Showing 102001 words to 105000 words out of 120733 words
aunty."
"Akwai in da yake miki ciwo ne?"
"Ba ko ina."
"Toh na tura miki text tun ranar kin gani?"
"Na gani aunty."
"Yawwa, ki yi hakuri kowacce mace da kika ganta a haka ta fara, girman kenan, ke dai banda gardama dan ita ke jawo ma mutum matsala, dama dai chan kinga ba wasu uban magunguna aka narka miki ba, mafi a'ala dai shine maganin sanyi, idan aka kwana biyu da kanki zaki nemi karin wasu abubuwan ba sai wani ma yaji ba, yanzu dai ki daure kiyi hakuri na lokaci ne da ya wuce shikenan, ki gyara jikin ki da mijin ki sannan kiyi masa biyayya iyakar iyawar ki."
"In sha Allah Aunty, nagode sosai Allah ya saka miki da gidan aljanna, ba dan ke ba aunty, da bansan ya rayuwata zata kasance ba, da nasan yanzu ina chan cikin wahala da tashin hankali, bani da abinda zan yi na biya ki Aunty."
"Abu daya zakiyi ki biyani, duk runtsi duk wuya karki taba bijirewa mijinki, kiyi kokarin kyautata masa sannan ki sani, soyayya karamar abu ce a zamantakewar aure, kuma ita kadai bata iya dorar da aure, hakuri da addu'a sune babban makami domin akwai kalubalai masu tarin yawa da zasu taso miki, wanda zasu bude miki ido kisan mecece ma rayuwar."
"In sha Allah aunty."
Tace cikin muryar kuka, ita kanta tasan akwai kalubale sosai a rayuwar aure tunda taga yadda ita kanta Auntyn tayi hakuri kafin yanzu da komai ya wuce sai dan abinda ba zaa rasa ba, ta kuma ga yadda Baffan ta yasha wahala a wajen Iya Lami , sannan ga yadda Yaya a kullum take labarin wahalar da tasha a rayuwar auren duk da ba lallai dan abu ya samu wane kai ma ya same ka ba, amma idan ka sawa ranka Allah zai iya jarrabarka shikenan zaka zauna lafiya kuma cikin shiri.
Hawaye Aunty take amma bata bari Jiddan ta gani ba, tasa bayan hannun ta, ta share sannan tace ta je su tafi kar yayi ta jira, zata aiko da sakon Baffa da zata tafi masa dashi. Tashi tayi jikin ta yayi matukar sanyi ta jawo mayafin ta har saman fuskar ta yadda ba zai ga fuskar ta ba har ya gane kuka tayi ba.
Waya yake ta fito tana kallon k'asa, ya zura mata ido yana so ya gano wani sauyi a tare da ita, yanayin tafiyar ta ya nuna kamar she's down, katse wayar yayi bayan ya ciro ya daga kunnen sa, ya mike tsaya ya zura ta a aljihun gaban rigar sa, ya riko hannun ta yana leka fuskar ta, hawaye ya gani yayi a kwance a fuskar tata, yasan definitely wata maganar sukayi da aunty amma be san wacce ba, baya fatan tasan maganar Salma da abinda yake faruwa wanda yayi tunanin Auntyn ma bata sani ba, tsoro ne ya darsu a ransa kar dai ko auntyn ta sani shine ta fadawa Jiddan
"Menene?"
Yace ciki nuna tsantsar kulawar sa, gefe daya kuma yana jin tsoron amsar da zata bashi dan be san a yadda zata kalli abun ba, tunda yanzu ne ta fara sanin sa bare ta banbance abinda zai iya da wanda ba zai iya ba.
"Ba komai."
"Tom ki daina kukan kinji? Muje mota sai ki fada min menene."
