Showing 48001 words to 51000 words out of 55418 words

Chapter 17 - HAMSHAƘIYAR-UWA 2

04 Jul 2024

6010

yin ?o?arin daurewa. Kuma na fahimci cewa kowane iyali suna da tasu matsalar wasu rigingimu da munafirci, kamar ahalin su Abbanmu kenan. Wasu 'yan shaye shaye suke da su a cikin nasu ahalin.Wasu kuma ?arayi. To sukuma nan manemin mata Allah ya basu gane nima ya zama cikin ?addara ta. In na tada bala'i na tafi bansan dawa zan ha?u ba a gaba.
Ranar asabar na sake bincika wayar sunyi magana cewa zai aiko a ?auke ta tsakanin shabiyu zuwa ?arfe ?aya.
Na tashi zaune na ?are mishi kallo cikin dare yana bacci nace zan gwada wata dabara Allah ka tsaya min.
Na ri?e cikina ina ta juyi ina ?an kuka ina fa?in wayyo cikina. Ya farka a gigice ya kamani yana tambaya ta, da kyar nace cikina ne ke ciwo. Ya tashi ganin yadda ciwon ke ?ara tsananta ya kira wayar Hajiya ya fa?a mata. Tace "Subhanallah! Ka zo ka amshi ko plagin ka bata kafin asbashi a kira likita." To haka dai aka kwana a kaina ina birgima,yau da ga salla wannan zaman na safe na gurin Hajiya ranar bai samu ba, da zai tafi salla sai na yi laf kamar bacci ya sace ni. Yana fita na tashi na yi salla na dawo na ?ora ina juya juya har na fa?o daga kan gadon. Shi kuma bayan sun gaisa da Hajiya ta tambayi jikina yace sai gefin asbahi sannan bacci ya ?an sace ni, yace shi kanshi bacci ya ke ji yanzu idanunshi sai ra?a?i suke yi. Hajiya tace "Ka kira likitan ko?" Yace munyi waya yana hanyar zuwa nan ?in,. Hajiya tace "Allah ya sawa?a kuma ba ciki gareta ba ko?" Shamaki yace gaskiya dai bansani ba, amma a wannan sati tayi al'adar ta. Hajiya tace To" bari likitan ya ?araso muji."

Kiran likitan ya shigo,Shamaki ya ce gashi nan ma bari in shigo da shi. Har Hajiya suka nufin ?akin Shamaki ni kuwa lokacin ina tsaka da kukan ba?in ciki jin motsin su ya sa na dafe ciki na shiga juyi. Shamaki ne ya rugo da gudu yana fa?in "Subhanallah fa?owa ki kayi ha?a Baby! Ya ?auke ni ya mayar kan gadon yana min sannu, sai naji muryar Hajiya itama tana min sannu cikin magana da ?yar nace a kai ni gurin Ummanmu zan mutu ne. Hajiya tace "Inda mutuwar ce 'yannan wane ke ki furta ta,zafin ciwon ne Allah ya ba?i lafiya likita ka duba ta sosai ni bari in koma Allah ya sawa?a."

Duk inda likita ya latsa da hannu a cikina sai in saki ?ara, yace a sani a mota kawai muje Asibiti a yi hoto domin a gano ina matsalar ta ke, ya kira Hajiya ya fa?a mata, sannan ya canza kaya ni kuma ya zira min hijabi akan kayan bacci ya ?akko ni kamar ya ?au jinjiri muka fita mota.
Iya gwaje gwajen likita bai iya go komai a cikina ba, don haka sai ya gayyaci wani likita wanda ya yi shura a fanni cikin kafin yazo aka min allurai dan rage ra?a?i sannan aka samin ruwa da allurar saka bacci. Bacci ya yi gaba da ni wanda har likitan ya zo suka yi hoto an gane wane ina da sanyin mara da kuma tsakuwa wanda ake ganin tsakuwar ce ma ta soma taruwa, za a bani maganin ta taru guri guda in ya so sai a yimin aiki. In kuma anga yiwuwar ba sai anyi aiki ba sai a bani magani ta narke.

