Showing 21001 words to 24000 words out of 69829 words
ne suka dallare ko'ina da-dal da-dal tamkar rana mai tsananin kwalewa.
Tundaga kan dan karamin bakinta dake dauke da labba jajaye. Zuwa siririn hancin ta dake da hujin hancj da barimar hancib agefen dama. Har ya zuwa manyan idanunta tubarkAllah dake dauke da kwalli. Zuwa girarta da ke cike da gashi tamkar zasu hade da juna.
"Tsarki ya tabbtata ga Allah Wanda ya halarci wannan halitta tubarKAllah" ya karasa fada yana sake kurawa Nawraah idanu
A haka suka karasa gaban motar rasa. Yayi hanzarin zare lock , wasila da Raudah da faty sukayi shigewar su baya suna mata daria.
Takaici ne ya isheta ganin itada suka bari da shiga gaban gashi Raudah ta ja hannun Amnah sun shige baya duka.
A kufule ta bude gidan gaba ta zauna tana waiwayawa baya ta dankara musu harara. Anees na hankalce da ita ta wutsiyar idanun sa. Dariya ta taho masa ya danne Kai yana zura mukullin motar hadi da tashinta bakinsa dauke da addua.
"Sannu ku....." Ya fada a hankali yana karya kan motar.
Suka dube shi dukan su. Kafin su fara gayshe da shi. Sai da Nawraah ta mula ta sha iska tukun sannan ciki ciki tache da shi,
"Ina wuni?"
Ya nemi magana a fatar bakinsa ya rasa ya kasa amsa mata. Gashi zuciyar sa na wani irin rawa tamkar Zata fado kasa. Muryarta kadai ta saukar masa da wani irin farin ciki daya kasa bayyana adadin sa, Amman haka kawai bakinsa ya masa bakin ciki yayi nauyi wajen mayarwa sahibar ransa amsar gaisuwar ta.
Ta sake juyawa tana duban sa hadi da tabe baki ta hararo shi. Tana Kara kambama mamaki irin na rashin mutincin sa da tsanar da yake mata. Wato kowa ya gayshe shi ya amsa amman da ke ita ya tsaneta shine yayi shiru ya cigaba da tuki..
Anees kuwa kuka ne kawai ya rage baiyi na. Kwata kwata ya kasa mayar mata da gaisuwar da tayi masa, me zata kira hakan idan ba wulakanci ba? Ya sauke ajiyar zuciya yana girgiza Kai kawai. Ba wani abu da zai fada yanzu a yadda dashi.
Jikinsa a sanyaye duk ba dadi haka ya karasa da su har unguwar su dai dai kofar gidan marayun na su ya faka motar. Suka fita dukan su. Banda kofar Nawraah data saka hannu zata bude tajita a rufe.
"Dan ciremun lock" ta fada masa tana mai nuni da murfin dayaki murduwa.
Yana sane ya saka lock din ya rufe. Wai dan ya samu yayi mata magana ya bata hakuri da ba halinsa bane shariya da sauran su. Amman baki daya gangar jikinsa ta hade Kai da fatar bakinsa sa, sum masa butulci sam ya kasa tabuka komai. Sai juyawa da yayi kawai ya zube mata manyan idanunsa tubarkAllah akanta.
Ta kasa jure kallon da yake mata kamar zai cinye ta. Gashi dama wani irin idanu ne dashi tamkar yana bacci Kuma manya tubarkAllah.
"Ka budemun mana." ta sake fada tana juyawa baya ganin su Raudah sun shige ciki sun barta
"Naw.... Raaah" ya fada ararrabe yana jan kasan lebensa.
Duban sa tayi da sauri Daman yasan sunanta? Ko da yake ai ko awajen mahaifiyar sa zaiji tunda tana temaka musu sosai wani abun ma shi ake aikawa ya kowa musu gidan marayun
"Dan Allah ka budemun" ta sake marairaicewa tana kokarin bude kofar.