Da ka ta amsa masa, ya karbi yar jakar daga hannun ta ya rike mata dayan hannun suka fita daga falon. Motar na nan in da ya ajiye ta dan haka kawai bud'e mata baya yayi ya taimaka mata ta zauna sannan shima ya shiga da sauri, ya jawo ta baki daya jikinsa da yake motar tinted ce, kukan shagwaba ta saka masa ya rikice ya rasa yadda zai yi, ita bata san baki daya kukan ta rikita shi yake ba, kuma shine babban weak point dinsa, tapping bayan ta ya dinga yi a hankali har ya samu tayi shiru, ya zaro tissue daga saman dashboard ya goge mata fuskar bayan ya dago ta daga jikin sa
"Menene?"
"Ni Baffa na."
"Kike so ki gani? Shiyasa kike kuka?"
"Eh." Ta gid'a masa kai, ajiyar ya sauke da karfi jin ba waccan magaanar bace yace
"Zaki ganshi gobe in sha Allah."
"Sai me kuma?"
"Babu komai."
"Ok..." Ya zare jikinsa a hankali ya fito ya dawo mazaunin driver yaja motar suka bar gidan.
***Masifa aunty Nafi take Salma kuma na ta gursheken kuka, tsabar wulakancin abinda Ya Tariq yayi musu ace a gaban su sai dinga romancing matar sa, gashi wallahi ita da gaske take tsananin son sa da kaunar sa take kamar ta je ta shake Jidda har lahira, ita kanta Aunty Nafi taji haushin wulakanci da yayi musu ai ko ba komai ita matsayin uwa take a wajen sa, amma saboda wulakanci shine zai maida su yan iska yana rungumar mace a falon mahaifiyar sa. Banko kofar akayi Mama ta shigo tana huci kamar zakanya, tashi aunty Nafi tayi tana kallon ta da mamaki
"Ki tattara yarki da tsummokaran kayan ki, ki bar min gida na, kuma wallahi wallahi Tariq ba zai taba auren Salma ba, tunda ke muguwa ce makira, baki duba karfin alakar mu ba, har ki kala wa dana sharri saboda kawai son zuciya."
"Ban gane sharri ba, kina nufin Salma sharri tayi wa Tariq kenan, kuma kin goyi bayan sa?"
"Eh sharri kikayi masa bakar muguwa, wallahi sai kin tafi bani ba ke kuma wallahi."
"Ahayye! Tab Amma sannu Aisha, kina nufin zaki rabu dani akan danki? Yaran yanzu da ba shaidar su ake ba?"
"Nayi, kuma kema kinsan duk abinda kuka fada akan sa karya ne, toh wallahi ko ku tafi da kafarku ko securities su fidda ku."
"Aikuwa wallahi ba zai yiwu ba, a dake mu a hana mu kuka, ba za'a bata min yarinya kuma ace zaa kore mu ba, wallahi ba inda zamu ko Tariq ya karbi Salma ko kuma zance ya karada dukka kasar nan."
"Idan kin ga dama ki dau loud speaker ki zaga kaf duniyar nan kina fada, babu abinda zai faru illa kanki da zaki WA illah, dan ko a yanzu babu me karbar yarki da wannan banzan halin nata ballantana son zuciyar ki yasa ki bata suna, kinga zata kare a haka ba aure."
Mamakin yadda Maman take kokarin wargaza musu plan dinsu ya saka jikin ta sanyi, amma sai ta hana ta gane halin da ta shiga tace
"Ai akwai hukuma ko? Wallahi sai naje sun bi min hakkin 'ya."
"Kije binnin sin ma, kuma wallahi ko a hanyar gidan mu na chan Kano na sake ganin ki sai na saka an rufe min ke an jefar da mukullin."
"Naji duk abinda kuke fada ke da yar taki kuma nayi recording din komai, dan haka sai a bi wani sarkin ,tunda baki san halacci ba."
Shiru Aunty Nafi tayi ganin dai da gaske Maman ta gano plan din su, kenan ta ji maganar ko dai so take ta sakata fara feeling quilty?
Juyawa Maman tayi ta fita, jim kad'an sai gata ta dawo da wasu masu aiki daga bq su biyu kedaru majiya karfi,suka shigo dakin tace su kwashe kayan su Anty Nafin su fitar mata dasu, tsoro ne ya shigi Anty Nafi, tana so tayi magana amma kuma tana tsoro dan bata taba ganin bacin ran Maman haka ba sai yau, dan komai akayi mata bata cika tankawa ba, shiyasa tayi tunanin zata iya amfani da wannan damar ta cutar da Maman ta kakabawa Tariq Salma ta samu hankalin ta ya kwanta.
