Showing 84001 words to 87000 words out of 120733 words
rumfa da jikinsa. Ran Salma ya kai kololuwa a baci amma sanin Amira ba zata biye mata ba yasa bata ce komai ba, ace dan wulakanci tunda ta shige bata saka fitowa ba, ko sai da safe ai ta ce musu, gashi babu damar bin bayan su amma dole ta kira mamin ta gobe ta fada mata Ya Tariq din yana son Jidda dan ko makaho zai iya tantancewa tsananin son da yake mata a yan sakanni da basu wuce biyar ba, bata san Jiddan ma A bace sai da taga ta kama hannun Ya Tariq din ba kunya sun yi shigewar su, ita duk kallon wawiya yar kauye take mata duk da wayewar da tayi amma ta raina ta sosai, sai gashi tayi abinda ya bata mamaki ya kuma daure mata kai dan Ya Tariq din ma bata taba kawo zai iya yin abinda yayi jiyan ba, su Mama bonono suke wato rufe kofa da barawo, a tunanin su ba zai taba son Jiddan ba sai gashi zata basu mamaki. Tana kallon Amira tana jan munshari amma ita ta kasa tana tunanin me yake wakana a chan wajen su, son Ya Tariq din take da mugun kishin sa, dan tun ba yau ba Anty Nafi take kwadaita mata auren Tariq din shiyasa duk tabi ta gama tsara rayuwar ta, da yadda take so ta kasance, ko wannan gidan da suke ciki a buri da hasashen ta yayi mata mugun kad'an gida take so na alfarma na kece raini da ma'aikata birjik suna mata hidima ta huta sosai taji dadin rayuwar ta. Ta dade tana wannan lissafin wasikar jakin kafin ta samu bacci ya dauke ta mara dadi.
Amira ce ta rigata tashi ta riga su dukka ma tashi dan har su Jiddan basu fito ba a daki Ya Tariq din ma yayi sallar asubah shi da Jiddan suka koma suka kwanta duk da nokewar da take tana jin kunya amma yaki barin ta, dole ta kwanta tana zara ido ya kanainaye ta da hannayen sa ko kwakkwaran motsi tayi a jikin sa zatayi shi. Godiya taje ta taso tazo ta gyara falon tas tayi moping Amiran na guiding dinta ta dauko turaren wuta ta saka a burner nan da nan gidan ya dau kamshi ta koma daki tayi wanka ta fito kenan Salman ta tashi daga baccin wanda bata jin ko sallar asubah tayi tana bacci, mika tayi tana kallon Amiran da ita ma kallon ta take
"Kinyi sallah kuwa?"
"Yanzu zan yi."
Ta sakko daga gadon ta dauki towel din da Amira tayi amfani dashi ta shige toilet din, tsaki Amiran tayi dan bata son sharing da kazanta kuma akan towel din kusan sau uku suna fada amma taki daina dauka. Cigaba da shiryawa tayi tana cikin shiryawar Jidda ta kwankwaso ta shigo ciki ta zauna a gefen gadon tana kallon yadda gadon ya hargitse.
"Goodmorning Matar Yah."
"Kina da matsala, ina Salma?"
"Ta shiga toilet,jiya shine kika gudu kika barmu."
"Bacci nayi da wuri shiyasa, "
"Fadi gaskiya dai, ko dai Ya Tariq ya hanaki dawowa?"
"Eh shine ya hanani, tunda haka kike so kiji."
"Good, a cigaba da rikita min yayana, I trust you."
Dariya Jiddan tayi, Salma dake tsaye jikin kofar toilet din taki fitowa ko zasu fadi wani abun ta samu dorawar sai taji tace
"Kunyi breakfast kuwa?"
"A ah, amma aunty ta kira a wayar ki dake falo, dan har zan sama mana wani abun sai kuma ta kira na dauka tace Sam ya taho."
"Yawwa, na huta bari na kirata."
Ta mike ta fita, sannan Salma ta fito, Amira ta kalleta ta tabe baki ta dau wayar ta.
