Showing 42001 words to 45000 words out of 55418 words

Chapter 15 - HAMSHAƘIYAR-UWA 2

04 Jul 2024

6011

layin direba.

Yau ne ranar farko da na fara shiga ?akin baccin Hajiya, wani mugun ?amshi ya bugi hancina. Sai dai ban tsaya kallo komai ba, domin ina tsoron ko akwai kyamara.. Amma fa ?aki ne na alfarma. Na dur?usa na mi?a mata nace gashi.

Tace "To tunda kin?i tambayar shi ni ga tawa gudummawar nan ki bata Allah bata lafiya. Na fa?a miki tun daga ?arfe biyu sai ki shirya ki jira zuwan direba kar yazo a barshi yana ta jira." Nace sanyi duk yadda ki ka ce Allah ya saka da alkhari.
Na fito tasa Juma ta ?auki ledar ta kai mota sannan na fita,sai da na tabbatar gani zaune a mota sannan na kira Jamila ta wayar Umma nace gani a hanya. Sai naji ta kwashi ihu da murna na kashe wayar na jefa a jaka,,sannan na bu?e ledar inga abinda ke ciki. Turmin atamfa guda biyu, sai wata farar Envelope na bu?e ku?i ne 'yan ?ari biyu rafa ?aya. Tabbas zargina ya tabbata Hajiya latsa ni ta yi .
Tabbas sai na zama mai kula domin na fuskanci Hajiya ta iya latsin basira.
A bakin lungun gidanmu ya tsaya, ya fito ya bude min ?ofa, sannan na fito ya amshi ledar ya biyo ni.
Kamar na taka da gudu in isa gida haka babu,amma sai na tafi sannu saboda direba da ke biye da ni cikin girmamawa.
Na amshi ledar na yi masa godiya sannan na shiga da sallama, kamar taron suna gida ya cika, ban ko tsaya amsa gaishe gaishe ba na nufi ?akin Umma da gudu tana zaune a kan gado sanye da atamfar ankon bikina. Na zauna bakin gado na kama hannun ta ina sannu Umma. Sai fara'a ta ke yi tana kallo na. Na gaishe ta na tambayi jiki sannan na gaida sauran mutane. Sai fa?i ake yi amarya tubarkaalla. Umman Amina tace ya surukar ki kuwa? Ai mun taho muna hirar ta wannan mata tana da kirki kuwa? Na yi murmushi nace tana da kirki sosai kuwa. Na ?akko laidar nace gashi ma tace a kawo wa Umma. Nanfa kuma aka shiga yaba mata.
Jamila ta kama hannu na muka shiga ?akinmu na da muka zauna,tace "Yaya Baby wai don Allah kina da ciki ne?" Nace ke Jamila yaushe ki ka zama haka? Tace "Ba wai yaushe na zama haka bane, kinsan dai nice abokiyar shawara,nace bani da komai me ki ka gani? Tace "Kinyi kyau." Nace danma baya samun zama Jamila kinsan ko hira bamu ta?a yi ba,amma karki fa?awa Umma. Tace "Kamar yaya ko hira ba ya kwana a gidan kenan?" Na bata labari dai dai da fahimtar ta. Tace "To kinsan me za kiyi?" Nace 'a'a tace da rana kisha bacci da dare ki tashi ki dire ki ce bakya jin bacci shima ki tsare shi da hira."
Nace Gaskiya Jamila kina da kwanya, amma kuma zan tausaya mishi ai in har zaije da rana ya sha wahalar kasuwa dare kuma in hana shi ya huta. Tace Hajiyar ta rage mishi lokacin lissafin da ranar ko da daren mana.
.....
Nace Jamila kenan, zan gwada Allah ya sa dai kada hakan ya zama wata matsalar a gidan kinsan komai a gidan ?an ?a'ida ne.
Jamila tace "Ameen insha Allahu ba wata matsala, yanzu dai nasan za'a canza miki waya, ina ri?on taki, ko kiba ni 'yar dubu biyar in sai mai botura." Nace ina naga ku?in da zan baki, kinsan Allah banda ku?in nan da Baba ya aiko ki kika ki ka kar?a da sai in ce miki ni ban ta?a ganin takardar ku?i a gidan nan ba. Shi kanshi ban ta?a ganin ku?i wai yau gashi a hannun shi ba.
Jamila ta saki baki tana kallo na. "Dama duk kirarin ku?in basu a zahiri kenan suna ?oye a banki?" Nace to ?ila hakanne. Tace "Rannan wata 'yar Ajinmu tana labarin Gidan Hajiya Zeena da irin dukiyar da ke dan?are a gidan wai 'yan uwansu ne. Na ce mata ni yayata a gidan ta ke aure. Da farko ta ?aryata wai ?an Alhaji Baita ba zai auri 'yar gidan mu ba. Shiru na yi mata sai da wasu 'yan ajinmu suka tabbatar mata shine ta yarda,tace gaskiya ta dangwalo, ance gidan suna da ?akin ku?i ko ?ananan yaran gidan sai dai su shiga su ?iba, sannan Makka duk wata." Na kwashe da dariya nace kai mutane Allah ya kyauta. Jamila ta ce "Dama ni na musa wannan labarin amma ina kokwanto nace bari dai zan tambaye ki inji tunda na san dai ke yanzu kinsan komai." Na kauda zancan da fa?in, tashi ki rakani gidan su Zuhra mu gaisa da su.
Umman su Zuhra tace "A 'a ,ga fa amare muka gaisa ta tambayi Hajiya nace tana lafiya duk tace a gaida ku. Tace ai wannan mata daga gani zaki sha ?ani a gurin ta, sam mace ba rahma magana ma da kyar a ke yinta ita dole ga mai ku?i." Nace la kuma Umma sau?in kai ne da ita dan baki zauna da ita bane. Hajiya ba ruwanta wallahi. Ta ta?a baki, "To kenan mu ta wula?anta? Nace ta yi muku wani abu ba daidai ba ne? Tace "Koda yake ke kina rufe radda muka kai ki. Kallo ma bamu ishe ta ba, bare washe gari da muka koma." Nace ikon Allah ?ila dai ko mutane ne suka mata yawa kin san shi'anin taro. Haka dai na yi ta kare Hajiya domin ko iyayena bazan bari su ji sirrin zama na da Hajiya ba, kar in ?aga musu hankali,ko kuma su zo suna jin haushin ta. Jamila ma sai da nayi mata kashedi domin kar ta fa?a.Na san kuma bazata fa?a ba.