"Ba sai an mana wulakanci ba zamu fita." Tace tana yin wajen kayan, zata taba Mama ta dakawa masu aikin tsawa tace bata son jira su kwashe kayan, da sauri suka suri akwatin tasu sukayi waje, Salma babu ko mayafi akan ta sai wata hula ita kuma Aunty Nafi sai mayafi suka fito Maman na tsaye suka wuce, already tayi waya gate tace sam ya sauke su a tasha suna fita aka saka musu kayan a booth Salma sai kuka take Anty Nafi kuma ta kasa cewa komai saboda yadda ran ta yayi bala'in baci.
Zama Mama tayi a nutse tana dafe kanta da yake mata kamar zai rabe biyu, bata san ta tara damuwa haka ba sai yau da Baba ya birkice mata, ta kuma san kafiya irin tasa shiysa ba zata taba amincewa ya aiwatar da abinda yayi niyya ba, da kanta zatayi kokarin ganin Tariq da Jidda sun bar kasar baki daya gwara su je su karata a chan duk da bata son Jiddan bata kuma san yaushe zata so ta ba amma gwara ita akan salma.da ta gama saida mutuncin ta a titi.
Maryam ce tazo ta zaune a gefen ta, ta dago tana kallon ta sai ta girgiza kanta
"Ya akayi? Zaku je gidan Safiyya daga nan ku wu kaiwa Umaima kaya."
"Ok sai muje gidan Ya Tariq?"
"Bana son neman magana."
"Dan Allah Mama, ba zamu dade ba."
"Toh naji, idan kunje KU gaishe su "
"Har Jiddah?"
"Ban sani ba." Tace tana jan tsaki
"Wai Mama, Anty Nafi yar gidan ku ce itama Hajiya Babba ce ta haife ta?"
Girgiza kanta tayi
"Bamu da alaka ta jini ko kad'an, yar abokin Alhaji ce, zumunci irin na da da iyayen suka rasu shine aka bawa Hajiya Babba ita dan dama gida daya muke tun a dah, shine muka taso tare babu wani banbanci, amma kinga ai yanzu ta nuna min jini ba karya bane ko? Tunda na tabbata abinda tayi min Mimi ba zatayi ba, anyways, we learn from our mistakes, ya wuce in sha Allah."
"In sha Allah."
"Tashi kuje kar kuyi dare."
"Ok ina kayan suke."
"Suna cikin daki na, ki taho min da wayata na kira Dr Iman tazo tayi mun bp."
"Ok mah." Ta wuce ciki ita kuma Maman ta kurawa waje daya ido tana tuna abinda ya faru.
[11/25, 3:54 PM] Rano2: _SL__**
©®*_*_Hafsat Rano_*_*
Page (53)
***Kusan tare suka shirya a gurguje saboda saura kiris su makara, tea kawai suka sha da slice bread suka fito Faisal ya dauke su zuwa Embassy din. Da zuwan su Alhaji Tahir ya fito har kofa ya shigar dasu bayan ya rike hannun Tariq din jidda kuma ta bi bayan su zuwa wani hadadden office. Zama Tariq yayi a kujerar dake facing ta Alhaji Tahir din ita kuma ta zauna akan couch din dake baya da dan madaidacin table a gaban wajen, fridge ya bud'e ya dauko musu ruwa da lemo sannan ya karbi takardun ya dan duba su kad'an ya mike ya fita bayan yace yana zuwa. Juyowa yayi gaba daya da kujerar suka hada ido ya dage mata gira tayi murmushi tana kallon kofar shigowa.
"Sai na taso ma." Yace yana kokarin mikewa, da sauri ta hau girgiza masa kai
"Dan Allah kayi zaman ka anan."