Ni dai ban farka ba tunda a kwai bashin bacci sai kusan ?arfe biyu, ina ganin Asibiti na tuno komai da komai zan motsa sai ?aran wayar shi ce ta tashe ni, bai san na farka ba yana magana can ?asa ?asa daga can kusa da bakin ?ofa da yake kunne na kamar na maciji ya ke ba dai jiyo magana ba, naji yana fa?in. "Na fa?a miki cewa na miki magana ta Whatsapp ki duba mana mata ta bata da lafiya yanzu haka muna Asibiti in na samu lokaci za mu sake saka rana don haka karki sake kiran wayata.
Alhamdulillah na furta a hankali, na wahala kuma na yi ?arya,amma na yi nasarar hana aikata babban laifi wato zina. Ya dawo ina mi?a tare da salati, yace "Baby kin farka sannu ya jikin.?" Ya kama hannu na yana murzawa. Na zuba mishi idanu, kishi da son shi suka sake tirni?e ni. Nima na matsa hannun shi a hankali nace dan Allah kana so na sosai? Ya tsuguno ya ?ora karan hanci shi a kan nawa, yace "Baby me yasa ki ke ta kokwanto?" Ka sake tabbatar min, na fa?a hawaye suna zubowa daga cikin idanuna. Yace "Baby ina matu?ar son ki." Na sa tafin hannuwa na guda biyu na ?ora akan kumatunsa, nace Ni kuma nayi maka al?awarin zan yi maka duk wata biyayya zan rufa maka duk wani asiri zan baka duk wata kariya wadda nake da iko.
Ya ?anyi shiru, can ya yi murmushi "Baby za dai ki min biyayya amma rufin asiri ko kariya ai nine zan miki wannan amma ki taya ni da addu'ao nan da ki ka saba." Nace to ba damuwa muje gida tunda na samu sau?i, gashi baka je kasuwa ba kai sam yau. Yace "Ya zanje kasuwa mata ta tana cikin mawuyacin hali." Nace na gode da kulawa. Yace bari inje in yiwa likitan magana.

An sallame ni da tarin magunguna,muna isa gida Hajiya ta min sannu su Juma kuwa har ?aki. Ranar dai Shamaki bai fita kasuwa ba,kuma banga Hajiya ta damu da rashin fitarsa ba, yana gurinta ka?an ka?an ya zo ya duba ni.


Kwana uku bayan wannan diramar ina zaune gaban Hajiya ina yi mata tausa a ?afa, tace "Me yasa baki sanar da iyayenki rashin lafiyar ki ba? Irin wannan ciwo da ki ka yi mai azaba zai iya kai mutum lahira." nace na ga ana kula dani sosai kuma kar in tada musu hankali shiyasa. Tace "Kinyi tunani mai kyau, Allah ya ?ara lafiya, ta ci gaba Shamaki ya na sonki, ki yi amfani da hakan ki taimaki rayuwarsa." Kalaman suka ?aure min kai, me hakan ke nufi? Na tambayi zuciya ta. Hajiya ce kawai zata iya wayar min da kai, don haka sai na ce. Tayaya zan iya amfani da haka in taimake shi? Kuma wane irin taimako? Tace "Babu bu?atar dogon bayani ni dai zan ci gaba da kula da yiwuwar hakan." Nace to Allah ya bani iko, ni zanyi koma menene matsawar hakan zai taimake shi. Hajiya tace kin kyauta
Juma ta shigo ta zauna tace ina son magana da ke ne Hajiya.
A duk lokacin da Juma ta yi irin wannan furucin Hajiya ta san tana bu?atar su ke?e ne. Dan haka sai ta ce, " Rabi'atu ba mu guri mu yi magana. Na tashi na nufi gurin yara. Azima tana zaune kamar kullum da littafin a hannun ta. Ban damu da ?in amsa sallama ta ba,domin nasani ta saba. Yaran suka nufo ni su duka suna tambaya ko zanyi musu tatsuniya. Nace su bari sai gobe Alhamis tunda babu islamiyya in mun gama karatu sai in yi musu. Juma tayi sallama muka amsa tace "Azima Hajiya tana kira." Sai da ta ja dogon tsaki sannan tace fa?a mata ina zuwa. Juma ta jima da tafiya kafin Azima ta sake yin tsaki ta yashi tana ?un?unai. Nabi bayanta da kallo ina mamakin wani fa?i da naga ta yi. Ji nayi duk na tsargu, na tashi na nufi ?akina,

