Showing 51001 words to 54000 words out of 120733 words

Chapter 18 - SANADIN-LABARINA BY HAFSAT RANO

04 Jul 2024

38901

dariya ya zauna ya gaida Yayan sannan Tariq ma ya gaishe ta da k'yar.

"Wai Yaya ya akayi ne ranar baki bani labarin jirgi ba, ya kika ji?"

"Jirgi ni Hajara, ai ban hau ba, su dai chan suka hau ni da Jidda muka bi hanya nan da nan muka isa mu ma."

"Baki hau jirgi ba Yaya? A ah ko dai bacci kikayi dai bayan kun shiga?"

"Da ido na biyu sarai ni banga an hau jirgi ba."

"Ah toh inaga hakan ne, toh shikenan."

"Yawwa." Tace tana gyara daurin kallabin ta

"Dama kawo miki shi nayi Yaya, gashi nan tunda Allah yayi ya dawo, sai a sanar dashi abinda yake faruwa ba sai an wani jira ko bata lokaci ba."

"Tabbas, tunda dai yarinyar nan dai tayi hakuri zaman jiran shekara guda ai ba wasa bane."

"Tariq..."

Baba ya kira sunan sa, gaban sa ne ya fadi, ya daure da k'yar ya amsa

"Na'am Baba."

"Masha Allah, toh magana ce guda daya zuwa biyu, na farko dai mun yi maka wani abun alkhairi duk da babu sanin ka, amma sanin cewa Tariq ba me bijire umarnin iyaye da magabatan sa bane, nasan ba zai taba wasa mana k'asa a ido ba, shiyasa har mukayi maka abinda mu muke ganin gata ne, muka aura maka kanwar ka Hauwa'u."

Shiru yayi kamar ruwa ya chinye shi, adam apple dinsa ya dinga motsawa yana yin sama da k'asa, haka yake a duk lokacin da ransa ya baci. Duk a tunani da halokokon sa ai auren ake shirin hadawa, kenan har an daura tsawon shekara daya kenan idan har kunnen sa ya ji masa daidai.

"Yarinya me hankali da nutsuwa, sam bata bijire mana ko kin bin umarnin mu ba, cikin saukin kai ta amsa mana."

Yaya ta dora tana kallon Tariq din da yayi tsam yana jin kamar an sassare masa kafafunsa.

"Muna fatan zakayi mana biyayya kamar yadda Hauwa'u tayi mana, in sha Allahu ba zakayi dana sanin karbar zabin mu ba."

"Nagode Baba, Allah ya kara girma."

Yace yana damke hannun sa. Fuskar Baban ce ta fadada da fara'a, ya shiga sakawa Tariq din albarka, Yaya tana amsawa. Da k'yar ya mike ya fito daga part din, yana fitowa yasa dukkan karfin sa ya bigi ginin wajen

"Damn it!" Ya fada yana yarfe hannu, gaba yayi kamar zai koma part din Mama, sai kuma ya dawo ya wuce gate ya zauna a wata kujera yana jin dama be dawo ba, yana zaune yaga fitowar Baba daga part din Yaya, sai ya tashi da sauri ya nufi part din ya shiga yana kumbura ya sameta ta cire riga sai daurin kirji alamun kwanciya zatayi

"Ya akayi?" Tace ganin ya tsaya daga kofa yana cika yana batsewa

"Bana son yarinyar nan, gwara ma a raba auren nan dan ba zan taba iya zaman aure da ita ba."

"Na'am? Kace me?"

"Bana son ta, bana son auren."

Matsowa kofar Yaya tayi tana kallon fuskar sa

"Ina jinka, baka so kace ko?"

"Eh, dan Allah Yaya, ki taimaka min."

"Tam, zan taimaka maka, amma ka bani sati uku ayi shagalin bikin nan a gama, ni nasan yadda zan bullowa al'amarin dan nima ba wai inason auren naku bane, tunda kuma kace baka so ai an gama."

Kallon ta yayi a cikin ido, ta gid'a masa kai alamar eh, ta gimtse fuska kamar gaske,

"Shikenan tom, dan Allah kiyi yadda zakiyi."

"Dole na, yanzu dai ka kwantar da hankalin kar Babanku yace baka masa biyayya ba, ka barmun komai a hannu na, Kaje yanzu ka huta ka kwanta."

"Nagode Yaya, nagode sosai."

"Karka damu yiwa kaine."