Muka dawo ana ta raha duk wata budurwa ta lungun mu da taji labarin na zo sai ki ganta wai tazo mu gaisa. Kamar yadda Hajiya tace daga ?arfe biyu in shirya haka na yi, ina yin azahar na shirya ina jira direba. Jamila tana ta mita wai maimakon in kai dare. Nace ana wanke tukunya dan tuwon gobe ne, bazai yiwu in wuce lokacin da aka bani ba. Da naga uku ta kusa na kira Hajiya na gaisheta cikin girmamawa na ha?a ta da Umma ta yi godiyar sa?o, sannan na tambaya ko direban ya iso. Tace "Aka ta aike shi ne in ya dawo zai zo.

Sai biyar da wani abu ya iso,muka kama hanya zuwa gida.
Umma dai citta da daddawa ta bani wai in kaiwa Hajiya. Na kai mata nace inji Ummanmu tace "To an gode jeki kaiwa Juma.
Na kai mata kicin ta ce amarsu ansha gida kin dawo da wuri ko Hajiyarmu ce ta baki lokaci? Na yi ?an murmushi nace sai anjima. Tace kinga a nan babu wannan na'urar hakan yana ?aya daga cikin abinda zai sa Hajiya ?i ta barki ki zo nan ?in. Nace kalle ta ban yi magana ba. Taci gaba da fa?in "Ko da yake jimawarki a nan shima abin tuhuma ne a gurin Hajiya. Na yi 'yar dariya nace Baba Juma kina da abin dariya wallahi. Tace 'yar nan da ba?in wayo ki ke, kin ?i ki ?ara dan kar ince kin yi munafircin Hajiya ko? To sha mutumin ki, Hajiya bata amsar magana sai da hujja ba bugar cikin ki zanyi ba. Nace ni Bab Juma bana gane irin wa?annan zantukan. Tace "Ba wani bakya gane wa, daga ganin wa?annan wayayun idanuwan naki kar ki ke kallon kowa.

Ni dai na fice, zan nufi gefena. Hajiya tace "Basa cikine naga kin jima? Nace suna ciki munyi magana ne. Tace to madallah.
?arfe sha biyun dare ina kwance a tafkeken gadon Shamaki ina ta nin?aya, ina son in gwada hikimar Jamila ne in tsare shi da hira. Na ?auki wayata ina shirin tura masa sa?o cewa yau dai ina jiransa hira na ke son mu yi.Sai kawai naga sa?onsa kamar haka.
"Baby ban samu dawowa ba ?ila ma ba gobe ba, amma zan sanar da ke in zan dawo. In kin kira ni baza ki same ni ba,amma ni zan kira ki a duk lokacin da na samu dama."
Na karanta na sake karantawa. A fili nace tofa! Ni wai dama wannan ne auren da mata ke cewa Allah ya kai su gidan hutu su yi aure su huta? Hummm gaskiya kam ina hutawa in dai bacci da cin abinci da nama shine hutu.
Na sauka a gadon na nufi ?aki na na kwanta.

