Showing 27001 words to 30000 words out of 55418 words

Chapter 10 - HAMSHAƘIYAR-UWA 2

04 Jul 2024

6000

mata zanin gadon da ku ka kwana a kai ba. Saboda haka ina baki shawara ki yi ?o?arin cinye jarabawa." Nace Na gode, amma don Allah zan iya tambaya? Kai ta ?aga. Nace wace irin jarabawace ki ke ta min magana tun jiya? Juma ta yi ?asa da murya tace "Jarabawar zaman gidan nan ce kuma shekara ?aya ce, zan sake tambaya ta ?aga min hannu tare da fa?in ki bi a sannu." Nace To me rashin aiko ki cire zanin gado ya ke nufi? Tace "Kenan ta gane ke kin kawo budurcin bata bu?atar ta ga shaida." A zuciya ta nace Hajiya dai ta matsa wa kanta a wannan fannin duk da na gamsu da bayanin ta.
Na sauke ajiyar zuciya, nace, Da ku zamu yi aiki anjima? Ta ce "E dama zan tambaye ki ko mu rage aikin tun yanzu?" Nace Hajiya baza ta yi fa?a ba? Tace "A'a ai ita ba ruwan ta kece zaki kula da komai." Nace to kamar me zaku rage. Tace tafashen kaji in za a soya ne sai ki bamu umarni, da naman rago kuma akwai kifi ma. Nace to ku soya ?in. Tace "Za ayi pepe ne ko kuwa?" Duk da ban iya ba sai na ce e har pepe ?in ma kuyi, shima kifin ku yi zan shigo kamar goma. Tace "To aike 'yarnan baki da girman kai amma sauran ko kallo bamu ishe su ba, sai dai ace wanke min wannan yanka min waccan sai sun gama Hajiya ta kasa ci. In kuma har Hajiya bata ci ba to kin fa?i jarabawar farko, daga ranar kun ?ulla. Basa tuna mune gidan mu muka san kanshi. Na yi ?an murmushi na gode Baba Juma. Da sauri tace "Allah ya yi miki albarka 'yarnan kin san darajar tsofaffi."

Tana fita nace Yawwa kai Allah na gode maka da ka bani mafita, sannan wannan kam akwai ta da magana, zanji abubuwa da dama a gurin ta cikin hikima. Naci nama gasashe da yaji na sha shayi da wainar ?wai, ?osai
da kunun gya?a kuwa ko kallon su ban yi ba domin ba ba?i na bane.

