Showing 18001 words to 21000 words out of 55418 words

Chapter 7 - HAMSHAƘIYAR-UWA 2

04 Jul 2024

6003

da ake yi fa? Kuma a katin gayyata ka ?ora sunan Ali Baita. Ya ?ara ?asa da murya. "Ba zan iya hana su kyautata min ba Baby, saboda mun zama ?aya da su mutanen kirki ne hatta katin su suka buga sai ganin shi na yi. Kuma don Allah kar ki damu kanki kar ki saurari kowa abinda na fa?a miki kawai zakiji, ko mutane sun yi wata magana duk hasashe ne. abinda ni na fa?a miki shine kawai zaki y arda da shi kinji ko?" Na sunkuyar da kai nace To. Ya sauke ajiyar zuciya, "Yawwa amaryata, amma fa kin ?aga min hankali da ace ni ?an cikin Baita ne yanzu shike nan gobe sai a fasa aurenmu?" Na turo baki tare da fa?in e mana, ha?ura zanyi. Ya yi ' yar dariya maimakon kiyi murna kin samu mai ku?i." Nace ta? aini bana ra'ayin auren mai ku?i gara ma in muna tare kayi ku?in, ance suna da wula?anci ga sakin mace ayi ta mata gori, arziki, kaga kaina ka rabu da matanka har kashi uku kaga kuwa dole in yi ta kaina. Haka iyayen ta ba a basu daraja dan suna talakawa. To da in aure ka ka sake ni Yaya gara ba muyi auren ba. Ya ?an yi shiru. Can yace "Baby da aure da saki iri daya ne da mutuwa, nasan kina damuwa ne saboda na saki mata har uku, kar ki damu da wannan ke dai ki yi aure bautar Allah ,kuma Baby ni da ke alkawarin da zan miki duk juyi bazan sake ki ba, kema ina son ki yi min al?awarin cewa duk wahala bazaki guje ni ba." Cikin sauri nace na yi maka. Yace to "Mun kashe wannan wutar gobe kamar haka kina gidana jiya Abba ya kira ni zancan kafi na kayan ?akin ki. To jiyan ana fenti ne yau kuma mun tashi da perty , amma gobe bayan ?aurin aure sai akai kayan ko?" Nayi murmushi Wannan maganar ku ce ta manya. Yace "Haka ne, to ga kaji nan a leda da madara da sauransu don Allah ki ci ki ?oshi kinji?" Nace kai ka ci abinci? Yace "Hajiya a baki yau ta bani fura wai tun jiya banci komai ba kamar wani ?an ?aramin yaro ta ajiye Ni ta bani." Muka sa dariya. Nace kai ?an gatan Hajiya ne. Yace "Ke 'yar gatana ce, zauna in ba?i a bakin kema." Nace'A'a. Yace "To shike nan ki koma ciki ki ci sosai don Allah Alhaji Shamsu ya kawo ni yana jirana dan ya koma gurin iyalinsa da wuri." Nace wai dama kana da Abokai? Yace "E mana duk zaki san su a hankali." Na ?auki ledar na shiga ciki, shi kuma ya wace, na dawo ina le?enshi ya tafi da sauri. Yanzu kam hankalina ya kwanta koda ?arya ya yi min."
Jamila ta tare ni da fa?in "Me muka samu ne?" Nace Yaya da abinsa wai yasan banci abinci ba shine ya kawo min naman kaza. Nan fa suka ?auki sowa da gu?a suna fa?in wannan ango yana ji da ke. Kaji uku ne nace Jamila ta cire ?aya ta ?auki madarar ta ha?a ta kai wa su Umma, na ?auki nawa nace Amina ta raba musu. Muna gamawa sai ga mutane sun shigo da gu?a wai za ayi kamu, suka fesa min turare irin dai yadda ake yi a al'ada aka gama kowa ya watse sai mu 'yan kwana.
Cikin dare bacci ya ?aurace min wai gobe zan zama matar aure, na ?akko waya ta ina kallon hotunanmu da Shamaki, fa?in cewa na dace ma ?auyanci ne, Allah ne kawai ya bani shi ba wayona ko wata dabarata ba a kyan fuska duk da yana namiji ya fi kuma ko da ina mace ban san a gaba ba, amma ni da kaina na san bani da wata ?ira mai ?aukar hankalin maza ?an gara ko daga sama. Wata zuciyar ta ce gobe kamar yanzu muna tare da shi. Gabana ya fadi ni ba ?an?anuwar yarinya bace na san meye aure duk da bansan shi a zahirance ba, dole inji fargaba ban sani ba ko ina da budurcin da ya tambaye ni ko babu.

