Showing 51001 words to 54000 words out of 55418 words

Chapter 18 - HAMSHAƘIYAR-UWA 2

04 Jul 2024

6745

Tace "Babban abinda ya fi komai ?aga min hankali shine inga Shamaki a damuwa, ina yin kowane irin abu dan in samar masa da kwanciyar hankali aurenki misali ne." Na yi shiru, ina tunani Hajiya tana yi wa ?anta makauniyar soyayya wadda ta sa sam bata iya hango matsala. Na dube ta, zan yi iya yi na inga bai shiga cikin wata damuwa ba daga yau. Na?aga yatsa kamar mai ?aukar al?awari. Bata ce ?ala ba ta ?aga waya ta kirashi,ya zo ya zauna yana satar kallo na. Tace "Shamaki matar ka ta dage akan babu komai da ka yi mata, sai dai ina mai baka shawara ka yi ?o?ari ka gyara abinda ka ?ata a idanunta. Ya kalle ni, na yi ?an murmushi ka yi hakuri da yanayin da na saka ka a ciki. Shi dai idanu ya zuba min yana kallona. Anisa ta shigo ta nufi gurin Hajiya da littafi a hannu ta gaisheta sannan ta gaida Dadynsu,sai ta dube ni Momy ina kwana, ta zauna kan cinya ta,tace Momy Anty Azima bata yi min Homework ba. Na amshi littafin ina dubawa, nace to zo muje gefe mu yi. Na koya mata Rahin ta zo ta tafi da ita domin yi mata shirin makaranta. Na dubi Hajiya suna magana ?asa ?asa da Shamaki nace zan dawo kafin su Juma su ha?a abin karyawa.

Lokacin da ya shigo domin shirin tafiya kasuwa ina gyaran gadon shi, ya tsaya ya har?e hannayen shi yana kallo na, na ce akwai wani abu ne? Ya girgiza kai sannan ya shige ban?aki.
Na fito masa da kaya kamar yadda na saba ya shirya tsaf na ?auki jakarsa na rataya a kafa?a. Ya janyo ni zuwa jikinsa ya rungume ya sa hannuwan shi guda biyu ya ?ago fuskata ido cikin ido muke kallon juna, yace "Baby yanzu bazaki fa?a min.. Nasa tafin hannu na narufe mishi baki tare da fa?in shissss ya wuce babban ba?o. Muje ka tafi Allah ya tsare gabanka da bayan ka. Yace kimin al?awarin cewa bazaki yi kuka ba." Nace bazan yi ba. Ya sunbaci goshina sannan muka tafi tare.

Cikin satin na zama cikin taka tsantsan kuma na duba wayar shi naga 'yan mata sun masa magana amma duk bai bada amsa ba. Babu da?in ganin haka tabbas an ?an samu ci gaba domin hakan da ma ya taimaka inda na tada bala'i da sai ya tada borin kunya ya yi bala'i kuma ya murje harma ya ke min gadara a gabana sai ya yi wayar shi tunda ya lura bazan iya komai ba.
Matar Abokin shi Alhaji Shamsu ta haihu , yace in shirya da dare zamuje barka. A gaban Hajiya ya yi maganar na ji da?i domin ina son muna ?an fita da shi. Hajiya tace ka je kai ka?ai ita kuma anjima ta shirya direba ya kaita ka bata abin barka. In kuma taron suna zata je shikenan sai ta bari sai ranar. Ya kalle ni kamar yana son yaga yadda zanyi tunda yasan ina son mu fita da shi na sha fa?a masa cewa ina son mu ?an fita ko a ?afa ne, sai ya ce inyi hakuri in ya samu lokaci ?asar waje ma zamu fita.

