Showing 27001 words to 30000 words out of 69829 words
Chapter 10 - KWANKWASON JIMINA BOOK 2 COMPLETE BOOK 2 hausa novel
kenan, ke da iyalan ki baki daya da su Nawraah. Mai kika yanke? Yauwa sannan idan baki amince ba mai gidan nawa yace gaskia shi ya kawo karshen temaka muku da yake na jyayan abinci da sauran su. Hakama wadannan kayayyaki dana kawo yau sune karshen kawowa. "Ta karasa tana nuni da kayayyakin da yatsan ta
Nusaiba ta shiga wani hadiye wani tokararren abu daya tsaya mata a wuya. Duk ta yi wani iri cikin kankanin lokaci tamkar takardar da aka sanya a ruwa. Tabi ledojin da kallo dake maqe da kaya cikin su.
"Kinyi shiru nusaiba. Ba damuwa idan baki amince ba ba takura. Mutane da yawa sunason wannan damar aka tsallake su aka baki. Amma ba damuwa"
"To hajia misali shi wannan gidan namu kinga ya za'ai da shi? Sannan mu tafi wani garin bamu da matsugnin zama acan. "
Dr bintu ta dubeta tana yamutsa fuska tace,
"Duk wannan ba zai gagara ba. Amincewar ku kawai muke bukata"
Nusaiba ta sakeyin shiru tana ta nazari acikin kwakwalwar ta,
"Kuma kunga su Nawraah basa wajenmu yanzu"
"To fa suna Ina?"
"Suna gidan marayu..."
"Gidan marayu Kuma?"
"Eh. Nan din taga ba zata iya zaman su ba. Sun rena inda ake basu suna kwanan. Sun koma can"
Dr bintu tayi shiru. Don bata san su nawraahn basa nan ba. Yanzu ya zasuyi kenan.
"Ba zeyiwu ki mata magana ba?"
Nusaiba ta girgiza Kai tana nisawa tace,
"Ai Nawraah KWANKWASON JIMINA ce. MAI WUYAR SHAFAWA... In ta saka abu agaba yarinyar nan sai taga bayan sa...."
Dr bintu tayi shiru tana nazari itama. Nusaiba ta dubeta kafin tache,
"Amma hajia. Meya faru da lokaci daya zakice mu bar Naduka?"
"Ba komai... Kawai dai"
"Kawai me?" Nusaiba ta tanbayeta
Dr bintu ta danyi shiru. Can ta tuno ai nusaiba ba kaunar su nawraan take ba don haka tace,
"Magana ce ba wani boye boye. Kema ai kinada ya mace Kuma kinason tayi aure inda zata huta kema ki huta ko kuwa?"
"Kwarai dagaske hajia. Itace Layla yata diya kwaya daya mace. Ita ce kanwar Ahmad da kika basu gurbin karatu kyauta a jami'a"
"Mashaa Allahu..Allah ya raya mana su to. To azahirun gaskia. Dan waje nane. Da na kenan wallahi bamma sani ba. Sai zuwa yayi ya same mu wai yanason aje anema masa auren wata yarinya. Na karkare miki zance dai baban sa yake tanbayar sa wacece? Mulki ne da su ko sarauta yar wace zuriyar ce? Kinsan meyace?"
Nusaiba ta saka hannu a kirji ta dafe..yayinda idanuwanta suka furfito waje tache,
"Nawraah?"
Dr bintu ta kada mata Kai cikin tabbatarwa tache,
"Nawraah wai yake so da aure. Tsakani da Allah Ina shi Ina Nawraah?"
Nusaiba ta gyara zama idanunta sun kada sunyi jazir saboda bakin ciki tache,
"Ina bazeyiwu ba. Wai yanzu de yaron wajen ki zai auri wata Nawraah? Banda sharrin farar fuska na bilicin kwailin fa take, baka ce wuluk kamar bayan tukunya, sai shegen yauki da iya feleke na Nawraah ai ba kyakkyawa bace..Banza abanza ma irin ta" ta karasa fada tana sharce gumin daya tsattsago na bakin cikin zantukan ta.