"Bani minti biyu please" ya fada a wahale yana jinginar da kansa jikin sitiyarin motar.
Zuciyar sa na harbawa cikin wani irin fizga da takeyi. Gumi na kokarin keto masa dukkuwa da na'urar ac dake bazawa a motar.
Tarin kalamai ne na love confessions akansa da zuciyar sa, Amman ya kasa samun kwarin gwiwar gaya mata. Nawraah ganin abun nasa bana kare bane ta sake cewa
"Zan fita malam"
Bai ce komai ba. Ya Saka hannu ya danna wani button take kofar ta bude. Ta futa da sauri tana buga murfin motar da karfi hadi da hararo motar ta shige cikin gidan marayun da sauri.
Ya dade a zaune amotar kansa akan sitiyarin har sai da ya tabbatar ya samu nutsuwa sukun sannan ya daga kansa. Saitin kirjinsa ne kawai yake masa nauyi mai wani irin radadi marar dadi
A daddafe ya karasa gidah yaga akwai motoci biyu da direbobi. Nan take ya sanar musu sakon Mamin su. Daga baya shima ganin ba zai iya komawa can wajen bikin ba ya sauka daga motar ya bawa wani direba ya hau tasa suka koma can wajen bikin dan cigaba da jigila da mutane..
Yayinda shi Kuma ya karasa shiga gidah ya shige dakin sa direct bandaki ya fada yayi wanka ya dauro alwala ya zube akan gado yana sauke numfashi. Hannunsa dafe da saitin zuciyar sa dake masa zugi...
=====
Koda ta shiga dakinsu sai data tabbatar ta bankawa daya bayan dayan su harara tukun sannan ta fara mita
Suka fashe da dariya suna bata hakuri. Dakyar ta yadda ta sakkoo take gaya musu yadda akayi. Sunata cewa kila bashida lafiya ne waye waye.
Ita kuwa Nawraah bandaki ta shiga ta sakeyin wanka. Tab sauyawa Amnah kaya zuwa na bacci tayi bacci..
Sannan itama ta koma nata gadon ta kwanta ba dadewa marwaan ya kirata suka sha hirar su take gaya masa yadda akayi. Yake sheda mata itama wajen mahaifan sa zashi yayi maganar ta azo a saka rana ayi auren su.
Bayan ta katse wayar ne take gayawa su Raudah yadda sukayi da marwaan. Nan sukaita tayata murna suna tsallen ihu.
Ranar duka dai baccin dadi sukayi baki dayan su musanman Anees daya samu kansa daga baya. Sai murmushi yake idan ya tuno yau yadau Nawraah amotar ya dawo da ita gida har sunyi magana ta fatar baki ma gashi har yanada number ta. Ranar dai har mafarkin ta sai da yayi da ita saboda tsabar zancen ta daya kasa curewa a zuciya da ran sa
:::
Tana Kai Amnah makaranta ta shige library din makarantar su. Kasancewar akwai wani elective course da suke atare da Layla Kuma an basu assignment zasuyi presentation. Don haka tanata sauri ta karasa library din
Sai dai Kash students sun cika shi ba masaka tsinke an hana shiga. Haka ta hakura ta koma wajen wasu kujeru tana jiran Layla.
Wayarta ta janyo tanata dannawa. Can dai ta shiga cikin files din wayar tana sauraron wakokin ta na baya datayi recording.
Wasu tayi dariya dan ta tuno yadda tayi recoding din wasu su sakata hawaye inta jiyo muryar yan gian su haka. Da haka har tazo kan wani recoding din wakar Maher Zain datayi agidan su dr bintu. Tana cikin jine ta fara jiyo zancen da sukeyi. Komai da komai da sanda ummyn su tabarar da plate din tana basu hakuri.
