Showing 108001 words to 111000 words out of 120733 words

Chapter 37 - SANADIN-LABARINA BY HAFSAT RANO

04 Jul 2024

45435

Ba dai kuka zaki mana ba."

"Ka ganta nan bata girma Sam, duk sanda tazo sai tayi kuka saboda shirme."

"Murnar ganin ku ce Baffa."

"Kai dai kare ta kake."

Yace sanda suka shiga zauren gidan, kallon ta yayi ya girgiza mata kai a hankali k'asa kasa yace

"Don't waste my tears please."

Ta jishi sai kawai ta shige ciki da sauri ta bar su suna kokarin shigowa tunda Baffan a hankali yake tafiya ssosai duk da kafar sa ta samu sauki amma kuma yana dan lallabawa.
Iya Lami na zaune a kofar dakin ta da yasha fenti da duk dakunan da suke cikin tsakar gidan nasu in da taga sabon gini daga gefen dakin baffan, kafin ta gama tunanin yaushe akayi hakan sai ga wata mata farar dattijuwa ta fito tana duba abu a kofar dakin kafin dukka su lura da Jiddan da take kallon gidan nasu.

"Jidda!"

Iya Lami tace tana mikewa rike da gefen zanin ta ta hau gyara shi tana washe baki.

"Jiddan Bingel? Ah maraba lale da mutanen birnin taraiya "

Matar tace tana sakin murfin kofin da ta dauka a hannun ta tayo wajen Jiddan tana wuce Iya Lami da ta saki baki ta dakata da karasowa. Murmushi me kama da yake Jidda tayi ta gaida matar wadda ta cika da murnar ganin ta tamkar ta santa ko ta taba ganin ta.

"Sannu da hanya Hauwa'u, sannu da zuwa wuce muje ciki."

"Malama ki kyale yarinya da gidan ubanta ai tasan gidan ba sai kin nuna iyayi da kinibibi ba, uwar munafukan duniya."

"Shigo nan Jidda."

Tayi banza da maganganu Iya Lami din ta kama hannun Jiddah zuwa dakin da tafito, tayi saurin shinfid'a mata tabarma sannan ta debo ruwa me sanyi a randar ta dake gefen dakin ta, ta kawo wa Jiddan hade da mahuci saboda yanayin zafin da ake a garin da ya dan busa wanda ake kira da daure cikin dawa. Zama tayi a kubin Jiddan ta dauki muhucin ta hau mata firgita sai ga Baffa ya shigo Tariq na biye dashi har cikin dakin da Jiddan take ba tare da ya kalli ko da bangaren da Iya Lamin ke tsaye ba. Wata tabarmar ta mike ta sake shinfidawa kafin taja mayafi ta rufe kanta ruf sannan ta zauna tana amsa gaisuwar Tariq din.

"Yau dai ga yarki nan na tazo tare da Maigidan ta, shikenan sai murna."

Yace yana dariya

"Aikuwa yau ina cike da farin ciki mara misaltuwa, buri na kuwa ya gama cika."

"Baffa na ina wuni?" Jidda tace tana shagwabe fuska ganin kamar yafi damuwa da ganin Tariq din a kanta

"Lafiya Lou, alhamdulillah sannun ku da hanya."

"Baffa! Bakayi murna da gani na ba?"

"Nayi murna mana Jiddan Anty." Yace cikin sigar zolaya,

"Sai dai nafi murnar ganin dana Tariq."

Murmushi Tariq din yayi suka hada ido da Jidda ya kashe mata ido daya ta turo baki gaba tana kin sake kallon sa. Dago labulen akayi Iya Lami ta shigo ta samu gefen kofar dakin ta zauna

"Maraba sannun ku da zuwa."