"Kema dai kya fada. Ruwa ai ba saan kwando bane. Ko cikin kawayen mu dukkanin su yaran su yayan manya suke aure masu usuli da kudi ko sarauta ko yan kasuwa manyan attajirai da ake ji dasu a fadin kasar nan. "
"To yanzu hajia batun karatun nasu fa da sukeyi?"
Dr bintu ta girgiza Kai tana duban Nusaiba tache,
"Dan me ake karatun ba dan ayi kudi bane? Idan aka baku kudin da zai isheku baki daya rayuwar ku baa an rufe babun ba? "
"Hakane kam..."
"Toh wannan shine abunda ke tafe dani..Ina Kuma faran zaki karba kokom barar mu?"
"Ai kin kawo babban abunda ko waye ma zai amince. " Nusaiba ta fada tana jin zuciyar ta na zafi. Kenan Nawraah har samari masu kudi take da? Gaskia ba zata taba barin Nawraah ta yi aure ta shiga gidan nasu hali ba.
"To yanzu Ina zancen mu ya kwana?"
"Toh hajia ba matsala. Bari baban su ya dawo. Sai muyi maganar ko kuwa? Don kinga ita nawraahn ma sai na tausashi mai gidan yaje ya yi mata magana ya hilata su sannan"
"Banason adau lokaci ne Nusaiba "
"Hajia bakida damuwa. Ni ma bana goyon bayan auren nan nasu. Zan shiga cikin lamarin kakki damu"
"Tohm shikenan sai na jiki. Ga wannan ba yawa" ta karasa fada tana mika mata wata envelop dake dauke da kudade aciki
Nusaiba ta karba envelope din tana riketa gam tana murmushi,
"Angode hajia. Sai kinjini inshaa Allah"
"Ba damuwa"
Har bakin kofar mota ta rakata tanata dashare mata hakora. Dr bintu ta shiga mota tatafi tana kambama son kudi da zuciya irin na nusaiba. Yayinda Nusaiba ta koma gidah ranta fes ga kudi da kayan abinci da burikanta da zaa cika.
::::::::
Da sauri ta ajiye wayar data kammala da marwaan agefen gado tana zare wa Amnah rigar makarantar dake jikinta tace,
"Ki wanka sai ki canza kaya muje gidan Mami kafin marwaan yazo. Idan muka gaysa sai na zo na dauke ki mu dawo gidah ko?"
"Tohm Adda"
Amnah ta shige bandaki bakinta dauke da addua tayi wanka. Nawraah ma tashiga bayan Amnaan ta fito itama tayi wanka ta zura wata riga marar nauyi ta dora hijabi akai.
Abincin da aka musu ta dakko ta zubawa Amnah faten doya ne da bushasshen kifi da ruwa su kaci suka ajiyewa su Raudah nasu.
Tana rike da hannun Amnah suka shiga gidan nasu hajia Qibdiyya. Kai tsaye suka nufi parlornta bakunan su dauke da sallama bayan sun danna door bell an bude musu.
Suna zama ba dadewa sai gata ta sakko tana murmushin ganin su.
"Ah lale marhaba Amnah da Nawraah na ne, Sannun ku"
Nawraah tayi murmushi. Suka durkusa suka gaysheta itada Amnah. Sun zauna a kasa kamar kodaa yaushe ta tilasta musu suka koma kan kujera suka zauna
Bayan sun gaysa ne tasa akawo musu abinci Nawraah tace sunci, duk da da haka ta saka a kawo musu snacks da lemuka da ruwa da chocolates. Ta kuma sanyawa Amnah acaroon tache ta kalla.
"Nawraah mucigaba da addua fa, inshaa Allah komai zai bayyana. Jiya munyi magana da baban su Anees yake shedamun anyi bincike akan sassan jikin motar da aka gani atare da kayan marigayiya. So akwai progress inshaa Allah"
Nawraah tayi murmushi tache,
"Allah ya amince Mami. Nima dama kusan abunda ya kawo ni wajen ki kenan.... Akwai yan wasu abubuwan da na keda su Wanda Ina tunanin zasu zama mukulli na bude ko ince bankada dukkanin boyayyan lamarin "
Hajia Qibdiyya ta kada kai tana duban Nawraah tace,
"Mashaa Allah, kamar Mai da me kenan?"
