Showing 105001 words to 108000 words out of 120733 words
su kaisu chan main house din su Mama akwai abinda zai yi kafin su wuce masaukin su, sabon gidan da sukayi anan nasarawa gra. Zasu shiga motar kenan taji an kira sunan ta, tsayawa tayi chak muryar sa na dawo mata tar akanta. Ya Isma'il ne,
"Jiddah." Safeera ta kirata ta juyo da sauri idon ta ya sauka akan sa, yana cikin ashe colour din suit idon sa sanye da siririn medicated glasses fuskar sa dauke da murmushi
"Safeerah,Ya Isma'il!"
Ta fada a lokaci d'aya cikin jimla daya. Tsayawa Tariq yayi rik'e da murfin motar idon sa akan wanda aka kira da Ismail din da yadda yake kallar masa Jiddan sa. Hugging din Safeeran tayi sannan ta gaida Ya Isma'il din ya amsa yana matsawa ya mikawa Tariq hannu
"Oga barka da rana."
Kamar ba zai mika masa hannun ba dan sai da yayi dan jim kafin ya mika suka gaisa.
"Safeera ce da brother din ta." Tace tana murmushi
"I see!"
Yace a d'age yana sake kallon Isma'il din wanda yake ganin kamar tunda yazo wajen Jidda kawai yake kallo.
"Muje ko?" Yace
"Ok zan shigo na gaida Mom in sha Allah."
"Ya dai kamata wallahi, Ya Tariq sai anjima."
"Sai anjima." Ya maida mata
"Ok sir, ku gaida gida, Jidda bye." Ya ware yan yatsun sa guda biyu ya dagawa Jiddan su
"Ok 👌."
Motar ta shiga sannan shima ya shiga ransa na baci sosai, haka kawai yaji baya son Isma'il din.
"She's my best friend."
Tace tana kallon sa da murmushi a fuskar ta. Nodding kansa yayi be ce komai ba,shiru tayi ganin kamar mood dinsa ne ya chanja. Tunanin yadda zasu kwashe da a gidan su Maman ta shiga yi. Bata san wacce irin tarba zata samu ba, shiyasa duk jikin ta yayi sanyi ga Tariq din ya gimtse fuska yaki yarda ma ya kalli side din da take.
Wayar sa ya zaro zai kira Ishaq yaga missed calls din Yasmin kusan kullum sai ta kirashi ko tayi masa message a WhatsApp, da gaske take ba zata barshi ba kila sai ta ganshi tare da Jidda sannan zata kyale shi. Fasa Kiran Ishaq din yai ganin an zo gate din gidan su maman.
Idon ta akan gate din ganin irin girman gidan bata taba kawo Maman daga irin wannan gidan ta fito ba duk kuwa da dama kana ganin ta kasan masu kudi ne amma bata kawo har haka ba, shiyasa Maman tayi mugun raina Anty dan ko kusa ba tsarar ta bace idan banda kaddarar aure babu yadda za'a yi su hadu inuwa daya.
Harabar gidan zata ci motoci kusan sha biyu saboda girman sa, ga motocin nan a faffake wasu lullube wasu kuma daga gani ba'a dade da hawan su ba. Fita yayi be ce ta fito ba sai tayi zaune tana tunanin ko ba fitowa zatayi ba, har yayi gaba sai ya juyo ya ganta a zaune duk da an bud'e mata kofar bangaren ta. Dawowa yayi da baya yace ta fito, ta fito tana satar kallon fuskar sa. Hanya ya nuna mata yace tayi gaba ya take mata har suka main entrance din. Door bell ya danna jim kad'an aka zo aka bud'e. Da sallama suka shiga dukkan su cikin falon da yake dauke da kujeru set uku saboda tsabar girman shi. Hajiya Babba na zaune a falon ta dago idon ta sanda taji sallamar kamar ta Tariq, shi din ne kuwa sai taga ya kara girma sosai. Al'amin ne yayi karaf din cewa
"Wa nake gani kamar Captain?"
Murmushi yayi wanda ya tsaya iya saman labbansa yace
"Ni ne."
"Ah lallai yau nazo a sa'a, Hajiya Babba kinyi babban bako mutanen turai da basa ziyartar yan uwa."
"U r not serious!"
