Showing 45001 words to 48000 words out of 69829 words
Chapter 16 - KWANKWASON JIMINA BOOK 2 COMPLETE BOOK 2 hausa novel
jikinsa tuni sun masa sanyi.
Bakida daya dukkanin wasu kalamai da zasu fito taa fatar bakinsa tuni ya neme su ya bace. Ya bude bakin ma yayi magana ya kasa.
Anees ya juya ya shige gidah Kai tsaye yai dakinsa ya zauna akan kujera. Baki daya maganganun da Nawraah ta fada ne suka jefeshi acikin yanayin tashin hankalin da yake ciki ba.
Aa yadda nawraahn ke cikin tashin hankali ne. Maganganun da takeyi yadda take maganar jikinta har dawa yakeyi saboda tsananin tashin hankali. Idanuwan ta sun kawo ruwa.
Anees ya samu kansa da dora hannunsa akan habarsa ya tallabe yana fuzrar da iska mai zafi daga bakinsa.
"Yaa Rabb ka kawowa s
Wannan baiwar taka dauki ka kawo nata sauki acikin lamuran ta. Allah ka iya mata. Ka rayasu da tsarewar ka... Nawraah" ya kira ta daga karshe yana sauke numfashi.
Marwaan dake waje abakin mota a tsaye. Sai a sannan ya dan samu hankalinsa ya dawo jikinsa ya dubi daman sa da hagunsa yaga Anees ma ya tafi kenan.
Baki daya jin kansa yake yana mai nauyi. Ga tarin maganganun da tayi sun masa gunguma gunguma acikin ka. Iyayen sa suka kashe mata iyaye da wan su?
"Subhan'Allah..." Ya fada yana buga hannunsa akan sitiyari
Ko da wasa bai taba zato ko tsammani ba. Dan ko faifon bidiyon nan badan yasan shidin ne yayi ba Kuma yana da tabbaci ba to da zai musanya yace baai hakan ba.
Ya rasa Ina zai dosa ma. Ya daga Kai ya dubi fuskar gate din gidan Alhaji Abubakhar dollars. Kunya ma duk ta gama dubibiyeshi na maganganun da Nawraah tayi agaban Anees. Ya tabbatar Anees din shysa ya shige gidah batare da jira sunyi sallama ba. Ina kunya ma ba zata iya bari suyi magana ba.
Jikin sa Sam ba karfi yaja motar tasa ya nufi gidansu kaI tsaye. Ya faka y motar ya shiga cikin gidan da sauri ..
Duk suna a zaune a babban parlorn su. Cike gabansu yake da abinci d abin sha kala kala .
"Meye haka? Wawan inane Kai zaka shigo haka ba sallama" Alhaji sambaso yacee da marwaan daya shiga ciki tsabar tashin hankali nema yasa bai yin ba.
"Afuwan afuwa"
"Na gaban goshin Maa dinsa.. Me zaa zubo maka?"
"Ba abinci nakeso na ci ba, magana nakeso muyu da ku a yau dinnan a yanzun nan dan Allah"
"Kaji aikin rashin hankalin nasa ko? menene yanzu ?"
"Kuyi hakuri ,ku duba lamarin da nake ciki. Meyakwan ku..."
Wayar Alhaju sambaso ce tayi karar shigar Sako. Ya janyota a aljihu yana dubata.
Zare idanuwansa yayi lokaci daya ya mike daga zaunen da yake. Yana duban screen din wayar sosai tamkar zai shiga ciki
"Alhaji menene?"
"Wait.... Ina zuwa" ya fada da sauri yana fucewa waje..
Marwaan yajuwa yana duban sa. Sai Kuma ya sauke kansa ya mayar kan mahaifiyar tasu yace,
"Wai Maa me ake boye mun. Wane irin rayuwa akeyi a cikin gidan nan? Maa ni ne fa babban da agidan nan yakamata ace dukkanin wasu abubuwa ba aboye mum.. Zaa bayyana. "
"Wai menene kaketa wannan babatun marwaan?"
