Showing 15001 words to 18000 words out of 55418 words
yana bin kumatuna lokacin da na kalli gurin da jama ar dake gurin a domin ni, a zuciya ta fa?i na ke, Allah na gode maka. Allah ka sa in masa biyayya. Da muka zauna yace kalle ni sai yaga hawaye. take ya rikice ya sunkuyo gurin kunne na yace. "Baby me akayi ba daidai ba? Kukan me ki ke yi ne amaryata."
Na motsa baki zanyi magana sai muryata ta soma rawa, yace "To karki yi maganar, ya kai hannu ya ciri hankici a aljihunsa fari tas yasa hannu ya dafa ?ankwali na ta baya yana tsane hawayen fuskata cikin lallashi yana fa?in haba soyayyata zaki ?ata gayunki mana." Na ware idanu ina kallon fuskar shi a zuciya ta ina godiya ga Allah daya min baiwar miji irin wannan. Ya ?akko ZEENA table water ya tsiyaya a kofi ya bani. Yana fa?in "Sha masoyiya." Sanyinsa ya ratsa ma?ogwarona dai dai lokacin da MC yace " Kai Don Allah ku tafawa Ango da Amarya ha?i?a zai iya kula da amaryar nan tasa da kyau. Sai mukaji tafi da sowa sam na manta akwai mutane a gurin duk zatona mu biyu ne sai sautin dake tashi, na manta da akwai dubunan jama'a da ke gurin.
To haka dai aka ci gaba da shagali, abinda ya ?aure min kai kalaman da MC ke fa?a in zai ambaci ango ko danginsa, sai ya ce Shamaki Aliyu Ali Baita shugaban rukunin kamfanonin ZEENA. ?aya cikin Antys ?in shi ta zo gurinmu sai ya ce Hajiya A'isha Ali Baita kenan uwar marayu da marasa ?arfi shugabar ZEENA Foundation. Tofa! kaina ya soma kullewa duk yadda aka yi akwai abinda Yaya ya ?oye min. Haka da aka zo matakin rawa, sunyi watsi da sabbin 'yan dubu dubu har abin tsoro ya bani. Kuma ga masu kirari suna ta yi wa Yaya Shamaki Ali Baita. Suna fa?in shaharar ?an kasuwar nan mai ku?i da ake labari ko kwatance dashi. To haka dai aka kawo wani cake mai mugun girma inda muka yanka ni da Yaya, abin dai zallar al ajabi. Da aka tashi suka shigar dani wani ?aki aka kawo min abinci, nace na ?oshi ni dai bu?ata ta in je gida inga Ummana tun jiya ban ganta ba. Sukace ai daga goben zaki jima baki ganta ba. Da?yar dai na ci ?an cake na sha ?an lemo. Yaya ya zo yace in zo ya maida ni gida Abbanmu ya kira shi yanzu. Haka dai muka firfito kowa ya kama hanya. A baya na zauna shima haka abokinsa kuwa ne ke kanmu. Ya zura min ido ni kuma na ?i kallon sa, hardai na kasa jurewa na sa hanuwana na rufe fuskata ina dariya. Yace "Baby ji nake kamar in wuce da ke gidana gobe in an ?aura shike nan." Na saci kallon sa, dama ana yin hakan? Abokinsa da ke jan motar ya sako baki da fa?in "Za a fara yau." Na dafe bakina cikin kunya. Yaya yace Alhaji Shamsu me ya kawo kunnen ka. Shima ya sa dariya tare da fa?in "Ba da ku nake ba Ango da Amarya." Yaya ya matso daf da ni, ya kwantar da kan shi a bayan kujera yadda har ina jin iskar numfashinsa, a gurin kumatuna, ya ce, "Baby in ?an ta?a hannunki ?unshin nan ya min kyau sosai. Na waiwaya na masa wani irin kallo, ya hure ida nuna, na lumshe su gaba na yana wata irin fa?uwa. A cikin kunne na naji kalmar ina son ki Babyna. Na na?e hannuwa na a ?irji, domin tsigar jikina naji ta yi wani yarr tamkar zazza?i zai rufe ni. Alhaji Shamsu yace zumu?i. Duk muka sa dariya. Haka muka iso bakin lungun mu.