Tace tana dariya

Fita yayi ta bishi da harara sannan ta rufo kofar ta

"Ja'iri zaka yi bayani ne, idan ma aljanun suka zugo ka daidai nake da su wallahi."


Yana fita yaji zuciyar sa ta dan yi sanyi, maimakon ya wuce bangaren su sai ya juya zuwa part din Auntyn dan yana so yaje yaga yarinyar da tsaurin idonta har ya kai ta yarda a hada su aure, sai ya nuna mata iyakar ta, da matsayinta dan shi ba sa'an ta bane, tukunna ma nawa yarinyar take? Dole ya koya mata hankalin da zata je ta samu Baba da kanta tace ta fasa.
Knocking yayi a kofar da dan karfi, shiru ya sake kwankwasawa sai ya gwada turawa, ta bud'e ya shiga yana kallon falon da yake a share neat sai kamshin turaren wuta da yake tashi me sanyin kamshi, shak'ar turaren yayi ya kalli katotuwar television din dake tayi ita an kunna cartoon network. Aunty na part din Baba dan yau itace da gidan, shiyasa shirun yayi yawa masu aikin kuma duk sun wuce bq, tunawa da yayi da babu abinda yasa a cikin sa yasa shi tunawa da abincin da yaji kamshin sa dazu.
Tana tsaye a kitchen sanye da doguwar sakakkiyar rigar bacci me dan kauri, kanta babu ko dan kwali tana tsaye gaban microwave tana warming abincin da akayi dazun don shi wanda Fauwaz ne kawai yaci sai Aunty da masu aikin. Tun da ta dawo daga wajen su dazun aunty tace a kai masa sai ta doje tace baya nan sun fita, har magriba Aunty ta sake tambayar Fauwaz yace eh ya dan fita be dawo ba, har ta gaji tace a saka a fridge kawai ta tafi part din Baban.
Yunwa ce yanzu ma ta taso ta, bayan ta shaki kukan ta, ta koshi ta gode Allah, taji ciwo fiye da tunanin me tunani, amma ba zata taba bari ko Amira taga weakness dinta ba, dazu ma haka Fauwaz ya sake kiranta amma ta nuna masa babu komai, duk da deep down she's hurt, very hurt da ta kasa iya daukar abun, da kunnenta taji yana ikirarin ba zai so ta ba, tayi masa siranta da yawa, ba ajin sa bace. tabbas duk abinda ya fada haka ne, amma kuma zuciyar ta, ta k'asa karbar gaskiyaar yafi karfin nata, shiyasa har abun ya tsaya mata a ranta sosai.
Kashe microwave din tayi, ta dora abincin akan dan madaidacin tray ta saka ruwa da lemon kwakwar da duk shi akayi wa. Zuciyar ta ce ta sake karyewa tana kokarin daukar abincin, sai ta dora kanta akan kitchen cabinet din ta sake sakin kuka me cin rai.
Kitchen din ya nufo, da niyyar ya duba abincin ko zai samu, sai yaji kamar shasshekar kuka k'asa -kasa, da dan saurin sa ya karasa kofar, ya hangi bayan ta, kanta a duk'e tana fidda sautin kuka irin me taba ran duk me saurare. Gashin kanta idanun sa suka sauka akai, ya bud'e baki cike da mamakin tsawo da bakin sa, yana tsaye ta ware hannun ta, ta jawo tissue dake gefen daman ta, ya bi dogayen zarara-zararan hannayen nata da kallo, sun sha kunshi baki da ja me matukar kyau da daukar hankali abinka da farar mace. Yana nan a tsaye ta gama share fuskar ta, ta jefa tissue din a dustbin ta daga kanta sama tana kokarin maida ragowar kukan da yake taso mata, sannan ta sauke ta dauki tray din a hannun ta, ta juyo idanun ta suka shiga cikin nasa, yana tsaye a jingina da jikin kofar yana kallon ta, irin kallon wacece ke? Irin kallon da ya fara yi mata ranar da ya fara ganin ta. Duk da ya chanja yayi kiba da haske fatar sa ta murje, amma be sauya mata ba, shi din ne dai na ranar farkon nan, idanun sa a shanye kamar me jin bacci, kallo daya biyu tayi masa, sai kalaman sa suka shiga dawowa mata daya bayan daya, da sauri ta sauke kanta k'asa zuciyar ta na harbawa, da sauri da sauri, daga kafar ta, tayi daga wajen da take tsaye, tazo ta gifta ta gefen sa, har jikin ta na gogar nasa dan yadda ya cinye kusan fiye da rabin kofar. Juyowa yayi ya bita da kallo, har ta shige dan corridor din da zai kaita dakin ta, tana shiga tayi saurin dire tray din ta saka key a kofar, ta durkusa a wajen tana sakin kuka.