Amma na damu kasancewar bamu karya tare da ango na ba,
har tara saura bai shigo ba, na ?an kashin gi?a a gefen gado na kira wayar Umma, kamar in shiga ta wayar in ganta, idanuna suka kawo ruwa lokacin da ta ?auka, nace Umma ina kwana? Ta amsa muka gaisa, na tambaye ta Abba tace ya fita. Nace zan kira shi,ta ce su Jamila za su zo anjima ko ina son wani abu?".Na ce tazo da su Jafar da Baba Habu. Umma tace "To dama suna ta mitar basu je ba." Nace to. Na kira Abba na gaida shi, yana ta min nasiha, hawaye na bin kumatuna. Muna yin sallama Shamaki ya na shigowa, ya tsaya yana kallo na. "Ke da wa kike waya naga kina kuka?" Na mi?a mishi ya amsa ya ce A"bba ki ka kira." Ya zauna yana share min hawaye, "To menene abin kukan kuma?" Ya sakar min cakulkuli, na saki dariya tare da fa?awa kan gado. Yace da fatan kin karya dai ko?" Cikin zolayar nace najira ka baka dawo ba, sai nace ?ila acan ka ke ?ari. Ga mamaki na sai naji yace kamar kin sani, bana iya karyawa da kowa sai da Hajiya, abinda zai baki mamaki ko ?asar na bari to na bar karin safe har sai na dawo." Na ?oye mamakina sannan nace abin birgewa ina son irin soyayyar nan tsakanin ?a da mahaifi.
Sai naga ya saki baki ya zuba min ido gaba ya fa?i nace na fa?i ba dai-dai ba ko? sai ya sa hannu ya kuma janyo ni zuwa jikinsa yana fa?in Allah na gode Allah yarinyar nan li?ifi kamin da ka bani ita. Nace kamar ya ke nan fa? Yace A kan karin kummalon da nake yi tare da Hajiya a cikin matana akwai wadda tace wai in auri uwar tawa, dukkan su kamar irin wannan ranar ba wadda bata min ?orafi ba. wannan mummunar kalma tafi komai ?ata min rai har kuka na yi." Nace bata kyauta ba. Yace ke ka?ai ce baki min ?orafi ba kuma ban gani ko a fuskarki ba, don Allah kar ki canza kinji?" Na kwantar da kai ?irjinsa kar ka canza min kaima. Yace insha Allahu.
Yace "Bari inje in shirya zan fita kasuwa." Na dube shi ba hutu? Yace matane zasu cika gidan." Nace haka ne, to abinci fa? Ya kama kumatuna, "Za a kai min har kasuwa yau zanci jagwalgwalon Baby Allah ya sa Hajiya ta ci ina ro?on ki ki ?ure basirar ki, abinda baki gane ba ki tambayi Juma." Nace to kuma zan baka mamaki.Ya mi?e zai tafi, nace Yay sai na rufe baki na. Ya saki dariya bari Hajiya ta jiki garama kin yi saurin samo min suna ko kice Shamaki. Na matse kafa?a bazan iya cewa ba. ."Amma jiya ki ka ce Shamaki Aliyu dan girman Allah! Na nufi gurin shi da gudu na ?oye fuska ta a cikin shi ina fa?in don Allah ka dai na ?azu wai har a gaban Hajiya kuma wai zaka fa?a? Muje in taya ka ka shirya ka tafi. Yana dariya yana fa?in "Ok kina korata neko? Muka nufi ?akinsa, naga an cire zanin gadon an yi shinfi?a an gyara komai. Nace waya gyara ?akin nan? Yace "Menene" na yi shiru, yace "Bakya son a gyara ne?" Na ?aga kai alamun e. Yace"Bazaki iya gyaran ?akin nan ba." Saboda me? Na tambaye shi tare da zuba mai ido. "?angaren nan yana da girma za a kawo miki mai aikin da zata kula da naki sasan da kuma wasu bu?atunki." Nace kar a kawo min, sannan kuma abar min gyaran nan gefen na ka a hannunna domin Umma da Abba sun fa?a min aikina ne in kula da kai da duk wani abu naka da ka aje a gidanka. Sun ce aljanna ta a nan zan nema amma kai kuma kana son ka hanani samun wannan damar. Na ?arasa maganar cikin tura baki a yanayin shgwa?a. Ya aje rigar da ya cire zai shiga ban?aki, ya kama hannuwana guda biyu. "Zanyi ta addu'a ga su Umma ina gode musu da irin ginin da suka min ta tarbiyyar da suka miki, ni suka taimakawa da yarana da zaki haifa min ?ilama har da wa?anda ba ke ki ka haifa ba. Allah ya sa jiyan nan mun samu Zeena." Na rufe fuska ina fa?in shiga wanka kafin ka canza maganar kuma ni ce zan fito maka da kayan da zaka sa. yace "Ni da kayan duk naki ne yadda kika dama haka kowa zai sha, ina nufin duk yadda ki ka shirya ni haka kowa zai lalle ni."

Na bu?e durowarsa na tsaya kallon kaya, kaya iya kaya, na yi ta bu?e ?ofofin ina kallon ko wane ?angare, ?arin agoguna ne da gilasai na ido, abin dai ya cika ni da mamaki. Na fidda masa wata shadda mai kalar sararin samaniya da malun-malun na je duniya hulunansa na fidda wadda zata dace, har agogo da gilas na cire komai.
Yana shafa mai ina kallo yadda suma ta kwanta a sassan ?irji sa, zuwa ?waurin sa, abin ya matu?ar birgeni ni. Ya kalle ni ta cikan madubi, "Zaki taimaka min a bayana?" Na mi?e tare da fa?in sani kawai zaka yi Ni nawa aikatawa ne, na lakuci mai ina shafa masa a baya, ya lumshe ido Baby tsigar jikina tana ta shi, nace in bari ne? Ya ce "A 'a kimin sosai." Ya juyo ya rungume ni, "Baby komai na ki ya yi min." Na yi murmushi. Mu
Haka ya saka kayan na wanke shi da turare, na ?aukar masa jakarsa mai ?auke da laptop. Na kai shi har bakin ?ofar da zai shiga falon Hajiya. Yace "Yaya Baby a iya nan?" Nace Nice Yaya kuma? Hajiya zata ga cewa daga zuwana har na rako ka zai zama kamar na za?e ne. Ya lakuci hancina tare da fa?in soyayyata mai wayo.
....
Da na dawo zan shige zan shige gurina sai naji kukan yara, sai na samu kaina da nufar gurin su. Rahin ta yi musu wanka tana ta fama da su zata sa musu kaya amma Mubina bata son kayan da aka ciro musu, ita leshi za a sa mata, Anisa kuma ba wannan takalmin take wa kuka ba, sai an canza. Meema tana kicin kicin saka nata kayan. na shiga nace me ya same su? Cikin girmamawa Rahin ta ce Rigima suke jin yi Anty kinga ga kaya wai kowccen su bata so." Na ce to ki barsu kowa ta ?auki wanda ta ke so mana ina ganin ai kamar ba matsala ko? Rahin ta ja baya tace "To ku za?a amma don Allah kar ku zubo kayan domin shirya su ba ?aramin aiki bane durowa uku, aiki ne." Nace kije kusa sai su nuna miki sai ki ciro wa kowaccen su yadda ba zai ?aci ba ko? Ta ce "To " Yara suka bini da kallo sannan suka kasa nuna wanda suke so. Nace In za?o muku? A tare suka ?aga kai.
Na dubi Rahin anko ake yi musu kullum?. Tace "Wani lokacin suna sa daban daban." Nace Hajiya tafi son su sa kaya iri ?aya? Tace "Ban ta?a jin Hajiya ta yi magana akan haka ba ."
Na kama hannun su suka nuna min duk abinda suke so, nace to muje ?akina sai in shirya ku a can. Da sauri suka yarda suka bini Rahin ta bini da kallo. nace ki gyara musu kayan kawai.