"Ni kawai a auramun Nawraah. Shine kwanciyar hankali na da na ku. "
Dariyar gefen baki tayi tana duban sa shakeke tace
"A aura maka Nawraah?... Harda cewa hakan ne kwanciyar hankalin ka da Kuma na mu. Nace sannu ishasshe.. Ah uban mu ma Kai. Mai fada aji. Yadda ka daama haka zaa sha kam "
Marwaan ya sassauata muryar yana kwantar da Kai yace
'Maa karki manta Anees bama sa'ana bane.. Ga sa'ah na nan yayansa junior. Shine kusan mate dina, shima yayi sure Ma, haifa itama tayi aure kanwar s. "
"dakata da kaketa yakankana maganar sunyi aure aure. Bakasan da zasuyi auren zuriyar Wa suka auro ba? Daga yayan manyan masu kudi saii manyan masu mukamin Mulki. Ko manyan yan kasuwa da ake damawa da su a kasa. Har shine zaka zo kana nuna kenan anyiwa kannen kasa da Kai kenan. To sai ka gaya mun su zuriyar da suke da itaa?
Alhaji sambaso ya dawo ya cigaba da duban wayar hannunsa hankalinsa baki daya kacokam akan wayar
"Kaji Alhaji... Abunda yaron nan yake sake fada ko?"
Alhaji sambaso ya daga mata hannu yana cigaba da wayar da yakeyi,
"An duba babu ko?." Ya fada yana ajiye wayar hannunsa.
"Alhaji menene?" Dr bintu ta tambaye shi
Mikewa yayi a kufule ya daga hannu ya shararawa marwaan mari.marwaan ya rike tafin kuncinsa dayan Alhaji sambaso ya sake daga hannu ya zabga masa mari a dayan gefen..
Dr bintu ta mike da sauri tana rike hannun mijin nata.
"Alhaji menene dan Allah. Ya zaka mare shi? Inde akan yarinyar nan ne ba ze aureta ba shima ya sani shi din me"
"Wace mace? kinsan akan me na mare shi?" Ya tanbayeta a razane yana kokarin kwace hannunta.
"Nasan bazai wuce akan maganar mace ba dai ayi hakuri"
"Kinsan me yayi?faifon bidiyon aka turomun da wata number bidiyon na sanda muna sa insa da mijin matar nan daya fada ta barandaa"
"Bangane ba Alhaji. Bangane ba"
"Ina nufin wai marwan daa na na ciki na. Shine Wanda yayi recording video din da mukayi da shi awaya ranar ta call muna waya ta system. "
"Wallahi gaba daya Kai na ya kulle na kasa ganewa"
"Da Hausa fa nake magana Kuma da manyan baki. Nace maki yaron nan marwaan shine yake mun barazana, Har yana sawa a aikomun da faifon bidiyon wallahi na dauka camera ce duk na dude ashe ba cctv a office dina. Yanzu da ace hakan bata faru ba. Ace baisan yarinyar bama. Kenan yaron man dama ya shirya bayyana haka ko?"
"Innalillahi Wa inna ilaihi rajiun... Marwaan. Marwaan fadi gaskia dai.. hadaku akeso ayi da mahaifin ka ko?"
Marwaan ya goge hawayen da suke zuba daga idanun sa yace,
"Maa... A ajiye batun maganar nan a gefe. Maa meyasa kuka kashe iyayen Nawraah? Babanta, mamanta da Kuma babban wan su saboda Allah Kuma a haka muke ganin Allah zai barmu dukan mu?"
Dr bintu ta juya tana duban Alhaji sambaso. Sai sukayi sakeke lokaci guda dukan su aka kasa samun mai bawa marwaan amsar tambayar da yayi....
