Showing 21001 words to 24000 words out of 55418 words

Chapter 8 - HAMSHAƘIYAR-UWA 2

04 Jul 2024

5999

ne?" Nace shi kanshi ne a hoton nan kenan kinga shine babban ba?on. Jamila ta yi dariyar mamaki ta lakuci kumatuna tare da fa?in "Lalle shi wannan ?an wasan kwaikwayo ne, to bin ya birge sosai." Ta zaro ido, kamar ta tuna wani abu. "Kenan shine ya sai kayan ?akin nan?" Na sa mata hannu a baki na toshe domin bana son su Zuhra su ji. A hankali nace tabbas shine. Muka zubawa juna ido nace ina tunanin yadda zan yi masa zancan.

Jamila tace. "Kawai ki shere azuwan baki gane ba." Nace barshi yadda ya yi wasa da hankalina haka zan yi da nashi, sai ya fa?a min da kansa cewa shine. Jamila tace "Duk ba wannan ba, ya zakiyi da girkin gobe?"
....
Nace ko a jikina ban wani damu sosai ba, nafi damuwa da yaudarar da Yaya yamin, ni gaskiya a tsarina bana son in auri mai ku?i saboda gudun wula?anci, na yi ?asa da murya me mata uku suka yi masa duk ya raba su da 'yayansu ya kore su? Bakya tunanin yadda zan zama bazawara? Bakya tuna yadda masu min dariyar nuna min farin cikin na dace zasu koma yi min dariya tare da Allah ya ?ara?Dan haka wannan yafi zancan yin girki a gobe. Abinna na iya shi zanyi, kuma sun san daga ina aka ?akko ni.

Jamila tace "Allah ya dafa miki, kuma zan zo goben in taya ki." Nace kefa nan zaki kwana kuma ba zaki shiga kicin ba. Ta zaro ido. "Rabani da fa?an su Umma, na dai dawo goben kamar yadda suka ce za a iya zuwa amma gaskiya bazan kwana ba. Na yi alamun kuka, tace "Garama kar ki sa a ranki.
Haka dai Su Fati da sauran 'yan layinmu suka bu?e kofar suka shigo da sallama duk zatona sun tafi. Jamila tace "Na zata kun wuce?" Sai sukace sai an rako ango tukunna.

Bayan sallar Isha aka kawo abinci tuwon shinkafa da miyar alayyaho ta ?au kifi da nama, sai jalaf ?in shinkafa ta ji naman kaji ga lemuka masu sanyi. Nan suka hau ci. Ni kam duk da ina jin yunwa amma zan iya cin komai ba, saboda far gaba sai dai ruwa na ?auka na sha.
Bayan sun gama Jamila ta ce su Amina su kai kayan ita kuma za ta gyara gurin, sai tsiya suke min wai ba su ga laifina ba in banci ba anjima da kazata ta amarci anjima kar in cika ciki yanzu. Ni dai ban kula su ba, sai fargaba da suka da?a jefani ciki.

Takwas da rabi ina gyara fuskata bayan nayi salla, sai kiran wayata ya shigo. Cikin fa?uwa gaba na sa wayar a kunne ban iya ko sallama ba. Yace "Baby" a sanyaye nace na'am. Yace "Gamu nan shigowa yanzu ke da su waye?" Gaban ya sake faduwa naji kamar cikina ya karta. Nace su Jamila ne. Yace "Ok sai ki gyara sosai ki rufe jikinki nake nufi." Nace to. Yana aje waya Maman Iman tana ?wankwasa ?ofa suka bu?e mata suka gaisheta kai tsaye ta shigo cikin ?akin ?ayar mai min kwalliya ce. Tace Karamar mu babbar mu ga ango nan zuwa bari a gyara min ke.
Na gaishe su cikin kunya da girmamawa. Sannan nace shima yanzu ya kira wai zasu shigo. Tace Bari in ?ara in dakatar da su. Ta dube ni, ya naga duk jikin ki ya yi sanyi? Na yi ?an murmushi nace ba komai. Tace "Ni dai sai kinyi kyau." Ta kirashi ta dakatar da su. Nan fa ta kuma gyare min fuska da kwalliya, aka turare min gashi da jiki, ta ?akko lafaya tana cewa "Cire a layyace min ke cikin wanna lafayar." Mai kwalliya tace ina kika sai wanana lafayar? Tace kayan 'yan gayu ne DEEJANGALA ENTERPRISE kin san kayan su akwai kyau ga sau?i, kuma abin birgewar kin ga wannan lafayar ta jikin ta, zai wahala ki ganta jikin wata.

