Showing 6001 words to 9000 words out of 55418 words
A hankali ya furta "Hajiya" ta yi kamar bata ji ba. Ya sake matsawa kusa da ?afarta, yace Hajiya. "Fa?i ina ji." Ta furta ba tare da ta waiwayo ba. Yace tun tuni nasan kina min so fiye da irin wanda ki ka furta. Ba zan iya kawo bayanin irin soyayyar da kike min ba, ni da 'yan uwana. Ha?i?a na samu 'yan uwana mu yi magana, amma ba kamar yadda ku ke zato bane Hajiya. Nauyi nike ji in sameki da irin wannan zancan. Hajiya ta maido kallon ta gare shi, ta soma fa?in "Ni fa na ?auki cikin ka, na haifeka, na shayar da kai da wannan maman nawa, ni ce wadda na ri?e ka aka yi maka kaciya. Aliyu ka tuna ban daina yi maka wanka ba sai da na ga alamun balaga sun fara bayyana atare da kai. Lokacin ka shiga ajin farko na ?aramar Sakandire. Anyi haka? Shamaki ya ka?a kai alamun ya tuna. Tace "To a kanme har zaka ce kana jin nauyi na?" Shamaki cikin tsananin kaunar mahaifiyar sa ya ce, Hajiya na yi kuskure mai girma, kece ya kamata in tunkara amma ki yafe min tare da sauran 'yan uwana a ?o?arin su na nuna ?aunarsu a gare ni, amma ko da na fa?a musu duk sunce gurinki za a dawo sai dai su za su zo a madadi na. Hajiya tace a a bana bukatar su a gidana game da wata matsala taka. Ni da kai muna kwana a gida daya su da ke kwana a gidan mazajen su shine har sai sun wanko ?afa domin yin gyara a matsalar gidana?" Ayi mana afwa Hajiya, zan sanar da su ba sai sun zo ba. Kuma insha Allahu zan sanar da ku damuwar a yanzun nan in har kun yi min izni.
Hajiya ta share kamar bata son ji har da cewa "Yau ka canza mana tsari, har lokacin bacci ya kusa ba muyi abinda ya kamata .ba." Shamaki yace insha Allahu za mu fidda komai kafin mu kwanta. Sannan ya sake marairaice murya in fa?a Hajiya?" Ta tattara hankalinta gare shi "Fa?i ina ji amma da shara?i, ko ka fa?amin koma menene, bana bu?atar ka fara ro?o na in amince da bu?atarka." Ya?an yi shiru. Tace Inhar haka zaka yi to ina son ka bar zancanka. Sai yanzu ya fahimci gaba ?aya Hajiya batasan komai ba tsabar lissafi ne kawai ta rikitashi ga shi har ta yi nasarar tarfashi zai fa?a mata, ?ila in da abinda ta sani bai wuce tasan ya je gidan Maman Umar shida sauran 'yan uwansa ba. Ya dube ta ta kafe shi da ido. Ya sunkuyar da kai, yace Wai Hajiya wa ya fa?a miki cewa mun ha?u da su 'yan uwana? Tayi ?an murmushi mai sauti. Ta fahimci ya gano shurinsa ta ke yi bata da masaniyar komai. Ta ?aure fuska. " Sai ana magana ka sauka daga kan layi kasan da lokacin bacci na ya yi zan mi?e kira min Azima ta shafa min maganin ?afa. Yace to Hajiya bari mu gama maganar, dama fa kan batun girki ne na ranar taron ki da amarya ke yi, sai kuma maganar budurci. Ya ?anyi shiru ko zata ce wani abu amma bai ji ta ce komai ba, dan haka ya ?ago kai ya dube ta. Shi take kallo har lokacin. Ya ci gaba, saboda ita Baby 'yar talakawa ce ba lallai ta iya girkin zamani ba,, a taimaka a sa su Juma.. Ta ?aga mishi hannu. "Na ta?a cewa ga kalar girki da Amaryarka za ta yi?" Ya girgiza kai. Tace to "Wannan ban kar?a ba,ta zo ta dafa irin wanda ta iya na gidan nasu ta bamu muci, anrufe wannan batun sai kuma wanne ka ce?" Ya ha?iye yawu maganar budurci ne ce kawai duk yadda tazo bama sai mun tattauna maganar ba. Saboda likitoci suna ta bayani shine har Maman Afra take bada misali da matsalar Afra ta kwanaki. Hajiya ta ?aga masa hannu, bana son wannan maganar ka barni akan ra'ayina. Yayi ?if domin ta rufe ?ofar magiya tun farko, dan haka ya ?akko ?aramar laptop ?insa dake gefe a jaka zai fara yi mata bayanin kasuwa. Azima ta shigo da sallama ta tambayi Hajiya cewa a fara shafa magani yanzu? Hajiya ta yi mata izni.