Yace suna karasowa tsakiyar falon in da second set din kujerun suke kuma in da Hajiya Babban take tana karatun Qurani akan dan katakon ta.
"Sannun ku da zuwa." Tace tana rufe karatun ta yunkura da dan k'yar ta mike daga k'asa idon ta akan Jidda dake ta sunne kai cikin taraddadin abinda zata tarar
"Bismillah, zauna mana Hauwa'u."
Ta kira ainahin sunan nata da Baba ne kawai yake fada mata a yanzu sai ko course mates dinta, nutsuwa taji kad'an ganin a kalla tasan wacece ita har ta kama sunan ta haka radau. Zama tayi a k'asa Tariq kuma ya haye kujerar sai ya dan zamo kadan yace
"Hajiya barka da gida."
"Ba zan amsa ba." Tace tana kauda kanta, ta dawo kan Jidda tana share shi
"Dalilin ki Tariq yazo gidan nan,dan rashin kirki."
Sunkuyar da kai Jidda tayi ta danyi dariya kad'an
"Ba zaki kulani ba granny?"
"Ba dan ni kazo ba, yanzu ace Tariq gidan nan kamar baka san hanya ba,yaushe rabon ka da kazo? Itama uwar taka da laifin ta wallahi."
"Ayi hakuri Hajiya kinsan turawa basa san mutane sosai."
"Kana da matsala."
Yace yana kallon al'amin din
"Sai su ci kansu ai." Tace tana daga wayar dake gefe da take communicating da duk ma'aikatan gidan
"Nayi Baki." Tace ta katse
"Malam ya gida ya aiki? Ya kwana da yawa?"
"Alhamdulillah wallahi, aiki ana lallabawa gashi nan ba dadi, kai fa?"
"Toh gashi nan dai, zan koma ne ma cikin next week in sha Allah."
"Kace zaka sake guduwa sai an kuma ganka kenan."
"A ah fa."
"Ai naji aikin naku ne kullum kuna tafe shiyasa, ina wani time na irin wannan ziyarar."
"In sha Allah ma.zanzo, zan shigo gidanka ma kafin mu bar kano muzo mu gaida madam."
"Da ka kyauta kuwa."
"In dai Tariq ne ba zuwa zai ba fa, shi in dai harkar mutane ne toh babu shi a ciki sam."
"Haba Hajiya ba haka bane ba."
"Fadawa wanda be sanka ba."
"Hauwa'u, tashi ki zauna sosai kinji?"
"Nan ma yayi Hajiya "
"Toh bari na shiga ciki na turo miki Nu'ayma, idan kuma zaki shigo cikin ne toh."
"Nu'ayman tazo Hajiya."
Yayi charaf ya amsa kamar dashi ake.
"Ok toh, ka biyo ni inason ganin ka."
"Dollars zaki bani ko pound sterling?"
"Duk wanda kake so."
Dariya sukayi shi da al'amin ta shige ciki, maimakon ya tashi ya bi bayanta sai ya kasa dan ba zai iya barin ta daga ita sai al'amin din me shegen surutun tsiya ba, jira yayi sai ga Nu'ayma ta fito da fara'arta, ta gaishe su sannan yace ta kai Jiddan dakin su. Tashi Jiddan tayi ita kuma ta daukar mata snacks da juice din da aka kawo mata suka shiga ciki, sai sannan ya tashi yabi bayan Hajiya Babba ya bar al'amin din shi kadai!
[11/25, 3:54 PM] Rano2: _SL__**
©️®️*_*_Hafsat Rano_*_*
Page (54)
***Sun jima a gidan Hajiya babba fiye da yadda tayi zato ko tsammani, suna daki sai ga aunty Mimi ya shigo cike da murnar ganin Jiddan wadda ita tayi duk kokarin ta wajn wayarwa da Hajiya Babba kai akan Jiddan da yanayin halin kirkin ta, a dah su Nafi sun fanfa ta amma da Anty Mimin ta yi mata bayani sai taji ta sauka sosai, har ma tana son Jiddan shiyasa da tazo tayi mata tarbar da Jiddan batayi tunani ba.