Nawraah ta dakko wayarta acikin jaka ta dubi hajia Qibdiyya tace
"Mami ko zaki iya tunowa?"
Hajia Qibdiyya ta dubi wayar tana duban Nawraah.
"Waya ce dai gatanan a hannun ki.."
"Kin manta wata waya da kika bawa ummyn mu?"
Hajia Qibdiyya jikinta ya fara rawa kamar mazari ta duba wayar tana jujjuya Kai,
"Wallahi itace. Allahu Akbar. Itace tabbss. Ya akai wannan wayar tazo hannun ki Nawraah?"
"Daga hannun ummy tajr hannun hamma shir. Daga hannun hamma Ashir tazo hannu na. Hamma Ashir yamun wasiyya kan karnayi amfani da ita har sai na shiga babban aji na uku zuwa na hudu.."
"Me hakan ke nufi kenan Nawraah?"
Nawraah ta dan sake muskutawa dawayar a hannun ta tana kokarin mikawa hajia Qibdiyya tache,
"Ko zaki saurari wannan ma....
Bata karasa fada ba aka budo kofar parlorn aka shiga. Marwaan ne da Anees suka shiga ciki bakinsu dauke da sallama . Da sauri ta mayar da wayar cikin jakarta. Suka amsa musu sallamar da sukayi...
_ADVERT👇👇_
_YERWA INCENSE AND MORE_
_(DUNIYAR KAYAYYAKIN KAMSHI MASU MATUKAR DADI DA KAMA JIKI, GIDAH, KAYA DA SAURAN SU)_
_INA MA'ABOTA TURARE? KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE_
_TSAFTA KUMA TANA CIKIN IMANI… TOH KU MAR-MATSO KUSA_
_MUN KUMA ZUWA DA HAJAR KAYAYYAKIN_
_*YERWA INCENSE AND MORE*_
_DOMIN SAMUN ZAFAFAN TURARUKAN WUTA NA GIDA, KAYA, JIKI, TSUGUNNO, GASHI... AKWAI KHUMRAHS MASU DADI YAN BORNU, CHADI, SUDAN DAMA SENEGAL, AKWAI OIL PERFUMES, DA TURARUWAN MOPPING DANA WANKA DANA WANKI DANA GADO DA KUJERU DA BANDAKI DA DRAWER DA MOTOCI.._
_AKWAI MAN GASHI NA FESAWA ME SA KAMSHI DANA KITSO. AKWAI KAYAYYAKIN KAMSHI DANA GYARAN JIKI SOSAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA. •_
_ADIRESHI: KANO.. AMMA SUNA TURA KAYAN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE..._
_INGANCI KYAU RAHUSA DA DADEWA A GIDAH DA KAMSHI SAI KAYAYYAKIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE_
_NAMBAR WAYAR SU: 08095215215, INSTAGRAM/THREADS/TWITTER:yerwaincense_and more_
_YOUR NUMBER ONE STOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS... THEY 'VE GOT YOU AND YOUR HOME COVERED_
_K'K'J_
_(M/W/S)_
_BOOK TWO_
_✍️:MX_
_23_
:::::::::
Suna shiga yayi tozali da ita. Samun kansa yayi da tsayawa daga bakin kofa yana biye da ita da wani irin kallo tun daga kan kafafunta dake sanye cikin bakar safa ya zuwa kan kyakkyawar fuskar tah...
Marwaan ya karasa wajen su da sauri ya zube kallon sa fes akan sahibar zuciyar sa Nawraah...
Ita dinma shi take kallo tana murmushi hadi da saye fuska.
"Ah Marwaan" hajia Qibdiyya ta kira sunan sa tana murmushi
"Mami Ina wuni...?"
"Lafiya kalau marwaan. Ya su dr?"
"Suna nan kalau Alhamdulillah"
"Mashaa Allah! Meye haka kai kuma kaa tsaya daga can sandar ba'are?'"
Hajia Qibdiyya ta fada tana duban Anees dake tokare ajikin bango.