Zuwa tayi ta kira Aunty tana dauka ta fara fada
"Amira da Salma a gidan nan suka kwana wai?"
"Ya Aunty, jiya suka zo."
"Jiya? Ina Tariq din? Me zai sa su kwana a gidanku?"
"Zuwa kawai sukayi Aunty."
"Karya ne, turo su akayi wallahi, wannan wane irin abu ne, kina ji na, karki yarda ki yi sake ki saki mijinki har su samu dama akanki, yarinyar nan Salma ba dan Allah aka turo ta ba, idan kika tsaya shashanci sai ta raba ki da gidanki."
"Aunty, waye zai turo ta? Kuma tayi me?"
"Ta kashe miiki aure mana."
Zaro ido tayi,
"Ni? Akan me yasa?"
"Oho, karki tsaya tambaya kiyi abinda ya dace, kuma bari, dani suke zancen wallahi na daina kyalewa, Yaya zan fadawa wallahi."
"Aunty dan Allah ki daina shiga matsala akai na."
"Ba wata matsala, na daina kyalewa kawai."
Fitowa yayi sai tayi shiru tana sauraron Auntyn, a gefen ta ya zauna sai tayi saurin cew
"Shikenan aunty, sai yazo."
Ta kashe ta ajiye wayar a gefe,
"Sam ne zai kawo mana breakfast in ji Aunty?" Gid'a kansa yayi yace
"Ni nake nake so."
"Nawa?"
"Um... Golden morn zan sha."
"Ok,." Ta mike ta nufi kitchen din, ta shiga taga ko ina an gyara tsaf, tasan da tainakon Amira dan amira sam bata da son jiki ko kad'an, bud'e cabinet din da tarkacen kayan su madara suke ciki ta dauko golden morn din ta ajiye akan iceland ta dauko mug, motsi taji a bayan ta ta juyo sai taga Salma ce ta shigo kitchen din, ta wuce kai tsaye wajen sink ba tare da tace komai ba, dauke kai Jidda tayi dan bata isa itama ta kula ta ba, musamman bayan aunty ta fada mata dalilin dayasa aka turo ta, cup ta dauka ta dauraye a sink din sannan tazo gefen ta, ta bud'e ta dauko kayan tea ta zuba a cup din tana had'awa. Fita jidda tayi bayan ta dora komai akan dan madaidacin tray ta wuce daki dan ya bar falon, ta kai masa sai ta tuna babu ruwa a fridge din cikin dakin ta dawo da nufin dauka, tana shiga tsantsi ya kwasheta, ta kwalla kara da karfi kafin ta zame gaba daya ta fadi a daidai kofar kitchen din. A guje ya fito Amira ma haka suka nufi kitchen din a rikice
*_RANO SCRUMPTIOUS MEAL_*
_(Where every flavour tells a story .....)_
*_By HAFSAT RANO_*
_(Mother/wife/writer)_
_08030811300_
_IG:Rano_scrumptious_meal_
_INA MA'ABOTA ABINCI? WATO *TRADITIONAL FOOD IN KANO*? GANGARIYAR ABINCI NA AL'ADUN HAUSA DA NAHIYAR KETARE? BA ANAN KADAI MUKA TSAYA BA. MUNA DA LEMUKA WATO *LOCAL DRINKS*. ZAKU IYA KAWO NA HIDIMOMIN LIYAAFA MUYI MUKU_
_MU NA YIN:_
*_FUNKASO_*
*_ALKUBUS_*
*_SINASIR_*
*_WAINA_*
*_ASSORTED MEAT (KAYAN CIKI)_*
*_COW TAIL/COW LEG (DAB'URI)_*
*_CHICKEN AND FISH PEPPER SOUP_*
*_LOCAL DRINKS:_*
_HIBISCUS (ZOBO)_
_GINGER_
_AMAANI FRUITY SHAKE_
_MUN TANADAR MUKU MOUTHWATERING ABINCI KALA KALA WADANDA KE GINA JIKI DA KARA LAPIA. ABINCIN MU A TSAFTACE YAKE. KUMA MUNA YIN SU NE AKAN YADDA KOWANNE MUTUM ZAI IYA CI . AKWAI SPECIAL SOUPS NA MASU ULCER WADANDA BABU YAJI. AKWAI KUMA NA PEPPER DEM GANG GA MASU SON HOT AND SPICY...._