Na farka na ganni kwance kayana a ji?e sharkaf kaina a cinyar Umma, ga Abba na min fifita. Ajiyar zuciya irinta masu kuka na ji Jamila na yi, na tashi zaune da sauri nace Umma menene? Sai naji gaba ?ayansu suna min sannu, na tuna me yafaru. Da sauri nace Dan Allah Umma ban ta?a gani kuna fa? ba sai a kai na. Na soma kuka, Abba ya ce ke komai ya wuce kar kiyi kuka. Umma tace ba inda ke miki ciwo? Na girgiza kai alamun babu. Umma Ta ce "To mi?e kije ki cire kayan." Na tashi Jamila ta zo da sauri ta ri?e min hannu muka nufi ?akinmu, ina jin Abba yana lallashin Umma wai ita ma ta tashi taje ta kwanta.
A ?aki na tambayi Jamila ko na yi Alhaji ne. Tace suma na yi Lokacin da nake ?o?arin furta cewa na fasa auren Aliyu." Nace iko Allah ni wannan wane irin so ne nake masa?Jamila tace Abba da Umma jikinsu ya yi sanyi da wannan son da ki ke masa. Abba ya ce gara kawai a ?aura a kai ki. Wani da?i naji a zuciya ta, na ?akko Al'?ur'ani na ce bari in sake jaddada karatuna gobe a gabansa zan yi ina son in burge shi sosai. Gashi na ci Sa'a ina daga cikin ?alibai mu uku da Malam ya ware zamu yi karatu mu ka?ai kuma biyun maza ne ni ka?aice mace. Jamila tace kinsan kina da muryar ?ira'a ne sosai Yaya Baby. Nace na sani 'yan ajinmu sai suce wai ina shan na'a na'a ne. Jamila tace "Baiwa ce. Haka na shiga raira karatu muryata tana ratsa tsakar gidanmu ko ina ya yi tsit. Na tabbata iyayena suna alfahari da ni in suka ji ina rero karatun Kur'ani. Washegari tun daga sallar asbashi ban koma ba, kafin bakwai tuni na gama shiri na sha atamfarmu ta anko da sabon hijabi, Umma tace in ?auki takalmi a cikin kayan lefena in saka. Na gama shiri tsaf sannan na zauna na rubutawa Shamaki sa?o kamar haka..
Sanyin zuciyata fatan ka tashi lafiya tare da dukkan yaran mu da kuma Hajiyata. Dan Allah ina ?ara tunasar da kai cewa yau ne saukarmu zuwanka ya fi komai mahimmanci a guri na. Ina saka ido. Bayan na tura na jira amsar shi, amma bai aiko min ba, na kira layin naji yana waya. Ance ?arfe takwas ta yi mana a makaranta amma ni harda minti goma, gaba ?aya duniya ta daina min da?i bani da tabbacin zuwan masoyina. Har Jamila ta fahimta ta tambaye ni,na fa?a mata damuwata. Ta shiga lallashina akan tasan zai zo, kawai dai wani abin yake yi bai amsa kira na ba. Nace amma ai nayi masa sa?o sai ya bani amsa. Jamila dai ta shiga lalla?ani, muka tafi gurin sauka.