Washe gari ya bani zannuwa biyu da dubu goma ya ce inje barka shi baya son zuwa suna ?in nan. Nace to. Na sanar da Hajiya tace to in shirya baya azahar.
Mace mai fara'a maman Haidar wai takwara aka yi wa Shamaki, nace a lallai ki ce ni aka yi wa haihuwar amma bai fa?a min ba. Tace ai bai fa?a masa ba sai ranar zaiji. Nace to ki ce in zuge baki na. Tace gaskiya kam. Da tare zamu zo sai kuma yana da uzri. Tace "Ko kuma Hajiya ta hana ba." Nace Ya zata hana mu fita tare, cikin mamakin yadda aka yi ta san maganar na yi tambayar. Tace "Ba gulma ba amma ko zuwanki na sha mamaki, duk matan Shamaki sai dai su saci hanya su ziyarci mutane, bata son su yi hul?a da kowa, shiyasa ki ka ga ko gurinki ban zo ba." Na gyara zama domin jin kanun labarai. Nace to ko domin ni ban jima bane shiyasa bata fara min ba? Tace "?ila dai ?an ke yarinya ce ?arama shiyasa bakya ganewa. Shekara ?aya na cika ta ke sa shi ya saki mace tace wai bata ci jarabawa ba,ko uban me ta ke jarabtawa oho mata." Nace ce duk bansan wannan ba,ke ya 'aka yi kika sani? Tace "Tsoro na ke kar magana ta fito." Nace sai dai in ke ki ka fa?a amma ni bana haka kamar kin ha?a rami kin saka.
Tace "Ai Kinsan Maman Anisa ?awata ce munyi makaranta a gurin bikina suka ha?u da Shamaki suka yi aure, kar ki ga irin son da suke yi wa juna amma shekara na cika ta sa ya sake ta. Har yanzu suna son juna kuma tace min kuma zasu iya maida auren su." Gabana ya fa?i amma sai na saki murmushi nace ya fa?a min ai baya ?oye min komai, ta ce "Haba dai." Nace ?warai kuwa. Tace Kenan har irin zaman su da maman Mubina da Meema?" Nace kina shakka ne? Tace "A 'a Naga ita Maman Anisa bai ta?a fa?a mata komai game da su ba." Nace Kinsan so kala kala ne ni komai na shi na sani. Tace ni Uwar gidana sun saba da Maman Meema sun zama ?awaye tunda matan abokai ne,to ita ke ba uwargidana labarin zaman su shine ta ke bani." Nace dama ku biyu ne? Tace e uwargidana anjima nan zaki ganta tunda muna zama lafiya. " Nace yafi muku sau?i yaushe zaka tsaya fitina akan namiji? Tace ashe kin gane ga mazan nan namu masu neman matan tsiya kuna nan kuna fa?a wasu na can na faranta musu. Na ce ai kuwa Allah dai ya shirye su. Ta sake kallo na da taji bance komai ba. "Ashe kinsan suna neman mata?" Nayi "yar dariya akwai wani da zaka sheda ne yanzu a maza? Ta ta?a baki tace babu. Amma ya fa?a miki har yanzu suna fita da maman Anisa?" Na yi shiru da alamu matar nan so take ta hasala ni kuma kamar aike. Nace duk na sani, nifa da kika ganni duk wadda ta zubda kanta ta bashi ya bi ya tsallake ruwanta. Ta bu?e