?????????
*HAMSHA?IYAR UWA????*
*NA*
*HALIMA ABDULLAHI K/ MASHI*
_PAID BOOK_
_Ku?in karatu ?600_
_Account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank a turo shaidar biya ta wannan number 08140004302 ko katin Mtn_
_Phone 08140004302_
*DOKA*
_Ban amince wani ya ?ora littafin nan a wani Social media ba,ko a maida mini shi Audio ba tare da iznina ba yin haka daidai yake da fuskantar fushin hukuma. A kiyaye_
*Masu son a Tallata masu hajarsu suyi magana ta wannan number 09068032427*
*Page 17*
Yace tsaya nan direba mai sa ido. Muka fito shine ya ri?e min rigata ta baya na tsallaka kwata, muka isa ?ofar gidanmu yace shiga ciki zan kira ki anjima. Na shige cike da ?okin ganin Ummana. Gidan ya cika da Jama a, 'yan ?auye da na birni. Innarmu ?anwar Ummanmu ta rugo da gudu ta rungume ni tana cewa ga amarya. Na samu su Umma da su Umman Amina a ?aki suna ta tattaunawa. Umman Amina ta ce ke 'yan nan dama ?an gida Ali baita ne mijin naki. Na yi sukuti ina ta sauraron su, suna ta murna. Ni kuma zuciyata bata murna, kuma na kasa gane me yakamata inji farin ciki ko takaicin Aliyu ya min ?arya. Ina son insan gaskiyar abinda ake fa?i. Na canza kayan jikina Umma tace inje gidan Umman Amina can zamu kwana da su Jamila domin gidan ya cika. Nace to sai inyi salla acan. Umman Amina tace zata aiko mana da tuwo in an ka?a miya. Nace ina su Amina tace in yi gaba sunje ?akko marka?en kunun safe ita da Jamila da Zuhra. Naje Dakalin ?ofar gidanmu na zauna jiran su domin dai abikin nan sune ?awaye. Sai ga Fati mai Awara, tace "Jamila ina amarsu." Nace ba Jamila bace. Ta zauna "Ashe kece da kanki, haba gaskiya naji ?amshi duk ya bu?e ko ina, amarya mai maganar zuma, kaga matan manya. Ai munje perty ke kuwa ina kika za?ulo ?an gidan Alhaji Baita? mamakin da kowa ke yi kenan Baby." Nace ina ya za?ulo ni dai, wannan amsar kuma shine zai bada ita ?an gidan Ali Baitan. Tayi dariya tare da fa?in "Koma dai menene kin dangwalo, yanzu ina zaki." Nace gidan Umman Amina can zamu kwana. Tace "Bari in fa?awa Umman mu sai inzo mu kwana ai duk mune ?awayen Maimuna ma tun ?azu ta ke zuwa nemanki." Cikin mamaki nace to sai kunzo. Na bita da kallo ina mamaki wai harda Maimuna yarinyar da ko magana bata min saboda Babanta yafi Kowane uba sukuni a lokonmu. Muryar Jamila ta sa na waiwayo ina kallon su sun taho da bokitai a kansu na marka?e Jamila tana ta ba su labarin gidan Maman Iman da kuma guraren data kaimu, wai ita tun daga nan ta san dangi arzi?i ne.
