Showing 39001 words to 42000 words out of 120733 words

Chapter 14 - SANADIN-LABARINA BY HAFSAT RANO

04 Jul 2024

38893

ya koma,sai dai kuma bayan da ta fita ranar ta dawo sai ta sake ganin sauyi sosai a tattare da ita dan hatta kuzarin ta sai da ya ragu, gashi bata ce mata komai ba balle tasan abinda yake damun ta.
Knocking akayi a kofar, suka kalli juna ita da Aunty kafin ta tashi ta bud'e kofar,

"Hajiya tayi bako."

Sai ya juya Isma'il dake tsaye a bayan sa tun farko ya bayyana a gaban ta, da sauri ta janye kanta daga kofar cikin tafiyar sauri-sauri ta wuce falon zuwa bedroom dinta dan dan siririn mayafi ya saka ta yane kanta, jikinta sanye da riga me gajeren hannu da skirt. Tashi Aunty tayi ganin mutum a tsaye sai duk kunya ta kamata tace ya shigo ciki,ya shigo jikin sa a sanyaye, ya zauna sannan ya gaida Auntyn cike da girmamawa, ta amsa ranta duk babu dadi dan har ga Allah bata so Jidda ta rasa miji kamar Isma'il.

"Bari a kawo maka ruwa." Tace tana neman hanyar barin falon, dakatar da ita yayi ta hanyar cewa

"Aunty dan Allah a bar ruwan nan a koshe nake wallahi."

"Toh shikenan, ina zuwa."

Sai tabi bayan Jiddan, zuwa dakin Jiddan ta sameta a zaune a saman drawer ta zurma Hijab har k'asa fuskar ta babu fara'a ko kad'an, kallon ta Aunty tayi da ta gama gano bata son Isma'il din tun ranar farko tace

"Kije kuyi magana, dan Allah ki saki ranki, Usman zaizo ya zauna."

Dan sakin fuskar tayi, tayi gaba har ta fita Aunty ta kirata

"Kina ji? Baka wulakanta mutum ko baka sansa Jiddah,kokari za'a yi a rabu lafiya, duk tsiya mutumin da yace yana son ka ai ya gama maka komai a duniya , kuma be kamata ya zama makiyi a wajen ka ba."

Kara sakin fuskar tayi ta gid'a wa Aunty kai sannan tafita, maimakon ta tsaya a falon sai ta wuce shi ta fice ko kallon sa batayi ba, sai da taje ta riko hannun Usman sannan ta dawo falon, ta zaunar dashi a gefen ta, kanta a kasa ta gaishe shi,

"Lafiya lou." Yace duk ya gama tsorata da yanayin ta. Shiru tayi tana taba botir din jikin rigar Usman, har lokacin bata yarda ya dago ba bare har su hada ido, kamar wanda aka tsoma a cikin ruwan zafi haka yake jin sa, ga wata iriyar fargaba da faduwar gaba, shi be taba samun kansa a irin wannan yanayin ba, baya iya komai sai tunanin ta, haka duk abinda yake ita yake gani, amma kuma zuciyar sa ta soma karaya ganin irin tarbar da ya samu daga wajen Jiddan a yau bayan ba haka ya santa ba

"Jidda, maganar ranar nan ce tasa na sake dawowa, kinga ba zan hanaki karatun ki kawai dai inason a san dani ne, you can take all the time you want, ba zan taba magana ba, zan jira ki shiga university, idan ma har sai kin gama ne fine, zan iya jira."

Banza tayi masa dan bata tsinci komai a maganganun sa ba, ita ba dan karatun ta, take kin sa ba, shi so halitta ne, haka kawai taji bata son shi so na soyayya, tana dai respecting dinsa a matsayin shi na Yayan Safeera.

"Jidda baki ce komai ba, dan Allah say something, my heart is beating so fast, ba zan iya jure shirun ki ba, just say yes, ba zan sake takura miki ba, zan baki duk lokacin da kike so."

Dagowa tayi, tayi masa kallon cikin ido, sai kawai shaidan ya hasaso mata shi da wani irin zumemen kai, wanda bata taba gani ba sai ranar, sauke kanta tayi da sauri ta hau girgiza kanta hawaye na biyo kuncin ta

"Kayi hakuri ni dai."