A Kan gadona nace su hau Meema tace "Hajiya ta hanamu tace gadonmu kawai zamu hau amma banda na manya." A raina nace tofa! Sai nace ai Hajiya bata nan kuma ni bazan fa?a mata ba. Sai suka kalli juna, Mubina ta zau a kan kafe ?in gaban gado, Meema ta ce "Hajiya ta fa?a mana in bata nan Allahnta yana nan, kuma zai ganar da ita inhar muka yi ba daidai ba. Na sauka kan Kafet ?in batare da na sake magana ba, nace bari a fara shirya Anisa ita ce 'yar ?arama ko? Meema ta ?aga kai, sannan tace "Anty ke ?in wacce ke ma nan gidan ki ke?" Nace ni Mominku ce, ba sunana Anty ba. Mubina da Anisa duk suka kalle ni , Mubina tace "Kema a nan gidan ki ke?" Nace e mana ga ?akina ma. "Kece Momin da Dady yace zaki zo in anyi biki?" Inji Meema. Nace la! ashe ya fa?a muku, to ni ce. Anisa tace "To Momy anyi bikine?" Nace anyi jiya yau ma za ayi. Suka fara murna." Na gama shirya su muna ta 'yar hira suna min tambayoyi na shirme ita biye musu domin ni ina son hira da yara don haka naji sun shiga raina domin na lura suna da wayo. Na gama musu fesa musu turare, Meema ta kalli wayata "Momi in ?auki wayar ki?" Nace me zaki yi da ita? Mubina ta amshe da cewa "Akwai game a ciki?" Nace babu amma ku zo in ?auke ku hoto mukayi hotuna ni da su. Nace to sai ina? Suka ce za suje gaida Hajiya ne. Nace to ai ni baku gaishe ni ba, suka ce Hajiya ake fara gaishewa sai Dadi shikenan sai mu gaisheki. Nace to haka ya yi daga nan su gaishe min da Hajiya. Suka tafi ina bin su da kallo.

Goma saura na saka hijabi na fita, na nufi gurin Hajiya na tsugunna na yi mata sannu da hutawa ta amsa, nace nazo gurin yin aiki. Ta nuna min ?ofa da hannu bi nan zaki samu su Juma a kicin.
Hajiya ta bi Baby da kallo cikin wani kallo na nazari, kamar kowace amarya dai haka take zuwa a nuna mata kuxin ?arshe dai abinci ya ?i ciyuwa, ta ta?a baki bari dai mugani, domin ta lura yadda abubuwa ke faruwa a safiyar yau ana samun ?an banbanci da wanda suka faru a matan da Shamaki ya aura, a safiyar farko misali in ya bar gurinta ya nufi ?akinsa don ya shirya ya tafi kasuwa ya kan ?auki lokaci bai fito ba, haka ma dai a wannan karon, ya ?ata fiye da awa ?aya sai dai banbancin da ta lura da shi shine fitowar wannan karon akwai banbanci da na sauran, a yanayin sa a fili yana cike da nisha?i da kamanin angwaye, sannan kayan da ya saka ta tabbatar ba za?in shi bane domin tasan a guri ?aya yake saka babbar riga shine in zashi wani taro. Tace Allah ya sa dai a dace. Ta mi?e domin yin sallar walha.