baki cikin mamaki, tace "Kin ?aure mishi gindi kenan? Nace To Maman Haidar ina son mijina ya yi abinda ya ke so. Tace "Yanzu na gane abinda ya sa Hajiya bata nuna muku mugun halinta ba. Ita ke ?aure mishi gindi yake bin mata." Nace To shi Mijinki wa ya ?aure mishi nashi gindin? Ta saki dariya gaskiya kullum muna ?orafi muna masa addu'a. Nace to ya bari? Tace ya dai rage da har a gabanmu yake waya da 'yan matan shi, sai da muka tada balli. Shine yake yi a ?akin shi .
Sallamar wasu mata muka ji ta amsa ta le?o sai naji tana fa?in a kamar ha?in baki ga Maman Anisa da Maman Meema. Gabana ya yanke ya yi wata muguwar fa?uwa.
????????
?Na dake domin na gane duk yadda aka yi kiran su ta yi a waya,ko ta tura musu message tun da na lura wayar ta tana hannun ta tunda na zo, amma dai banga ta yi waya ba. Muka bi juna da kallo ni da su, lokacin da suka zauna, na gane Naman Anisa domin suna da kamanni, na kalli. Wadda nake zaton ita ce uwargidan maijego ta ce "Amarsu ce aka zo mana Barka?" Na bi ta da kallo ban amsa ba. Wadda na ke zaton Maman Meema ce tace "Amaryar ma?" Wai a zuwan bata sani ba. Mai jego ta amshe da sauri ta ce "Amaryar Shamaki mana." Maman Anisa ta zaro ido, Tare Da fa?in Shamak dai "Dama ke ce Amaryar Allah sarki, har kin bani tausayi ta yatsina baki, gata yarinya wannan tafi sha biyar ma, kai Allah sarki ya zaman ?aki? Har yanzu kwanciya bata gundire ki ba.? Kin lura dai gidan Zeena akwai na'ura ki bi a hankali. Ta ci gaba.
"Yawwa ki lura da su Juma 'yan le?en asirin Hajiya ne. Kin gane ai?" Murmushi na yi,
Kasu dai kamar wayayyu kuma dai kyawawa ne dan na yarda sun fini a kyau,amma abin takaici babu iji ba iya magana bare tauna kalma.
Na maida kallo na ga Maman Meema wadda take fa?in "Ko bata iya magana ne?" Na yi ?an murmushi sannan nace ina yininku?" "Ai ashe bamu gaisa ba." Inji Naman Anisa. Sai kuma suka amsa lafiya lau." Maman Anisa sai yatsina take yi tana hare harare ta mi?e tana danna waya,can ta kara a kunne sai tana fa?in Dadyn Anisa wannan karon kuma a haka aka ?are? Duk mu ukun da ka rabu damu muna da kyau da diri bana kuma muciya da zani aka ?akko." Mai jego ta tashi da sauri hanka?a ta ciki tana fa?in shiga kiyi a ciki uwar neman jaraba. Na yi ?an murmushi, ko kusa ban ji wani haushi ba,domin dai ko ma me zata fa?a yanzu dai ni ke da miji to wane kula su zanyi? Maman Meema tace "Nima dai sai kallon ta nake ina mamaki wai ace kamar Shamaki ya auri wannan yarinyar, koda yake tausayi ma ni take bani wallahi, watan ta nawa yanzu?" Kishiyar maijego tace ?ila zata yi wata biyu ko uku.