_ADVERT👇👇_
_YERWA INCENSE AND MORE_
_(DUNIYAR KAYAYYAKIN KAMSHI MASU MATUKAR DADI DA KAMA JIKI, GIDAH, KAYA DA SAURAN SU)_
_INA MA'ABOTA TURARE? KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE_
_TSAFTA KUMA TANA CIKIN IMANI… TOH KU MAR-MATSO KUSA_
_MUN KUMA ZUWA DA HAJAR KAYAYYAKIN_
_*YERWA INCENSE AND MORE*_
_DOMIN SAMUN ZAFAFAN TURARUKAN WUTA NA GIDA, KAYA, JIKI, TSUGUNNO, GASHI... AKWAI KHUMRAHS MASU DADI YAN BORNU, CHADI, SUDAN DAMA SENEGAL, AKWAI OIL PERFUMES, DA TURARUWAN MOPPING DANA WANKA DANA WANKI DANA GADO DA KUJERU DA BANDAKI DA DRAWER DA MOTOCI.._
_AKWAI MAN GASHI NA FESAWA ME SA KAMSHI DANA KITSO. AKWAI KAYAYYAKIN KAMSHI DANA GYARAN JIKI SOSAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA. •_
_ADIRESHI: KANO.. AMMA SUNA TURA KAYAN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE..._
_INGANCI KYAU RAHUSA DA DADEWA A GIDAH DA KAMSHI SAI KAYAYYAKIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE_
_NAMBAR WAYAR SU: 08095215215, INSTAGRAM/THREADS/TWITTER:yerwaincense_and more_
_YOUR NUMBER ONE STOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS... THEY 'VE GOT YOU AND YOUR HOME COVERED_
_K'K'J_
_(M/W/S)_
_BOOK TWO_
_✍️:MX_
_36_
:::::::::
Tunda ya shiga dakinsa ya wuce bandaki yayi wanka ya yi alwala. Ya sauya kayan sa zuwa na bacci. Kansa nata masa zugi yana radadin ciwo sosai..
Sallolin nafilfili yayi yana kaii kukan sa zuwa ga Allah. Damuwa ce fal a kirjin sa. Ga wani bugu na daban da kirjin nasa yakeyi.
Dama ya jiyo horn din motar mahaifin sa ya fita. Yanata adduar kada Allah yasa dai mahaifin nasu ba sani abun zai sake hadawa ba.
Nawraah da yan uwanta nata kawo masa a zuciya. Hawaye suka shiga zuba daga idanunsa tafasassu masu quna....
Jikinsa dik ba kwari ya koma bakin gadonsa ya zauna yana duban wayar sa dake gefe. So yake ya danna lambar ta ya kirata. Amman idan ya kirata yace me?
Ya ja dogon numfashi ya sauke.. ya kwantar da kansa ajikin pillow. Abubuwa na nata masa yawo akai.
Duka zantukan da suke masa yawo akai kaso cassa'in na Nawraah ne. Kashi biyar na iyayen sa sai Kuma daya kashi biyar din na wajen Anees. So yake ya kira Anees dinma ya kasa. Kunya duk ta dubibiye shi baisan da wani bakin zai Wa Anees din magana ba.
Yanata tunani dai ya kama ya saki dare yaja ainun. Kusan befi awa daya da mintina ba zuwa salatul fajr.
Yajiyo karar horn din motar mahaifin nasu ya dawo. Ya daga Kai ya dubi lokaci cike da mamaki..
Ina baban na su yaje? Bai taba futa ya Kai wannan daren haka a waje ba. Idan ma fita ne Dr bintu mahaifiyar su tafi futa da daddaren ta dawo tsakiyar dare idan aiki ya kicimewa kananun likitoci tana zuwa musanman idan za.ai aikin haihuwa ko zaa curo wani abun aciki na surgery.
Jin motar mahaifin nasa an faka Kuma baa fito ba yasa ya dan daga kansa labulen dakinsa. Dake sashen yana kallon parking lot din gidan
Yana labe ta mudubi yana leko motar mahaifin nasa.. sai da Alhaji sambaso ya jima sosai acikn motar sannan ya futo daga ciki yana rike da wayar sa hannun dama yans magana yana dashare baki kamar gonar auduga.
