Showing 54001 words to 55418 words out of 55418 words
sani ce kuwa,kai abinnan fa da ban tsoro. Sam ban fa?awa shamaki ba,sai dai Hajiya na ?an ja jiki da zuwa gurinta isai in yana gurin, duk da cewa bata sake yi min maganar ba. Umman mu ta sanar da ni tana son ta zo ranar lahadi domin ta ga ?akina tunda bata ta?a zuwa ba, nace Allah ya kai mu. Da dare ina yi wa Hajiya tausa suna hira da Shamaki nace Yawwa Hajiya Ummana tace zata zo ranar lahadi ta ziyar ce mu. Ta ?ago ta dube ni "Wace ce Ummarki?" Yau ne naji na fara jin haushin Hajiya domin zan jure ni amin komai amma bazan jure a ci zarafin iyayena ba. Shamaki yace mahaifiyar su mana. Ta kalle shi "Ta sanar da kai kenan?" Yace nasan dai ita ce Umman su.. Na kasa ?ago kai dan haushi. Yace Allah ya kaimu amma dai harda su Jamila zata zo ko?" Ya tambaye ni,kamar yana son ya gane ko raina ya ?aci ne ko kuma ya san cewa ba ayi min adalci ba. Hajiya tace "Yaushe ki ka ce ma?" Na dube ta cikin murmushi takaici nace Hajiya ka wai zance ta barshi ba sai ta zo ba in zuwan nata akwai wata damuwa ne, ni sai in saka lokaci inje ta ganni. Hajiya tace "Tace yi 'yar dariya tare da fa?in yau dai na ga hassala a fuskar ki Rabi'atu ba yadda za a yi mahaifiyar ki baza ta zo gidan ki ba, domin gidanki ai nata ne. Sai ki fa?i abinda ya kamata a bata in zata tafi." Nace ba sai an bata komai ba Hajiya, ita kawai zata ziyarce mu ne.
A ?aki Shamaki yace ki yi hakuri banji da?in yadda Hajiya ta yi ba." Nace haba ya wuce ka wai. "Yace ki tuna min ana gobe zata zo,nace nan da kwana uku ne zan tuna maka.
Yace "Ina ta son mu yi wata magana kuma ina ta tunanin ta ina zan ?ullo wa lamarin ne.." Nace ka fa?a min mana. Yace kin san maganar Azima?" Nace wace maganar a ciki ta auren ku, ko ta ?arin da ta yi? Ya zaro idanun cikin rawar baki ya ke tambayar "Waya fa?a miki?" Na kama tafin hannun shi na sar?afe cikin nawa nace nifa 'yar gidan nan ce karka manta, dole zan sani, amma ka sani wajibi ne in rufe duk wani sirri na gidan aurena, wannan amana ce. Yace "Amma me kika sani game da ?arin da ta yi?" Nace bansan komai ba banda ?arin. Yace "An saka auren mu wata hu?u ina fatan baza ki shiga damuwa ba." Yawun baki na ya tsaya cak. Gaban sai wani irin duka ya ke yi. Na sa?ule hannu na daga na shi, nace a haba ba wata damuwa Allah ya baku zama lafiya, amma dai ita ma a gidan nan zata zauna? Yace "To shine dai har yanzu ba mu gama tattaunawa da Hajiya ba." Hawayen da nake ta ri?ewa ya kwaranyo min kafin in goge har ya gansu, ya tashi ya je ya kulle ?ofar ?akin shi ya zare makulin ya saka a aljihu. Ya zo ya zauna kusa da ni ya saka hannu ya ?ago fuskata ya saka yatsa yana share min hawayen yace "Nasan zaki fice ki tafi dakin ki ne kije kiyi ta kuka, bayan kin yi min al?awarin baza ki ?aga hankali ba." Na kir?iri murmushin ya?e, hawayen suna sake kwaranya,nace kayi hakuri ina ta ?o?arin inga cewa na tsaida hawayena amma na kasa. Yace, "Karki damu fa, ko mata nawa zan kawo Baby kinsha gaban kowace a zuciyata, kuma Baby ke ce mace ta farko da nake shakkar in ganta a damuwa bayan Hajiya. Ki tattala hakan Baby ina da tabbacin za muyi rayuwa mai tsawo da tsawon rai." Ya ?ago fuska ta muka ha?a ido "Kinsan me yafi damuna?" Na girgiza kai, ya kai hannu ya ja doguwar rigata ya zura hannu ya shinfi?a shi a tafin cikina, na ?osa inga kin samu ciki,na fara tsoron ko akwai wata matsala." Nace duka wata uku da kwanaki ai ba 'a jima ba." Yace "An jima mana, mace bata wata a gidan nan sai ta ?auki ciki fa." Nace to muyi addu'a jinkirin ya zama alkhairi kuma duk ga yara a gidan. Yace "Wallahi ban ta?a samun kai na da son ganin mace da ciki kamar ke ba." Nace Allah ya bamu masu albarka.