_INA MASOYA KUMA MA'ABOTA KAMSHI MA SU KAUNAR KAMSASAWA A KODA YAUSHE? DOMIN KAMSHI RAHAMA NE.._

_TO KU MATSO, DOMIN WANNAN KARON MA ZAFAFA BIYAR SUN ZO MU KU DA TALLAN MASARAUTAR KAMSHI NA KAMFANIN TURAREN *YERWA INCENSE AND MORE*_

_A *YERWA INCENSE AND MORE* ZA KU SAMU TURARUKAN WUTA NA *GIDAH, NA KAYA, NA TSUGUNNO* BA A NAN KADAI SUKA TSAYA BA. AKWAI *KHUMRAHS* MASU KAMSHIN LARABAWA DANA FRUITS KAI DAMA KAMSHIN TURAWA. AKWAI KHUMRAHS TA MATAN AURE DA TA YAMMATA_

_SANNAN SU NA DA *TURAREN WANKA DANA SHAFAWA BAYAN AN KAMMALA WANKA.* BA ANAN TURARUKAN NA SU SUKA TSAYA BA. AKWAI *KULACCAM* MAI MATUKAR KAMSHI DA SANYAYA ZUCIYA, SANNAN SU NA DA *MADARORIN TURARUKA NA JIKI DA NA KAYA*_

_AKWAI TURAREN *AL'AJABU NA TSUGUNNO DA KHUMRAH* DIN SA_

_SANNAN SU NA DA *TURAREN GASHI NA CREAM DA KUMA SPRAY DIN SA NA FESAWA*_

_BA ANAN SUKA TSAYA BA. SU NA DA *TURAREN MOPPING, DA NA BANDAKI AKWAI NA RUWAN WANKI DA NA FESAWA A DRAWER KO AKWATI*_

_AKWAI KAYAN GYARARRAKI NA FATA. KUJERAR TSUGUNNO, KASAKE NA WUTA, COAL IGNITER TA KUNNA GARWASHI, ELECTRIC BURNERS DA ENGLISH COAL_

_AKWAI LAFFAYAS DA SAURAN TURARUKA NA KAMSHI KALA KALA_

_SU NA BADA KAYAYYAKIN SU AKAN FARASHIN SARI KO SAYA AKAN DAYA DAYA. SANNAN SUNA TURA KAYAYYAKIN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE. KAYAN SU YAN CHADI NE DA SUDAN DA KUMA YERWA WATO MAIDUGURI._

_KYAU, INGANCI DA RAHUSA SAI KAYAYYAKIN KAMFAMIN YERWA INCENSE AND MORE. SAI KUN GWADA ZAKU BAMU LABARI_

_NAMBAR TARHON SU DA ZAA KIRA KO MUSU MAGANA TA WHATSAPP ITACE: 08095215215_

_INSTAGRAM HANDLE DIN SU: @yerwaincense_and_more_

_YERWA INCENSE AND MORE: A NUMBER ONE STOP SHOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS AND MORE_
[11/25, 3:54 PM] Rano2: _SL__**

      ©®*_*_Hafsat Rano_*_*

                  Page (26)



Tana tsaye a gaban mirror taji shigowar motocin alamun sun dawo, gaban ta ne ya fadi cikin ta yayi wata irin murdawa, ji tayi kamar tana bukatar shiga toilet amma tasan irin wannan yanayin ne da mutum yake tsintar kansa when he's nervous. Tafin hannun ta ne taji yana mata wani iri sai kuma tafi kafarta, samun waje tayi ta zauna da sauri tana sauke tagwayen ajiyar zuciya, ta dan dan mintuna a haka kafin ta tashi ta karasa shiryawa cikin sabon kayan ta riga da skirt, ta yafa madaidacin chantilly akan kayan nata, ta feshe jikin ta da turare me sanyin kamshi, wanda baya hawa ka.

***Kafafunsa ya zuro sanda suka iso cikin gidan nasu, idanun sa na kan gidan da yanayin tsarin gine-gine wanda yayi saurin banbance kowanne,.

"Ina wajen Mama?"