"Dan Allah Jiddah, ki taimaka min wallahi zan miki duk abinda kike so, idan ma bakya so na dinga miki magana zan daina, ni dai kar kice min a ah dan Allah."

Cigaba da girgiza kanta ta dinga yi dan bata jin zata iya zaman aure inuwa daya dashi, be mata ba ko kad'an..ita kanta mamakin kanta take dan tasan idan banda fuskar ta da take da wani irin sihirtaccen kyau babu abinda zata nunawa Isma'il da har zata ki shi saboda shi.

Kamar zai jamo kasa haka yayi, rabin jikin sa baya kan kujerar saboda tsabar dimuwar da ya shiga,

“Ina son ki Jiddah, ina son ki fiye da yadda nake son kai na, dan Allah ki ceci rayuwata ki so ni ko da kwatan son da nake miki ne.” Ya furta bakin sa ararrabe yana rawa, shafe idanun ta, tayi da toka ta mike ta sungumi Usman tace

“Kayi hakuri Ya Isma’il, ba zan iya ba, ba zan iya ba.” sai tayi gaba da sauri har da dan hadawa da gudun ta, daga muryar sa wadda take rawa yayi yace

“Shikenan Jidda, shikenan sai watarana!”

Amsa kuwwa karshen kalamen sa suka dinga mata a kunne, har ta dangana da bedroom dinta, in da ta bar aunty a zaune rike da wayarta tana kallon hotunan Tariq da suka kusa cinye dukkan gallery din, a yanayin da Jiddan ta shigo ya sakata dire wayar ta fita da sauri. Kansa a k'asa ya dora shi akan tafukan hannayen sa ta same shi, kiran sunan sa tayi a dan tsorace, ya dago idanun sa da suka rine sukayi masifar ja

"Subhanallahi, Isma'il." Aunty tace ganin yadda idanun suka kad'a sukayi ja

"Aunty Jidda bata so na, Jidda bata so na." Ya fada kamar wani zararre, sai ya mike yayi hanyar fita daga falon da sauri, Aunty ta kira shi amma yaki tsayawa, ya dinga sassarfa har ya dangana da wajen da yayi parking motar sa, ya shiga sai ya kasa kunna ta, hannun sa na wani irin kakkarwa, key din ne yafadi kasa, sai kawai ya kifa kansa akan sitiyarin motar yana jin wani irin makaki a makogwaron sa. He's shattered, be san ya zai yi ba, be san yadda ta ina zai fara ba, da kyar ya lalubo wayar sa, ya kira Farouk yace yazo ya tafi dashi, cikin kankanin lokaci yazo Nabil ya kawo shi, taimakawa Isma'il din sukayi ya koma baya ya zauna yana rintsa idanun sa da suke masa masifar zafi da zugi. Farouk ne ya ja motar Nabil ya bisu a baya.

Washegari Baba yazo Kano, tare da wasu ministoci su uku, gaisuwa suka je sukayi sannan suka je wani kauye chan da aka samu matsalar bandits suka duba su suka kai musu tallafi, hanya ce ta biyo dasu ta garin su jiddah sai kawai Baba yace su tsaya garin su duba su. Baffa be san da zuwan su ba, dawowar sa kenan daga gona ana ta kokarin nome amfanin gona, wanka yayi ya chanja kayan jikin sa sababbi kasancewar juma'a ce yaje masallaci yayi sallah ya dawo ya zauna kofar gidan, kamar daga sama yaga motoci na nufo shi, ya tashi da sauri sanin waye yazo, dan tunda Baba ya samu mukamin nan be samu shigowa ba sai dai yana yawan waya da Baffan kuma yana masa aike akai akai dan hatta gidan sa an gyara masa shi sosai, ga kuma shago babba da Baban ya bude masa a chan kasuwa yana saida kayayyaki nan da nan yayi fes dashi kamar bashi ba. Dama iya Lami tunda taga ya dawo daidai ta daina rashin mutuncin ta dan tasan ba kamar da bane da tayi masa zai auna ta gaba, duk da haka bakin halin nata yana nan shi ma kuma ya sani sarai kawai yana rabuwa da ita ne.
Tun kafin motacin su ta tsaya DSS din suka dire kowannen su fuskar nan a tamke, jama'ar gari da suka soma tururuwar zuwa gani su duk suka lallabe daga baya dan dama labari ya karade ko ina sai gashi kuma sun gani da idanun su.
Dukkannin su mutane ne masu cike da kamala tamkar Baban, tarar su Baffa yayi cikin tsananin farin ciki gami da mamakin ganin su, suka gaisa a mutunce sannan yayi saurin shiga gida ya dauko babbar tabarma ya shinfida musu daga gaban gidan, suka zazzauna su kuma securities din suka tsaya daga gefe.