Ta kalle ni " Ki fara ?irga lokacin barinki gidan. Allah ya sa dai kema kina da ciki, duk rintsi randa gado ya taso dole sai kin shigo ciki." Hajiya dai ba?in ciki take yi kar a zauna da ?anta a samu gado, da ace zai yiwu ta bawa ?anta abinda matan shi zasu bashi wallahi bazata ta?a barin shi ya yi aure ba.

Na lalle ta nace, da farko banyi niyyar cewa komai ba, domin bani da magana da ku duk kun girme ni, kuma banga laifin ku a cin zarafin da kuka yi min ba, laifi nane da nazo barka har maijego ta kira ku domin ku taru ku ci zarafi na, da sirika ta da kuma mijina.
Na mi?e tsaye na turawa mai jegon ledar gashi nan Allah ya raya. Na ciro waya ta na soma kiran layin Hajiya. Ta ?aga nace Hajiya barka da yamma tace "Yawwa Rabi'atu." Nace direban ya taho ne? Tace yanzu ya kawo min sa?o da nace ya bari sai ya yi la'asar sai ya zo ya ?akko ki. " Nace in babu damuwa ya zo kawai yanzu. tace to bari insa a sanar da shi.

Ina kashe wayar mai jego tana ri?e hannu na haba amarya wallahi ban yi dan in wula?anta ki ba, kuma ba wadda na kira kawai dai arashi aka samu. Dan Allah ki zauna mana kafin direban ya zo."
Na kwace hannu na nace zan jira shi a waje. Tace "Ki rufa min asiri. Kishiyar ta kuwa sai dariya ta ke yi.
Sai kira ya shigo, na duba naga Shamaki ne a zuciya ta nace sun gama waya da Naman Anisa ta gama ci min zarafi na shine ni kuma zai kira ni me zai fa?a min.
Amma sai na ?aga inji me zai ce,. Sai naji yace "Shugabar ?alibai kina gidan jegon ko kin koma gida?" Wani lokacin yakan fa?a min haka tun da na sa mishi babban ba?o. Take na gane cewa wayar ?arya ta yi. Nace babban ba?o gani yanzu zan wuce, danma tsofaffin matanka sun zo ana ta labari. Yace "Su waye suka zo!? Nace kaji ni fa. Cikin shagwa?a na yi maganar. Sai naji ya kashe wayar. Maman Meema tace "Lallai yarinya mune tsaffin?" Kishiyar maijego tace ita ma kwana nawa ne wai maye ya yi amarya. Maman Anisa ta fito ta na fadin wai me take cewa! ?aran wayar maijego ya tsai da ita, mijin maijego ne ya kira ta. Ban san me yake fa?a ba, naji dai tana fa?in nifa ba wanda na kira, to ance maka za 'ayi fa?a ne." Sai ga Shamaki ya sake kirana,"Ina fata dai ba wadda ta zage ki?" Nace , To ko an zage ni babban ba?o ai na kai ne. Zan jira direba a waje ko ka yarda in hau adaidaita sahu? Yace "Na yarda ki ?auki drop ki bar gidan." Nace yanzu insha Allahu. Ina kashe wayar naga duk suna kallo na. Mama Meema tace Abin tausayi kya gama kicifin ki fice ki bar gidan ba dai Hajiya Zeena da Shamaki ba." Na yi mata kallo sama da ?asa sannan nace, in banci Jarabawa ba ke nan, kinsan wani abu? Ko a makaranta ban ta?a fa?uwa Jarabawa ba,bare ta gidan Hajiya Zeena mai sau?i, ku rungumi ?addara a kwai zafi ka kasa cin Jarabawa musamman ta shiga ajin gaba.
Na Kalli Maman Anisa nace da?i?i shine ya ke maimaita aji, Allah ya sa dai kin fahimta. Na dubi maijego nace Dole Hajiya ta hana zuwa gidan ire Iran naki domin hakan yafi alkhairi. Allah ya raya miki ?anki. Na rataya jakata na fice, ina ji suna banza a banza kawai.

Ina fita direba yana isowa na shiga muka wuce.
Hajiya ta tambayi maijego da jariri na ce duk suna lafiya. Tace "Amma lafiya lokacin da kika kira ?azu nake jin 'yan surutai?" Nace hira ce 'yan barka ke yi ni surutun nema ya ishe ni shiyasa nace zan tafi. Ta yi murmushi "Mata ai in sun taru basu da labari sai gulma ko hirar mazajen su, mai tunani kuwa bata da wannan lokacin."
Nace Allah ya kyauta na shige ?akina.