Sai a sannan Nawraah ta cire Kai ta dora akan sa. Idanuwan su suka sarke dana juna tayi azamar janye nata da sauri don kwayar idanunsa kansa ka tsaya kana duban sa sosai. Yanada wasu irin idanu tubarkAllah manya manya masu dauke da gashin ido Zara Zara baki wuluk
"Au wai bai taho ba? Yan mulkin sun motsa kenan" marwaan ya fada yana duban Anees.
Anees da ya kasa magana ya Kuma ki takawa daga inda yake zuwa wajen su Mami. Ji yayi bugun zuciyar sa ya sauya yana wani irin bugu sosai daya kasa tantance Wa saboda har wani zillo yakeji acikin kirjin sa.
Ba kadan ba Nawraah ta sakeyi masa kyau. Har ya sake cire Kai ya mata kallo na biyu. Bai sanda ya sauke ajiyar zuciya ba
"Mami...Ina zuwa" ya fada da sauri yana juyawa ya fuce daga parlorn
Nawraah daman jikinta ya bata sai yabar parlorn. Kasancewar yadda yake kyamatarta aganinta ba zai iya zama idan tana waje ba. Don haka ta dubi marwaan kawai ya daga kai suka sakarwa juna murmushi..
Juyawar da zaiyi yaga hajia Qibdiyya na duban su yayi saurin sakaa hannu a keya yana sosawa...
"Ina wuni?" Nawraah ta gayshe shi tana lankwasa hannuwanta.
Ya saci kallon hajia Qibdiyya yaga su take kalla.
"Lafiya lau" ya amsa ta yana mikewa tsaye
"Mami bari na je"
"Har zaka tafi marwaan. Ka tsaya Kaci abinci mana"
"A koshe nake Mami...." Ya fada yana satar kallon Nawraah datayi kicin kicin kanta akan tv
"To shikenan. Ka gayshe da Dr."
"Zata ji inshaa Allah" ya amsa da dan karfi ko Nawraah Zata waiwaya su hada idanu
Tana hankalce dashi don haka taki juyawa tana cigaba da kallon tv dake nuna hotunan faifon bidiyon fim din wasan na tom and Jerry.
Fucewa yayi bayan ya sake zuwa wajen bakin kofa yana dan daga murya,
"Mami shikenan"
"Tohm ka gayda gidah"
Ransa ya Kai koluluwar baci ganin Nawraah tayi kicin kicin bayan tasan wajen ta yazo. Amman ta nuna tamkar ma bata taba ganin sa ba
Wayar sa ya zaro agaban riga ya danna mata kira. Dauka tayi tana duban screen din tasan sarai daman shine zai kira.
"Ki dauka mana ba Kiran ki ake ba?"
"Ba komai Mami"
Hajia Qibdiyya tayi murmushi tana duban ta tace,
"Marwaan ne ai ko? Tashi kije mana ko na baki waje zai zauna anan?"
Nawraah kunya sai ta lullube ta, Daman hajia Qibdiyya tasani? Yaushe ta sani? Kunya duk ta sake gauraye ta. Ta Saka tafukan hannuwanta tana rufe fuskar ta.
Hajia Qibdiyya tayi murmushi tana mikewa tsaye,
"Bari mu baki waje ko?kice ya shigo nan. Amnah zo muje can parlorn na saka miki wani cartoon din. "
Amnah ta mike. Hajia Qibdiyya ta rike hannunta suka nufi dayan parlorn
Nawraah ta dubi wayar da marwaan ke sake kiranta a karo na wajen takwas ta dauka,
"Hello...."
Marwaan dake dakin Anees a tsaye daya shiga ya gyara tsayuwar sa yana amsata. Anees na zaune akan kujera yana danna wayar hannun sa.
"Habjbty...."
"Naam"
"Shine kika nuna tamkar bakisan Allah ya halicce ni ba kina waskewa, Nazo inata murmushi kin hade rai kina kallon tv, Haba babe meye haka?"
Nawraah ta hararo wayar kamar shi take gani cikin turo baki gaba cike da shagwaba tache,
"Mami fa na wajen ai da kunya"
"Banda ke da abun ki. Mami ai mahaifiyar mu ce.. Albarka ma zata saka mana. Amma kika wani shareni. "
"Hakane. To kayi hakuri"
"Ki fito Ina waje "
"Ai Mami tace ka shigo parlor ta bamu waje"
Marwaan ya fashe da daria yace,
"Su duk saye sayen fuskar da kike sai da mami ta gane?"