Sun fito zasu tafi bayan an saka mata kyautar Hajiya Babba a booth suna sake yin sallama sai ga Anty Nafi da Salma sun shigo a motar Anty Nafin driver ya kawo su, kallo daya Tariq yayi musu suna shigowa ya dauke kansa ya shiga motar sannan ya zuro kafafuwan sa waje yana zaro wayar sa, maganar da Hajiya babba tayi masa kenan a ciki akan maganar Anty Nafin da abinda ya faru yayi mata bayanin komai shine ta kira tace su zo ita da Salma sai gasu sun iso dan dawowar su kenan ma daga Abujan ko kaya basu chanja ba suka fito dan dama ko hajiyar bata kirata ba tayi niyyar zartowa tazo ta fada mata irin wulakancin da Mama tayi mata akan Tariq. Mamakin ganin Tariq din da Jidda a gidan yasa ta fitowa da dan sauri bayan ko gama parking daidai driver be ba.
"Tariq dai kaki barin Jidda da tayi zaman ta anan ai, Hajiya ma zata ji dadi."
"Anty zamu dawo, yanz akwai in da zamuje daga nan ne."
"Toh shikenan, sai kun dawo din."
"Sai anjima Anty Mimi."
"Sai anjima Jidda, bye."
Baya ta shiga shi kuma dama yana gaba tare da driver sai dayar motar da take bin su, suka fita daga gidan yana kallon mirror din gaba yaga sanda Anty Nafin ta karaso tana kallon motar tasu ita ma yar iskar yarinyar idon ta akan motar. Shafa kansa yayi yana jin wani dum kamar wanda yayi wani babban aiki. Direct gida aka wuce dasu daga nan. Gidan da ma'aikata masu kula da gidan dan yanzu yawanci Baba anan yake weekends kuma mafi yawancin lokuta tare suka zuwa da Mama dan itace me sabgar yi ga shagunan ta dan ma fauwaz shine karfin kula da duk wasu business dinta shiyasa ko yaushe yana tsakanin Kano din da Abuja yana duba yadda abubuwan suke tafiya.
Daga bq ta fito ta bawa Jidda key din part din nasu da aka sake gyara shi dazu, mika masa tayi ya karba yana amsa waya ya bude sannn ya matsa mata ta shiga sannan shima ya shiga yana jan suitcase din su zuwa ciki yana cigaba da wayar sa. Ta rasa gane dalilin sauyawar sa lokaci d'aya, duk da haka suna yawan had'a ido amma sai ya fuske yana cigaba da wayar da take tunanin kamar da gayya yake jan hirar. Kayan nasu ta dauka tayi ciki tana kallon sanda ya bita da kallo. A gefe ta ajiye kayan tana karewa bedroom din kallo me dauke da hadadden royal bed din da aka sakawa red bedsheet me zanen heart. A gefe ta zauna ta fito da charger ta, ta jona wayar ta sannan ta nufi toilet din dake manne a falon. Wanka ta fara yi sannan ta dauro alwala ta fito daure da towel Babba. A wajen kayan su ta ganshi yana duba abu, tayi kamar bata ganshi ba saboda rashin kayan dake jikin ta, kad'an ya kalle ta sai tayi tunanin zai mata magana amma kuma sai ya cigaba da abinda yake kamar shima be ganta ba. Juyawa yayi ya fita, jiki a sanyaye ta shirya ta yi sallah sannan tazo ta dauki wayar ta,ta kira Safeera dan taga kiran ta sanda suna gidan Hajiya Babba .
Suna cikin wayar ya shigo sanye da dogon wando fari da t-shirt kamshin turaren sa ya cika dakin daga gani wanka yayi babu ko tantama. A gefen ta ya zauna ya saka hannu ya zare mata wayar daga kunne sannan ya katse kiran yana kallon ta
"Haka ake lallaba miji?"
Ya kalle ta rike da wayar bayan yaga da wadda suke yin wayar.
"Na'am?" Tace a dan kaikaice tana kokarin hana idanun sa tasiri akanta
"Eh, haka akeyi? Baki san fushi nayi ba?"
"Fushi? Me yasa?"
"I'm jealous, kishi nake and you just pretend as if baki gani ba ma."
"Kayi hakuri."
"Ai kinji... A dake ka a hana ka kuka, ayi maka laifi a yi saurin baka hakuri da kazo zakayi yar mitar ka."