Yace bayan ya fito daga motar, da hannu Fauwaz ya nuna masa, yana kokarin bawa yaran dake harabar gidan masu kula da gyaran compound din da duk aiken gidan jakunkunan Tariq din dan kai mishi su part dinsu.

Takawa ya shiga yi zuwa part din Maman wanda tuni su Maryam sun isar mata da labarin isowar sa, tana tsaye a tsakiyar falon ya turo kofar ya shigo, ta saki baki ganin wani irin chanjawa da Tariq din yayi. Murmushi ya sakar mata yana karasa ciki da dan saurin sa, ya russuna ya gaida Maman bata san lokacin da ta rungume shi ba.

"Welcome home son, sannu da hanya."

Ta sake shi tana fada, sai kuma tace ya zauna, ya zauna bayan ya dan kalli falon. Gaishe ta ya sakeyi sannan sukayi maganar bayan rabuwa, ta saka aka kawo masa ruwa da juice yasha ruwan kawai tace sauran abincin suna chan a part dinsu aka jera masa, mikewa yayi yana zuwa hannun sa a cikin dogon wandon sa yace zai je ya huta zai shigo anjima. Har kofa ta raka shi cike da jin dadin ganin sa.
Yana fita suka hadu da Fauwaz ya gama shigar masa da kayan, ratayo kafadar sa yayi ya yi maganar a hankali

"Rakani na gaida Aunty, sai Yaya daga nan ina so na huta dan wani banzan transit mukayi a Ethiopia wanda yayi draining baki daya energy dina."

"Wai, matsalar kenan dama, ina zamu fara zuwa?"

"Wajen aunty, dan Yaya idan naje surutun ta nasan zai kara min ciwon kai, kaga ina fitowa sai naje na huta gaba daya."

"Allah ya dawo damu ai, kai da Yaya ai kamar Tom and Jerry, Jidda ce kawai daidai da ita ta iya lallaba ta wallahi."

"Jidda?" Ya kira sunan kamar me tunani, sai kuma yace

"Ohh, that slim girl?"

Dariya ya bawa Fauwaz,be bashi amsa ba saboda karasowa part din Auntyn da sukayi, suka shiga Fauwaz na gaba yana bin sa a baya yana nazarin part din shima, kamshin abinci ne ya daki hancin sa, irin kamshin da be taba jin irin sa ba, lumshe idon sa yayi ya bude sanda Auntyn ta fito fuskar ta cike da fara'a tana masa maraba, murmushi yayi ya amsa sannan suka dan taba hira, yace zai dawo ya mike sai kuma ya tsaya

"Aunty wannan kamshin abincin, inason naci"

"Naka ne ai, tunda dan kai Jidda tayi."

Shiru yayi kamar ruwa ya cinye shi, sai kuma ya kada kansa alamun ok, sannan yace

"Zamu ci dadi."

"Sosai, jiddah expect ce in dai girki ne."

Ya Fauwaz ya kara dan duk ya sake samun hanyar convincing dinsa. Gid'a kansa yayi, yace suje suka fita sai part din Yaya, wadda ta cika tayi fam dan tunda tasan sun shigo take zurara ido a hanya amma dan wulakanci sai yaje ya gaida uwarsa sannn zai zo wajen ta. Suna shigowa ta tsuke fuska kamar ba jiran shi take ba, kallon fuskar ta yayi sai ta bashi dariya ganin yadda tayi kicin kicin da fuska ita a dole tayi fushi, fushin da be san na menene ba.

"Ai da ma baka zo ba, tunda sai ka gama gaida iyayen ka zaka zo waje na."

"This woman and her wahala."

Yayi maganar a kasan makoshin sa, ya zauna a gefen kafarta yace

"Yi hakuri bazan kara ba."

"Dama ba laifi kayi ba..." Tace kunya kuma sai ta kama ta yadda tayi masa bayan dawowar sa kenan

"Mun same ku lafiya?"

"Alhamdulillah, Allah ya kaddara saduwar mu, na zata fa da sai mun mutu zaka zo taaziyya."

"A ah, ban isa ba." Yace yana murmushi

"Ikon Allah, ashe dama kana murmushi, dama dan uwanka yana murmushi kai." Ta kalli Fauwaz tana rike haba

"Dariya ma har da kyalkyalawa."

"Ah lallai magani yayi aiki, dole na kira Malam na sake godiya, ya kuma sake aiko maka da wani rubutun."