Fili ya cika tantsam Malaminmu ya nuna min ajin da aka ware mana mu 'yan sauka, na shiga dukkan masu saukar sun hallara kowa na cikin farin ciki masu hoto suna ta ?auka. Na samu guri na zauna, Fatima Shu'aibu ta kalle ni. tace "Lafiya kuwa Rabi'a Abubakar naganki shiru. Na yi ?an tsaki tare da fa?in ba komai. Na ?a?aro ?an murmushi Malam Awwal ya ce za a bar Mutum uku su yi karatu ?ai?aya ya fa?i suna? Na tambaye ta cikin sanyin jiki. Fatima tace "A'a, amma dai nasan kina ciki. Nace ba lallai bane. Ina rufe baki yana shigowa. Ya ?ara tunatar da mu yadda zamu natsu sosai a gurin karatu da kuma yadda zamu fito cikin tsari. Sannan ya kira sunan maza biyu, Aminu Sani da Ashiru Ya'u. Suka fito, ya dube su yace akwai ta ukun ku ita ce Rabi'atu Abubakar na tashi da sauri na fita domin nasan cewa ina cikin wa?anda za a sa su yi karatu ?ai?aya, makarantarmu suna ji da muryata a ?ira a. Malam ya ce ku ukunnan kune zaku yi karatu, kuma Alhamdulillah kune kuka zo na ?aya zuwa na uku. Dan haka ku zama cikin shiri na amsar kyautuka. Nan dai muka shiga murna duk da cewa bamu san waye zakara ba. Ni dai nasani bana wuce ta biyu ko ta uku a duk jarabawa ban ta?a yin ta ?aya ba, yanzun ma ban yaudari kai na ba, na fi zaton ta uku. Shiko Aminu kowa yasan baya tsallake na ?aya. Bayan an kiramu mun fita zuwa rumfar da aka tanada mana kujeru mun zauna sai na soma raba ido ina zan hango wani nawa. Na hangi .Abbanmu a rumfar iyayen yara cikin sabon yadinsa shi da Abba su Zuhra. Sannan na hangi Umma tare da wasu danginta na Kurna. Can a wata rumfar na hango Dangin mahaifina matan har da yaransu, amma damuwata ban hango masoyina ba. Duk sai naji raina yana ?aci. Da aka fito da mu muka karanta fatiha da shafi biyu na ba?ara sannan muka koma muka zauna, aka ci gaba da gabatar da abubuwa har zuwa lokacin da aka zo kan karatunmu. Ashiru aka soma kira aka ce ya za?i surar da ya ke son karantawa ya karanta. Ya zabi suratul Yasin. Da ya gama aka tsai da shi akan mumbari aka gabatar da shi a matsayin wanda ya zo na uku, aka bashi allonsa,sannan aka bashi kyautar sa ta musamman daga hukumar makaranta saboda taimakon Malamai gurin koyar da ?alibai na ajin ?asa. Sai kuma aka kira Aminu Sani cikin mamaki ya lalle ni, Nima haka domin dai na bayar ni za a kira. Shima dai bayan ya gama karatu an gabatar da shi a matsayin shugaban ?alibai, ya kuma amshi kyautar yabawa da zuwa sahun bayan liman a lokutan salla a makarantar. Lokacin da aka kira ni sai da ta kusa sani ta ta?ani domin takaicin rashin halartar Aliyu yasa komai ya sa?ule min. Na tashi jiki ba ?arfi na hau mumbari, an bani damar karanta duk surar da ta min, sai na samu kaina da karanta suratul Muhammad domin ina son ta. Ina fa?in Muhammadur Rasulullah! Sai na ji muryata ta soma rawa lokacin da na ji ?aukacin gurin an amsa da S.A.W. Haka na kammala ciki zubda Hawayen da ba zan iya fassara dalilin zubar su ba. Guri ya ?auki kabbara ga masu hoto da bidiyo amma babu sanyin zuciyata. Malam ya gabatar da ni a matsayin ?alibar da ta zo ta ?aya acikin kaf ?aliban set uku da muka yi sauka. Sannan aka bani kyautar Shugabar ?alubai wato Amira. Sannan aka bani kyautar ?alibar da tafi kowace ?aliba ladabi da biyayya ga malamai. Har zan sakko sai aka sake tsaida ni aka bani wata kyautar itama an na?e ta, aka ce daga mijin da za a ?aura mana aure da shi sati mai zuwa....
?????????