Idanuwanta suka kawo ruwa. Ta mike da sauri tamkar an tsikareta tana tafiya hanyar gate. Ta samu waata kujera ta daban daga gate ta zauna tana cigaba da kunna abubuwa. Har ya zuwa videos gasunan Wanda Alhaji sambaso ke maganar komai da komai da sanda ya tura mahaifin su a baranda ya mutu.
Hannunta ta saka akan bakinta jikinta sai rawa yake. Ta mike tsaye tana kyarma. Idanuwanta na futar da ambaliyar hawaye.
"Innalillahi Wa inna ilaihi rajiun.... Su suka kashe ummy... Suka kashe abbiey... Kuma suka kashe Hamma..."
Juyawa tayi da sauri tana tafiya tana goge hawayen fuskar ta. Ta nufi gidan marayun da suke ta shige daki ta saka mukulli.
Filla filla tayiwa wayar ta saurari komai taga komai. Fargaba, tsoto, karfin gwiwar atare lokaci daya taji sun kamata.
Tashiga zagayen dakin tana nazari sosai kan yadda zata bullowa lamarin. Sai girgiza Kai take. Hawaye daya nabin daya...
"Ni Nawraah... Nayi alkawari da yardar Allah sai karashen mugayen nan yazo inshaa Allahu.... "
"I count all my hopes n you Nawraah... Kefin KWANKWASON JIMINA ce Nawraah, MAI WUYAR SHAFAWA" ta tuno kalaman da mahaifiyar ta da hamman ta ke yawan gaya mata.
Tabbas inshaa Allah ba zata tankwaru ba sai taga karashen mugayen azzaluman da suka kashe mata iyaye da dan uwa...
Littafi ta dakko da biro ta ajiye akan cinyar ta tana daga kanta sama,
"Alhaji sambaso.... Dr abubuakhar dollars, Dr. Bintu... Hajia Qibdiyya... Alhaji ateeks... Waye shi?" Ta tanbayi kanta tana jijjuya shi..
::::
Zaune yake yayi zaman gurfane agaban su. Gabansa na dukan uku uku gefe daya kuma yanada babbar hujjar da zai bayar idan an hanashi yace,
"Na samu matar aure ne... Anan cikin Alharamein university."
Dr bintu tayi murmushi tana duban mai gidan nata tache,
"Lalle mashaa Allah. Finally marwaan ana maganar manya"
Alhaji sambaso shima murmushin yayi yana sakaace hakoran sa da toothpick yace,
"Yar waye? Mulki suke takama dashi ko sarauta?"
"Ba yar kowan kowa bace ... Cuz iyayenta ma sun rasu"
"What?"
"Nawraah mana.. daya daga cikin yaran da kika bawa scholarship ."
Dr bintu na zaune sai ta mike. Alhaji sambaso ya dubeta ya dubi marwaan don baki daya ma ya manta wacece wata Nawraah.
"Wacece Nawraah?" Alhaji sambaso ya tambaye shi yana duban Dr bintu mai dakin sa.
"Alhaji Nawraah fa... Diyar Hindu mai aikin nan ta shekarun baya"
Tana karasa fada Alhaji sambaso ya mike tsaye yana hade rai kamar tsohon zaki ya saka dan yatsa yayi nuni da marwaan cike da bacin rai kololuwa yace,
"Idan ma mafarki kake gwara ka farka, idan tunanin kake gwara ka dakata. Kasan me ake nufi da kwarya tabu kwarya? Ina nufin ba Kai ba auren na kasa da Kai. Kaje ka nemo koma yar wacece na daga sashen masu mulkin ko sarautar zan aminta kayi aure, Amman ba wannan zuriyar kananan mutanen ba"
"Ita nake so ita nake kuma muradin aura ..."
"Idan anyi auren nan to ka tabbatar ba rai na. Ko bayan rai na akayi auren nan ban yafe ba wallahi. Gafara" ya Saka kafa ya shure cinyar marwaan ya wuce.
