Showing 39001 words to 42000 words out of 55418 words
labari a halin na fa?awa Jamila zan ke kira ina samun labarin halin da Umma take ciki amma kona kira bata ?agawa. Shima Abba shiru, shikuwa mijina fushi ma nayi ban ?ara gwada wa ba. Addu'o'in dai ba irin wadda bana yi.
Sautin wayata ya sa na tashi da gudu na nufi ?alkota ina dubawa Shamaki ne, na zauna a ?asa ina kallon wayar harta yanke, ya sake kira har lokacin ban ?aga ba. Gani nake babu wani amfani ko na ?aga. Karan da wayar ta addabe ni da shi ya ci gaba da kirai shi ya sa dole na ?aga amma ban iya magana ba na kara a kunne Yace "Baby Ina meeting a Abuja lokacin da ki ka kirani yanzu ina filin jirgi nan da minti talatin ina Kano me ya faru?" Na saki sabon kuka, cikin muryar da na yi kuka na gaji nace Umma ta mutu ina ta kiranka baka ?aga ba ?ilama yanzu an kaita. Yace "Wace Umma?" Nace Ummanmu na kashe wayar na ?ora sabon kuka.Ni na gama yanke wa tunda suka ?i ?aga wayata bashakka Umma ta mutu na rasa ta har abada.
Shamaki ya yi tsam a filin jirgi ya ?aga waya ya kira Number Abba. Abba ya ?aga Shamaki ya gaida shi cikin girmamawa, sannan yace "Yarinyar nan ce ta kira ni tana min kuka
"Wai da gaske ne Allah ya yi wa Umma Rasuwa?" Abba yace Baby akwai ru?a??iyar yarinya, shiyasa ban so Jamila ta fa?a mata ba. Kuma shine dalilin da ya sa nace karsu ?aga kiranta.Ummansu addu'a take bu?ata, bata rasu ba yanzu dai sun ce mu tafi asibitin Malam Aminu Kano. Aiki ne za'ayi mata. Shamaki yace Abba ina ganin ku tafi asibitin Zeena Hospital zan sanar da likitan kafin kuje ya ?u?e mata fayal.
Abba yace alhamdulillah na gode Aliyu Allah ya sa a mizani. Yace ba komai sai munzo asibitin.
Ban kuma ji daga kowa ba har magariba.In
Kwance inda nayi salla. Juma ta shigo da abinci ta ga na rana yana nan. Tace "yannan ki daure ki ?an ta?a mana." Nace Baba Juma karki aje ha?a duka bazan iya ci ba. Tace "Banga laifin ki ba yarnan Uwa ta wuce wasa. Kuyi addu'a Allah ya fisshe ta. Nace Ameen. Yau ce ranar farko da na ganshi ya shigo a irin wannan lokacin.
Ban Ko ?ago ba bare in dune shi. Ya tsugunna a gaba ya sa hannu ya ?ago ni fuska ta ta yi suntum yace "Subhanallah Baby kinga fuskar ki kuwa? Na soma sabon kuka ya rungume ni ki samu natsuwa, ki shirya muje Asibitin mu duba ta. Nace bata mutu ba?
Yace ta samu sau?i muje
ki tabbatar Na tashi da sauri na shiga ciki na wanko fuska na saka Hijabi yace "A' a ki canza shiga mai kyau, sannan ki ci wani abu naji tace haka ki ka yini.
Nace zan canza shigar amma abinci kam ka min afwa sai na ga jikin.
A falon Hajiya mun rusuna ya sanar da ita cewa mun fito. Tace Juma ta ha?a abincin da za'a kai asibitin.
Muka fita tana cewa mu yi mata sannu.
Muna baya Bala direba ya na jan mota muna baya ya sar?e
hannuwanshi cikin nawa har muka kai Zeena Hospital. Nace
ba Murtala aka ce ba ? Yace "?ila daga can aka turo su nan." Muka shiga ni dai da kyar nake cire ?afa, ban damu da gaisuwar girmamawar da Nurse ?in ke yiwa Shamaki in mun ha?u da su jifa jifa ba. Ya kira yaawar wani yana tambayar sa da turanci lambar ?akin. Ya fa?a masa har mun ?an wuce sai muka dawo baya. Abba na zaune bakin gadon da Umma ke bacci ya ri?e mata hannu da ake yi mata ?arin jini.Kan tabarma kuma Jamila ce da Umman su Amina.