Ban sake ji daga mijina ba sai bayan kwana biyu ina zaune shiru zama ya ishe ni, na tashi na nufi sasan su Mubina, sai ina jiyo hayaniyar su a wani guri. Nabi hanyar sai na riski wani ?an gurin shan iska da 'yar rumfar gargajiya, ga lilon yara sannan gurin akwai ni'imar bishiyu. Suna ta wasa can kan wata kujera Azima ce tana karanta wani littafi na Hausa. Nace Azima kuna nan kuna shan iska kenan? Ta ?ago ta lalle ni haka sama-sama tace "Umm." Ta maida kanta ga karatun. Na isa gurin su Meema nace ku daina wasa kuzo in koya muku karatu kuna s? Duk duka ce e, suka biyo ni nace muje ?akin karatun ku inda Antynku ta lesson ta ke koya muku, ni na islamiyya zan muku.

Muna tsaka da karatu daga izifi biyu muka fara zuwa ?asa. Sai waya ta tayi ?ara,na ?aga da sauri ganin Shamaki ne. Na yi sallama na ce sannu. Ya amsa. Tare da fa?in Baby gaskiya ki samin suna kafin na dawo in kin ?aga waya sai dai ki dinga wani kame kame abinda zaki kirani da shi. Nace to zan nemo amma ka taya ni mu za?a. Muka gaisa,yace "Abubuwa na sai kinyi ha?uri kinji?" Ina son ki fa Baby karki zata bana sonki." Nace nasani ,yace yanzu kina ina? Nace ina nan tare da yarana. Yace to ha?a ni da su." Na dubi Meema na ce ga Dady. Ta amshi wayar tana murna ta ce Dadynmu yaushe zaka dawo?" Yace "Duk lokacin da na gama abinda ke gabana zan dawo." Tace a kawo mana tsaraba.
Yace to ba mubina ita ma mu gaisa. Ta amsa tace Dady ga mu a gurin Momy muna yin karatun ?ur'ani Momy ta iya karatu mai da?i. Yace to ku dage ku yi sosai zan kawo muku tsaraba." to zaka kawo wa Momy yace "E ita momy ai babbar tsaraba zan kawo mata sabuwar Baby kuna so?." Tace Muna so Dadi Ya ce "To ana Anisa ita ma." sun gaisa kafin daga bisani na amsa. Yace sannu Malama Baby Allah ya bada sa'a." Nace wai yaushe zaka dawo ne? Ni fa na.. sai na yi shiru,yace "Fa?a min kinyi me?" Kin ?osa in dawo?" Na ce E "Kina kewata kenan?" Na ?ara ?asa da murya nace E. Yace "To zaki daina jin kunya ki yi min duk abinda nace kimin ina so?" Nace amma banda ?ayan, cikin shagwa?a na yi maganar. Yace "Wanne a ciki ne baki so?" Nace ba nace maka ina jin kyama ba?" Yace shikenan ni kuma shi nafi son shi.. zan koya miki amma ki daina jin kyama banda abinki Baby akwai wani abu da zai baki ?yama a tare da ni? Nace ka ga akwai yara dama zaka kira anjima.
Yace "Yanzu na ?an samu dama Baby. Nace to zanyi. Yace "Kin ?auki alkawari? " Nace zan dai yi ?o?ari in ga ko zan iya. Yace "To ki shirya na fa?a wa yara zan zo da tsarabar Babynmu sabuwar jaririya kin shirya?
Na ce Duk yadda Allah ya yi fatanmu dai mu samu masu albarka. Yace "Amin, to bari in barki ku yi karatun ku ko? Nace To Na gode.

Cikin dare ina bacci kiranshi ya tashe ni, a tsorace na ?aga wayar" yace "Nasan kin yi bacci kuma na yi laifi na tashe ki, gobe zan dawo Baby a matse nike gida zan wuto don Allah ki shirya. Nace to ba damuwa. Da safe da naje gaida Hajiya nace mata gashin kaina ya yi datti ina son inje gurin wanke wa. Ta saki ?an murmushi, "Mijinki zai dawo ko? To haka yana da kyau ina ki ke wanke wa?" Nace sai dai ko in yiwa Maman Iman magana wadda ke min a gida ne can Unguwar mu. Tace ba damuwa zan fa?a mata sai direba ya kai ki. Nace To. Na koma ?aki ina mamaki.
Tun takwas aka ce in fito. Aka kai ni wanki kai aka min ba?in lalle zuwa sha ?aya da rabi na zama tsaf,sai da na dawo na karya. Hajiya ta dama wani abu a cikin madarar shanu ta aiko min.