Dr bintu ta sulale akan kujera gabanta na dukan uku uku. Marwaan ya mike cikin zafi nama yayi dakinsa da sauri
Laptop dinsa ya ciro acikin akwati ya sanyawa dakin mukulli ya kunna laptop ya danno can file din daya yi masa maboya can cikin system din nasa..
Da code ma ya shiga ya bude shi ya fara kallon faifon bidiyon tiryan tiryan har ya zuwa sanda mahaifin nasa ya tura mutumin ta baranda ya fadi ya mutu...
Daga kai yayi sama yana tunanin sunan, yana kuma fadan sunan a labbansa. Malam Junaid. Ah Nawraah Junaid... ?
"What??? "Ya fada da karfi yana mikewa tsaye. Baki daya jikinsa sai yau kyarma..
Kenan dama mahaifin Nawraah . Babansa ya kashe? Salati ya farayu yana rufe bakinsa da tafun hannunsa. Yayinda jikinsa ya dau rawa lokaci daya tamkar mazari..
_ADVERT👇👇_
_YERWA INCENSE AND MORE_
_(DUNIYAR KAYAYYAKIN KAMSHI MASU MATUKAR DADI DA KAMA JIKI, GIDAH, KAYA DA SAURAN SU)_
_INA MA'ABOTA TURARE? KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE_
_TSAFTA KUMA TANA CIKIN IMANI… TOH KU MAR-MATSO KUSA_
_MUN KUMA ZUWA DA HAJAR KAYAYYAKIN_
_*YERWA INCENSE AND MORE*_
_DOMIN SAMUN ZAFAFAN TURARUKAN WUTA NA GIDA, KAYA, JIKI, TSUGUNNO, GASHI... AKWAI KHUMRAHS MASU DADI YAN BORNU, CHADI, SUDAN DAMA SENEGAL, AKWAI OIL PERFUMES, DA TURARUWAN MOPPING DANA WANKA DANA WANKI DANA GADO DA KUJERU DA BANDAKI DA DRAWER DA MOTOCI.._
_AKWAI MAN GASHI NA FESAWA ME SA KAMSHI DANA KITSO. AKWAI KAYAYYAKIN KAMSHI DANA GYARAN JIKI SOSAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA. •_
_ADIRESHI: KANO.. AMMA SUNA TURA KAYAN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE..._
_INGANCI KYAU RAHUSA DA DADEWA A GIDAH DA KAMSHI SAI KAYAYYAKIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE_
_NAMBAR WAYAR SU: 08095215215, INSTAGRAM/THREADS/TWITTER:yerwaincense_and more_
_YOUR NUMBER ONE STOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS... THEY 'VE GOT YOU AND YOUR HOME COVERED_
[5/5, 10:57 PM] Hafsaat🧕💞: _K'K'J_
_(M/W/S)_
_BOOK TWO_
_✍️:MX_
_19_
:::::::::
Kansa ne ya fara masa nauyi yana masa wani irin zugi tamkar zai ballo daga gangar jikin sa ...
Take kuma gumi ya shiga wanke masa ilahirin jikin sa. Gabansa na matukar razana yana bugawa da karfi
Ya sanya hannun sa akan goshin sa dake tsattsagar da ruwa na tashin hankali.
"Subhan'Allah!" Ya ambata a hankali yana rufe bakin sa.
Baki daya lamarin ne yazo masa a baibai ce bai taba zato ko tsammanin haka ba.
Yanzu ta Ina zai fara? Ina bakin zaren yake? Me ya faru da har mahaifin sa ya kashe mahaifin Nawraah? Duk wadannan tarin tambayoyin da ma wasu sune kunshe a asansajin kirjin marwaan .
Kansa ya kulle sosai ya rasa wace madafa zai kama. Ganin bashida yadda zaiyi sai ya mike kawai ya futa daga cikin dakinsa zuwa sashen mahaifiyar su
Yana zuwa ya kwankwasa mai aiki ta bude masa ya shiga.
Zaune ya hango mahaifiyar tasu Dr bintu tana zaune akan kujera ta zabga uban tagumi.