Nace to Zubaina ku nake jira ku shiga ku aje ku zo muje. Suka fara murna ga amarya ga amarya. Da sauri suka fito. Zuhra ta ce, "Wannan ?amshi Yaya Baby har kin koma kalar bota ?in." Nace kun fiye surutu. Muka kama hanya Jamila ta ce "Su Mariyan can lungun dama ?awayanki ne?" Nace wai ta gidan gurasa? Tace "Su." Nace ina ni ina wa?annan marasa kamun kai? Tace "To sau uku suna zuwa nemanki, kuma na gansu gun party sunsha rawa." Na kwashe da dariya, nace yanzu Fati mai awara ta barnan, wai zasu zo mu kwana kin san su dawa? Tace 'a' a, su da Maimunar gidan Alhaji. Gaba ?aya muka sa dariya. Zuhra tace "Ki kore su ne, saboda abokan ango suke yin wannan shishshigin ko suma wani zai ce yana so." Amina ta ce "Haka ne Yaya Baby. Na ce ba kora su zo. Kuma ba lallai akan tunanin su cewa Yaya shi ?an Ali Baita ne tunda har zuwa yanzu banji daga bakinsa ba. Jamila tace "Haba yaya Baby karmu ru?a kan ki mana, wace sauran hujja ki ke jira? Jiya ganin shi da 'yan uwansa ya isa hujja, ?ila ya dai ?oye miki ne ko yana son ya miki bazata ne, kuma salon ya birge, Abba cewa ya yi shi tun a katin gayyata ya so ya fahimci haka." Da sauri nace wake da katin a cikin ku? To ni ban ma tsaya na kula da katin ba. Amina tace "Mu shiga gida in ?auko miki." Tabarma muka baza a tsakar gida muna zama sai ga su Fati, nan suma suka saje da mu ana labari. Nace Amina ina katin? Tace "Shi nake dubawa na Abbanmu ne Allah ya sa bai fita da shi ba." Can kuwa sai gashi ta samo. Na kunna fitilar wayata ina karantawa. Tabbas iyalan marigayi A Baita. Shi kuma a sunansa sai aka sa Aliyu A.Baita, sam ban gane komai ba sai yanzu. Na mi?a mata kati tare da fa?in biri ya yi kama da mutum. Na Dulmiya cikin tunani, nifa zuciyata da son Aliyu Shamaki mai tsare kaya ko sai da kaya shagon mai gidansa a Zeena plaza kanti kwari ta kamu. Bawai Aliyu Ali Baita ba. Na ?auki wayata na soma rubuta sa?o zuwa ga Yaya. Kalmar da na soma rubutawa itace...Yaya akwai babbar matsa. Ina bu?atar sanin wasu abubuwa game da kai.
Ina tura sa?on na tashi naje nayi alwala na shiga ?akin Umman Amina nayi salla, ina idarwa Jamila tana shigo wa, ta zauna kusa da ni. "Yaya baby wai lafiya naga duk kin canza tunda ki ka karanta katin nan?" Na ce Jamila in har ta tabbata Yaya shine ?an Ali Baita to bazan aure shi ba. Ta rufe min baki da tafin hannunta. "Menene haka ki ke fa?a, maimakon ki yi murna ki ce Alhamdulillah Allah ya miki gata sai kuma ki ?ebo wata rigima? Na ce Jamila masu ku?in nan suna da wula?anci, in zargin nan ya tabbata Hajiyar da muka je gurinta ita ce mahaifiyar sa. Ta yaya zan iya zama da wannan Hamsha?iyar. Me yasa har zuwa yau bai fa?a min gaskiyar shi ba, dubi yadda 'yan matannan suka cika gidan nan saboda kawai zan auri ?an Ali Baita, ki tuna yadda za su yi dariya a lokacin da ya sako ni. Gara yanzu aji ni nace na fasa. Jamila tace "Duk wannan hasashen ki ne, waya fa?a miki zai sake ki?" Nace ya saki mata uku ni ce 'yar gwal? Tace "Shawara ta ?aya ki kira shi ku yi magana." Nace na tura masa sa?o. Ta amshi wayata da sauri ta shiga ta karanta abinda na rubuta. Ta kalle ni. "Wayyo Allah Yaya Baby, ya zaki masa irin wannan sa?on." Nace To me zance masa. Sautin kiran wayata ya katse mu, ta mi?o min "Gashi yana kira." Na ?aga tare da sallama. Yace "Babyna kin ci abincin kuwa?" Nace ba zan iya cin abinci a halin da nake ciki ba. Yace "Subhanallah me yafaru?" Nace baka ga sa?on na ba kenan? Yace Gaskiya babu wani sa?o da ya shigo cikin wayata. Ki fa?a min menene?" Amma kafin nan ?ifara cin abinci. Nace ba'a gama miya ba tukunna. Yace "To ki jira ni." Ya kashe wayar. Na kalli Jamila, na san ya gani kawai zai ce min bai gani bane. Jamila ta ce "Ki bari ya zo ?in karki yanke hukuncin da ba haka bane."