"Alhaji sannun ku da hanya, wallahi ban yi tunanin zuwan ku ba,nayi mamaki matuka wallahi."

"Hanya ce ta biyo damu Yaya, duk da dama lahadin nan na sa rai zamuzo da Alhaji Adamu da Malam Nura, sai kuma naga kawai tunda muna kusa mu karaso kawai."

"Masha Allah, nagode nagode Allah ya saka da Alkhairi."

"Amin Yaya, mun zo ne gaisuwa da kuma rokon iri, idan babu damuwa."

Da sauri Baffa ya katse shi

"Kar muyi haka da kai Alhaji, idan har akan maganar da Halima tazo min da ita ne akan Jiddah, toh babu ni a cikin wannan harkar, kaine mahaifin Jiddah bani ba, dan haka ba zaa tambaye ni amincewa ta akan Jiddah ba."

"Yaya ba haka bane ,wai dama kaga..."

"Alhaji kayi hakuri, amma kai ne mahaifin Jiddah, duk abinda ka yanke akan ta daidai ne."

"Duk da haka da ka saurari honourable muji me zai ce."

Daya daga ciki yayi maganar yana yabawa da dattakon Baffan

"Toh ina jinku Alhaji, ni dai idan har akan maganar auren jidda ne da yayanta toh wallahi na amince, na bashi duniya da lahira, idan a shirye kuke ga mahaifin jidda nan a zaune (Ya nuna Baba) ku bashi sadakin Jidda a hannun shi, zan kira makwaftana tunda duk yan uwana basa raye a daura auren nan kafin ku bar wajen nan "

"Yaya babu takura kuwa hakan?"

"Babu ko daya Alhaji, idan ma har na bari kuka bar nan bamu gama magana ba ai anyi ba'a yi ba kenan bari Kuga."

Sai ya mike ya zagaya bayan gidan, jim kadan sai gashi da mutane dattawa su shida, ya shiga yakaro wasu tabarmin sannan ya gabatar dasu a matsayin shaidu. Ba karamin mamaki su Baba sukayi ba, nan da nan cikin kankanin lokaci aka gabatar da komai, aka daura auren MUHAMMAD TARIQ NASIRUDDEEN DA HAUWA'U IBRAHIM JIMO, akan sadaki naira dubu dari.
[11/25, 3:54 PM] Rano2: _SL__**

      ©®*_*_Hafsat Rano_*_*

                  Page (21)

***Alawa da goro aka raba sannan daya daga cikinsu yayi rabon kudi sosai, sannan suka bawa Baffa kudi masu dan kauri kafin suyi sallama su tafi, nan da nan labarin ya zagaye dukka kauyan. Zuciyar Baffa cike take da farin ciki mara misaltuwa, ya rasa in da zai tsoma kansa dan murna..Allah ya dube shi ya dubi maraicin Jidda yayi musu sauyi rayuwar da basu taba hasashe ba.
Da magribar fari Baba ya shigo gidan, yadda yake cike da farin cikin abinda ya faru ba zai bari har sai Yaya tayi bacci ba sannan ya shigo gidan,shiyasa ya rage schedules dinsa ya barwa gobe. Dukkan lissafin YAYA akan wannan lahadin ne, Allah Allah tayi, satin ya zagayo amma sai ta ga yayi nisa sosai, gashi bata son a samu matsala komai kankantar ta, shiyasa take cike da wasi-wasin jiran zagayowar ranar.
Idar da sallah magriba kenan da tayi, ta mike kafafunta da suke dan mata ciwo akan abun sallar, tana rike da tasbah tana ja lokaci zuwa lokaci tana daga kai ta kalli cikin dakin nata kamar me neman wani abu. Sallamar Baba ya sakata katse abinda take ta mike da dan saurin ta, ta fito falon tana son ta tabbatar shi d'in ne ko kuma dai muryar sa ce take mata gizo, shi din ne kuwa,nan da nan ta hau murnar ganin sa kamar wannan ne zuwan sa na farko wajenta saboda tsabar yadda ta cika da farin cikin ganin sa, tasan zai iya fasa zuwa wannan satin idan wani abun ya taso masa shiyasa take ta Allah Allah yazo.