Da dare Shamaki suna cin abinci, ina dama masa wata fura da ya zo da ita, yace "Wai kuwa Hajiya yarinyar nan ta fa?a miki matan nan sunje gidan Shamsu?" Tace wa?anne matan ne? Yace "Su Naman Anisa da Maman Meema ne nasan tabbas su ne domin Maman Mubina na san bata ?asar nan, ko tana nan ma bazata zo ba."
Hajiya ta Kalle ni, haka ne? Nace e sune, suma sunzo barka ne. Tace sunzo gulma dai,Allah ya sa dai ba su yi miki wata maganar banzar ba." Nace 'a'a hirar su suke yi. Yace "Ba wata hirar su, yarinyar nan bazata fa?a bane Allah ka ?ai ya san abinda su ka yi mata." Na kalli Hajiya wadda ta zuba min ido. Nace To yanzu kam koma menene ai ya wuce, ni nayi musu uzri domin babu da?i kana son abu ka rasa shi, sannan ka ganshi a hannu wani kuma wanda ka ke ganin bai kai ya samu ba,kuma ace ya zama nasa,kai kuma shari'a ta shata maka layi da shi. Ni na yafe musu, kuma don Allah ku yafe musu ko domin albarkacin 'yan yaransu.
Suka kalli juna yace "Kinji ko Hajiya, yarinyar nan a kwai ta da ?ume abu a zuciya, to kafin mu yafe sai ki fa?a mana abinda suka ce."
Hajiya ta ?aga masa hannu, sannan ta ce an yafe musu, Allah ya yi miki albarka.

Na soma tunani cewa ?arya ne baya nema da Naman Anisa, domin na bincike wayar shi babu alamun sunan ta duk da cewa akwai lambobin da ya ajiye su da haruffa.

Kwanaki uku bayan wannan bada?alar sai Hajiya ta aiko Juma musamman ta kira ni, na zo,tace min "Abinda ya sa ta kirani,tana son ne ta min wani taimako ta min gata, amma tasan cewa bazan fa?awa Shamaki ba." nace To, tace "Nasan kina samun komai a gidan nan tafannin ci da sha haka ne?" Nace haka ne. Tace "Amma baki da ku?i ko taro mijinki baya baki ko sisi ko yana baki?" Nace baya bani. Tace "To zan saka dire ba zai kai ki gidan wani malami zan biya shi zai miji aiki yadda zaki samu damar karbar wani abu a gurin shi." Na ?ago kai cikin mamaki na kalli Hajiya. Tace kina mamaki ne ko?" Babu abin mamaki ina son ya zama sai yadda ki ka ce masa zai yi, kuma zaki nesan ta shi da wa?an can mata.Ina jin takaici iyayenki ya kasa yi musu wata kyauta a matsayin shi na ?an Alhaji Baita." Ina son ya sai miki mota ki ke hawa da kanki." Yanzu dai je ki shirya." Na tsurawa yatsun kafa ta ido ina kallo,nazarin maganar Hajiya nake yi, kamar ba ita ba mai mugun son ?anta da ?oye laifin shi ita ce zata ce wai in mallake shi kuma ita zata biya.
Bana zaton za a samu wata uwa ko da mahaukaciya ce da za ta aikata hakan. Wata zuciyar ta ce ko kuma duk cikin gwajin ne. Hajiya ta katse ni. Ki tashi ba'a.bori da sanyin jiki.
Na sunkuyar da kai nace Hajiya ki yi ha?uri, ba sai mun yi masa haka ba, bani da bukatar ku?i a hannu na, domin yana yin komai yadda ya kamata,rannan cewa ki kayi ya bani abin barka na gidan abokinsa kuma ya bani na kai. Iyaye na kuwa aure suka turo ni suka fa?a min cewa ibada ce zan yi har ma suka tabbatar min anan zan samu aljanna baza su yafe min ba in har suka ji layin da na koma.
Kuma Hajiya yana yi miki biyayya ni kuma yana sona, don Allah kar mu yi masa komai ba zan iya cutar da shiba. Harara ta jeho min, sannan tace Kin Fini sanin abinda ya dace ne?" Nace a a,tace to duk ranar da na saka lokaci dole kije ayi masa wannan aikin." Na ?ata rai ban kuma magana ba. Tace ni kike ?atawa rai dan zan taimake ki da dangin ki." Tashi ki bani guri. Na mi?e na tafi ina mamaki.

Wai Hajiyar da na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login