*HAMSHA?IYAR UWA????*
*NA*
*HALIMA ABDULLAHI K/ MASHI*
_PAID BOOK_
_Ku?in karatu ?600_
_Account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank a turo shaidar biya ta wannan number 08140004302 ko katin Mtn_
_Phone 08140004302_
*DOKA*
_Ban amince wani ya ?ora littafin nan a wani Social media ba,ko a maida mini shi Audio ba tare da iznina ba yin haka daidai yake da fuskantar fushin hukuma. A kiyaye_
*Masu son a Tallata masu hajarsu suyi magana ta wannan number 09068032427*
*Page 14*
Take fuskata ta canza zuwa murmushi, na shiga kalle-kallen ko zan iya hango shi Mijina. Sai dai har na sakko Jamila ta zo da gudu ta amshi kyautukan ban hango shi ba. Daga nan sai malamai suka gabatar da asusun makaranta domin neman taimako. Kabbara da naji an ?auka ita ce tasa na ?ago kai na dubi ta kusa da ni nace menene? Tace "Babban ba?on da aka gayyato ne ya ke jawabi cewa ya bada Miliyan uku ayi gyaran makaranta." Sai na sa hankalina a gurin ina fa?in gaskiya ya taimaka. Sai naji yana fa?in "Wannan yarinyar mai albarka Allah ya yi mata albarka tare da iyayen ta wadda ta zo ta ?aya ga sheda da ta samu ta ladabi ha?i?a ta zama abar alfahari ce." Sannan ya ci gaba da fadin "ina yarinyar tazo nan. " Malam ya zo da sauri ya tasani. Kyakyawan Basarake ne yana zaune cikin shigarsu ta sarakuna yasha gilashi ba?i. Na dur?usa a gabansa. Yace yarinya zaki ci gaba da karatu ne? Na zuba masa ido kenan abin nawa ya kai duk wanda ya yi magana sai inji muryar sa irin ta masoyi na. Malam yace "Aure za ayi mata ranka ya da?e kunya ta ke ji shi yasa ta yi shiru." Ya ce "To Allah ya albarkaci auran mun zaci zakici gaba da karatu ne mu fa?a miki zamu ?auki nauyin karatun. Amma tunda ance aure za a miki to in mahaifanki suna wannan guri muna saanar da su cewa zamu sai miki kayan ?aki da kayan da duk wata gara. Allah miki albarka Ya sa ki yi amfani da abinda ki ka karanta, kuma muna yi miki nasiha da ki bi mijin shima ya shede ki kamar yadda ki ka samu sheda daga Malaman ki . Su kuma sauran yaran da suka ci jarabawa zamu basu dubu ?ari ?ari. Ragowar yaran da suka yi sauka kuma za su rabauta da naira dubu ashirin ashirin. Ta ke aka soma kabbara. Da?i ya rufe ni addu'a na ke Allah ya sa ba mafarki na ke yi ba. Allah mun gode maka ya kawo mana mafita ni da iyayena. Babban ba?on shine ya mi?a mana allunanmu aka ?auke mu hotuna. Lokacin da zai bani nawa sai na ji ya ce abar alfahari kin na tabbar mijin ki in yana nan to yana cike da farin ciki da godiya ga Allah. Na zubawa fuskarshi ido muryar Aliyu na ce. Malam ya min tsawa wai in wuce, Sannan ya basu ku?a?ensu a Envelope ni kuma ya ce a bashi lambar wayar mahaifina. Malam ya sa lasifika ya ce in Mahaifin Rabi'atu Abubakar yana gurinan ya iso nan ana son ganin shi. Abba yazo cikin murna suka gaisa da babban ba?o yana ta godiya sannan Abba ya yi godiya ya bada lambar waya inda wani da ke tsaye da wayoyin babban ba?on ya amshi lambar ya saka a ?aya daga cikin wayoyin. Suka tafi malamai suka raka su gurin wasu manyan motoci.
Haka dai sauka ta tashi ana ta farin ciki da murna a gurin . Su Umma abin ba a magana. Ni kam tun kafin mu ?arasa gida na amshi wayar a hannun Jamila na soma kiran layin Yaya. Na kira ya fi sau goma amma ?an tahalikin nan bai ?auka ba. Na ja tsaki