada hannuwansa zai roketa ta dakatar dashi,

"Hmm. Alhaji sambaso da Dr bintu sune face behind my parents killers.. And my beloved brother "

"Nawraah. Bansan me kike fada ba"

"Kana nufin bakada masaniyad komai? Mahaifan ka daya kashe iyaye na da wana babba. Ka sani ka baka sani ba?."

Marwaan ya dubi Anees yana jan kasan rigar sa yace,

"Anees pls"

Anees ya bude baki zaiyi magana.. Nawraah ta dube shi ta watsa masa wani kallo tace,

"Dakata malsm. Ba neman ta cewa da ga bakin ka nake ba." Ta fadawa Anees tana sake dankara masa harara

Anees yayi shiru yana komawa gefe. Marwaan ya shiga matsa hannuwa yana yage su,

"Yes or no?"

Nawraah dan Allah "

"Malam amsa kawai zKa ban"

"Mahaifiyar ki da wanki, wallahi bansani ba, hear me out"

Nawraah ta girgiza kai ta dauki hanyar komawa ciki.. marwaan yayi saurin riko kasan mayafin ta,

"Nawraah please. Baby ki"

"Dan Allah ya isa haka.. ..daga yau ta bani ba kai, Na warware duk wata mu'amala da ke tsakanin mu.. bakasan ta mahaifiyata da yayana ba Amma kasan ta mahaifi na. Daman ance barewa ba zatai gudu ba dan ta yayi rarrafe. Bird of the same feather. Mugu bai da kama. Kauna tarufemun idanu na kasa tabbatarwa da zuciyata Kasan komai ba. Allah ya Saka mun"

Juyawa tayi da sauri ta shige gidan marayun nasu.....

_ADVERT👇👇_

_YERWA INCENSE AND MORE_
_(DUNIYAR KAYAYYAKIN KAMSHI MASU MATUKAR DADI DA KAMA JIKI, GIDAH, KAYA DA SAURAN SU)_


_INA MA'ABOTA TURARE? KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE_
_TSAFTA KUMA TANA CIKIN IMANI… TOH KU MAR-MATSO KUSA_

_MUN KUMA ZUWA DA HAJAR KAYAYYAKIN_

_*YERWA INCENSE AND MORE*_
_DOMIN SAMUN ZAFAFAN TURARUKAN WUTA NA GIDA, KAYA, JIKI, TSUGUNNO, GASHI... AKWAI KHUMRAHS MASU DADI YAN BORNU, CHADI, SUDAN DAMA SENEGAL, AKWAI OIL PERFUMES, DA TURARUWAN MOPPING DANA WANKA DANA WANKI DANA GADO DA KUJERU DA BANDAKI DA DRAWER DA MOTOCI.._

_AKWAI MAN GASHI NA FESAWA ME SA KAMSHI DANA KITSO. AKWAI KAYAYYAKIN KAMSHI DANA GYARAN JIKI SOSAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA. •_

_ADIRESHI: KANO.. AMMA SUNA TURA KAYAN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE..._

_INGANCI KYAU RAHUSA DA DADEWA A GIDAH DA KAMSHI SAI KAYAYYAKIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE_

_NAMBAR WAYAR SU: 08095215215, INSTAGRAM/THREADS/TWITTER:yerwaincense_and more_

_YOUR NUMBER ONE STOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS... THEY 'VE GOT YOU AND YOUR HOME COVERED_
_K'K'J_
_(M/W/S)_


_BOOK TWO_


_✍️:MX_


_34_


:::::::::

Marwaan ya qame a tsaye tamkar mutum mutumi.. Maganganun Nawraah na masa yawo a ilahiran Kai da rai , zuciya dama gangar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login