Cikin ikon Allah na shiga ban ?aki zan yi alwala azahar sai ga ba?on mata ya riga shi zuwa. Na zaro ido.

kai tsaye gida ya nufo lokacin ?arfe ?aya dan haka ya aiko da kaya ya shiga Masallaci.
?????????
Tamkar kazar da ?wai ya fashe wa a ciki haka na koma. Falon Hajiya na nufa lokacin da Juma ta zo ta ce Hajiya tace a sanar da ni mijina ya dawo. Har zan ce ki ce ina yi masa sannu da zuwa sai na ji Juma ta yi wata magana, tace kema dai makar sauran ce a fa?a masa kina yi masa sannu da zuwa. Masa sannu da zuwa?" Nace 'a'a ina zuwa dai zaki ce Baba Juma, Yaya mijina zai dawo tafiya ta kwanaki a kira ni kuma in aika da sa?on sannu? Tace "Ashe dai kinsan kan ki. Ta fice wannan ?in duk cikin jarabawa ce, ki na gani kamar ba gaske bane ko?" Bance komai ba ta fice. Na tashi Na je gaban madubi na dubi leshin jikina ya yi kyau, na shafa janbaki na ?aura ?an kwali na baza gashin zuwa kafa?a ta tunda na san yana son gashin. Na fesa turaruka sannan na nufi falon Hajiya cikin taku irin na matar so. Ya na zube gaban Hajiya kamar zai mata sujjada nan kuma ga Juma nata fito da kaloln abinci, wani da?i naji ya rufe ni da na ganshi, na nufeshi ina fara'a ina fa?in sannu da zuwa ka sha hanya. Ya zuba min idanu har na zo kusa da shi na tsugunna. Yace bazan amsa ba sai na ji sunan, na kalli Hajiya sannan na fara gaishe shi, ya amsa tare da kai hannu ya shafi gashina, na sake kallon Hajiya da sauri sai naga ita murmushi ma ta ke yi. Na zauna sannan nace ko in sa maka abincin ne? Yace "Da kin kyauta amma fara bani ruwa." Na bu?e murfin robar ruwan na cika tambulan na ni?a mishi, sannan na ce wane abinci zaka ci a ciki?" Ya dire kofin yace duk abinda ki ka ga ya dace Baby ni zanci." Na kuma kallo Hajiya yanzu kam idanuwan ta suna kan talabijin amma na tabbatar kunnan ta yana tare da mu.
Nace zan fi so ka za?a amma tunda ka bani za?i zance ka ci tuwo ?ila shine tunda kaje can baka ciba. Yace "Gaskiya banci tuwo ba, kuma yana cikin abincin da nake so. Na zuba masa komai da farfesun kaza sai zo?o. Yana ci ina ?an danna waya ta shi kuma yana satar kallo na da mun ha?a ido ya ?aga min gira. Yace amma ke kinci abincin ko?" Nace sai anjima yana ?aki. Ya yanko lomar tuwo da cokali ya nufo baki na, ki ci anan daga nan ?akina zamuje ki ?an matsa min jikina na gaji da yawa. Na kalli Hajiya har yanzu bata tare da mu a ido amma a kunne nasan tana ji. Na bu?e baki na amsa, sannan nace to ya isa haka ban jima da karyawa ba, kai dai ka ci sosai yanzu ka dawo daga tafiya.

Yace na ci da yawa, to ke ma ki ?an ?ara ko so ?aya ne, ya kuma mi?o min, na amsa nace. To na gode. Yace "Rama min za kiyi ki daina fa?in wani kin gode." Nace wannan mai sau?i ne yana cikin aiki na da zaka bani dama in kullum ka ke son in baka abinci zan fi ka murna domin dai nice da ?aruwar. Muryar Hajiya ta katse ni da fa?in "?aruwar me?" Na sunkuyar da kai nace Lada na ke nufi Hajiya. Ta kuma ?auke kai. Na fara ba shi a baki ina satar kallon Hajiya, tamkar bata san muna gurin ba. Zan bashi Lemon zo?o ya min cakulkuli na gantsare saura ka?an in saki kofin cikin dariya nace zaka sani in saki kofin in yi ?arna. Na je kusa da kunnan sa, nace ka bari Hajiya tana kallo fa. Yace "Hajiya wai kina kallo? Kin gani Mamanmu ce bazata hana mu yi wasa ba ko Hajiya?"

Ta dube shi. "Me ka ke cewa? Yace "Wai kunyarki ta ke ji." ?an tsaki ta yi sannan tace ku daina sani a shirmen ku ina kallon wani shiri ne a gidan Talabijin. Haka dai yana ta tsokana ta har muka gama, yace mu tafi ciki.
Har mun wuce Hajiya ta kirani, ta mi?amin wata ?aramar ?walbar zuma mai kyau, tace "ki yi amfani da wannan. Kinsan ya ake yin amfani da shi? Na girgiza

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login