"Ai naji dadin maganin nan Yaya, nagode sosai."

Yace yana biye mata dan ya gano da dadewa wahalar da kansa kawai yayi da ya kasa fuskantar halin Yayan

"Ba komai ai yiwa kai ne, ka dai samu daddad'an labarin bikin ka wajen ita uwar taku ko?"

"Biki? Wanne biki Yaya?"

"Bari Yaya zan masa bayani kinji?"

"Wanne biki ake magana Fauwaz?"

"Muje part din mu, muyi magana."

"Ok." Yace a sanyaye, ya tashi suka fita, ita dai Yaya ko a jikinta, murnar ta kawai take tasan kuma duk tsiyar Tariq din ba zai taba kin jiddaa ba.

Suna shiga part din nasu Fauwaz yayi wa Jidda text wadda take rufe a daki tun shigowar su wajen Auntyn har suka fita, tana jiyo echo din muryoyin su amma ta kasa fitowa

"Kawo ruwa part dinmu jiddah." Ta karanta text din, sai ta mike tana sake kallon kanta a mudubi, kafin ta fito ta shiga kitchen ta dora ruwa akan tray tare da cup ta fita zuwa part din su Fauwaz din.

Ransa ne yayi kololowar tun kafin ma Fauwaz ya gama maganar, ya dakatar dashi ba tare da ya gama fahimtar abinda ma yake nufi ba, abu daya kawai ya tsaya ya fuskanta shine ana so a hada shi aure da figaggiiyar yarinyar nan jidda, be ma ji karshen bayanin ba, bare yaji har ma an daura musu auren shekara daya kenan. Hannu yasa ya dakatar da Fauwaz din ta hanyar cewa

"Ya isa!!!"


“Ya Tariq amma…” Fauwaz yace zai cigaba da bayanin

“Look fauwaz, ba zan iya auran yarinyar nan ba, tayi min kankanta da yawa, plus bata cikin spec dina gaskiya. Bana so mace ta cika siranta da yawa, plus she’s young. Very very young da rainon ta zanji ko da aiki na!?”

“I know, amma when last kaga Jidda? When last ka ganta face-to-face?”

“Ba zan iya tunawa ba, infact na manta kamar ta ma baki daya ni. So it’s better kaje ka sanar da Yayah, ba zan iya ba gaskiya, gobe goben nan zan koma in da na fito, daga dawowata? Haba!”

“Calm down and give it a second thought, karka yanke shawara base on abinda ka sani a baya, jiddan da ka sani shekara biyar baya ba itace wannan Jiddan ba! Ka daure ka ganta.”

“Fauwaz!”

Sai ya mike tsaye

“Kana bata bakin kane kawai, ba zan iya ba gaskiya, ba zan daukar ma kaina abinda na san ba zan taba iyawa ba.”

Mikewa shima yayi, yana girgiza masa kai, zai yi magana ya daga masa hannu

“Bana son sake jin komai. Ya isa haka nan, ba zan taba iya soyayya da ita ba, bare har ta kai ga maganar aure! Never!!!


****Tray din ruwan da yake hannun ta ne yake neman subucewa, tayi saurin rike shi hawaye na saukowa a kuncin ta, ya zatayi da auren sa da yake kanta? Ya zatayi da rayuwar ta yanzu kenan? Innalillah wa inna ilaihi raji’un. Ta shiga maimaitawa. Takun takalmin sa ne ya iske ta, tayi saurin matsawa jikin dan corridor din dake jikin dakin ta makale, fuskar sa a hade take tsaf, yana cikin shigar farar tshirt wuyan sa sakale da necktie navy blue sai dogon wandon chinos dake sanya a jikin sa. Dogo ne sambal, kuma giant na ajin karshe, zuwa yayi ya wuce ta, ba tare da ya lura da ita ba, tana jin kiran da Ya Fauwaz yake kwala masa amma yayi biris kamar be ji ba. Ya wuce kansa a gaba cikin yanayin da ta kasa hange ko hasashen sa. Ji tayi tamkar kafarta ba zata iya daukar ta ba, duniyar na juya mata, shekara guda kenan tana dauke da igiyar auren sa, igiyar da ta raba ta isma’il me tsananin son ta da kaunar ta, ta zabi zaman dakon jiran shi, duk da bata da yakinin abinda zata tarar daga gareshi. Zuciyarta tayi nisa a kaunar sa wanda har take jin bata da wani katabus idan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login