"Yaya irin wannan farin cikin duk na gani na ne?"

Yace bayan sun gaisa ta kawo masa ruwa kamr ko da yaushe

"Eh da murnar ganin naka ma, da kuma murnar na gama cire rai ba zaka zo wannan satin ba, kasan kuma alkawarin mu."

"Yaya baki manta ba?"

"Na manta kace? Tab!"

"Toh Yaya albishirin ki."

"Goro, fari kal kal."

Ledar dake cike da goro da alawa ya mika mata gabanta, taja ta bud'e tana leka ciki

"Me muka samu?"

Ganin alawa da goro yasa ta kalli Baban da sauri

"Ba dai aure kayi ba?"

Darya ta bashi, yayi murmushi yace

" A ah Yaya, goron auren Jiddah ne da Tariq."

"Dan Allah! Kai kai kai kai Masha Allah, Masha Allahu, da gaske kake wai?"

"Da gaske Yaya, mahaifin Jiddah mutumin kwarai ne,wallahi hanya ce ta bi damu, sai na gabatar masa da maganar,anan yayi tsalle ya dire sai dai ayi komai a gama, kuma fafur yace shi bazai karbi sadakin Jidda ba dan nine mahaifin ta, naji dadi kwarai da karramawar da yayi min, su kansu wadanda muka je tare tunda muka dauko hanya suke yaba masa."

"Kai Alhamdulillahi, Abu kamar almara?"

"Wallahi Yaya, kinga dai abinda Allah ya tsara, ko jiddan ba'a fara tuntuba da maganar ba, Allah yasa kar taga rashin kyautawarmu."

"Ba dai Jidda ba, na gamsu da tarbiyyar ta, ko ma zaa bijire sai dai wanchan sahoramin, shima kuma be isa ba."

"Haka ne."

"Allah ubangiji ya saka muku da gidan aljanna, ka gama min komai a duniyar nan, Allah ya kare ka daga sharrin makiya, ya sa 'yayanka kai ma su rama maka, naji dadi nagode nagode."

Sai ta fashe da kuka, kukan da ya saka Baba mikewa dan sarai yasan halin Yaya, yanzu sai ta rikice musu,

"Amin Yaya, Amin Amin."

Sai ya fice dan yana jin kukan nata har ya fara sauya salo, duk da kukan farin ciki ne amma yasan tsaf zata birkice tayi tayi tana farfado abubuwan da suka faru da irin fadi tashin da tayi dasu suna kanana musamman shi da zai iya cewa itace koman sa a rayuwa, ita ta tsaya masa har yayi karatun da a yanzu yake alfahari dashi.

Waya yayan ta dauka bayan ta ajiye kayan a gefe, ta dinga dannawa tana kiran duk wanda hannun ta yazo kan number sa, tunda ita ba iya karatun tayi ba bare ta gane sunan waye, idan ka daga taji ba kai take nema ba sai kawai ta katse, haka tayi ta kira har tazo kan number Mama da tunda aka saka mata number ba su taba waya da ita ba,kowa dai yana da ta kowa ita Yaya Safwan ne ya saka mata a wayar. Mama na zaune bayan sun fito hutu daga wani taro na matan ministoci, suna zaune a wajen da aka tanadar domin hutawar su, suci abinci da sallah. Da la'asar aka fara taron da magriba tayi sai aka tafi hutun minti talatin sai a sake komawa zuwa isha a tashi. Hajiya huwaila ce a gefenta dama tunda tazo Abuja da ita suka fi sabawa sosai. wayarta ce ta shiga vibrating, ta ciro ta daga yar madaidaciyar jakarta, cike da mamaki take kallon number Yaya, dan bata taba kiran ta ba, bata kuma san akan dalilin da zai saka Yayan kiran ta ba sai dai idan tabbas ba lafiya, tashi tayi da dan saurin ta, ta fita daga wajen sannan ta daga kira

"Assalamu alaikum."