Murmushi yayi ya girgiza kai, ya juya daidai lokacin Alhaji Tariq din ya dawo yace su taso, suka bishi ta wata kofa ba wadda suka biyo dazu ba, ya kai su wani babban office yace su shiga su zauna, suna zama Mr Biden ya shigo shima. Cikin kankanin lokaci suka gama abinda zasuyi suka fito bayan sun wuce layi me yawa a reception din wajen. Godiya sukayi masa yace su gaida Baba suka fito shi kuma ya juya zuwa ciki.
Jirgin rana zasu bi zuwa Kano, shiyasa sai da suka fara komawa gida suka karasa shiryawa, kwana Jidda take so tayi a gidansu amma taka take-taken Tariq din kamar ba zai barta ba, kwana biyu yace kawai zasuyi wai idan suka je kano yau gobe da wuri sai su tafi garin su Jiddan, su dawo da yamma, su sake kwana sai su dawo da next day, kaya ta dauka kusan set biyar incase ko zai chanja shawara ya barta, yana lura da ita da tana saka kayan a suitcase yayi kamar be gani ba dan be shirya barin ta ba, bayan yasan duk rayuwar da ta shiga a wajen Matar baffan ta, SANADIN LABARIN da ya saka masa tausayi da kaunar ta, tun ranar farko da ya fara dora ido akanta, ya samu kuma labarin ta, yake dawainiya da son ta shi kansa ba tare da yasan me yake ji ba, ya damu da ita sosai har ya zama yana tuna ta a kowanne lokaci har bayan tafiyar sa, dalilin da ya saka shi kiran Aunty a wanchan lokacin. Duk a tunanin sa tausayin ta kawai yake yi, shiyasa ya dinga chusawa kansa ra'ayi akan irin matar da yake so ya aura, yana kokarin dakushe zuciyar sa da nuna mata ai jiddah bata cikin wannan layin.
Tasowa yayi ta bayanta tana ciro undies dinta a bobboye dan kar ya gani tana turawa a cikin kayan nata. Rungume ta yayi tsam yana dora kansa a saman kafadarta, da sauri ta saki sleeping dress din da ta ciro zata sake chanja mata waje cikin wanda Aunty ta aiko mata, irin fitinannun sexy nighties din nan ne dan rigar ko kusa da zuwa waist dinta batayi ba, da kad'an ta kai saman cibiya sai wani transparent pants sannan rigar ta baya a bud'e take gaba daya. Yaga sanda ta yadda rigar, sai ya cikata ya duka ya saka hannu ya dauki rigar yana dagata, kamar wadda aka dasa a wajen haka tayi ta dauke numfashi tana rufe idonta sanda ya dauki rigar ya dagata yana kallon ta idon sa a shanye kamar wanda yasha wani abun, shiru taji yayi ta dan bud'e ido kad'an suka hada ido ya kad'a mata kai yana daga mata rigar
"I love this."
"Ajiya fa aka bani." Tace still idon ta a kulle.
"Waye?"
"Em.. Ami... Ya Safiyya ce ta bani ajiya."
"Me yasa ta baki ajiya?"
"Nima ban sani ba."
"Shikenan ta zama tamu, zan biya kudin amma ba zamu bata ba gaskiya."
"A ah gwara a bata mu ba abinda zamuyi da ita."
"Ko? Mu ke da abinda zamuyi da ita ai, beside ko kyauta ne ma Sofy zata bani matata ta saka min na gani."
"Innalillahi!"
Dukawa yayi ya tura ta a suitcase din sannan ya rufe yana yin wani irin shu'umin murmushi sannan ya rufe yana daga su
"Nasan in da ake saida irin su don't worry zan siya miki kinji?"
"Ni bana so."
"Allah sai kinso, tunda ni inaso."
Turo baki tayi ya matso daidai fuskar ta yayi magana a hankali
"Inaso na dinga ganin ki cikin lingerie and bikinis. I don't mind idan ma kika zauna haka, eh kin gane...."
Ya kashe mata ido daya, da sauri ta juya tana kunshe dariyar ta.