Kallo daya marwaan yayi masa ya yi sauri ya zare kansa daga ciki labulen daya dage yana duban mahaifin nasu ta cikin window.
Dakin nasa yashiga Kai da kawowa ya tabbatarwa kansa wannan dariyar da baban nasa yake da alama wani babban lamarin ne ya gama nasarar sa.
Wayarsa ya janyo yana dubawa. Ya shiga kan sunan Anees. Ya danna wajen kira yana dafe da kansa...
Anees da alokacin ya na dakinsa a kwance bai bacci ba shima ya kammala sallolin daren sa kenan yana kwance kansa na kallon pop tunani dankare acikin kijrinsa.
Wayarsa ce fara Kara. Ya janyo ahankali yana duban sunan tamkar ba zai dauka ba. Sai Kuma ya dauka ya Saka a kunnen sa .
"Assalamu alaikum"
Marwaan ya fada a nasa bangaren yana sauke numfashi
"Waalykm Salam... Guy" Anees ya amsa shi
"Kana sauraro na?"
"Ina sauraron ka maza"
"Anees ... Bakina ya mun nauyi! Zuciyata ta na tafarfasa... gabban jikina na sassaramun Anees. Ina cikin damuwa"
Anees da shima acikin damuwar yake matuka, yayi kokarin saisaita kansa cikin sanyin murya Mai kwantar da hankalin Wanda yake cikin wani hali yace dashi,
"Kowani tsanani yana tare da sauki aboki na. Meya faru? " Anees ya ce dashi haka don bayasan ya dakko zancen da Nawraah tayi agaban sa..
Marwaan ya sake suake gwauron numfashi, bai ce komai ba..
"Ina sauraton ka marwaan" Anees ya ce da shi cike da damuwa
Marwaan ya dan samu kwarin gwiwar zayyanewa Anees dukkanin abunda ya sani gameda fefen bidiyon nan don shi kadai ne shedar sa a iya abunda ya sani, Yana fada yana Kuka sosai .
Anees ya shiga tausasar sa yana bashi hakuri, shima kukan ya barke da shi suka shiga bawa juna hakuri.
Sai da sukayi mai isar su sannan marwaan ya cigaba da magana ya karkare masa da,
"Anees!! Dan Allah maganar da zan fada yanzu kayi mata duba na tsakani, ka dena cutar kanka dan Allah. Kuma wannan shi kadai ne alfamar da nakeso dan Allah ka mun Anees kaji?"
Anees ya gyara zamanta yana duban screen din wayar tamkar marwaan din yake gani. Gabansa ya shiga dukan uku uku, yanata sako abubuwa kala kala.
"Kana saurarona?"
"Ina sauraron ka marwaan"
Marwaan din ya shiga sanarwa Anees dukkanin abunda yake so ya gayamai. Anees idanuwansa suka furfito waje saboda tsananin mamaki. Yakasa cewa komai. Marwaan din nata Kiran sunansa ta waya Anees ya kasa amsa masa. Marwaan ya katse jin ko network me.?
Bayan ya katse kiran. Ya samu kansa da shiga Whatsapp . Ya danno kan sunan Nawraah ya sauke bahagon numfashi, kafin ya fara mata voice note muryar sa nata rawa, luckily enough Kuma tana online...