_KADA KU MANTA MUNA YIN NA TAKEAWAY/ORDER . MUNA KUMA YIN NA BIKI (WE CARTER TO SMALL/LARGE EVENT...._
_FUNKASO TO PAIR WITH COW TAIL:2K_ _WITHOUT COW TAIL:1K_
_ALKUBUS TO PAIR WITH ASSORTED MEAT (KAYAN CIKI) 2K. WITHOUT ASSORTED MEAT :1K_
_PLS NB: PAYMENT VALIDATES INTEREST..... DELIVERY WITHIN KANO:500 NAIRA_
*_ZAFAFA BIYAR COMPLETE DOCUMENTS_*
*ZAFAFA BIYAR BACTH A*
1.. _WUTSIYAR RAƘUMI_ 350
*(Bilyn Abdul)*
2.. _KAI MIN HALACCI_ 350
*(Miss xoxo)*
3.. _BURI DAYA_ 350
*(Mamu gee)*
4... _DAURIN BOYE_ 350
*(Huguma)*
5... _SAUYIN KADDARA_ 350
*(Hafsat Rano)*
_Duka biyar 1500_
*___________________________*
*_ZAFAFA BIYAR BATCH B_*
1... _DAURIN GORO_ 350
*(Hafsat Rano)*
2... _ALKAWARIN ALLAH_ 350
*(Huguma)*
3... _QAUNAR MU_ 350
*(Mamu gee)*
4... _IGIYAR ZATO_ 350
*(Miss xoxo)*
5... _GUDU DA WAIWAYE_ 350
*(Bilyn Abdull)*
_Duk biyar 1500_
*_____________________________*
*_ZAFAFA BIYAR BATCH C_*
1... _MIN QALB_ 350
*(Mamu gee)*
2... _SARAN ƁOYE_ 350
*(Bilyn Abdull)*
3... _KIBIYAR AJALI_. 350
*(Miss xoxo)*
4... _ABINDA KE CIKIN ZUCIYA_ 350
*(Hafsat Rano)*
5... _SIRADIN RAYUWAR BILKISU_ 350
*(Huguma)*
_Duk biyar 1500_
*____________________________*
*_ZAFAFA BIYAR BACTH D_*
1... _ALKIBLA_ 350
*(Huguma)*
2... _DALAAL_ 350
*(Miss xoxo)*
3... _UBAYD MALEEK_ 350
*(Mamu gee)*
4... _MABUDIN ZUCIYA_ 350
*(Hafsat Rano)*
5... _MAKAUNIYAR KADDARA_ 350
*(Bilyn Abdull)*
_Duk biyar 1500_
*____________________________*
*_ZAFAFA BIYAR BATCH E_*
1... _SO DA ZUCIYA_ 350
*(Mss xoxo)*
2... _TAKUN SAAKA_ 350
*(Bilyn Abdull)*
3... _HALIN GIRMA_ 350
*(Hafsat Rano)*
4... _DAB'IZAR ZUCIYA_ 350
*(Huguma)*
5... _DEEN MARSHALL_ 350
*(Mamu gee)*
_Duk biyar 1500_
*______________________________*
*_ZAFAFA BIYAR BACTH F_*
1... _BAKAR INUWA_ 350
*(Bilyn Abdull)*
2... _RAYUWAR MACE_ 350
*(Hafsat Rano)*
3... _NOOR ALB_ 350
*(Mamu gee)*
4... _MASARAUTA_ 350
*(Mss xoxo)*
5... _KUFAN WUTA_ 350
*(Huguma)*
_Duk biyar 1500_
*_____________________________*
*_ZAFAFA BIYAR BATCH G (Da ake kanyi yanzun)_*
1... _FARHATAL QALB_
*(mss xoxo)*
2... _GURBIN IDO_
*(Huguma)*
3... _SANADIN LABARINA_
*(Hafsat Rano)*
4... _INAYAH_
*(Mamu gee)*
5... _BABU SO_
*(Bilyn Abdull)*
_Kuɗinsu a yanzu 1k duk biyar_
*YADDA ZAKU BIYA NAKU KUDIN BOOKS DIN:*
_ACCOUNT NAME:_
*HAFSAT UMAR KABIR*
_BANK NAME:_ *ZENITH BANK*
_ACCOUNT NUMBER;_
*_2270637070_*
_SAI A TURA SHEDAR BIYA ZUWA GA:_
*_07040727902_*
_IDAN KUMA KATIN MTN ZAKU TURA KO VTU SAI A TURA TA:_
*_09134848107_*
*_Muna godiya da zaɓin zafafa biyar 😘😘😘🙏🏻_*
[11/25, 3:54 PM] Rano2: ._SL__**
©®*_*_Hafsat Rano_*_*
Page (45)