"To ba dole ta gane ba ka sakani agaba kana kallo kamar mudubi"
"To ai kedin mudubin zuciyata ce ke zuciyata ke dubawa take samun annuri da farin ciki"
"Uhm lalle fa. To kazo dai parlor ko lokaci na kurewa"
"A'ah ba wani lokaci daya kure. Ni da bamuyi zancen bama"
"Ba gashinan munyi ta waya ba?"
"Wallahi baki isaba. A'ina mukai zancen kinma isa. Chab"
Nawraah ta fashe da daria. Har Anees yana jiyo ta. Daman dukkanin hirar da suke tanata masa yawo a kunne. Don sauraron muryar Nawraah kadai idan yaji wani nutsuwa ce ke gauraye shi.
"Dan wahala na tafi zance" Marwaan ya fadawa Anees yana dafa kafadar sa
Anees yayi murmushi yana girgiza Kai yace,
"Ga ku nan yan wahala Kai da ita..."
"Karya kake senior man. Ko comrade zance me ko. Oho maka dai. Ni na tafi zance"
"Madalla"
Marwaan yayi daria kafin ya futa yana girgiza Kai. Yana fita Anees ya mike da sauri ya rufe kofar dakin
Ya koma dakyar ya kwanta akan gadonsa, Ya sanya hannunsa daya ya dora a saitin zuciyar sa dake wani irin bugu da rada'di. Ba komai bane ya sanya zuciyar sa cikin yanayin da yake ciki. Fyace Nawraah daya gani Kuma gashi zasuyi zance da marwaan. Wannan al'amari yana takurawa zuciyar sa. Yayi yayi ya cure komai na Nawraah a tattare dashi, Amma hakan ya cimma tura. Tamkar sake ingiza lamarin yake, Ko da yaushe cikin tunanin ta yake. Kullum yaumun ba fashi.
"Ya rabbi ka shiga cikin lamurana. Ka mini zabi nagari ya Allah. Kada ka barni da iyawata Allah. Yaa Allah ka dube ni. Kamin zabin ka mafificin alkhairi. "
Wasu siraran hawaye suka shiga zuba daga idanun sa. . Wayar sa ce ta fara Kara. Ya daga yana duba screen din mahaifiyar sa ce. Mami da sauri ya dauka yana kokarin saita kansa
"Anees..." Ta kura sunansa.
"Naam Mami"
"Abincin ka fa yana nan bakazo Kaci ba. Kana Ina ne?"
"Mami Kai nane yake dan ciwo na sha magani idan ya tsurga zan zo "
"Kai Kuma? Subhan'Allah Allah ya baka lafiya kaji? Tashi muje asibiti to"
"No Mami ba wani babban abu bane. Normal headache ne na stress . Nasha painkillers kakki damu"
"To shikenan inde ciwon ya dena kazo Kaci kaji? Idan Kuma ba zaka iya zuwa ba sai akawo maka"
"To shikenan idan ya tsurga din"
"Toh sannu" ta katse Kiran tana ajiye wayar a gefe suka cigaba da kallon su da Amnah.
Yayinda Anees ya gyara kwanciyar sa akan gadonsa idanunsa na kan pop yana tunani sosai .
Marwaan na karasawa parlorn ya nemi kujera ya zauna yana duban nawraah.
Kanta a kasa tanata murmushi. Marwaan ya zage ya dinga jan ta da hira. Tun tana boye boyen fuska tana magana ahankali kar Mami ta jiyo su har ta saki jikinta suka shiga zance Ka'in da na'in
Sai da marwaan ya mike zai tafi yaje bakin kofa ya juya da sauri yana cewa
"Ai ni ba na manta ba.... Munyi magana da su Maa . Mamanmu kenan da babanmu. Inshaa Allah soon zaazo nema mun auren ki. Yanzu akwai yan issues da ake settling na business din su baba. He's so occupied ne. Amma yace daya gama zaa zo" ya karasa fada yana murmushi yana kuma adduar Allah yasa ta yarda da karyar daya fada don bayasan ya gaya mata gaskiar lamarin. So yake ya cigaba da ba iyayen nasa hakuri su amince a nema masa aurenta.