Koda ya ci gaba da sarrafa ni domin biyan bu?atar sa yanayin kishi bai barni na taimaka masa ba kamar yadda muka saba, hasali ma hawaye na na ci gaba da zubdawa har ya samu kansa. Ya dube ni yace "Yau dai ni nayi ki?a na da rawata ko Baby?" Nace kamin afwa da uzri. Yace shike nan muje muyi wanka.
Gaskiya ina da kishi mai yawa ?iri?iri na kasa bacci kuma duk da na tashi na yi sallar dare na fa?awa Allah damuwa ta hakan bai hana zuciyata sa?amin cewa in nemi saki daga gare shi ba. To amma ya zanyi da wutar sonshi da ke ruruwa a zuciyata.
Ranar Lahadi tamkar ranar salla ce a gurina tun safe kowa na gidan ya fahimci hakan Shamaki ya ce to in har Umma zata zo da wuri zata iya samu na, nace bari in kira inji. Jamila na kira na tambaya ta ko da wuri Umma zata zo, sai tace sha biyu zata zo ta dawo ?arfe biyu.
?aya saura wayar ?akina ta yi ?ara,na ?aga Hajiya tace "Ki zo ga Ummanki da murna nace To.
Na fito da sauri ina shiga sam na manta da kowa ita kawai idanun na ke gani a falon naje na rungume ta ina fa?in Oyoyo Umma. Tace "Kai jama'a to ?agani mana. Na tashi na zauna muka gaisa, na kalli Hajiya wadda ta zuba mana ido tana murmushi. Tace "To kije ki ce Juma ta kawo mata abin sha da abinci." Nace Umma ina su Jafar ke ka?anki wai ki ka zo? Tace "Abbanku ya hana." Nace Allah sarki ina son in gansu. Na tafi gurin Juma nace a kawo wa Ummanmu abinci. Tace "Au dama Ummanki ce ba?uwar da Hajiya ta sa ayi wa girki na musamman? Lallai ke da alamu kina samun shiga a gurin Hajiya,ko kuma ku ?arawa malamin ku sadaka domin ina ganin canje canje a gurin Hajiya." Nace ki kawo mata abincin yanzu. Tace "To za 'a kawo yanzu, ?akin ki za"a kai ko kuwa gurin Hajiya? Ina ki ke ganin zai fi dacewa? Na tambaye ta. Tace "Tunda ki nemi shawara za a baki tsaya kinibibin cewa a kawo musu ?akin ki ba, a kai mata gurin Hajiya su yi hirar su ta manya. Sannan kar ki tsoma musu baki wai domin kinga Ummanki, abu na gaba ki jira har sai Hajiya da kanta tace Ummanki taje ta ga ?akinki. Nace Na gode Baba Juma. Na dawo na zauna a gefe shi Shamaki ma ya shiga ciki. Nace Hajiya suna shiryo abincin. Hajiya ta zura min ido tana tambaya ta. ?akin ki za'a kai mata ne?" Nace A"a nan dai gurin ku ko Hajiya..Juma ta zo tana jerewa. Umma tace kayya sai da na gama abinci na taho a ?oshe nake. Nace haba Umma ai dai ko yaya kyaci abincin gidanmu. Hajiya tace "Ai wajibi ne ma ki ?auki plate ki zuba mata, sai kije mijinki ya shiga ciki zai shirya ya tafi kasuwa." Umma ta yi karaf ta ce kije ki sallame shi zanci kafin in tafi yanzu dai bana jin yunwa. Nace to. Na tafi da sauri, na same shi yana waya da wasu kwastomomin shi ya ce zai fito nan da awa ?aya.
Na bu?e durowa na fara za?o mishi kaya, ya kamo ni "Zo nan mana kinsan yadda ki ka fito da murna da tsalle ki ka fa?a jikin Umma ina kallon ki sai naji kawai ina bukatar ki, dama yanzu zanje in kira ki. " Cikin mamaki nace haba dai aiko ka ?aga min ?afa yau ?aya Ummana ta zo tana gidan fa kuma ba jimawa zata yi ba, yace ai nima ba jimawa zamu yi ba...
KARSHEN LITTAFI NA BIYU
Mu hadu a littafi na uku
Taku Halima Abdullahi K/Mashi.