Showing 30001 words to 33000 words out of 55418 words

Chapter 11 - HAMSHAƘIYAR-UWA 2

04 Jul 2024

6001

kasuwa sai ya yaba da kayan da ki ka za?a min kuma kin san abin mamaki na ta?a saka kayan amma banji wanda ya ce na yi kyau ba sai yau, har wa?anda ba su san na yi aure ba da sun ganni sai suce kamar ango." Cikin mamakin irin zuba zance da Yaya ke yi nace naji da?i sosai da na saka a farin ciki, insha Allahu bazan ta?a canzawa ba, yin hakan fa dai-dai ya ke da juyawa aljanna baya. Yace me ki ke yi yanzu? Nace wanka zanyi inyi salla sai na shirya fita filin taron. Sai kawai naji subba ta ratsa kunne na ta cikin waya,ta bi sassan jikina wanda haka ya tilasta min sulalewa na zauna a kan gadon tare da kumshe ido. Na ?ago waya na kalla baya sautin ya katse layin .
Cikin sanyin jiki na shiga wanka. Bayan nayi salla yau ma dai kwalliya ce aka ca?a min na ci leshi ina ta ?amshi su Jamila sunzo da su Umman Amina har da ma?otanmu da yawa abu mamaki,dangin Abba ma sunzo. Wani ?aton fili ne a gidan an shirya shi kamar tantin larabawa. An zuba kujeru a gaban kujerun na alfarma Hajiya tare da wasu manyan Hajiyoyi ?awayenta suna zaune a kai kusan su goma dukkan su kowa tana ji da kanta.
Sai layi na biyu 'yayansu ne. Sannan sauran mutane da abokan arzi?i a sauran kujerun wanda teburi ke tsakiya. Kamar yadda Maman Umar ta shigo ?akina muna zaune, tace matar waliyina Umma su Zuhra ita ce ta ri?o ni har gaban su Hajiya. Haka aka yi, ina dur?usa na gaishe su, suka amsa cinkin isa da ?asaita. Sannan Na du?usa na gaida yayun mijina, aka kaini wata kujera da aka tanadar min. Wata malam ta tashi ta fara gabatar da nasiha game da zaman aure, biyayya ga miji, bin uwar miji, bin dangin miji tsafta iya girki da sauran su. Sai dai banji inda ta fa?i yadda ya kamata uwar miji ta mutunta matar ?anta ba,dangin miji su girmama matar ?an uwansu ba,haka banji ta yi magana game da hakkin mace akan miji ba,amma tayi magana sosai akan ha??in miji akan matarsa. A zuciya ta nace ko ina dai yanzu mutane suna kare abincin su ne suna yin abinda suka san shine fitar su.
Bayan an gama MC ta sanar cewa yanzu lokacin cin abinci ne wanda amarya ta dafa kuma zata fara gabatarwa a gaban Hajiya, amma kafin haka sai ta ?an ?ana dukkan abincin da ta dafa, sannan za a kai ga Hajiya da Aminanta. Yin hakan ba wai ana zargi ba ne al'adace.
Gabana ya fa?i na tashi na nufi gurin da aka jere kayan abincin kowa ya kallona, na zaci su Juma zasu zo su taimaka min amma sai na ga kawai kowa kallona yake yi. Na ?auki tire na jera plate hu?u suka cika shi na zuba shinkafa nasa tuwo a ?aya na saka dambu a ?aya sai kuma na sa Alala a ?aya, na kuma jera hu?u ?aya mai zurfi sa matsami na tsamo ?anwake na zuba a mai zurfin. Sai na zuba kaji da kifi da naman rago. Colsow kuwa shima madubi daban sai na zuma a karamin plate na sa cokali na ?iba na sa a baki ina ci, sai naji an kwashi tafi. Duk a ru?e nake, na ?auki tiren na soma kaiwa ina jerewa a teburin gaban su Hajiya. Sai da na cika teburin komai na zuba musu, lemuka dai dama na ga anjere su da ruwa a kan kowane tebur.
Na koma na ci gaba da zubawa, anan ne Juma suka zo suna mi?awa teburin su Maman Umar zuwa na sauran jama'a. 'Yan unguwarmu da yake a ko ina sai an nuna halin, nan suka fara zuwa suna cewa Baby a bamu. Juma ce ta kore su, ta ce kowa ya koma mazaunin shi zai samu. Bayan an gama da manya sai Mc Ta sanar cewa Amarya ta koma nata mazaunin yanzu masu rabon za su zo su raba. Wata mata tare da 'yan mata suka shigo suka soma rabon abincin ni kam Idanuna da hankalina suna kan teburin su Hajiya har zuwa lokacin da mutane suka fara cin abinci ta irin su ba'a fara ba, sannan yanayin kallon da wasu aminan ta suke min ya sa jikina yin sanyi, a zuciya ta kuwa addu'a nake Allah ya fiddani.
Kusan kusan mutum uku suka fara cin abincin sannan lura d Hajiya i ta fara ci, sai dai wani abin ban iya gane ko ya ta ji abincin yadda take komai cikin ?asaita.