Da sauri naje na ri?e mata hannu Abba ya ce ai bata farka ba ,bayan anyi aikin. Na dubi Abba da sauri nace wai dama aiki aka mata. Ya ce "aiki aka yi mata 'yan ta wahala kukan ta ?aya da aka ciro ta ta koma ga Allah." Allahu akbar, ina take Abba. Yace "An rufe ta ?azu nan kafin magriba ita kuma sai mu yi fata Allah ya bata lafiya." Muka amsa Shamaki suka gaida da Abba ya masa ya maijiki daga nan yace zaije ya duba wani ya dawo,ya fita .
Abba ya ce ki bi mijinki sau da ?afa dubi abinda ya yi mana banda shi da sai dai Ummanku ta mutu domin bani da ku?in da za a yi mata aiki. Na dubi Abba shine ya biya? Abba yace komai da komai. Bala direba ya shigo da kayan abinci Jamila ta amsa ta na yi masa sannu, suka gaida da Abba ya tambayi mai jiki sannan ya fita. Shamaki suka shigo da likitan na gaida shi. Likitan ya yi bayanin cewa saura minti arba'in ta farka anyi aikin cikin nasara kuma zata tashi lafiya lau. Sai yanzu na ha?iye wani tarin abu da ya ma?ale min a wuya. A fili na furta Alhamdulillah yace da ta farka kar su bata komai su sanar da shi.
Shamaki yace zamu tafi sai kuma gobe zamu sake zuwa. Nace ya barni in kwana,wata tsawa da Abba ya buga min bansan lokacin da a nayi waje da sauri ba.
Muna zuwa gurin mota Sahamaki ya ba Malam Bala ku?i yace ya hau mashin ya wuce gida bari shi ya ja motar zamu biya unguwa ne.
Na koma gaba ya ja muka tafi. Kawai gari muka yi ta zaga wa muna hira yana ?an Min wasanni, mushiga wannan Supar market yace in ?auki abinda nake so har goman dare sannan muka nufi gida lokacin zuciyata ta yi sanyi ta cika da nisha?i.
Muna shigowa Azima tana shafawa Hajiya maganin ?afa duk suka bimu da kallo, na ajewa Hajiya ledar hannu na domin naga tana kallon ledar. Tace Menene? Shamaki ya ce turarene mun biya na sayi nawa ne shine na sai muku,ta sa albarka ta tambayi yana yi jiki muka ce da sau?i. Nan da na barsu na tafi ?akina. Na yi salloli sannan na shiga wanka na shirya na nufi ?akin mijina.
Washe gari da safe da ya shigo daga gurin Hajiya zai yi shirin kasuwa nace zaka sa a kai ni asibiti ne ko in zaka kasuwa ne zaku sauke ni?
Yace jirana ake yi bazanbi ta can ba,amma game da naki zuwa ki tambayi Hajiya inta ce ki je zata sa a kai ki. Na yi sororo ina kallon sa kamar in ce Hajiya nake aure?Sai kuma na fasa na fita zuwa gurin Hajiyar irin tambaya tun yana gidan.
Na rusuna na sake yi mata sannu da hutawa, sannan nace Shamaki ne ya ce in tambaya ko zani asibiti? Jin shiru ya sa na ?ago na dube ta itama ni take kallo a zuciyata ta nace kema dai Uwa ce kinsan zafinta. Ga mamaki na sai baki tace ki je ki buga musu yawa kiji lafiyar ta, babu bu?atar zuwanki. Na rusunar da ?wayar idanuna sannan na mi?e tare da furta to. ?akina na koma na zauna a kan gado na ?ora sabon kuka. Ina jin shigowar shi ban ko ?ago na kalleshi ba , ya zauna kusa da ni yana tambayar abinda ke faruwa. Nace ba komai. Yace "Hajiya ce ?" Nace 'A 'a . Ya mi?e tare da fa?in shike nan ni zan tafi kasuwa, na mi?e ina share hawaye na amshi jakar kamar kullum domin yi masa rakiya.
......
Na raka shi har falon ?arshe ya amshi jakar ya ?ago fuskanta ki daina kuka ya kawo bakin shi kunne na ya ra?a min cewa zanbi ta asibitin zan kira ki in fa?a miki yadda jikin yake kinji?" Nace To kace cewa Umma don Allah ina son zuwa ban samu dama bane ina son in ganta kuma ina yi mata addu'a .