"Yawwa." Tariq ya amsa jidda kuma ta amsa a ciki tana kin bata wani attention dan ba zata taba mantawa da Iya Lami a rayuwar ta ba, ta kuma kasa manta memory din wahalar da tasha a wajen matar. Shiru ne ya biyo baya dan shi kansa Baffa ba wata doguwar magana ce take hada Shi da ita ba shiyasa ma daga karshe yayi auren sa ya auri kawar Maman Jiddan da Mijinta ya mutu sai dai bata taba haihuwa ba, tun daga lokacin rayuwar Baffa ta chanja ya murmure ya dawo cikin nutsuwar sa ya bar Iya Lami da bakin halin ta wanda ko a yanzu tayi nadama dan dai kawai baya son ya sakata a cikin irin masifar da ta sakashi shida Jidda amma da sakin ta ma kawai zai yi ya huta, amma ko  a hakan ma ya barta ya isheta dan shi kam idan ka cire hakkin aure da yake kanshi babu wani kuma da zata nema a wajen sa.

Fita waje tariq sukayi shi da Baffa suka barsu a ciki,Inna suwaiba da ta riga ta gano matar Baffan ce ta shiga nan nan da ita tana tarairayar ta kamar kwai, nan da nan ta hau girki bayan ta tambayi Jiddan abinda take so tace mata dambu. Nan da nan ta tashi aikin sa ita kuma Jiddan ta fada gidan su Saude ta samu Innar su tana wanki aikuwa tayi murnar ganin Jiddan ta tsame hannu ta zo suka zauna hirar yaushe gamo tana yi tana zuzuta Jiddan da yadda ta zama tamkar balarabiya saboda yadda ta sake fari da wani irin kyau na ban mamaki. Ta dade a gidan har sai da Inna suwaiba ta aiko tazo taci abinci sannan ta dawo tana shigowa bata dade ba Innar su Saude ta aiko mata da danwake. Taci dukka sosai ta ajiye ragowar na anjima haka aka kaiwa su ma wanda suka zo tare waj da ruwa da Baffa ya samo musu na pure water sannan ya samo fura me kyau aka damawa Tariq din da fresh madara me dumi. Sosai ya saki jikin sa musamman da yaga baffan na ta kokarin sai ya sake dashi dan hatta abincin tare suka ci sukayi sallah ya kuma rakashi daya daga cikin shagon sa na kasuwa ya gani sannan ya nunawa jama'ar sa shi a matsayin Mijin Hauwa'u.
  La'asar likis yayi mata text yace tafito su tafi, kwalla ta ciko mata tayi masa reply da dan Allah ya barta, ko sakan batayi da reply din ba sai gashi sun shigo ciki shi da Baffa, kallon ta yayi ta marairace masa ya kauda kansa yana amsa maganar Baffa da yake masa

"Tashi maza ki shirya kar dare yayi muku, ashe wai sallamar abokan tafiyar taku kayi sai da muka dawo naga basa nan."

"Eh wallahi, naga kaamar zasu gaji ne kuma dai dama ni ba wani so nake ba Baffa "

"Toh sai ku hanzarta ku tafi Allah ya tsare, Allah ya kiyaye ya bada sa'ar tafiyar da za'a yi ya kuma bada abinda za'a je nema."

"Amin Baffa."

Yace yana dan dukawa. Tashi tayi ta shiga ciki ta dauko handbag dinta da mayafi tana share kwallar da take kokarin zubo mata saboda yadda taso kwana tayi hira da Baffan ta gashi ba nan kusa zata dawo ba, ya kasa fuskantar yanayin ta, kansa kawai ya sani sai taji kamar be kyauta mata ba. Fitowa tayi tana kin kallon shashen sa, ta russuna tayi wa Baffa gaisuwa muryar ta na rawa sannan tayi wa Inna suwaiba da Iya Lami da ta zama yar kallo. Tausayin ta ne ya kama Baffa amma ya basar yana sake cewa suyi maza su tafi kar su yi dare, amma ya lura da yanayin Jiddan shima kuma zai so ace ta kwanan tunda kasar zasu bari gabaki daya amma ya zai yi? Tunda ya lura Tariq din be amince ba.