"I'm so sorry ba zan kara ba.”
“Ni ba zan hakura ba!”
“Please…”
“Sai da sharadi idan kinaso na hakura.”
Kallon shi tayi ya kashe mata ido
“Sai kin saka min rigar nan kin yi fashion parade sannan zan hakura.”
“Innalillah!”
“Yea! Idan ba haka ba nayi ta fushi na daina kulaki!”
Ya juyar da kansa gefe daya yana turo baki kamar karamin yaro.
“Shikenan zanyi, amma sai dai anjima!”
Juyowa yayi yana murmushi
“Why not now? Me yasa sai anjima?”
“Ni dai kawai.”
“Shikenan I will wait! Amma karma kizo min da wani excuse wallahi. Inaso naga matata ehe.”
“Tell me, waye wannan ismail din? How much did he know about you?”
“Ba zamu kyale maganar ba?”
“No it’s better ayi ta kawai Jiddaaaa.”
“Ok, yayan Safeera ne, both of them helped me alot a rayuwa ta, sun so ni a yar kauye ta da rama ta, basu taba kushe ni ba ko aibata ni.”
“OMG!” Yace yana kokarin rike ta, ta dan matsa kadan tana kin kallon sa
“He nuna interest akaina and I said no, be takura min ba, he left daga nan aka daura min aure, and I waited for good 1year, since then ban sake ganin sa ba coz dama a time din ya tafi karatu, this is the first time bayan long time da na ganshi, and yasan nayi aure, kuma nasan babu wani abu a ransa.”
“Jiddah!”
Ya kira ta ganin yadda mood dinta ya sauya. He misunderstood everything yazo yana ta fushi akan iska. Kin kallon sa tayi saboda yadda idanun ta suka cicciko zatayi kuka. Juyowa da ita yayi suna kallon juna, tayi saurin sauke kanta kasa ya sa hannu ya tallafo fuskar ta.
“I’m so sorry kinji? Dan Allah Kiyi hakuri ki daina tuna abinda ya wuce, nayi kuskuren fadan abubuwan chan Amma wallahi wallahi ba har zuciya ta ba, I was just looking for an excuse to hold on to, ba nayi ne don cin fuska ba, dan Allah forgive me! Wallhi nayi regretting, I regret everything har rashin dawowa ta,forgive me dan Allah!”
Kuka tasa masa ya jawota jikinsa ya rungume zuciyar sa na wani irin zafi, yasan zata dade bata manta ba, bayan ka zauna zaman jiran mutum ba shekara daya amma ya dawo yace baya son ka, dole da ciwo ontop of that kuma ma ya hada da kushe ka, dama zai iya dawo da lokacin baya ya goge duk abinda yace din, Amma Yanzu kam it’s too late. Ta dan dade tana kukan kafin tayi shiru sai ajiyar zuciya da take a hankali, tana da saurin kuka karamin abu yanzun nan zai sakata kuka sosai, bayan ta yake tapping a hankali ya kasa ce mata komai har tayi shiru din. D’ago ta yayi yana kallon yar fuskar tata, hannun sa yasa ya goge mata ragowar hawayen da take ya shafi saman lips dinta da yake ganin shine kawai last option dinsa da zai yi amfani wajen sake bata hakuri.
“I’m sorry.”
Yace muryar sa ta shige ciki sosai. Sai ya matso da fuskar sa daf da tata, ya dora hanci sa a saman nata yana gogawa kadan kadan yana kokarin saka mata idonsa a cikin nata saboda taga how sorry he is, a hankali ya kai bakin sa saman nata ya hade su waje daya, sannan ya sa hannun sa ya zagaye ta cikin ta ya matso da ita so so close.
Kusan minti biyu ya dauka yana kissing dinta a hankali, kafin ya cikata yana maida kansa ya hade goshin su waje daya, idon ta a rufe yake jikinta yayi wani irin sanyi, ya riga ya gano lagon ta. Kissing aaman
“Please Kiyi hakuri, ki daina tunawa kinji? Ya wuce ba zan sake ba. I love you so very much, bansan irin son da nake miki ba wallahi! Kukan ki is one of my weaknesses dan Allah ki daina kinji?”
G’id’a mishi kai tayi, ya rike hannun ta yana mata murmushi
“Did you love me?”