_ADVERT👇👇_
_YERWA INCENSE AND MORE_
_(DUNIYAR KAYAYYAKIN KAMSHI MASU MATUKAR DADI DA KAMA JIKI, GIDAH, KAYA DA SAURAN SU)_
_INA MA'ABOTA TURARE? KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE_
_TSAFTA KUMA TANA CIKIN IMANI… TOH KU MAR-MATSO KUSA_
_MUN KUMA ZUWA DA HAJAR KAYAYYAKIN_
_*YERWA INCENSE AND MORE*_
_DOMIN SAMUN ZAFAFAN TURARUKAN WUTA NA GIDA, KAYA, JIKI, TSUGUNNO, GASHI... AKWAI KHUMRAHS MASU DADI YAN BORNU, CHADI, SUDAN DAMA SENEGAL, AKWAI OIL PERFUMES, DA TURARUWAN MOPPING DANA WANKA DANA WANKI DANA GADO DA KUJERU DA BANDAKI DA DRAWER DA MOTOCI.._
_AKWAI MAN GASHI NA FESAWA ME SA KAMSHI DANA KITSO. AKWAI KAYAYYAKIN KAMSHI DANA GYARAN JIKI SOSAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA. •_
_ADIRESHI: KANO.. AMMA SUNA TURA KAYAN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE..._
_INGANCI KYAU RAHUSA DA DADEWA A GIDAH DA KAMSHI SAI KAYAYYAKIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE_
_NAMBAR WAYAR SU: 08095215215, INSTAGRAM/THREADS/TWITTER:yerwaincense_and more_
_YOUR NUMBER ONE STOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS... THEY 'VE GOT YOU AND YOUR HOME COVERED_
_K'K'J_
_(M/W/S)_
_BOOK TWO_
_✍️:MX_
_37_
:::::::::
"Assalamu alaikum.... Nawraah...! Kiyi hakuri dan Allah dan girman Allah kada kice ba zaki saurari wadannan maganganun da zan fada miki ba, Dukkanin abunda zan fada wallahi Nawraah ba wasa ko renin hankali ko hada zance acikin sa. Magana ce ta tsakani da Allah abubuwanda suka faru na baya tun muna school yakamata ace kin sansu tun daa ba sai yanzu ba. Amman dubada yadda yake janye jikinsa kada nasani da kema kada kisan masaniyar komai yasa ban gaya miki ba..da fari bansan abun nasa ya Kai haka ba by Allah..amma with time lokaci na ta tafiya ina nazarce da shi Ina bibiye da abubuwa da yadda zaiyi abu yace ace bashi bane. Dukkanin komai dai yakamata ace kin sani Nawraah. Nokewar batada wata muhinmanci. Dubada hakan na sanya kiyayyar sa a zuciyar ki. Domin shi a nasa wajen wata irin kauna ce da yake miki.... Mai wuyar fassarawa, kauna ce yake miki Wanda hankali sai ya auna sosai zai dauka, kauna ce wadda yake miki min indilllahi daga Allah take Nawraah. Ina fatan dan Allah dan Allah ba iska nakewa voice notes ba kina saurara ? Saboda zan karasa miki komai... Nan gaba ma nasan abubuwa zasu bayyana kansu. Dubada cikin hadarin da nake ciki Nawraah... Shysa nake fitowa a mutum nake sanar dake wadannan abubuwan..."
Ya karasa tura mata voice note din yana jiran amsarta da amincewarta don cigaba daga inda ya tsaya.
Nawraah ta sakala earpiece tanata sauraron muryar marwaan tiryan tiryan har ya Kai karshe ta masa reply da ,
"Bangane kan maganganun nan da kake ba. Wanene shi? Meye alakata da shi? Dan Allah idan har ba wani abu bane daya danganceni wanda yakeda dole sai na sani kada ka sake turomin sako" ta tura masa reply
Marwaan ya dauka da sauri ya duba. Ya dan saki tattausan murmushin yake yana girgiza Kai. Ya samu kansa da jingina jikinsa a bango ya cigaba da ce mata,
"Shi ya fara ganin ki alokacin da kika shigo jami'ar mu ta Alharamein. Kallon da ya yi miki bai taba yiwa wata ya mace shi ba ni sheda ni Nawraah, abunda yasa nakeson sanar dake wadannan abubuwan saboda halin rayuwa Nawraah. Dubi matsatsin da muka samu kanmu aciki. Kuma na zama kamar third party a tsakanin ku da shi... Dan Allah ki cigaba da hakuri ki saurara..."