Mai kwalliya tace don Allah zaki bani number ta. Maman Iman tace zan baki mana. Ni dai ina jin su na ta labarinsu, na ?au kyau kamar 'yar tsana. Maman Iman tace "Ki rufe min fuskar ki kar abokai su gane Kinji ko? Kya dai gaishe su ta cikin mayafin." Nace to. Sukayi sallama wayar ta tayi ringin, sai ta ?aga tana cewa, "Ku shigo ango mun. kammala"
Su Jamila suka .shigo suna bu?a fuskata suna le?awa suna fa?in kyau da ?amshi. Ni dai shiru na yi domin fargaba da wani irin tsoro suke gigita ni.

Cikin haka aka ?wan?wasa ?ofa suka amsa sannan Fati ta tafi ta bu?e Sai kurum naji ina fa?in Hasbunallahu wa ni'imal wakil. Suka zauna falo ina jiyo muryar Yaya yace "Jamila kiranta." Ta shigo ta ce Yaya Baby ki fito. Na ce na shiga uku Jamila wallahi tsoro nike ji.
Hannu ta ri?e min ta yi min jagora muka fita domin na ?i bu?e ido. Tace "Menene abin tsoro, na bita muka fita, sai naji ta zaunar da ni a kujerar kusa da shi, ya kasance har ina jin ?amshin turare sa. Shi kuma ya kashe ni da ido duk da fuskata a rufe a mayafi amma ina kallonsa.

......
Abokansa sun yi addu'o'insu sannan suka yi nasiha sannan suka ha?a da tsokana aje min ku?i suka yi, sannan kuma suka ba ?awaye suma wai na sayen baki, duk da basu ga fuskar amarya ba. Yaya yace "Alhaji Shamsu ku maida yaran nan don Allah." Alhaji Shamsu yace su fito mu kai su. Da sauri na ri?e hannu Jamila jikina yana rawa nace ke k i tsaya sai gobe. Tace "Yaya Baby so ki ke yi Abba ya kusan halaka ni, da duka kenan.' Yaya ce koma ki zauna kinji ai gobe zaku dawo ko Jamila? Na saka kuka yace "Jamila ki tsaya to sai ki kwana." Ya yi maganar cikin lallashi. Tace Wallahi ta sani in har na kwana Abba zai min dukan tsiya, ita tana nan lif a ?akinta. Yace "To Kiyi ha?uri kibarta ta tafi. Nace to ka kira Abba ?in ka fa?a masa. Ya ?akko wayar ya kira amma tana kashe. Na sakar mata hannu jikina a sanyaye, na yi baya na zauna akan kujera. Suka tafi ya raka su bakin ?ofa suna wucewa maida ?ofa ya rufe.

Yasa hannu ya bu?e fuska. Tabarakallah Masha Allah. Ya furta cikin jin da?i, ya saka yatsa ya ?auke siraran hawayen fuskata ya tsugunna a gabana. "Haba Baby ai kin gama hawaye insha Allahu menene zai saki tashin hankali haka? Fa?a min damuwar ki yanzu?" Cikin rawar murya nace gida zan koma. Ya zauna "Me zaki yi acan?" Ya tambaye ni a gigice. Nace ba komai ni dai ina jin tsoro ne. Cikin mamaki yace "Tsoro kuma? To tsoron wa?" Na yi shiru. Ya ce "Ko dai kin ?oye min ne dama baki so na?" Nan ma na?i magana. Ya mi?e cikin damuwa. Ni kuma na ci gaba da ?an kukana. Yace "Kinga bana son wannan kukan tashi in kai ki gida." Nace Abba zai dake ni ne. Sai naga ya yi 'yar dariya, yace "In har bazaki je ba to gaskiya ki yi shiru ki fa?a min abinda ki ke tsoro kuma ki fa?a min gaskiya in dama ba so na ki ke yi ba." Na rasa abin cewa sai dabara ta fa?o min, ai dama ya yaudara ni, nace Ka ?oye min gaskiyar ka, kuma ni bani da ra'ayin auren mai ku?i ina tsoron wula?anci bana son in zama bazawara ne. Sai naga ya yi dariya, sannan ya mi?e. "Zo muje. Ya kawo hannu zai kama nawa, cikin firgici na?an ja baya, ya kalle ni har sai da naji wani iri. Yace "Muje" nabi bayan shi dai dai lokacin da Juma ta nufo sashen mu tace masa "Ga kaji amarcin inji Hajiya tace a kawo Uban ?akina." Yace Je ki kai tana nan ko ta shiga ciki? Tace "Tana nan Azima tana mata tausar ?afa Yace "Ta ?afa.
Haka kuwa mun samu Azima ta na yi mata tausar. Ya rusuna cikin girmamawa, nima na yi kamar yadda ya yi. Yace Hajiya an samu wata ' yar damuwa ne. Ta kalli Azima "Je ki kwanta." Azima ta kllemu sannan ta fice. Hajiya ta zuba mana ido "Damuwa kamar ta me?" Ya ce game da yarinyar nan ne wai sai na kaita gida yanzu, tun da ta gane cewa ni ?an Ali Baita ne ban fa?a mata ko ni wanene ba, ya kwashe duk yadda mukayi tun kafin a ?aura aure da nace talaka nan nake so ya fa?a mata.