***Ruwa ya kawo mata ya taimaka mata ta sha ya ajiye yana hawa gadon. A hankali kukan da take ya dauke ya koma sai ajiyar zuciya da take saboda azabar da tasha, sanyi taji na ratsa ta, nan da nan ta soma rawar sanyi ya tashi ya kashe AC ya rage fan din, amma duk da haka bata daina ba, sosai zazzabin ya rafke ta wanda dama take ta jin alamun sa tun jiya amma ta daure sai gashi ya taso lokaci daya dalilin gyaran.
"Jikinki yayi zafi sosai." Yace yana kama hannun rigar ya zare mata shi, da sauri ta kalle shi shima ita yake kallo, ya girgiza mata kansa ya karasa zare mata rigar baki daya, wani irin yarrr yaji tun daka kansa har zuwa tafin kafafunsa, ya ja ajiyar zuciya ya daure ya ja karamin blanket ya rufa mata a daidai cikin ta zuwa saman chest dinta, idon ta dake a runtse tunda ya janye rigar ta dan bud'e taga ya dauka daga kan gadon, ya cire rigar dake jikin sa har singlet din, saurin maida idon tayi ta rufe tana jin sa ya hawo hadon ya jawo ta jikinsa ya gyara mata kwanciyar, zafin da jikinta yayi ya hadu ya chakude da bare fatar sa. Wani irin yanayi suka samu kansu a ciki musamman shi, ji yayi baki daya duniyar na juya masa, komai ya tsaya chak hatta bugun zuciyar sa ya karu da kaso me yawan gaske. A hankali zazzabin ya dinga raguwa har ya zama sai dan dumi kad'an.
"Gumi nake."
Tace sai ya sassauta rikon da yayi mata amma ba dukka ba, kanta na jikin kirjin shi tana jin yadda bugun zuciyar sa ke tsere, zufa na cigaba da keto mata ga wata matsananciyar kunya da ta rufe ta, dan babu komai a saman ta sai bra wadda itama kusan rabin kirjinta a waje yake saboda yadda karfen dake rige ta ya zare garin cire zip din rigar. Ta kasa motsi ko kad'an dan ko yaya ta motsa chest dinta zai iya haduwa da jikin sa.
"Are you feeling better?"
Ya tambaya da k'yar bayan ya daure yayi maganar dan hatta yawun bakin sa ya dauke da k'yar ya nemo shi, be taba samun kansa a irin wannan yanayin ba, shiyasa duk ya kasa controling kansa, wani irin heavy feeling yake ji gashi baya so a samu matsala. Da ka ta amsa masa sai ya zare jikin sa a kasalance ya tashi yana kin kallon ta, duk da dama idonta a rufe yake ita, ya dauki rigar sa ya zura ya shige toilet, mikewa tayi da k'yar ta yi kokarin gyara maballin bra din amma ta kasa, tayi tayi sai kawai ta hakura jin zai fito ta koma ta kwanta tana sake kudundunewa da bargon. Fitowa yayi yana goge kansa da ya jike da ruwa, yana daure da bathrobe alamun wanka yayi, ta k'asan idon ta, take kallon shi ya shafa man sa sai kawai ya zura jallabiya bayan ya fesa turare. Fuskar sa fayau sai dan idonsa da ya dan yi ja kad'an da kansa da yayi masa wani irin nauyi na ban mamaki. Gefen ta ya zauna ya sakar mata murmushi bayan ta bud'e idonta, ya dauki wayar sa yaga text din ban hakuri daga Dr Sufyan da missed calls dinsa, kiran sa yayi ringing daya ya daga yana bashi hakuri
"Ya hakuri captain, muna chan emergency unit wayar na batta anan Dr lounge."