Yana gaba tana bin shi a baya har wajen motar da ke cike da yara sunzo kallo, da kansa ya bud'e mata yana saka idon sa a nata amma taki yarda ta kalle shi, sai da ya rufe mata kofar bayan ya gyara mata veil dinta da ya fito sannan ya sake sallama da Baffa dake tsaye Inna Suwaiba na daga bayan sa ta cikin zauren sannan ya shiga motar ya tada suna daga musu hannu ganin an fara tafiya kawai sai ta fashe masa da kuka sosai.


*_ZAFAFA BIYAR COMPLETE DOCUMENTS_*


*ZAFAFA BIYAR BACTH A*


1.. _WUTSIYAR RAƘUMI_ 350
*(Bilyn Abdul)*


2.. _KAI MIN HALACCI_ 350
*(Miss xoxo)*


3.. _BURI DAYA_ 350
*(Mamu gee)*

4... _DAURIN BOYE_ 350
*(Huguma)*

5... _SAUYIN KADDARA_ 350
*(Hafsat Rano)*

_Duka biyar 1500_

*___________________________*


*_ZAFAFA BIYAR BATCH B_*


1... _DAURIN GORO_ 350
*(Hafsat Rano)*

2... _ALKAWARIN ALLAH_ 350
*(Huguma)*

3... _QAUNAR MU_ 350
*(Mamu gee)*

4... _IGIYAR ZATO_ 350
*(Miss xoxo)*

5... _GUDU DA WAIWAYE_ 350
*(Bilyn Abdull)*


_Duk biyar 1500_

*_____________________________*

*_ZAFAFA BIYAR BATCH C_*

1... _MIN QALB_ 350
*(Mamu gee)*

2... _SARAN ƁOYE_ 350
*(Bilyn Abdull)*

3... _KIBIYAR AJALI_. 350
*(Miss xoxo)*

4... _ABINDA KE CIKIN ZUCIYA_ 350
*(Hafsat Rano)*

5... _SIRADIN RAYUWAR BILKISU_ 350
*(Huguma)*

_Duk biyar 1500_

*____________________________*


*_ZAFAFA BIYAR BACTH D_*

1... _ALKIBLA_ 350
*(Huguma)*

2... _DALAAL_ 350
*(Miss xoxo)*

3... _UBAYD MALEEK_ 350
*(Mamu gee)*

4... _MABUDIN ZUCIYA_ 350
*(Hafsat Rano)*

5... _MAKAUNIYAR KADDARA_ 350
*(Bilyn Abdull)*


_Duk biyar 1500_

*____________________________*

*_ZAFAFA BIYAR BATCH E_*

1... _SO DA ZUCIYA_ 350
*(Mss xoxo)*

2... _TAKUN SAAKA_ 350
*(Bilyn Abdull)*

3... _HALIN GIRMA_ 350
*(Hafsat Rano)*

4... _DAB'IZAR ZUCIYA_ 350
*(Huguma)*

5... _DEEN MARSHALL_ 350
*(Mamu gee)*


_Duk biyar 1500_

*______________________________*


*_ZAFAFA BIYAR BACTH F_*

1... _BAKAR INUWA_ 350
*(Bilyn Abdull)*

2... _RAYUWAR MACE_ 350
*(Hafsat Rano)*

3... _NOOR ALB_ 350
*(Mamu gee)*

4... _MASARAUTA_ 350
*(Mss xoxo)*

5... _KUFAN WUTA_ 350
*(Huguma)*

_Duk biyar 1500_

*_____________________________*

*_ZAFAFA BIYAR BATCH G (Da ake kanyi yanzun)_*

1... _FARHATAL QALB_
*(mss xoxo)*

2... _GURBIN IDO_
*(Huguma)*

3... _SANADIN LABARINA_
*(Hafsat Rano)*

4... _INAYAH_
*(Mamu gee)*

5... _BABU SO_
*(Bilyn Abdull)*

_Kuɗinsu a yanzu 1k duk biyar_

*YADDA ZAKU BIYA NAKU KUDIN BOOKS DIN:*

_ACCOUNT NAME:_
*HAFSAT UMAR KABIR*

_BANK NAME:_ *ZENITH BANK*

_ACCOUNT NUMBER;_
*_2270637070_*