Gaban hoton mu na tsaya wanda yake bani kyauta ina kallo shi. wayata ta yi ringin na ?auka na kalli fuskar wayar na sa a kunne tare da fa?in babban ba?o ka dawo ne? Yace "Duk jan lokacin da aka yi ana nema min suna ?arshe in ?are da wani babban ba?o babu ko da?in ji." Na yi dariya nace in har kaine Babban ba?on mu na ranar saukar karatunmu to kuwa sunan da zaka ci gaba da amsawa ke nan. Yace "A hakan ma ni ne da godiya, domin a ke?a??en lokaci akan kira ni da Baby sweet heart da sauran sunaye cikin shagwa?a. To kina ina ne yanzu?" Nace ina zani ina gida akwai wani abu ne?" Yace "a'a' Na kira Hajiya ne bata ?aga ba, nace ina ?akina ne amma bari in duba maka, kari?e wayar har inja falon, yace "to kije ina jinki.
Na isa falon Azima ce zaune su da Hajiya kan Azima a ?asa kamar dai tana kuka, Hajiya kuma cikin wani yanayi da bazan iya fassarawa ba. Na ?arasa nace Hajiya Shamaki ne ya ke son ku yi magana. Hannu kawai ta ?aga min, wanda bana bukatar sai an fa?amin cewa bata son jin maganar kowa.
?????????
*HAMSHA?IYAR UWA????*


*NA*


*HALIMA ABDULLAHI K/ MASHI*


_PAID BOOK_
_Ku?in karatu ?600_
_Account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank a turo shaidar biya ta wannan number 08140004302 ko katin Mtn_
_Phone 08140004302_

*DOKA*
_Ban amince wani ya ?ora littafin nan a wani Social media ba,ko a maida mini shi Audio ba tare da iznina ba yin haka daidai yake da fuskantar fushin hukuma. A kiyaye_


*Masu son a Tallata masu hajarsu suyi magana ta wannan number 09068032427*

*Page 34*

Ta katse ni, "Bakya bu?atar dogon tunani Rabi'atu, akwai wani sirri ne da ki ke ?oye wa na sa?" Na girgiza kai babu Hajiya. Tace "Gaskiya ban yarda ba, kina dai rufawa mijin ki asiri ne, ina son ki sani kalmar ki da kika furta ita take nuna cewa mijinki ya na le?e le?e." Na ce Subhanallah Hajiya bana zargin sa kuma bashi da kama da haka, in kin duba sam bashi da lokacin kansa bare na yawon banza,kawai dai na furta ne saboda akwai masu yi, ni kuma godiya ce ga Allah da bai bani irin wancan ba,ya bani wanda zai aje mu mu hu?u.
Hajiya tace "To iya magana Sarkin zance Allah ya shiryar da duk ?an musulmi. Nace Ameen,tace tashi ki kai masa kankanar, saura kije ki fa?a masa abinda na ce game da ?ara aurensa. Na ce bazan ce komai ba.