Sai dai ina da tabbacin ban ta?a zina ba. Ni dai har kiran sallar farko idona biyu ina ta sa?e sa?e daga binasi bacci ya ?auke ni. Da safe na yi wanka cikin shadda Maman Iman ta kirani ta ce ta turo direba zai kaini gidan kwalliya. Na sanar da Umma tace to muje da Jamila amma karmu jima kafin ?aura aure mu dawo.
Yau ?in ma dai kamar jiya, tsara min kwalliya tamkar wata 'yar tsana. Ta bani wasu kayan tace inyi canji cikin wani ?aramin akwati sai wata leda mai ?auke da sar?o?i a jikin ledar an rubuta DIJANGALA ENTERPRISE. Kenan acan suka sai min. Ta sa direba ya ?akko mu. Layin mu cike da mutane da motoci ya tsaya nesa ka?an da lungunmu dan ba gurin fakin, muka sauka mukayi masa godiya muka nufi lungunmu. Jamila ta ce "Yaya Baby kalli ?ofar gidan Abbansu Zuhra ki ga motoci kuwa.?" Nace kinsan ?an kasuwa in yana da mu'amala da mutane za su zo masa. Tace "kin dai ?i yarda." Nace wai bana fa?a miki yadda muka yi da shi ba a jiya, amma kina ta musu, ki barsu in an kaini sun ga gidansa sai su samuwa kan su lafiya. Mutane sai kallona suke masu min Allah ya sanya alkhairi suna yi har muka shiga gida. Ya cika ?ajim da mutane sai kallo ya dawo kaina.

?awayen dolena suka shigo duk sun sha wanka, sai ga mai hoto da me ?aukar bidiyo aka shiga ?aukar hotuna. Can Jamila ta mi?o min wayata "Kina da sa?o daga ango." Na duba da sauri, "Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!! Na zama mijinki Baby." Na ?ago a sanyaye na kalli Jamila, idanuna suka cika da hawaye, ta ce "menene"? Sallamar Abba ce ta sa na maida kallona gareshi, yana fa?in "Alhamdulillahi an ?aura Allah ya basu zaman ha?uri. Sai hawayen suka kwaranyo bazan iya fassara ko kukan menene ba. Jamila ta ce "Kingani zaki ?ata kwaliyarki ke da ki ke ta zumu?in zaki auri Yaya meye na kuka?" Nan abokan wasa suka taso ni a gaba. Jamila ta dubi Abba zai fita ga mai hoto ana ta ?auka. Tace Abba don Allah zo a mana hoto." Sai akace a kira Umma. A nan kam ban jure ba sai da na zubar da hawaye sosai hoton har su Jafar da Baba Habu ?aramin mu ga cikin Ummanmu.
Jamila ta jani ?akin Umma na canza kaya ta ?an goge min inda hawaye ya min jirwaye a fuska. Muna fitowa sai tankani ake yi dan kyau. Atamfa ce mai adon zaiba, ta ?auki ?inki. Lokacin aka ce ga angwaye za su shigo su yi gaisuwa a yi hotuna. Nan naga munafircin mata. kowacce ta maido hankalinta ?ofar shigowa.

Yaya da Abokansa ?amshin su ne ya fara shigowa kafin su shigo, ya yi kyau cikin shadda mai ruwan siminti tsananin kyan shaddar shine ya bayyana tsadar ta.

Ya murza hula sa?ar Gabas wadda ta tafi da kayan. Yadda kowa ke kallon sa haka nima nake ?are masa kallo, fara'a fuskarsa ita ta bayyana tsantsan farin cikin da yake ciki.Ha?orin Makkansa yana haskawa, ina son ha?orin sosai ya ?ara masa kyau.
Suka tsugunna suka gaida su Umma abokan wasanmu sai tsokanar sa suke yi. Jamila ta kamo hannuna tana fa?in "Kifito kin la?e kuma kina le?ensa." Na fito ya bini da kallo. Abokan suka ce mai hoto ya matso. Haka dai aka yi ta ?aukar hotuna Ango fara'a ta kasa yankewa. Murya ?asa ?asa yace "Baby ina son mu yi magana ga shi ko ina mutane." Nace to ya za ayi? Ko zamuje gidan Usman Amina tunda duk suna nan? Yace " Ina ne?" Nace inda ka same mu jiya. Ya ce "To." Har abokan muka taka da Jamila soron gidan muka shiga muka bar abokan da Jamila a waje tana yi musu tayin abinci suka ce walima zasu tafi yanzu. Muna shiga Yaya caraf ya kama hannuwana cikin ?oki, duka biyun yana musu wani irrin kallo, tsigar jikina ta tashi yarr, zan kwace sai yace "Kiyi ha?uri Baby an ?aura mana aure, tun a ,jiya ina son in shafa wannan fulawar amma bani da damar aikata haka, saboda nasan shara'a bata bani dama ba." Na jure yana shafawa da lallausan hannunsa sai kurum naji ya sunbaci bayan hannuna, ya kafe ni da ido, duk tsoro ya bayyana a fuskata cikin rawar murya nace, Yaya kar fa wani ya ganmu. Ya girgiza kai, muryar shi a sar?e ya ce in ?an rungume ki Babu?" Na kwace hannuwana da sauri, sannan nace suna jiran ka a waje fa. Ya matso naja baya da sauri nace Jamila. Ta shigo tana fa?in "Menene?" Ta kalleshi har lokacin ni yake kallo, batare da ya lalle ta ba ya yi mata alama da hannu wai taje. Ta yi yar dariya ta fita. Ya matso ina ja baya har naje bango daf dani ya tsaya ya saki ?an murmushi. "In Jamila ta iya cetonki yanzu anjima ko gobe wa zaki kira?" Gabana ya yi mummunar fa?uwa, na ganni wata 'yar tsuntsuwa a gabanshi. Muryata na rawa nace ina son inje in sha ruwa ne Ya yi murmushi. Yasa yatsa ya lakuci janbakin le?ena, ya lasa akan harshen sa. Sannan ya kauce gefe tare da fa?in "To soyayyata, kunga ga hanya nan nasan dai yanzu sai. in an rako ni, ko da yake zamu yi waya aiko?" Da sauri na nufi ?ofa ina cewa e zamuyi waya. Sai na ji ya saki dariya tare da fa?in "Matsoraciya." Mukayi sallama da su suka tafi ina ta bin Yaya da kallo, ashe dai shima ?in ba kyalle bane. Sannan ya ?ara jefa ni cikin tunani.
????????
?Maganganun shi sun jefa ni a fargaba, na shiga ?imuwa sosai, harma na kasa cin komai, kuka na yini yi, mutane suna zaton kukan barin gida ne, duk da cewa akwai hakan amma dai fargaban karon battar da zamu yi da Yaya ya fi komai ?aga min hankali.
Da taimakon su Jamila na yi ta canjin kayana. 'Yan kafin kayan ?aki sun dawo duk sun ru?e suna bada labarin gidana Gidan Hajiya Zeena ne. Sun gigice da ciye ciye da aka basu, wasu kuma suna murna sunga Hajiya Zeena. Nace to kenan dai Yaya ?ara rufe ni ya yi.
Jamila ta ce na fa?a miki, to ke menene na ki na ?aga hankali mai maimakon murana Allah ya baki sai ki yi masa godiya. Shiru na yi domin bazata fahimce ni ba.