Masu hotuna da bidiyo ana ta ?auka gaskiya ni tsarin ya yi min, wata zuciyar tace tunda kin tsallake Hajiya ta ci kyace abin ya birge ki mana. Haka dai aka ci aka sha sannan aka gama. Aka kai wa Hajiya abin magana zata yi jawabin godiya amma kafin haka sai ?awarta Hajiya Zulaiha ta amsa ta isar da sa?on Hajiya game da abincin da amarya ta ciyar da su, tace "Zan yi ?an bayani ka?an kafin Hajiya ta yi godiya, gaskiya amarya girki ba laifi amma a ?ara gyara hannu sosai, ta ?an ta?a baki, ya yi da?i sai dai ?an gyara guda biyu dazan miki, na farko ?anwake mai da yaji ne sai kika bamu da miya. Na biyu kin mana ?an zubi a dambu sai ki ?ara sakin hannu ka?an saboda rowa bata da wani amfani kuma bata cikin sunnar gidan nan. Na sunkuyar da kai, ina mamaki amma duk da haka ni ce da godiya tunda ?orafin ya tsaya a haka,,Hajiya ta ci abinci Allah ya soni ni.
Hajiya ta amshi abin magana tayi godiya ga kowa tare da fatan duk za su koma gidajen su lafiya.Sannan ta sa albarka tare min fatan zama jarumtar mace musamman gurin yi wa miji biyayya. Aka abin maganar wai ince wani abu bani wai nima in yi godiya. Gabana yana fa?uwa na amsa. Nace Mun gode Allah ya maida kowa gida lafiya, kuma insha Allahu zan yi amfani duk shawarwarin da aka bani zan kiyaye. Haka taro ya tashi kowa na san Barka. Ana tashi aka kira la'asar. Hajiya ta kirani inyi sallama da ba?inta. A lokaci ne wannan mai cewa ina da rowar same ta tana cewa "Hajiya Zeena duk matan da ke Kano amma Shamaki ya rasa wadda zai ?auka sai wannan cokokuwar ko cikin 'ya 'yanmu ya kasa zuwa ya duba. Na kalli Hajiya lokacin da takecewa
"Bar ?an yau da abinda ya ke so Hajiya Zaliha. Wani mugun so ya ke yiwa yarinyar nan ba domin na samu tabbacin ba asiri suka yi masa ba da a haka zan kalli abin. Gaggawa fa ya yi aka je aka nemo masa auren ta. Ni kuma kinsan matsala ta, ina son ?ana da yawa kuma ya rayu akan samun duk abinda ya ke so, in ba ?ana abinda ya ke so matsawar yin hakan ba sa?on Allah bane." Nace su sauka gida lafiya na juya raina ba da?i, na soma jin takaicin kushe min halitta da ake yi. Gefena tan?am da 'yan uwa da 'yan unguwa sai kallo na suke suna min murna. Na zauna bakin gado Jamila ta zo ta ce "Abinci ya yi da?i Yaya Baby kuma ke ki ka dafa?" Na ce e mana. Wayata ta soma ringin ta mi?o min. Na amsa Mijina ne Hajiya ta hana ni fa?a masa Yaya To bansan wane suna zan saka masa ba. Na ?aga, yace " Yaya Baby gaske ne ke kika dafa abincin nan?" Cikin shagwa?a na ce wai don Allah nice Yaya? Yace "Ina son yadda su Jamila suke fa?a ne." Abicin bai yi da?i bane ko? Na tambaye shi. Yace "Inji wa, ai in fa?a miki abincin Hajiya ne ka?ai ya fi naki da?i." Na yi murmushi a zuciya ta nace ai ita Hajiya komai nata ya fi na kowa. "Sannu soyayyata ,kin yi ?o?ari sosai.
.....
Da na dawo zan shige zan shige gurina sai naji kukan yara, sai na samu kaina da nufar gurin su. Rahin ta yi musu wanka tana ta fama da su zata sa musu kaya amma Mubina bata son kayan da aka ciro musu, ita leshi za a sa mata, Anisa kuma ba wannan takalmin take wa kuka ba, sai an canza. Meema tana kicin kicin saka nata kayan. na shiga nace me ya same su? Cikin girmamawa Rahin ta ce Rigima suke jin yi Anty kinga ga kaya wai kowccen su bata so." Na ce to ki barsu kowa ta ?auki wanda ta ke so mana ina ganin ai kamar ba matsala ko? Rahin ta ja baya tace "To ku za?a amma don Allah kar ku zubo kayan domin shirya su ba ?aramin aiki bane durowa uku, aiki ne." Nace kije kusa sai su nuna miki sai ki ciro wa kowaccen su yadda ba zai ?aci ba ko? Ta ce "To " Yara suka bini da kallo sannan suka kasa nuna wanda suke so. Nace In za?o muku? A tare suka ?aga kai.
Na dubi Rahin anko ake yi musu kullum?. Tace "Wani lokacin suna sa daban daban." Nace Hajiya tafi son su sa kaya iri ?aya? Tace "Ban ta?a jin Hajiya ta yi magana akan haka ba ."
Na kama hannun su suka nuna min duk abinda suke so, nace to muje ?akina sai in shirya ku a can. Da sauri suka yarda suka bini Rahin ta bini da kallo. nace ki gyara musu kayan kawai.