Hajiya tana gama ji tsaf, sannan tace "Ke yaya sunan naki ma?" Yace Rabi'a. Tace ?ago kanki ki dube ni. Na kuma sunkuyar da kai, ta ci gaba da fa?in "Ni ce mahaifiyar sa Aliyu Ali Baita. Ni ce Hajiya Zeena wadda dai ki ke ji, shine autana a cikin 'yay'anmu biyar da muka haifa da Ubansu Alhaji Ali Baita, ya gaji mahaifinsa a suna, ya gaji mahaifinsa a ku?i ina nufin dukiya, ya gaji mahaifinsa a biyayya, ya gaji mahaifinsa a soyayya. shima bai ta?a neman wani abu na rasa ba, abu ?aya ya kasa samu shine mace ta gari ko ince miki soyayyar gaskiya shine dalilin ?oye miki asalinsa da ya yi kuma da ran yin hakan kwalliya ta biya masa ku?in sabulu." Ta numfasa sannan ta ci gaba. "Kar kiyi alaye kice wai ke bakya son mai ku?i, wannan labari ne domin mai ku?i shine abin so, dalilin haka ne ya ?oye miki cewa shi mai ku?i ne domin ya samu soyayya ta gaskiya wanda muke sa ran cewa ya samu, bai kamata ki shigo da wata damuwa kuma a irin wannan daren na f arko mai albarka da tarihi a gurin duk wata ?iya mace, ba." ta nuna ni da yarda ke bari in fa?a miki wani abu wanda ban ta?a fa?awa surukai na ba face 'ya'yan da na haifa. Ta ?ara rage sautin muryarta sannan ta nuna . Shatima tashi ka tafi, zan sa Juma ta r ako ta. Ya mi?e tare da fa?in sai da safe Hajiya , tace "Kana jina, karka damu kuma kabi komai a hankali kar ka manta da addu'a acikin ko a wane irin yanayi ka ksance." Ya ?an shafa kai tare da fa?in i nsha Allahu Hajiya.

Yana bada baya tace, "Ban yarda cewa bakya son ?ana ba, domin ya cika ta ko ina ?a namiji. Zanfi yarda in kince kina jin tsoron daren farko, tabbas 'yarnan daren nan na fargaba ne ga duk wata mace wadda ta alkinta mutuncita ko akasin haka, wadda bata san namiji ba, tana tsorata ya zata kasance, a farkon al"amarin, haka kuma wadda ta san namiji a waje tana tsoron kar fa angon ya gane." "Rabi'atu" Na ?ago na dube ta. Sannan na sake sunkuyar da kai. Taci gaba da tambaya ta. "Kin kasa cin binci yini yau? " Cikin raunanniyar murya nace Wallahi ni ko yunwar ma bana ji. Tace da zaku fito gida me kikaji a zuciyar ki ? Na sunkuyar da kai.Tace "kar ki damu fa?a min ni mace ce, 'uwa kuma kaka. sannan ina son in tantance in har da gaske baki son ?ana bazan bari ya ?ora miki idda ba zan sa ya sahale miki yanzu kuma ya kai ki gidan iyayen ki. Sannan ki sani ba a min karya a gidan nan ki amsa min tambayoyi na gaskiya." Nace Ni ada ina son sa sosai amma yau gaba ?aya ji nayi aure ya fita a raina, ko da muka zo gidan nan zuwa yanzu sai naji na daina son shi,Ni tsoron sa ma nake ji gaba ?aya. don Allah Hajiya ki ce ya maida ni gida.

Ta saki murmushin mai sauti, ki nutsu kar ki ru?a kanki, kin zo wani mataki mai mahimmanci a rayuwa wato daren farko. Ta matso ta kama hannu na tace,
"Yata bana manta irin wannan daren saboda kima da martabarsa, na ina fa?awa 'yayana martabar wannan daren domin na ta?a kasancewa a cikinsa, da a ce ni marubuciya ce zan rubuta in wallafa babban kundi mai shafi sama da dubu ina mai bayyana kima da darajar wannan daren. Don haka ina mai baki shawara kar ki bari vwannan daren ya tafi a haka batare da kin zama Hamsha?iya a gurin mijinki ba, zama Hamsha?iya a gurin miji shine ya ke sa ki zama Hamsha?iya a idon duniya har zuwa kan ahalinki. ?ila yanzu duk bazaki fahimci abinda nake son sanar da ke ba, sai nan gaba.

Da mata za su san darajar su game da wannan daren da sun kasance suna ririta kansu tamkar dai ?wai a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login