?aton kicin na riska kuma na zamani ta window kuma na hango wani kicin ?in na gargajiya inda wasu mata su uku suke ta aiki. Juma kuma tana ?arar magi, na yi mata sannu ta ce "Amarya kin fito?" Nace e, tace "Muje in nuna miki an gama suyar kaji, wannan ma magin fefe ?in da za'a yi ne na ke barewa." Nace Sannun da aiki, Mukaje na gani na yi musu sannu. Suka ce Me za a dafa?" Naja Juma gefe nace me ki ke ganin Hajiya tafi so a taro? Tace "E to tunda kin tambaye ni zan fa?a miki, muna yi shinkafa jalaf, tuwo, da alala, waina sinasir funkasau da sauran su, amma yanzu kin ga babu maganar waina ko sinasir, tuna da ba a tashi yin su ba yanzu ko ba gaskiya ba, sai dai a ?ara da wani abin." Nace in akwai kayan ?anwake za mu iya yinsa, da kuma dambu da funkason ko kina ganin mutane ba za su so su ci wa?annan ba?
Tace "Yannan ki ke maganar ba za su so shi ba,ai yanzu babu abinda ke kwantai in dai abinci ne. Muna da ?arjajiyar shi kafar dambu sai dai bata da yawa sosai, in kuma na kuskus za ayi to." Cikin sauri nace A'a za a yi shi haka ai ko ?anwake ba mai yawa sosai za ayi ba, na tare maganar kuskus ne domin ban ta?a yin na kuskus ba.
Tace 'To ki fa?i gaba ?aya abinda muke bu?ata wanda babu sai a kaiwa Hajiya list za ta aike ni in siya." Na ?an yi shiru, sai dabara ta fa?o min nace tuwo da kayan shinkafar ki lissafa ki fidda wanda babu, ni kuma sai in lissafa miki na dambu da ?anwake. Nayi haka ne dan su nafi iyawa. Haka dai muka tada lissafin tuwo za ayi miyar ganye da agushi shinkafa soyayya sai alala da funkaso dambu da ?anwake. Haka dai aiki ya rinca?e mana danma suna da hanzarin kuma komai an ?ora wasu akan gas ga kuma murahu. Ina yi ina addu'a Allah ya fidda ni kunya ?arfe ?aya da rabi komai ya kammala sai tuwo da suke ?auewa a leda Gida ko ina ya ?auki kamshi. Gaskiya su Juma sun iya girki kuma sun taimaka min sosai. Suka ce inje tunda kwashe tuwo ne ya rage in sun gama sai su kai inda aka jere komai.

Hajiya tana salla a. Falon ya soma cika da Jama'a yaranta duk sun iso da 'yayansu, na rusuna na gaida kowa sannan na nufi gefe na. Maman Nana tana cewa yanzu Maman Iman ke cigiyar ki. Nace ina kicin ina take? Tace tana salla, na ce nima bari inyi sallar
Na shiga ?aki zan shiga wanka sai naga wayarta a kan gado, sai lokacin na tuna da wata waya, na ?auka dan in duba ko an kira ni.
Kiran Shamaki yafi goma ga sa?o na fara duba sa?unan, magiya ya ke in naga kiran shi don Allah in kira.
Cikin rawar hannu na danna kiran shi tana shiga ya ?aga. Baby lafiya? Nace lafiya Lau, ina kicin muna aiki ne,ban tafi da wayar ba. Yace "Ko ina ki ke Baby ki zama da wayarki a hannu, na manta zaki yi mana girki, kinji yadda hankali na ya tashi ne ka?an ya rage in taho gidan." Nace da ka kira Hajiya zata fa?a maka cewa ina kicin. Yace "Ta? to ya za'ayi in iya kiran Hajiya in tambaye ta ke, akwai bu?atar ki lura da abubuwan da basu kamata ba. Ya ki ka san zata kalli abin?" Na yi shiru domin banga wata matsala game da hakan ba to kullum sai Hajiya ta yi abinda na sha mamaki. Yace "Tunda kina lafiya shike nan, dama dai inji muryar ki ne, yau na zama cikin yawan tuno ki da miki addu'a. Kin dasa wani abu a zuciyata iya jiya zuwa yau, dan Allah Baby kar ki canza ta min yaya. Kowa ya ganni a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login