"Ba damuwa... Allah zabar mana abunda yafu alkhairi,"ta amsa shi tana ta murmushi
"Ameen baby ta. Mrs marwaan to be"
Da sauri ta Saka hannu tana rufe fuskar ta da tafukan hannayenta. Marwaan yayi murmushin shima sukayi sallama ya wuce dakin Anees ya masa sallama ya tafi gidah yanata ayyana yadda zai sake yin maganar da iyayen sa. Amman kafin sannan so yake yanzu ya shiga zurfafa bincike akan faifon bidiyon nan.
🥳
_HGL CHARITY FOUNDATION_
_ASSALAMU ALAIKUM WA RAHAMATULLAH!_
JAMA'A BARKANKU DA _WARHAKA... ALLAH YA SAKA MUKU DA ALKHAIRI YA BADA LADA HADI DA BIYA MUKU DUKKANIN BUKATIN KU DA KUKE FATAN SAMU AAMIN_
GODIA DUBU GA TALLAFIN DA KUKA SAKA NA CIYARWAR AZUMI
INSHAA ALLAHU WANNAN GIDAUNIYAR MAI SUNA A SAMA NA KIRAN MUTANE AL'UMMA MASU SON SAMUN LADAN WANNAN MANYAN AIKI DA MUKE SAKA RAN FARA SHI KAMAR
НАКА
1• DAFA ABINCI A RABA GA MABUKATA RANAR JUMU'AH KO A KAI RUWAN SHA GA MASALLATAI RANAR JUMU'AH
2• HAQA RIJIYOYI ACIKIN KAUYUKA DA UNGUWANNIN DA BASUDA RUWA
3• RABA KAYAN ABINCI KO KUDI GA MABUKATA
MARASA HALI
4•KAI ZIYARA GIDAN MARAYU DA KAI MUSU
ABUBUWAN AMFANI DA SUTURA IDAN DA ME BAYARWA
5• KAI TALLAFI KO ABINCI GA ASIBITOCI WAJEN
MASU JINYA MARASA KARFI..
6•KOKARIN KARASA MASALLACI KO YIN MASALLACI
AWAJEN DA BASUDA SHI...
MAI NERA BIYAR MAI GOMA DiK
YADDA HALI YA KAMA ALLAH YA HADA MU A LADAN DUKA..
JAZAKUM ALLAH BiL JANNAH..
DOMIN SAKA TALLAFI GA ASUSU
9044191709
OPAY
JAZAKUM ALLAH BİL JANNAH💜
_K'K'J_
_(M/W/S)_
_BOOK TWO_
_✍️:MX_
_24_
:::::::::
Tana ta zaune su hajia Qibdiyya basu fito ba. Ganin ba lalle su san ta kammala zancen ba. Hakan yasa ta mike ta nufi dayan paroorn bakinta dauke da sallama
"Nawraah. Ya tafi ne?"
"Eh tun dazu" ta amsata tana satar kallon ta duk kunya taka ma ta
Hajia Qibdiyya tayi murmushi ta riko hannun amnah suka fito
"Munata zaune gaho bamu sani ba. Kinji fa Amnah"
Amnah tayi daria tana cigaba da shan capri-sun din da hajia Qibdiyya ta bata.
"Wallahi" Nawraah ta fada tana binsu a baya.
Babban parlorn suka koma suka zauna. Hajia Qibdiyya tache,
"Nawraah! Muna magana dazu su Anees suka shigo bamu Kai karshe ba ko ince banga abubuwan ba"
"Oh eh. " Nawraah ta fada tana gyara zamanta. Ta sake cewa,
"Mami waye Alhaji ateeks?"
Hajia Qibdiyya ta dubi Nawraah sosai kafin tace,
"To ai bazan san Wanne kike nufi ba. Dubada ta iya yiwuwa wani Alhaji ateeks din kike nufi na daban. Amman dai yadda kika ambaci sunan Alhaji ateeks ba atiku ba Ina tunanin Wanda Kike fada din shine Wanda nakeda masaniya akan sa."
Nawraah ta jinjina Kai cikin tabbatarwa tace,
"Kila shine.