Shigowar 'yan gidan gurasa ya sa raina ?ara ?aci. Jamila tana ta lallashina da ?o?arin nuna min cewa ?ila ya ?oye min ne saboda wani dalili nashi. Ta tilasta min zuwa gurin da 'yan matan suke muka gaggaisa ana ta hirar gurin Party tare da kallon hotunanmu. Duk kowacce tambaya take wai ina muka ha?u da shi. Nace shi ya kawo kanshi har lungunmu, inda ya ganni. Maimuna tace gashi daga gani yana mugun sonki, ko ina a hoton yana kallonki. Wayata dake hannun Jamila tana tura min hotunanmu a wayar Mariya ta soma ringin. Jamila tace ga ango yana kira, na amsa duk suka bi ni da ido, na ?aga da sallama. Yace ina ?ofar gida. Nace sai ka ?aro gaba gida na ?arshe a lungun can zamu kwana. Yace "To ki fito ki tare ni." Nace to. yace "Kada ki kashe wayar fa." Nace to. Na saka takalmi ina ce musu bari in dawo, sai naji kusan duk sun amsa da to amarya. Ina fita yana ?arasowa ya aje ledar hannunsa, ya zauna a bakin dakalin. Na ?arasa na zauna, na gaida shi cikin girmamawa kamar yadda na saba. Ya amsa sanan yace "Fa?a min wane sa?o kika Turi min?" Na sunkuyar da kai cewa na yi akwai matsala. Na ?ago na dube shi, Yaya ka fa?a min waye kai?" Yace "Me kike son sani?" Kai ?an Ali Baita ne? Na jeho masa tambaya. "Me yasa kika tambaye ni?" Na juya masa baya, ka bani amsa kawai In shine me zai faru?" Ya sake jeho min tambaya. Ban yi soyayya da ?an Alhaji Baita ba, da Aliyu na yi soyayya talaka mai tsaron kantin Zeena plaza.
?????????
*HAMSHA?IYAR UWA????*
*NA*
*HALIMA ABDULLAHI K/ MASHI*
_PAID BOOK_
_Ku?in karatu ?600_
_Account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank a turo shaidar biya ta wannan number 08140004302 ko katin Mtn_
_Phone 08140004302_
*DOKA*
_Ban amince wani ya ?ora littafin nan a wani Social media ba,ko a maida mini shi Audio ba tare da iznina ba yin haka daidai yake da fuskantar fushin hukuma. A kiyaye_
*Masu son a Tallata masu hajarsu suyi magana ta wannan number 09068032427*
*Page 18*
Kuma shi zan aura inyi rayuwa da shi cikin yanayin akwai ko babu. "Ya matso daf da ni. Yanzu ma dashi zaki rayu Baby ni yaron Alhaji Baita ne amma ba ?an daya haifaba, ?an jire kanti ne." Na juya muna fuskantar juna.ka tabbata? Yace "Na tabbata kuma zan tabbatar miki da zarar an gama bikin nan." Na sauke ajiyar zuciya tare da fa?in to duk kashe ku?in nan