A Kan gadona nace su hau Meema tace "Hajiya ta hanamu tace gadonmu kawai zamu hau amma banda na manya." A raina nace tofa! Sai nace ai Hajiya bata nan kuma ni bazan fa?a mata ba. Sai suka kalli juna, Mubina ta zau a kan kafe ?in gaban gado, Meema ta ce "Hajiya ta fa?a mana in bata nan Allahnta yana nan, kuma zai ganar da ita inhar muka yi ba daidai ba. Na sauka kan Kafet ?in batare da na sake magana ba, nace bari a fara shirya Anisa ita ce 'yar ?arama ko? Meema ta ?aga kai, sannan tace "Anty ke ?in wacce ke ma nan gidan ki ke?" Nace ni Mominku ce, ba sunana Anty ba. Mubina da Anisa duk suka kalle ni , Mubina tace "Kema a nan gidan ki ke?" Nace e mana ga ?akina ma. "Kece Momin da Dady yace zaki zo in anyi biki?" Inji Meema. Nace la! ashe ya fa?a muku, to ni ce. Anisa tace "To Momy anyi bikine?" Nace anyi jiya yau ma za ayi. Suka fara murna." Na gama shirya su muna ta 'yar hira suna min tambayoyi na shirme ita biye musu domin ni ina son hira da yara don haka naji sun shiga raina domin na lura suna da wayo. Na gama musu fesa musu turare, Meema ta kalli wayata "Momi in ?auki wayar ki?" Nace me zaki yi da ita? Mubina ta amshe da cewa "Akwai game a ciki?" Nace babu amma ku zo in ?auke ku hoto mukayi hotuna ni da su. Nace to sai ina? Suka ce za suje gaida Hajiya ne. Nace to ai ni baku gaishe ni ba, suka ce Hajiya ake fara gaishewa sai Dadi shikenan sai mu gaisheki. Nace to haka ya yi daga nan su gaishe min da Hajiya. Suka tafi ina bin su da kallo.

Goma saura na saka hijabi na fita, na nufi gurin Hajiya na tsugunna na yi mata sannu da hutawa ta amsa, nace nazo gurin yin aiki. Ta nuna min ?ofa da hannu bi nan zaki samu su Juma a kicin.
Hajiya ta bi Baby da kallo cikin wani kallo na nazari, kamar kowace amarya dai haka take zuwa a nuna mata kuxin ?arshe dai abinci ya ?i ciyuwa, ta ta?a baki bari dai mugani, domin ta lura yadda abubuwa ke faruwa a safiyar yau ana samun ?an banbanci da wanda suka faru a matan da Shamaki ya aura, a safiyar farko misali in ya bar gurinta ya nufi ?akinsa don ya shirya ya tafi kasuwa ya kan ?auki lokaci bai fito ba, haka ma dai a wannan karon, ya ?ata fiye da awa ?aya sai dai banbancin da ta lura da shi shine fitowar wannan karon akwai banbanci da na sauran, a yanayin sa a fili yana cike da nisha?i da kamanin angwaye, sannan kayan da ya saka ta tabbatar ba za?in shi bane domin tasan a guri ?aya yake saka babbar riga shine in zashi wani taro. Tace Allah ya sa dai a dace. Ta mi?e domin yin sallar walha.