Na tafi da kankana na tura falon a hankali na shiga baya fakon na aje masa a gurin da yake ajewa na nufi ?akin zan shiga da yake tun da na saka shi a tarkon zargina bana yin wani kwakwaran motsi in zan shiga gurinsa. Cikin Sa'a naji yana waya, yana fa?in "Sweetheart gaskiya ban ta?a samu mace mai suna mace kamar ki ba, a tafiyar nan ta sati ?aya kin ji dadi banso muka rabu ba. Ta fa?a masa wani abu sai naji ya ce "Da gaske Babyna to ai kin ha?u ne, bana son a yi min kishiya don Allah a dai ri?e min amana. Kuma a turo min hotuna in kalli abubuwan... Hannu na saka na toshe kunnuwa na,sannan na juya da sauri, cikin rashi sa'a na bigi wata tukunyar fulawa da ke aje a gefe sai ta fa?i. Da sauri ya katse wayar ya fito,daidai lokacin na mur?a ?ofar zan fita, yace Baby! Yadda ya kira ni kasan cikin fargaba ya ke.
Bazan iya juyowa in Kalle shi ba,kalaman sa suna min yawo a cikin kai dan haka sai kawai na fice,da gudu na ?arasa ?akina kan gado na fa?a ina maida numfashi na soma karanta duk wata addu'a da ta zo baki na. Ina jin ?arar bu?e ?ofa nasan shine, don haka sai na soma ?okarin daidaita yanayi na. Ya shigo ya tsaya yana kallo na. Na ?ago da kyar na zuba mishi ido. Hawaye suka soma kwaranya a idanuna. Ya zauna jiki a sanyaye, ya ce. "Menene ki ka fita da sauri ina kiran ki?" Cikin rawar murya da zubar hawaye nace babu komai. Ya kama hannuwa na, a yau sai naji tafin hannun sa mai taushi kamar ?aya . Yace Baby dole akwai wani abu ki fa?a min. Na girgiza kai ba komai. Na sa?ule hannu na daga nasa,kaje ka ci kankanar ka na ajiye. Ya ?ara kama hannu na "To tashi muje mu sha sai mu kwanta. " Na sunkuyar da kai, ka yi ha?uri yau zan kwana a nan. Ya yi shiru, yana ?o?arin tabbatar da zargin sa,tabbas yarinyar nan ta ji wayar sa. Ya sunkuyar da kai yana tunanin abinda ya kamata ya yi. Na zame a hankali na kwanta ina nanata ambaton sunaye Allah a zuciyata ba shakka duk matar da mijinta ke neman matan waje alal ha?i?a tana cikin masifa.Na lumshe ido hawaye suna kwaranya ta gefe. Ina jinsa ya mi?e jiki ba ?arfi ya kama hanya,na bishi da kallo har ya fice ya rufo min ?ofa,na tashi na zauna zaman dirshan na saka kuka. Nayi mai isata, sannan na mi?e na shiga ban ?aki na ?auro Alwala na zo na shiga jero salla, ba zan iya ?irga yawan sallamar da na yi ba har sai da naji ina jin kiri sannan na zube a sujjada ina raira kuka a gaban Ubangiji na kasa furta komai sai fa?i nake Ya Allah! kai ne mahalicci na, Allah ka gani,Ya Allah! Ka gani. Bacci ya ?auke ni a nan, a dur?ushe.