Wasu hawayen suka biyo kumatuna, ya sa hannu ya share yace "zan ha?aku da ita a waya. Nace to. Yace "Share hawayen ki" Nasa hannu na share sannan ya fita ni kuma na dawo, zan wuce nace cewa Hajiya sannu da hutawa. Ta amsa da "Yawwa."
Haka na koma ciki naci gaba da 'yan ayyuka na. Na gama na koma na kwanta . Gurin ?arfe goma sai ga kiran shi na ?aga. Yace gani a Asibiti jikin Umma ya yi kyau sosai ki je video call zan kira ku gaisa. Da rawar jiki na shiga video saiga Umma zaune tana min magana cikin murna na gaishe ta, nace ya jiki? Tace "Jikin da sau?i Alhamdulillahi ya naki jiki?" Nace na samu sau?i. Tace "Ki daina kuka akan sai kinzo tunda ba da?in jikinki ki ke ji ba, sannan ki yi godiya gurin Hajiya surukarki muna ganin aiken abincin safe da yamma Allah ya ?ara ?aukaka." Nace to zan fa?a mata, yanzu dai babu inda ya ke miki ciwo? Ta ce. " Babu inda ke min ciwo Baby ki kwantar da hankali ki, ki ?araiwa mijinki godiya ya taimaki rayuwata sosai." Nace To Umma. Muka yi sallama.
Naji da?in ganin Umma ta sami sau?i kuma ko da Hajiya ta hanani zuwa ashe tana aika musu da abinci, sannan bata hana mijina zuwa ba ya duba Umma ba.
Kwanan Umma uku a asibiti aka sallameta amma Hajiya bata barni na je ba, koda yake ban tambaya bane ina jin tsoro, da nace zanje sai ya ce in tambayi Hajiya. Ni kuma sai in yi shiru bana sake maganar , kuma ko a fuska bana nuna wata damuwa. Amma kira inna kira su sai munyi waya da kowa a gidan har su Jafar. Na dangana na zubawa sarautar Allah ido. Ranar da zata cika sati ?aya da 'yar tana raye sai a ce ranar suna, 'yan Kurna za su zo da ?awayen ta za'ayi ?an taro. Jamila ce ta tsegunta min gaskiya ina son zuwa dan haka tun yau na rubuta mashi sa?o cewa ina son gobe zanje gida in duba Umma saboda za 'a yi ?an taro.
Shina amsa ya aiko min da ita kamar kaka..." Ki je ki sanar da Hajiya." Na yi shiru cikin tagumi Hajiya ke aure na da komai zai ce in tambayi Hajiya. To shi mai zai hana ya tambayar min. Na danna kiranshi. Ya yanke ya kira ni. Na ?aga. Nace ya kasuwa? Yace "Alhamdulillah" Nace dama zance ne ko zaka tambaya min Hajiya ?in wallahi ni sai inke jin tsoro kar ta ga kamar na matsa mata.
Yace "Baby haka dokar gidan ta ke, ke zaki tambaya da kanki in taga ya dace shikenan zata barki, har yau baki fahimci Hajiya bane shiyasa ki ke jin tsoronta. Ki tashi yanzu kije ki same ta ki fa?a mata uzrin ki, in ta yarda shike nan." Nace To bari in gwada, mu kayi sallama.
Lokacin ?arfe uku zata yi domin an yi azahar. Na sameta tana karatun wani ?aramin littafin. Na dur?usa na gaisheta sannan na ce Hajiya dama ina son in tambaya ne ina son inje gida in duna Umma da jikin ta, goben ta ke kwana bakwai.
Ta ?ago kai ta ce za tayi taro kenan? Nace 'yan uwanta ne zasu taru. Ta yi shiru na ?an lokaci sannan tace "Mijin ki zaki tambaya Ni menene nawa?" Nace ai na tambaye shi yace min duk abinda ki ka ce shi za'ayi. Ta sauke ajiyar zuciya "Kira min Juma." Da sauri na mi?e domin kiran Juma. Tare muka shigo, tace "Juma dubi yarinyar nan sosai ki gani ta canza daga yadda ta zo gidan nan Ni kullum juya iyau na ke ganinta?" Juma tace ta canza gaskiya ta murje ta yi haske Hajiya ai dole a canza kinsan hutu daban ya ke. Hajiya ta dube ni. "Jeki Allah ya kaimu goben zan duba in gani inzaki samu zuwa.