"Wai waye shi meye darangami na da shi? Dan Allah dan Allah ka goge number ta daga wayarka. Dan wallahi duk wani abu daya danganceka banda shi. Ka sani har abadah inshaa Allah kaddara ma ba zata sake hadamu hanya da Kai ba."
"Nawraah calm down please.... Please...nasani Allah yabaki hakuri, sanin hakan shysa nakeso na warware komai duk da shima na nasan irin dakon son da yake miki na..abunda zan cigaba da ce miki shine by Allah Nawraah cuz Anees bama shi da masaniyar zyna gaya miki wadannan abubuwan sannan bashida masaniyar nasan abunda yaketa kunbiya kunbiya dashi acikin zuciyarsa game da ke. nasan zakiga kaman duk duniya a school dinnan ke yafu tsana idnya kinzo waje ya tashi. Idan muna tare dake yazo yaganki sai ya fasa zuwa. Idan kin Mai magana na gaisuwa yaki amsawa da sauran su. Nawraah... Wallahi zan iya rantse maki da Allah Anees yafi ni kaunar ki, ba wai Ina fada bane don kawo wata manufa ta daban..Anees aboki na ne. Kani na ne Kuma babban amini na. Dik duniuya idan kika cire soyayyar annabi bayan shi, da iyayena ba sanda mukai shauwa sosai nake jinsa kaman jini na irin Anees. Na san shi ya sanni. Yasan abunda zanyi da Wanda ba zan yi ba. Haka zalika Nima nasan komai amsa...."
Nawraah na kwance sai ta zauna kunnenta dauke da earpiece din ta tana cigaba da sauraron maganganun marwaan datakeji tamkar ta zuba masa mari ta wayar.
Takaici duk yabu ya isheta na maganganun da yaketa zuba kamar rediyo. Sai karshen zancen sa dataji yace,
"Amma bakomai, komJ zai bayyana kansa. Kawai dama inason na cire yar tsamamr dake tsakanin kune. Wanda kike ganin kaman kiyayya ce yake miki....bari na gaya miki abubuwanda ya yiyyi yace kar na gaya miki ma kar na nuna shi yayi..saboda bayason yayi aikin alkhairi ya fada haka halinsa yake... Kuma na tabbatar idan an sanar miki hakan zai rage miki wani kaso na daga cikin tsanar da kika sanya shi a zuciyar ki...
Nawraah ta zare earpiece din daga kunnenta tana sauke numfashi,
Pause ta sanya a voice note daya turo. Ta runtse idanunta ta matse su... Sannan ta koma tajingina da pillow tana rage volume din earpiece dinma ganin yan dakin nasu duk sunyi bacci karta tashe su...
"Anees shine Wanda ya fara ganin ki Kuma ya kamu da son ki. Nalura da yanayin daya kalleki tun ranar. Bai taba yiwa wata ya mace haka ba..infact ki tanbaya baya kula mata ,baya bin takan mata. Karatu kawai yake abunsa ba ruwanda da kowa, look ko cikin maza course mates Anees bayada wannan huldar kule kule. Sai bada hannu su gaysa ya koma wajensa ya zauna...kullum zaki ganshi da airpods yana sauraron karatu ne ba ruwan sa da harkar abubuwa da yawa na matasa. Ba karya ba. Sister na da muke uwa daya uba daya lily taso Anees amman bai bata fuska ba, yace baya sonta a budrwa yana mata kallon baby sis din sa itama...karamin yaro ne me hankalin manya sosai...."
"Kaga... Dan Allah idan ba akan maganar data shafeni kakeson na sani, ba wannan maganganun nake bukata ba. Yauwa nagode" Nawraah ta rubutawa marwwaan ganin yanata bayani kanta ma baya dauka.
Sai a sannan ya samu kansan da yin murmushi ganin reply din da yayi gaba dayan ranar.
Ya