Sallama ya sakeyi a karo na uku sannan ta farga ta gyara zaman da tayi tana duban sa,
"Ya akai?" Ta tanbaye shi tana sauke gwauron numfashi.
"Akan maganar dazu ne"
"Bakaji abunda mahaifin ku ya fada bane? Ni me zanyi akai?"
"Maa Kisa baki manaa . Saboda Allah Ina kaunar ta Allah" ya karasa fada tana sosa keyar sa da alama baisan karashen zancen zai fita ba
Dr bintu ta dube shi ta kauda kanta tana lankwasa yatsun ta tace,
"Wannan magana ma a barta kawai. "
"Ma please"
"Abar maganar nan marwaan. SON RAI KO ZABIN IYAYEn (littafi na) ka zaka bi?"
Bai amsa ba illa kasa da yayi da kansa. Don gaskia bayason ya rasa nawraahn yana son kasancewar ta mata agare shi.
"Kayi shiru"
"Ma ni dai nafi son na aureta"
Mikewa tayi zata bar wajen ya rarrafa ya riko kasan dunduniyar kafafunta. Ta daga kai tana duban sa ranta a hade yake. Muryar sa na rawa da jikin sa ya shiga rokonta,
"Maa! Dan Allah ki Saka baki na auri Nawraah. Kinji ma please?"
"Sakar mun kafafu marwaan kafin ranka ya baci"
Cikin haka sai ga sakkowar lily tana tafe tana danna wayarta. Ta dube su da kallon karin bayani. Marwaan da idanun sa suka cika taf da hawaye ya dubi lily,
"Dan Allah ki tayani rokon su kinji?"
"Meya faru?" Ta tanbaya kanta akan screen din wayarta
"Wata maganar banza yake nan. Wai yanason aje anema masa auren yarinyar nan ta makarantar ku"
Lily sanin Nawraah ce ta tabe baki tana turo shi gaba tace,
"Kai ma dai yaya wannan yarinyar Ina Kai Ina aurenta. Well Maa ku ku kyale shi mana ya aureta" ta fadi haka daga karshe sanin zai iya yanka mata rashin mutinci idan bata goyi bayan sa ba daga baya.
Dr bintu ta mike kafar tata ta shure hannuwan Marwaan ta bar wajen da sauri.
Kai tsaye ta nufi dakin mai gidan nata Alhaji sambaso. Ta kwankwasa kofar ta shiga bakinta dauke da sallama
Yana bakin gado a zaune ya dafe fuskar sa da dika hannuwan sa ya tallabe
"Alhaji" ta kira sunansa tana zama akusa da shi
Daga kai yayi ya dubeta yana mayar da kansa sama.
"Alhaji yanzu ya zamuyi da yaron nan?"
Daga kai yayi ya dubeta sosai yana cigaba da fuskantar ta yace,
"Kinsan dai ko mai zai yi bazan bari ya aureta ba ko?"
"Nima bana goyon bayan auren su gaskia. Duba da ni zan zama koma baya acikin kawayen mu. Kowacce yayanta bakaga wadanda suke aure ba. Ko Mulki ko sarauta ko shahararren yan kasuwa. Amman ance mu ga inda namu ya kare saboda Allah fa. Kana ganin hajia Qibdiyya ma dubi yaranta wadanda suka aura fa?"
Alhaji sambaso ya nisa kafin yace,
"Koma dai yaransu gayyan na ayya suka aura, Ni babu da na da zai auri wadanda basuda tushe na arziki mutanen da ba yan naduka bane zuwau ne fa. Haka kawai da jajibe jajibe masifa zai ce sai ita. Duk ke kika hada wadannan abubuwan wallahi"
"Alhaji kenan, wataran idan kana magana Ina tunanin mantawa kake da bangaren da Kai ne ka gina shi. Ni meye nawa aciki?"