?aton kicin na riska kuma na zamani ta window kuma na hango wani kicin ?in na gargajiya inda wasu mata su uku suke ta aiki. Juma kuma tana ?arar magi, na yi mata sannu ta ce "Amarya kin fito?" Nace e, tace "Muje in nuna miki an gama suyar kaji, wannan ma magin fefe ?in da za'a yi ne na ke barewa." Nace Sannun da aiki, Mukaje na gani na yi musu sannu. Suka ce Me za a dafa?" Naja Juma gefe nace me ki ke ganin Hajiya tafi so a taro? Tace "E to tunda kin tambaye ni zan fa?a miki, muna yi shinkafa jalaf, tuwo, da alala, waina sinasir funkasau da sauran su, amma yanzu kin ga babu maganar waina ko sinasir, tuna da ba a tashi yin su ba yanzu ko ba gaskiya ba, sai dai a ?ara da wani abin." Nace in akwai kayan ?anwake za mu iya yinsa, da kuma dambu da funkason ko kina ganin mutane ba za su so su ci wa?annan ba?
Tace "Yannan ki ke maganar ba za su so shi ba,ai yanzu babu abinda ke kwantai in dai abinci ne. Muna da ?arjajiyar shi kafar dambu sai dai bata da yawa sosai, in kuma na kuskus za ayi to." Cikin sauri nace A'a za a yi shi haka ai ko ?anwake ba mai yawa sosai za ayi ba, na tare maganar kuskus ne domin ban ta?a yin na kuskus ba.
Tace 'To ki fa?i gaba ?aya abinda muke bu?ata wanda babu sai a kaiwa Hajiya list za ta aike ni in siya." Na ?an yi shiru, sai dabara ta fa?o min nace tuwo da kayan shinkafar ki lissafa ki fidda wanda babu, ni kuma sai in lissafa miki na dambu da ?anwake. Nayi haka ne dan su nafi iyawa. Haka dai muka tada lissafin tuwo za ayi miyar ganye da agushi shinkafa soyayya sai alala da funkaso dambu da ?anwake. Haka dai aiki ya rinca?e mana danma suna da hanzarin kuma komai an ?ora wasu akan gas ga kuma murahu. Ina yi ina addu'a Allah ya fidda ni kunya ?arfe ?aya da rabi komai ya kammala sai tuwo da suke ?auewa a leda Gida ko ina ya ?auki kamshi. Gaskiya su Juma sun iya girki kuma sun taimaka min sosai. Suka ce inje tunda kwashe tuwo ne ya rage in sun gama sai su kai inda aka jere komai.

Hajiya tana salla a. Falon ya soma cika da Jama'a yaranta duk sun iso da 'yayansu, na rusuna na gaida kowa sannan na nufi gefe na. Maman Nana tana cewa yanzu Maman Iman ke cigiyar ki. Nace ina kicin ina take? Tace tana salla, na ce nima bari inyi sallar
Na shiga ?aki zan shiga wanka sai naga wayarta a kan gado, sai lokacin na tuna da wata waya, na ?auka dan in duba ko an kira ni.
Kiran Shamaki yafi goma ga sa?o na fara duba sa?unan, magiya ya ke in naga kiran shi don Allah in kira.
Cikin rawar hannu na danna kiran shi tana shiga ya ?aga. Baby lafiya? Nace lafiya Lau, ina kicin muna aiki ne,ban tafi da wayar ba. Yace "Ko ina ki ke Baby ki zama da wayarki a hannu, na manta zaki yi mana girki, kinji yadda hankali na ya tashi ne ka?an ya rage in taho gidan." Nace da ka kira Hajiya zata fa?a maka cewa ina kicin. Yace "Ta? to ya za'ayi in iya kiran Hajiya in tambaye ta ke, akwai bu?atar ki lura da abubuwan da basu kamata ba. Ya ki ka san zata kalli abin?" Na yi shiru domin banga wata matsala game da hakan ba to kullum sai Hajiya ta yi abinda na sha mamaki. Yace "Tunda kina lafiya shike nan, dama dai inji muryar ki ne, yau na zama cikin yawan tuno ki da miki addu'a. Kin dasa wani abu a zuciyata iya jiya zuwa yau, dan Allah Baby kar ki canza ta min yaya. Kowa ya ganni a kasuwa sai ya yaba da kayan da ki ka za?a min kuma kin san abin mamaki na ta?a saka kayan amma banji wanda ya ce na yi kyau ba sai yau, har wa?anda ba su san na yi aure ba da sun ganni sai suce

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login