_SAI A TURA SHEDAR BIYA ZUWA GA:_

*_07040727902_*

_IDAN KUMA KATIN MTN ZAKU TURA KO VTU SAI A TURA TA:_

*_09134848107_*



*_Muna godiya da zaɓin zafafa biyar 😘😘😘🙏🏻_*
[11/25, 3:54 PM] Rano2: _SL__**

©️®️*_*_Hafsat Rano_*_*

              Page (56)

***
Tafiya yake yana kallon gaban sa yana jin yadda kukan ta yake shigar masa ilahirin dukkannin jikin sa, baya so ya tsani duk wani abu da zai sakata kuka gashi ita abin kukan baya mata kad'an kwata-kwata. Birki ya taka ta dago ya zuba mata ido bayan ya saka motar a parking.

"Bakya so ki bini?"

Shiru tayi tana kokarin daidaita kukan nata

"Shikenan, zan maida ke sai na tafi, idan kin gama sai nazo mu tafi, hakan yayi miki?"

Girgiza kai tayi

"Mu tafi." Tace cikin muryar kuka

"No bakya so, kuma be kamata nayi forcing dinki ba, kina so kuyi magana da Baffa ko? Kinyi missing dinshi ko?"

Daga mishi kai tayi

"Shikenan ki daina kuka, I'm taking you back, sai na dawo mu tafi."

"Um um mu tafi kawai dare zai maka idan ka koma."

"Sai nima na kwana." Yace yana kallon ta

"Sai ka kwana." Tace tana murmushi

"Wasa nake miki, ina ni ina kwana gidan surukai? Sai dai idan tare zamu kwana."

Boye fuskar ta, tayi a cikin mayafin ta, yayi murmushi sannan ya shafi gefen fuskar ta, ya cire motar daga P ya maida ta R ya juya kan motar zuwa hanyar da suka biyo.
   Ido Baffa ya kura yana tunanin da gaske ne ko dai gizo idon ke masa, sai da suka matso sosai ya tabbatar da su ne suka dawo, ajiye butar hannun sa yayi yana jiran Tariq din yayi parking sannan suka fito.

"Lafiya?" Baffan ya tare su tun ma kafin su karaso, kasa Jidda tayi da kanta shi kuma Tariq yayi murmushi

"Lafiya Lou Baffa, dawo da ita nayi ta kwana."

"Akan wanne dalilin? Wato uzzura maka tayi ka dawo da ita kenan saboda bata da kirki ko?"

Da sauri yace

"A ah Baffa, ni dai naga dacewar hakan, tunda idan mun tafi zamu iya jimawa kafin muzo."

"Ban yarda ba, ba wani ita ta saka dole ka dawo da ita, maza ku juya kibi mijinki bana son shashanci da sakarci."

Ya cigaba da fada sosai irin wanda Jiddan bata taba ganin yayi ba, kanta a k'asa tana hawaye ta juya kamar munafuka tayi hanyar motar daidai lokacin da aka soma kiran sallar magriba a masallacin kusa dasu

"Baffa dan Allah kayi hakuri ka barta dan Allah." Tariq din yace yana rokon Baffan

"Sai dai kaima toh ka zauna gobe da safe sai ka tafi, amma sam ba zaka bi hanyar nan kai daya ba ga dare, kuma ko gaba ba'a biye wa shiriritar mata dan su ba ishashen hankali suke dashi ba, zo ki shige ciki kuma zamu hadu dake idan mukayi sallah."