Da yamma motocin ?aukar amarya suka iso motoci na gani a fa?a. Na ?an?ame Umma ina kuka sai lokacin naji duk auren ya fita kaina. Tace "Meye hakan kuma, ki tafi Allah ya bada sa'a ya albarkaci zaman ku ina fata zaki ?auki dukan shawarwarin da muka baki. Haka Umman su Zuhra ta ?an?are ni ina kallon Umma tana hawaye muka Fita gidan su Abban su Zuhra shida Annan mu suka min nasiha suna ta maimaita min in yi ha?uri, in zama mai yawan ha?uri har sai da na fara tunanin kalmar nan da ake ta nanata min akwai dalili. Muka fita nabi layinmu da kallo ta zuciyata ta sake karyewa sai naji tamkar na tafi kenan.

Ta ciki mayafi ina ganin harabar gidan na gane, kai tsaye suka shiga da ni falon Hajiya cike da mutane tana hakimce a kujerarta kamar yadda na zata, tana ta yi mana sannu da zuwa.

Aka kaini gabanta aka zaunar, aka ce ga 'yar ki Hajiya mun kawo miki. Tace "To Allah ya yi musu albarka ya sa mun ?ulla alkwairi ina fatan kun fa?a mata yadda zata zauna da mijinta lafiya. Yanzu ku kaita ?akinta, nawa shi'anin sai gobe inda ita amarya zata girka mana abinci tare da taimakon masu aiki ta bamu ni da mutane na, ina fatan zaku zo domin ku ci girkin 'yar tawa. Sai kallon kallo ake yi. Umman Amina tace insha Allahu. Ta ce Maman Umar ta jagorance mu zuwa ?akina.

Aljannar duniya, haka kowa ke fa?i, ni dai ina lullu?e a zaune bakin gado ina jin yadda suke labarin kayan kyale kyale da na kallo kyan ?akin ?aki sun tafi da mutanen don haka sai wa?an da suka yi kafin abin ya zame masu sabo. Haka dai ina zaune bakin gado kai na a rufe kowa sai bani shawara yake yi ki kwantar da hankalin ki ki yi biyayya ki ci arzi?i iyayenki su ci. Da haka duk aka watse, nace don Allah a barnin su Jamila sa dawo zuwa dare. Aka bar su bayan kowa ya watse sai na cire mayafi daga fuskata na fito falo ina ?arewa ?akin kallo. Na ru?e wai ni Rabi 'yar magini ni ce da wannan dakin. Kenan zanyi murna da ?aryar yar da Aliyu ya min? Na tambayi kai na. Abinda ya ?ara ?aukar hankalina shin me ya kawo hoton babban ba?onmu na gurin sauka inda yake bani allona? Naje na zurawa hoton ido, a take na gane komai, wannan babban ba?on wato dai Yaya ne, duk cikin raina min hankalin da ya yi ne.

Jamila ta zo gurin ta
tsaya a gaban hoton ta sa hannu ta dafa ni, tace "Wannan shigar tamkar babban ba?on gurin saukar ku." Nace shine, tace "Ashe babban ba?on ?an uwan su

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login