Ya tambaye ta for the first time cike da tsoron kar tace masa a ah.
“Umm? Kina son Ya Tariq dinki?”
“Eh…” ta daga kanta kunya na cikata
“Yes! Say it naji, pleaseee.”
Kasawa tayi, ta boye kanta a kirjin sa tana dariya kadan kadan
“Kunya kike ji?”
“Umm…”
“Ni dai sai kin fada min naji.”
“Ba zan iya ba.”
“Zaki iya, pleaseeee!”
Yawun bakinta ta tattaro fuskar ta har lokacin na cikin kirjin sa,
“Na rufe ido na, inajinki fada mjn, tell me you love me.”
Dagawa tayi kadan taga ya kulle idon sa, kallon fuskar ta dinga yi tana admiring din ta, ta dan kai hannu kadan ta taba gefen sajen sa, ya rike hannun yayi kissing dinsu still idon sa na a rufe
“I’m waiting…”
“I love you so much.” Tace da sauri kamar wadda aka tunkuda. Dariya ta bashi amma sai ya kanne ya bude idon sa
“Wow! I love you more baby.” Yace yana mata murmushi
[11/25, 3:54 PM] Rano2: _SL__**
©️®️*_*_Hafsat Rano_*_*
Page (55)
***Kallon hanya take cike da murna da farin cikin zata ga Baffan ta, yana lura da yadda ta cika da doki yayi murmushi yana murza hannun ta kad'an da yake cikin nashi tun sanda suka soma tafiya. Suna baya a zaune sai driver a gaba da mutum daya.
"Bafa kwana zakiyi ba." Yace ta juyo da sauri tana kallon sa
"Yes!" Ya dage mata gira
"Na dade ban zo ba fa."
"Zaki dawo ne, banda yanzu amma."
"Dan Allah."
"Nah!"
"Dan Allah Dan Allah!"
"Um um naki, tare zamu koma. Nayi missing dinki."
"Missing?"
"Ehen, ba zan iya hakuri ba jiya dai kin yi min wayo amma banda yau."
"Please dan Allahhhhh." Taja muryar ta cike da shagwaba
"La la la la,na murza gashin baki."
"Pl...." Hannu ya dora mata akan lips din nata yana girgiza mata kai
"Don't beg me pls, or i will kiss you."
Hadiye maganar tayi tana yin raurau da ido, yayi kamar be gani ba ya juyar da kansa yana murmushi. Bata sake magana ba har suka isa cikin garin ta soma ganin mutane kad'an kad'an har suka karasa kofar gidan nasu da ya samu sauyi sosai fiye da yadda tazo ta ganshi a baya. Baffan ta, ta hango yana tahowa daga hanyar kasuwa sanye da shadda fara tas daga gani sabuwa ce hannun sa rike da leda baka fuskar sa dauke da murmushi wanda ya kasance sunna.
"Baffa." Ta motsa bakin ta a hankali tana murmushi, kallon wajen yayi ya kurawa baffan ido, kasancewar ya jima be ganshi ba tun wani zuwa wajen Baba da ya taba yi sai yaga ya sauya masa sosai, kamannin sa da nutsuwar sa sak na Jiddan sa,hatta da tafiyar ta irin tasa ce. Bud'e motar yayi da dan sauri ya fito ya nufi wajen baffan tun kafin ya kai ga karasowa ya durkusa har k'asa, sai a lokacin baffan ya lura da su dukka ma, ya fadada fara'ar fuskar sa zuwa ta musamman
"Baffa barka da warhaka."
"Barka dai d'ana, zuwan kenan? Sannun ku da zuwa."
"Zuwan kenan," ya mika hannun sa ya karbi ledar hannun Baffan, ya sakar masa yana jin dadi idon sa akan Jidda dake tsaye tana murmushi.
"Muje ciki kaji, sannun ku da zuwa maraba."
Mikewa yayi yabi bayan Baffan yana kallon idanun Jiddan da suka kawo ruwa kamar zatayi kuka, yadda yayi wa baffan yafi komai yi mata dadi, a kalla ya girmama mahaifin ta girmama mafi girman gaske.
"Baffa." Tace tana matsawa kusa dashi ya yi yar dariya yana cewa
"Kin ganki ko?