Kallon wayar Yaya tayi jin muryar ta, har zata kashe sai kuma taga ai ita tafi kowa chanchanta da taji wannan labarin, sai kawai ta amsa gaisuwar da take mata

"Lafiya lou, ya yaran?"

"Lafiya lou."

"Kowa lafiya dai ko?"

"Lafiya Alhamdulillah."

"Toh Masha Allahu, kin samu labarin abun farin cikin da ya same mu ko?"

" A ah Yaya, me ya faru?"

" Batun auren Tariq da Jiddah mana, Alhaji be fada miki ba? Duk da dai ni dashi kadai mukayi maganar na kuma hane shi ko Tariq din kar ya soma fadawa har sai yazo da kafafun sa."

Wata irin zufa ce ta shiga karyowa Mama, ta dinga jin kamar kunnenta be ji mata daidai ba, ta kasa bude baki bare ta amsa duk bayanin da Yayan take mata. Daina gane komai tayi har Yayan ta gama jawabin ta, ta kashe wayar. Wata kujera ce a gefen wajen ta karasa da sauri wajen ta zauna duk ta rikice "Auren Tariq da wannan figalalliyar yarinyar nan? Sannan a rasa wanda zai nemi shawarar ta? d'an ta data haifa a cikin ta, a rasa wanda zai nemi shawarta saboda tsabar karfin hali da nuna iko. Sai yau ta kara tabbatar wa Yaya bata son ta, haka kuma bata son yayan da ta haifa, dan idan har tana son Tariq ba zata taba masa irin wannan auren ba, kamar wani karamin yaro ace har Tariq zaa iya irin wannan auren? Lallai duk wanda ya shirya wannan be so zaman lafiya ba, ko waye kuwa. Tsanar aunty ce ta kara karuwa sosai a zuciyar ta, dan tasan tabbas da saka hannun ta aka kakabawa Tariq munafukar yarinyar me zubin yunwa. Tunanin ta ne ya kawo mata wayar da taji Baban nayi da Tariq, wato dama abinda yake nufi kenan, shine suka boye mata dan kar ta hana, lallai kuwa dole ne ta nunawa Baban itama tana da iko akan Tariq dan ba shi kadai ya haife shi ba. Kasa zama tayi a karasa event din, ta fice bayan ta nemi ayi mata afuwa saboda tasowar wani babban al'amari.
Tun a hanya take jerawa Baban kira amma be dauka ba, kira ta cigaba da yi dan bata jin idan har be dauki wayar ta ba zata iya zama bata je ta same shi ba. Har ta karasa gidan be dauka ba, ta shiga yaran duk suka tashi suna kallon yanayin ta, zare dankwalin kanta tayi ta jefar da jakar hannun ta da Amira take shirin karba,

"Wallahi ba zai yiwu ba, ni za'a cutar saboda an ga sanda Muhammad ya mutu nayi hakuri, shine yanzu saboda tsabar wulakanci za'a yiwa Tariq irin wannan wulakantaccen auren, wallahi ba zai yiwu ba."

"Mama please calm down, menene ya faru?"

Safiyya tace tana rike hannun Maman, ta taimaka mata ta zauna a daya daga cikin kujerun falon, Maryam tayi sauri ta kawo mata ruwa ta zuba mata a cup ta mika mata, tasha kad'an ta ture ranta idan yayi dubu ya baci, ba dan dare ba a yau zata dira Kano wallahi, amma duk da haka da asubah zata dirar musu wannan karon ba zata kyale ba.

"Dan Allah Mama me faru? Wanne irin aure akayi ma Ya Tariq din?"

"Wai yanzu Safiyya ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login