Na ce to, ko fuska ban canza ba har naje ?aki. To ranar ma dai Shamaki bai dawo ba, daga can wai ya tafi Lagos sai text ?insa na gani, wai tafiyar gaggawa ce .Lamarin ya fara sani tunanin ko dai ba wani so da mutumin nan yake yi min. Bana samu wata kulawa da na ke bu?ata in nayi la'akari da yadda na ke karantawa a littafai, ko 'yan unguwar mu da na kan ga sun fita da mazajen su irin da da dare haka suna ?an zaga gari suna shan iska. Ni gani a kulle ba aikin fari ko na ba?i, bani da ko sisi sai dai inyi kallo in ci insha, ko hira mu yi da mijina ta gagara har yau bansan abinda ya fi so ba, shima bai san abin da na fi so ba ko wanda bana so ba .
Da safe bayan na gama komai naje na sake rusunawa gaban Hajiya nace dama na zo ne inji ko in shirya? Ta dube ni, "Kin fa?awa mijinki? ". Nace tun jiya yace in kin amince sai inje. Ta ce to yau kun gaisa da shi?" Nace 'A 'a, da sauri tace "To saboda me mijinki baya gari amma baki kira shi ba?" Na daburce nace na kira bai ?aga bane shine na aika mishi sa?o. Tace "Karantamin sa?on inji." A zuciya ta nace iko sai Allah. Na ?auki wayar na fara karantawa.
Fatan ka tashi lafiya,na kira ka baka ?aga ba,nasan kana cikin uzri dama dai zan gaishe ka ne, fatan zaka dawo lafiya Allah ya bada abinda aka je nema.
Ta dube ni tace "Ameen" Kin kyauta sosai ki yi ta yi wa mijinki addu'a, sai dai ba irin ?an sunan nan na ku na zamani yadda zai ?anji sanyi da irin "yan kalamai haka masu da?i? Na sunkuyar da kai. Hajiya dai son kanta ya kai inda ya kai.Na fa?a a zuciya, a fili kuma nace, zan gyara insha Allahu. Tace "Yawwa ai gara a gyara ?in. Kije ki shirya sai direba ya kai ki, ?arfe nawa zaki dawo?" Cike da murna nace duk lokacin da kika ce . Tace ki zama cikin shiri daga ?arfe biyu zai koma ya ?akko ki.
Ina fita falon na she?a da gudu ?akina harda rawa ina ?iban shoki tsabar murna. Na shirya tsaf cikin shigar Atamfa. Gaskiya na ?an ciko komai nawa ya ?an ?aru.
Na fito falon Hajiya na zauna a gefe. Ta dube ni. "Antyn zumu?i har a shirya kenan, to inga jakar me zaki kaiwa Ummar ta ?i?" Nace mi?a mata tare da fa?in ba komai zandai je in ganta. Ga mamakina sai naga ta caje kakar sai 'yar hoda ta ce sai tissue. Ta mi?o min jakata. Sannan ta ce Haka" zaki gidan hannu rabbana?" Nace to ai Hajiya Ni bani da abinda zan ba su. Tace Ai abin kunya ne kina auren mai ku?i kamar Shamaki amma kije gida hannu na dukan cinya haka, ba da?i ai kyanshi ace kinje jakar nan cike da ku?i duk wanda ya halarci taron sai ki bashi wani abu."
Take zuciyata ta fa?a min cewa Hajiya tana da wata manufa a maganar ta. Nace to ni kuwa Hajiya ina zan samu ku?i har in yi hakan? Tace "Ga Mijin ki da kin kira shi sai ya tura miki ta account ku biya da direba ki cire."
Na sunkuyar da kai ina ta nazarin maganar Hajiya duk da cewa sak ta yi maganar kamar daga ranta, amma sai najii a jikina cewa Hajiya tana sane ba domin Allah ta yi wannan maganar ba.
Ta katse min tunani da cewa "Ki kira shi mana." Nace Hajiya ni ko account ?in ma bani da shi,,kuma banda haka ma yaya za 'ayi yana irin wannan wahalar ko isasshen lokacin kansa baya da shi amma sai inkirashi ya bani ku?i ba tausayi kenan, inda ace haka ake yi Hajiya da ba'a kawo haka ba. Mu gode da irin ?awainiya ta kai abinci Allah ya saka a mizani, suma suna ta godiya su Umma da Abban. Ta zura min ido,can tace shike nan ki shiga ?aki na zakiga wata leda a saman gado na ki ?akko min." Nace to, na mi?e ita kuma ta ?auki waya tana kiran