Juyowa tayi sum-sum-sum ta shige shi kuma ya mikawa Tariq din ruwa a buta yace yayi alwala sannan suka nufi masallaci. Tana kan abun sallah tana tunanin rashin kyautawar da tayi sai ga sallamar Baffa, sai kuma ta Ya Tariq din da yake biye dashi. Rufe kanta tayi da Hijab din da tayi sallar cike da tsoron haduwa da Baffan.

"A gyara wanchan dakin ga net nan sai a saka masa a rufo dakin ."

"Toh Malam." Tace cike da girmawa

"Baffa da an barshi ma na gyara da kaina."

"A ah ba za'a barka ba, bismillah zauna."

Zama yayi sannan Baffan ya zauna shima yana kallon kofar dakin da yasan Jiddan na ciki.

"Hauwa'u."

"Na'am." Tace ta fito da sauri

"Jeki taya Mamaanki ku gyarawa megidanki dakin chan."

"Toh."

Tace ta wuce a tunanin ta ko wani fadan zai mata da taji kiran. Zuwa tayi ta samu Inna Suwaiba a dakin ta tayata suka gyara shi tsaf, dama akwai yar katifa madaidaci a dakin da carpet yawanci anan Baffa yake kwana ko idan yayi baki ya shigar dasu ciki sai toilet dan karami da banbun ruwa da already yake cike da ruwa. Babu wani datti a dakin nan da nan ta gyara shi ta gyara shinfidar gadon ta samu gefen katifar ta zauna tana tsoron fita su sake haduwa da Baffa yayi mata fada.
Tana zaune tana dan jiyo maganganun Baffan da nasa kafin taji sanda Baffan yace masa zai je baya ya dawo ya shiga ciki sauro. Dama yana lura bata fito ba tunda ta shiga, rabin hankalin sa yana chan shiyasa baffan na cewa ya tashi ya mike yana yi masa sai da safe har Baffan na tsokanar sa ba zai dawo su cigaba da hirar ba, murmushi kawai yayi Baffan ya fice shi kuma ya nufi dakin da dan saurin sa. Tana jin fitar Baffan ta yinkuro zata fito kafin ya dawo ta kwanta sai gashi ya turo kofar ya shigo.

"Ina zaki?" Yace yana tokare kofar da hannun sa

"Daki zan je kafin Baffa ya dawo, kar yayi min fada."

"Ba zai sake miki ba ai."

"Um um baka san Baffa ba, zai iya sakewa wallahi."

"Ba wani, ai ya wuce na masa bayani ni nace mu dawo ba bake ba "

"Ni ai tunda Baffa ya ganka ya daina so na."

"Shine kike kishi dani?"

"Eh." Ta daga kanta

"Yarinya haka zaki hakura, na riga nayi miki fashin Baffa kamar yadda kika kwace min Baba."

"Ni din?"

"Ehen, Baba yana son ki komai Hauwa'u komai "

"Nima inason Baba sosai."

"Shikenan an raba, ke Baba ni Baffa."

"Ni dai dukkan su nake so."

"Ai baki isa ba sai dai ki zabi daya."

"Um um dukka nake so ni dai."

"Idan kinaso na bar miki su sai dai ki kwana a dakin nan."

"Innalillahi!" Tace tana waro ido

"Sai da safe "

tayi hanyar fita da sauri tuno waye Tariq din, hannun sa da ya tokare kofar ya sake gyarawa sosai, tazo ta sa hannun ta wai zata cire hannun sa, dariya ma ta bashi ya tsaya yana kallon yadda take cijewa a dole sai ta cire hannun sa, sai da ta gama duk kokarin ta ko gezau bayayi sannan ya cire hannu ya fizgo ta gaba daya jikinsa ya matse ta yana dora habbar sa a saman kanta

"Karfin ki be fi cikin tsokali ba kece zaki iya cire hannu na Baby?"

"Ai dan na hakura ne." Tace

"Auw, haka kika ce?" Ya cireta daga jikin nasa yana kallon fuskar ta, daga masa kai tayi alamar eh

"Ok bari mu gwada wani abu "

Sai kawai ya dagata sama baki daya nufi katifar da ita, da sauri ta hau wuntsila kafarta ta hau rokon sa

"Dan Allah kayi hakuri."