"Ba ke kika jajibo su kika sasu a makarantar Alharamein ba ? Da bataje makarantar ba zasu hadu ne har yaji yana son ta?"
"Alhaji kenan. Yau lefi nane kenan ko? To da baka kashe mata mahaifiya ba zaa kawo haka ne ma?"
"Mu bar maganar nan ma. Aure dai ba za'ai ba ya hadiye zuciya ya mutu, Amma ba za'ai ba"
"Yanzu Kai me kake gani? Meye abun yi?"
"Bansani ba ai. Tunda ba karatu take ba yarinyar ko ta gama?"
"Basu gama ba. Bakuma nasan ace wai sai illata ta shiga ciki. Kawai dai a raba su ta ruwan sanyi"
"Meze hana ta dena zuwa makarantar gaba daya. Su koma can inda suka fito. Ko nawa suke bukata nizan basu. Su bar naduka gaba daya"
Dr bintu tayi shiru tana sauraron sa har ya Kai karshe.
"Kinyi shiru?"
"Eh abubuwan nake aunawa ne. Sai dai ko takan auntyn nan tasu. Tanata Kirana na ma tana turo Sako bana amsata. Ta takura mun wallahi tana da cinkisa"
"Yauwa to sai ki amfani da wannan damar ki hilaceta ta fadi abubuwan da suke so. Su tarkata su bar naduka. Idan ma wani garin sike so daban su koma. "
"Toh zan je wajenta da safe inshaa Allah. Amma kafin sannan ni kuwa ya batun kadarorin Alhaji Abubakhar ya sake yin maganar ko kuwa?"
Alhaji sambaso ya dubeta yana riko hannuwanta cikin nasa yace,
"Ki kwantar da hankalin ki. Wannan zance fa ya rigada ya shude. Dubi tsawon lokacin da aka dauka fa? Baki daya ma ko zancen aka dakko baya cewa komai yace ya hakura . Na yiyyi yadda zan hilato shi ko naji cikinsa naga alamar bashida wani interest akai sam, don haka tuni nama Saka an sauya sunan komai zuwa nawa. Nan da watan jibi takardun zasu zama ready inshaa Allah. Suna fitowa Kuma sai visa zamu danje koda kasashe biyar ne haka zuwa bakwai mu danyi shekaru biyu dai muna touring kafin mu waiwayo gidah ko ya kikache?" Ya karasa fada yana sumbatar bayan hannunta
"Hakan yayi Alhaji.... Allah ya kai mu"
"Aameen Aameen" ya rungumeta a jikin sa tsam yana shafa gadon bayan ta....
_ADVERT👇👇_
_YERWA INCENSE AND MORE_
_(DUNIYAR KAYAYYAKIN KAMSHI MASU MATUKAR DADI DA KAMA JIKI, GIDAH, KAYA DA SAURAN SU)_
_INA MA'ABOTA TURARE? KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE_
_TSAFTA KUMA TANA CIKIN IMANI… TOH KU MAR-MATSO KUSA_
_MUN KUMA ZUWA DA HAJAR KAYAYYAKIN_
_*YERWA INCENSE AND MORE*_
_DOMIN SAMUN ZAFAFAN TURARUKAN WUTA NA GIDA, KAYA, JIKI, TSUGUNNO, GASHI... AKWAI KHUMRAHS MASU DADI YAN BORNU, CHADI, SUDAN DAMA SENEGAL, AKWAI OIL PERFUMES, DA TURARUWAN MOPPING DANA WANKA DANA WANKI DANA GADO DA KUJERU DA BANDAKI DA DRAWER DA MOTOCI.._
_AKWAI MAN GASHI NA FESAWA ME SA KAMSHI DANA KITSO. AKWAI KAYAYYAKIN KAMSHI DANA GYARAN JIKI SOSAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA. •_
_ADIRESHI: KANO.. AMMA SUNA TURA KAYAN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE..._
_INGANCI KYAU RAHUSA DA DADEWA A