"Common... life din is too short let's enjoy our self Baby "
Kin kallon sa tayi, ya koma ya zauna yana murmushi kasa kasa , ya dauki wayar sa ya kira Fauwaz yace yazo ya kaisu airport daga nan zai aike shi wani waje. Fita tayi daga dakin taki yarda ta kalle shi kwata-kwata shi kuma babu abinda yake sake birgeshi da ita irin kunyar ta.
Dakin Godiya taje ta sameta a kwance tace ta hada kayan ta za'a kaita wajen aunty zasuyi tafiya su, tashi tayi da yar murnar ta tunda dama mamanta tana aiki a gidan nasu ne shine aka bata yar, a gurguje ta gama hade kayan ta dauko kudi ta saka mata a kayan sannan ta dauki waya ta kira gate tace Faisal ya kai ta gida dan ta kira Aunty already tace ta turo ta tunda basa nan kuma ko sun dawo ma daga kanon tafiya zasuyi gwara kawai ta dawo tunda babu amfanin zama. Tana kokarin komawa ciki bayan yarinyar ta fita sai ga Fauwaz ya shigo, tsayawa tayi ya karaso ciki suka gaisa sai ta tuno babu ko mayafi a jikin ta, tasan kuma halin oga aka, ciki ta shiga ta bar Fauwaz din bayan tace masa tana zuwa, ta shiga dakin ta, ta chanja zuwa bakar abaya tayi rolling sannan ta same shi a dakin sa tace masa Fauwaz yazo. Tashi yayi ya fito bayan ya jawo suitcase din tasu ita kuma ta cire musu cable din wayar su ta dauki bottle water a fridge sannan ta saka abinda tasan zata bukata a cikin handbag dinta ta fito sanye da flat shoe. A tsaye ta same su daga Tariq din har Fauwaz din suna magana, tana fitowa Fauwaz yaja kayan yayi gaba shi kuma ya juyo yana kallon shigar ta kafin ya kad'a kai, babu wani aibu she looks decent dan yasan ma'aikatan wajen zasu iya kalle mishi mata ganin how beautiful she is amma a kalla if shigarta is ok ko sun kalle ta ma sun kalli Allah ya isa kawai. Shi a ganin sa ma fa Jiddan sa ta kai matsayin saka nikaf kawai saboda baya so taji ta a takure ko taga kamar ya matse ta shiyasa yaki cewa din amma wallahi da zata saka shi sai yafi kowa jin dadi, babu shegen da zai kalleta bare har yayi admiring kyauwun ta a zuciyar sa.
Hannun sa ya sarke a cikin nata suka fito bayan ya karbi ruwan ya sha kad'an. Wani ne daban a mazaunin driver sai kuma wata mota daya da Tariq din be san ta ba, itama da mutum hudu a cikin ta, fitowa sukayi da sauri suka gaida Tariq din ya gansu wasu manya fuskar su a toshe da bakin glass gefen aljihun kowannen su dauke da bindiga
"Ban gane ba."
Yacewa Fauwaz bayan ya budewa jidda mota ta shiga, kad'a kai Fauwaz yayi yana dariya
"Abokin Babana ya samo mana su wallahi, shi Baba baya so amma yaki yace yadda rayuwar nan ta zama wallahi tunda dai mun shiga circle din dole ne muyi abu kamar nasu, this two naku ne har ku wuce tare zaku tafi Kano din ma yanzu.". Ya karashe yana dariya
"This is serious, kenan mutum ba zai yi rayuwar sa ba haka nan sai da wasu? Waye ma ya damu ne wai damu ma?"
"Haka kake gani fa, insecurity din ya wuce in da kake tunani, akwai wasu ma da zaku hadu dasu kuna sauka a airport."
"Are you kidding me? Kai aka sani ai bani ba."
"Allah I'm serious, muje kar kuyi missing flight."
"Abun babba ne." Yace sannan ya shiga gefen Jidda shi kuma Fauwaz ya shiga gaba.
***A mintiunan da basu gaza awa daya suka isa Kano, suna sauka kuwa suka hadu da wasu zugar securities din suna jiran su, shi abun ma dariya yaso ya bashi, sai kuma dai ya share yace