Kiran sallar farko ya farkar da ni, na tashi duk jikina ya yi tsami saboda irin kwanciyar da nayi dakyar na yo alwala nazo na ?ora sallah. Aka tayar da sallah inajin yana ?wan?wasa ?ofa ta,ban tashi ba na ci gaba da sallah. Bayan na idar na zauna ina tunanin kishin me zan tsaya yi da duk wadda zai auro, domin da ya kawo su ya aje zai komawa matan waje, kuma duk yadda aka yi Hajiya tasan yana bin mata, tana zaton ko na gano ne. Yanzu wane mataki ya kamata in ?auka shine damuwa ta. Na farko bazan nemi ya sake ni ba, domin yin hakan babban laifi ne,banda haka sonshi ko kyas bai ragu a zuciyata ba amma na san tabbas ina jin haushin sa a yanzu,yana fa?awa wata ?aruwa wai shi bai ta?a jin mace irinta ba,ni kuma fa?
Wata zuciyar tace ki dafa shi da ruwan sanyi dan kina sonshi kar ki yarda ki zama kamar wata shashasha. A fili nace Allah ka bani basirar yadda zan tafiyar da wannan bawan naka.Allah ka shiryar da shi.
Wayata ta soma ringin a firgice na ?akko ta kardai wani abu ne ya faru a gidan mu. Ashe shine, yace ki zo ki same ni a gurin Hajiya. Nace to.
Ashe shima haka ya kwana cikin tashin hankali ya tabbatar taji maganar dan haka sai da ya gama tunanin abinda ya kamata ya yi ?arshe ya yanke shawarar kawai ya fa?awa Hajiya ko ma dai menene ta shawo kanta domin shi duk nauyin ta ya kamashi balle da ya zauna yana tuna kalaman batsa da suka dinga musaya da yarinyar bai san tun yaushe ta shigo ba. Inhar ta ji komai gaskiya ya yi abin kunya babba.

Na dur?usa na gaida Hajiya kamar yadda na saba. Na dube shi shima na gaishe shi kamar ba komai.
Ya kalli Hajiya ya sunkuyar da kai, sannan yace Hajiya na kawo kaina ne bisa ga wani laifi da nayi Wa Baby,ina son a taya ni bata ha?uri kuma insha Allahu zan kiyaye. Ciki mamaki Hajiya ta ke kallon ba?on lamari Shamaki yana neman afwar Babu har da ha?awa da ita,to wane irin laifi ne haka? Na katse mata tunani da cewa Ya Salam! ni ce kaimin laifi? Yace ki bar wani alaye Baby na yi kawai tun jiya kin dage ba komai,amma kina ta kuka shi kuka dama ana yin shi haka kawai ne, kuma na ga tsanata a ?wayar idanunki kin ?auracewa shimfi?a ta ko bacci banyi ba. Bazan jure kiyi fushi da ni ba. Na kalli Hajiya wadda ta tsura min ido, na sunkuyar da kai. Hajiya tace ka tashi ka shiga ciki ka bamu guri.

Na gyara zama,ta ce Rabi'atu jiya ya muka yi dake anan gurin? Na ?ago na dubeta ina ?o?arin tunawa, nace munyi magana da yawa musamman ta aurensa da Azima. Tace "Yawwa amma ya muka rabu?" Nace kince kar in nuna masa munyi maganar. Tace Yawwa to kuma ya akayi kika yanke masa irin wannan hukuncin na azabtarwa?" Nace Hajiya wallahi yadda muka yi maganar nan a nan gurin wallahi a nan nabarta. Bance banji zafin kishi ba,amma wannan ba laifi bane dan zai ?ara aure zan bashi duk wani goyon baya Hajiya wallahi bazan ?aga masa hankali ba.
Tace to fa?a min menene ya yi miki?"
Na sunkuyar da kai nace Hajiya kiyi hakuri nasan Shamaki ?anki ne,kuma kina sonshi fiye da kowa, amma ni kuma mijina ne akwai wani sirri tsakaninmu wanda ya kamata in suturta shi daga ni sai shi sai Allah. Ina neman alfarma ki bar wannan maganar ta wuce a gurina ki ?ara yi masa addu'a kawai. Yau ce rana ta farko da naga jikin Hajiya ya yi sanyi harma ta rasa abin fa?i na kusan sakwan talatin. Sannan ta ja wani dogon numfashi tace, "Ki sani ri?e abu a zuciya yana haifar da ciwo,tattauna Matsala da wani yana rage damuwar kuma ni ce mafi dacewa ki tattauna wannan damuwar da ni." Nace Hajiya dole ne mu koyi yadda zamu kashe mu rufe domin samun kwanciyar hankalin ki, duk da ban kasance likita ba, a shekarun ki yanzu bakya bu?atar duk wani abu da zai tada miki hankali.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login