"Ba komai, dama nasan kila kana busy ne, ya aikin?"
"Alhamdulillah wallahi."
"Masha Allah, dama madam ce ta samu dan targade a kafarta, shine kuma sai zazzabi though da ban sameka ba daga gida an turo irin masu gyaran gargajiya din nan, sai kuma zazzabi daga baya."
"Ayya Allah sarki, kaji tsautsayi, Allah ya bata lafiya, bari sai Dr Amina tazo ta duba ta, ina fatan dai ba aiki ka jikawa yar mutane ba, tsohon tuzuru."
Da sauri Tariq ya kalle ta, yaga ta rufe idon ta, amma yasan taji me Sufyan din yace, murmushi yayi kawai yace
"Sai dai tazo din, please tazo da wuri."
"Ok shikenan, ka duba ta please."
"In sha Allah, thank you."
"DM."
"Zaki yi wanka?" Ya tambaye ta bayan ya gama wayar. Da sauri ta girgiza kanta
"Ina jin sanyi har yanzu."
"Ok Dr Sufyan zai turo colleague dinsa ta duba ki, in sha Allah zaki ji dadin jikinki."
"Thank you."
"Shissh, get well soon kinji? Pleasee."
Gid'a masa kai tayi ya mike ya fice tabi bayan sa da kallo sannan ta sauke ajiyar zuciya.
Zama yayi a falon yana tunanin abinda ya faru a while ago, wani irin abu me kama da mayen karfe yaji yana fuzgarshi toward her, da ace kalou take yasan ba zai iya resisting ba, yanzu ma kawai managing kawai yake shiyasa ya fito ya barta dan zama waje dayan ba zai yi masa kyau ba, baya so ya kara mata akan wahalar da tasha da kuma wadda take ciki. Be taba tunani ko hasashen getting intimate with her ba sai yau, yau din ma yanzu amma duk da haka zai kara jira, zai jira right time din.
Ba'a fi 30min da wayar ba Dr Amina ta karaso gidan ta hanyar amfani da address din da Tariq din ya turawa Sufyan din, a waje ta tsaya ta kira number Tariq din ya mike daga zaman da yayi daidai lokacin Salma ta fito ya kalle ta yayi gaba dan shigowa da ita. Fuskar sa a sake ya wuce mata gaba zuwa ciki ya nuna mata kujera ta zauna yace zai kirawo Jiddan, Salma na labe sai ta fito ta zauna a falon suka gaisa da Dr Aminan.
Bacci ya sameta tana yi, ya rankwafa kanta ya dan taba ta a hankali, da yake baccin ba me nauyi bane sai ta bud'e idon ta,
"Dr Amina tazo, zaki iya tashi?"
"Eh." Ta daga kanta
"Ok let me help you." Ya mika mata hannu sai ta noke kafada tunowa da tayi bata da riga, kallon ta yayi sai ya tuna
"Ohh, tashi toh ki sa rigar zan jira ki a kofa." Ya juya mata bayan, tashi zaune tayi ta saka rigar a haka, ta tashi tana dosana kafar ta dauki Hijab ta saka ta taka a hankali ta same shi a tsaye,
"Sannu."