"Abu zan gwada kawai, muga karfin da kike dashi."

Sauke ta yayi kafin ta yunkura ya bi ta ya dora mata dukkan nauyin sa akanta, yayi mata rumfa da jikinsa har baka iya ganin ta.

"Oya show me your strength."

Girgiza masa kai ta hau yi

"Ba zan kara ba, pls ka dagani wayyo Baffa na."

Toshe mata baki yayi da sauri yana mata dariya, sai da yaga ta fara jigata sannan ya dagata kadan ya juyar da ita ta dawo saman jikin sa suna kallon juna.

"I love you Jiddanah."

Ya samu kansa da furtawa cikin wani irin shauki.

"Bayan ka danne ni."

"Wasan soyayya ne, kuma kinga ai gwara ki saba daukata, kin gane?"

"Ni ba ruwana." Tace tana juyar da fuskar ta da sauri

"Shy shy girl." Ya danna mata hanci yana murmushi

"Zan tafi, kafin Baffa ya dawo."

"Ni gaskiya a'ah, gaskiya!"

"Ba zan tafi ba?"

"Eh." Ya daga mata kai

"I need my wife a kusa dani gaskiya."

"Ni dai dan Allah kayi hakuri, kar Baffa ya shigo."

"Ba zai shigo ba ai."

"Allah zai iya dawowa yazo, dan Allah ka barni na tafi."

"Zaki dawo toh?"

"When?"

"Idan Baffa yayi bacci, kowa yayi bacci."

"Um um ba ruwana."

"Toh ba in da zaki." Ya hau goga fuskar sa a saman tata, kafin ya ciji lips dinta na k'asa a hankali, shi kadai yasan me yake ji a game da ita, wani irin magnet ne yake jan sa, she's sooo sooo sweet da baya iya resisting kansa, yanzu ma kawai dan babu yadda zai ne amma he's desperate to be with her, motsin shigowar Baffa yasa shi daga ta ba dan yaso ba, ta fice da mugun sauri. Fadawa yayi saman katifar ya rike kansa kad'an sai kuma ya mike ya fito domin dauko abu a cikin motar sa.

Tsire Baffa ya siyo masa da lemuka ashe shine fitar da yayi, ya kawo masa har bakin dakin be shiga ciki ba ya fito ya karba yayi godiya sosai dan be so Baffan ya wahalar dashi haka ba. Jidda yasa aka kira masa suka zauna a waje daga kofar dakin sa suka shiga hira, hira irin ta tsakanin d'a da mahaifi, dama chan yana so ta kwanan dan dai ba zai nuna bane, yaji dadi matuka yadda Tariq din yake kular masa da Jidda kuma hankalin sa ya kwanta sosai. Sai wajajen sha biyu sannan Baffan yace taje ta kwanta ya shige dakin sa. Tana shiga daki yana kiran ta a waya, tayi kamar ba zata daga ba dan har ta soma cire kayan jikin ta ta daura zanin Inna Suwaiba da ta fito mata dashi, mayafi ta yafa akan zani da rigar ta fita a hankali cikin sand'a ta isa tana zuwa yana jikin kofar ya riko ta da sauri ciki ya maida kofar ya rufe yana sauke ajiyar zuciya

"Na zata ba zaki zo ba."

"I missed you." Yace yana zagaye fuskar ta da tashi.

"Gani."

"Ok muje mu kwata!" Yaja hannun ta

"Aina?"

"Anan mana, plsss don't say no, bansan me yasa ba nake jin wani irin feeling, dan Allah karki tafi ki barni."

"Idan Baffa ya fito fa."

"Ba zai fito ba, sai ki koma kafin asubah kinji Jidda nah."

"Ni dai..."

"Shsshh, babu kyau fa, mala'iku zasu tsine

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login