Yace yana kama hannun ta, suka fito hannun su sarke da juna. Hannun Salma ta kalla zuciyar ta, ta sosu taji kamar ta tashi ta ture Jiddan, da kansa ya taimaka mata ta zauna ya kuma zauna a gefen ta daf da ita har kusan rabin jikinta na nashi, murmushi Dr Amina tayi ta amsa gaisuwar Jiddan tace
"Sannu amarya."
Murmushi tayi shi kuma da tun fitowar su yaga Salma yace yana kallon ta
"Ki tashi ki bamu waje, we need some privacy."
"Eh?"
"Kinji ai, excuse please."
Tashi tayi wani kululun bakin ciki na tokare mata a makogwaro, ta wuce fuuu ya ja tsaki yana maida kallon sa kan Dr Amina din
"Dr I think targade tayi sai kuma fever."
"Garin Yaya amarya?"
"Zamewa nayi Dr."
"Bari na gani."
Hannun ta nuna mata da kafar ta dan taba hannun kad'an tace mata sannu sannan ta fito da magungunan da ta taho dasu ta mikawa Tariq din
"Dama Dr Sufyan ya fada min komai, so ga prescribe drugs din nan, sai kuma ko za'a dau jinin ta sai aje lab a yi mata Serum Pregnancy Test tunda yafi saurin nunawa."
Dauke wuta jidda tayi kunya na lullubeta, shi kansa kunyar yaji amma ya dake yace
"Bana jin Pregnancy issue ne."
"No ai sai an gwada za'a gane Captain."
"When last kika ga period dinki?"
"Na'am?"
"Feel free kinji? Yaushe?"
"Three weeks ago."
Tace tana hadiya yawu
"Ok, yaushe kike expecting nashi kuma?"
"Ending week d'in nan.".
"Okh Masha Allah, bari mu jira ko zaki missing period din tunda naga mijinki baya so ya taba masa lafiyar jikinki"
Dariya sukayi a tare, ya girgiza kansa
"Dr ba haka bane ba, kawai dai..."
"Shikenan ba damuwa ai, tasha wannan maganin ko ma da akwai pregnancy din ba zai effecting nasa ba, sai wannan da zata shafa Allah ya kara sauki."
"Amin thank you so much."
"Haba haba ba komai, Allah ya kara dankon soyayya."
Sai ta mike
*Bari na koma dan akwai patients sosai."
"Ok, zamuyi magana da Dr Sufyan din akan duk charges din, thank you once again."
"Ok, nagode sosai, amarya Allah ya kara sauki."
"Amin nagode." Tace ta rakata da ido har ta fice shi kuma ya zauna yana mata kallon k'asa-k'asa
"Amarya."
Yayi mimicking voice dinta, murmushi tayi masa wanda yake sake narkar dashi, ji yake zai iya fasa tafiyar baki daya yayi zaman sa a nan kawai dan baya son yayi nisa da ita ko nan da chan.
Mama ce ta kirashi a waya tace yazo tana son ganin sa, a dole ya fita ba dan yaso ba, ya barta tana bacci a daki ysa Amira ta dinga duba ta.
Da la'asar ta tashi sai taji dan dama-dama, ta fito falon ta samesu suna kallo Salma tayi wanka ta sha uwar kwalliya kamar wadda zata gasar kyau, kuma ba laifi tayi kyau sosai sai dai illa daya kitson attachment din dake kanta da ta zubo dashi gadon bayan ta. Ran Jidda ne ya sosu har taji kishi sosai a ranta amma ta danne dan duk yadda Mama taso ta ga gazawarta zatayi kokari wajen toshe ta. Daki ta koma bayan ta dan zauna kad'an taje ta hada ruwa me zafi ta gasa kafar da hannun sannan tayi wanka ta fito ta shirya cikin hadadden lace din da akayi musu ita da Ya Safiyya da Umaima, sosai ya zauna das a jikin ta ya fito da ainahin kyawun jikin, bata shafa komai a fuskar ta ba sai eye liner da lipstick kadai da ta saka, sai turare da ta fesa sannan ta dawo falon a lokacin Amira ce kawai Salman ta shiga ciki, gud'a Amira tayi ta saki duk da bata iya ba,hakan ya jawo hankalin Salmar