Showing 36001 words to 39000 words out of 55418 words

Chapter 13 - HAMSHAƘIYAR-UWA 2

04 Jul 2024

6013

zama tare da wayarki zan kira ki."
Nace Allah ya tsare ya bada sa'a. Na dawo na dur?usa gaban Hajiya Nace za 'a yi miki wani abu ne? Jin shiru yasa na ?ago na dubeta, ita ma ni take kallo. Na bu?e baki zan yi magana ta ?ora yatsanta akan le?enta da sauri alamun inyi shiru. Sannan cikin isa ta ce, "Haka ku ke magana kamar kuna yin magana da ma?ota? Haka ki ke yi wa ?ana magana? da irin wannan sautin ku ke hira lokacin da ya ke zuwa zance? Na yi shiru ina kallon ta. Ta girgiza kai sannan ta ci gaba da fa?in akwai bu?atar ki sake sabon tsari game da irin wannan hayaniyar da ki ke tsammanin cewa magana ki ke yi." Na ka?a kai alamun naji, domin ina tsoron kar inyi magana in sake yin sauti mai ?aran da tace. Tace "Tashi ki je kuma ba ina nufin ki kama baki ki min gum in anyi magana ki ka?a kai kamar ?adangaruwa ba." Da le?una na amsa ban bari sun fitar da sauti ba. nace To.
Na zauna a bakin gadona na yi shiru ina tunani wajibi ne in koyi yadda suke magana domin in samawa kai na sau?i, amma ta yaya? Wa zai koya min yadda suke magana? Amma kuwa anya ba nau'in wula?anci a lamarin Hajiya, shi so ?aya ya min magana tun yana zuwa zance,kuma daga lokacin na rage sautin muryata in muna magana da shi. Sannan su Juma da yaran ai duk na yi magana da su amma banji wanda ya ce komai game da sauti na ba. Na tuna yadda Hajiya ta wani toshe kunne kamar na kunna mata lasifi?a, kuma ita ma munsha yin magana da ita kafin yau. To ko yau ?in na ?aga murya ne? Na tambayi kai. Koma menene na sha alwashin yadda na shigo gidannan matsawar ba da mijina na samu matsala ba,zan jure komai da komai in samu zama hamsha?iya kamar yadda ta fa?a.
Na yi gyaran murya na soma gwada yadda zan yi magana a gidan da kowa a gidan.

Shamaki a kasuwa duk wani kaikawo da wata ganawa da manyan kwastomomin su da ya ke yi sai amaryarsa tana zuciyar sa Allah Allah Allah yake ya ?an samu dama ya kira ta ya ji muryarta kuma ya tabbatar ta na cikin ?oshin lafiya.

Ina tsaka da gwaji .kiransa ya shigo, a zuciya ta nace Yawwa bari in gwada da shi, na ?aga na amsa da muryata can ?asa. Da sauri naji ya ce, "Baby me ya faru? Ba lafiya ne?" Nace a a mekaji? Yace "Muryar ki wata iri." Nace ina koyon yadda zan ke yin magana da ku ne?
????????
?Ya ce "Kamar yaya kenan? Nace ashe ina ta magana da ?arfi maimakon ka fa?a min sai ka ci gaba da sauraron a haka sai da Hajiya ta nusar da ni a yau, don Allah ka yi ha?uri, kuma daga yau na saukar da muryata ni ma. Nayi ya yi shiru, can ya ce. "Karki takura kanki zuwa yanzu ni na saba da maganar ki." Ya canza maganar da fa?in "Fatan ki na cikin ?oshin lafiya."
Nace lafiya lau ya kasuwa? Allah ya taimaka. Yace "Ameen.

To yauma rana ta uku haka na fuska sai ?arfe shabiyu ya shigo, ni kuma na yi kwanciya ta na kulle ?aki, banji bugun sa ba sam. Ban farka ba sai kiran sallar asuba, da na farka na ganni a ?akina take naji fargaba, ko yaya wannan bawan Allahn zai ?auki bin oho. Cikin sauri na ?akko wayata na duba bai kira ni ba, na shiga ban?aki na yi alwala na fito naji ana ?wan?wasa min ?ofa. Da sauri naje na bu?e, shine a tsaye zashi massalaci yace " Ashe kin tashi ma toshi kenan na tafi masallaci." Babu wata alama ta damuwa data nuna a fuskar sa. Nace to, dama ka yi ta kirana ne baccin ne mai nauyi banji ba. Ya yi murmushi "Kada ki damu, ban kira wayarki ba ma,saboda zata tashe ki bacci kuma kinga kanki zai yi ciwo yanzu kije ki yi salla nima kada in makara.
Na idar da salla na zauna kan sallaya ina tunanin ta ina zan ?ullowa wannan al'amari. Yanzu ma nasan sai zai tafi kasuwa zai shigo ya shirya.
Na ?akko ?ur'ani na zauna ina ta karatu har ?arfe bakwai, na tashi da sake wani salon dabarar na shiga na fesa wanka na gyara fuska ta na zuba kwalliya na saka Atamfa doguwar riga na ?aura ?ankwani bayan na saki gashina a kafa?a. Na fesa turaruka mayafi na yafa kamar mai zuwa unguwa na nufi gaida Hajiya. Suna zaune kamar kullum suna zantuka ?asa-?asa.
Nayi sallama can ?asan ma?ogwaro suka amsa na dur?usa na gaida Hajiya ta amsa fuska a sake, sannan na juya na gaida shi ya amsa yana ta kallona, na ?an zauna jim,sai na dubi Hajiya zan iya zuwa in taya su Juma aiki? Duk suka Kalle ni, ya kalli Hajiya da sauri. Tace "Menene dalilin ki na so shiga kuxin?" Na ?asa ?asa da murya, dama dai ina son in koyi wasu abubuwanne wa?anda ban ta?a ya ba. Tace "To sai ki rubuto min abinda baki iya ?inba kinga sai in sa a koya miki."
Na koma gefe na zauna ina kallon su,sai satar kallona ya ke yi da mun ha?a ido sai ya faki idon Hajiya ja ?aga min gira. Can Hajiya tace. "Kinga tashi jeki iciki kin raba mana hankali muna magana. Na yi mata sallama cikin ladabi sannan na tafi.
Ina ta kai kawo a cikin ?aki ina neman shawarar da zan yanke. Hajiya bazata yarda in zauna kusa da su ba kuma bazata bari in ra?i su Juma ba,ga mijina munyi nesa dole dai in samawa kaina farin ciki na nufi gefen sa ma jiya Rahin da yara ana shirin makaranta,na zarce gurinsu. Ta taga na ke kallon yadda suke shirin, sai na shiga na ?ara gyara musu. Mubina tace "Momy saboda ke momy ce shine ki ke saka mana kayanmu?" Nace e mana ai ita Momy ta son taga yaranta sunyi kyau sosai sun fi kowane yara. Meema tace Zainab ?awata tace su Momynsu ta ke yi musu Homework mu kuma sai dai Anty lesson take mana. Nace wacece kuma Anty Lesson Rahin ta ce wadda ke zuwa gida tana ?ara musu karatu. Nace au, to ina kuma Azima ta ke? Rahin ta nuna min ?ayan dakin da hannu ta ce ita ga ?akinta can.
Na tashi na nufi ?akin tana zaune bakin gadon ta tana saka safa, ?akine sosai irin na mace da komai a ciki. Ta bini da kallo nima dai ita nike kallo zancan gaskiya kuma yarinyar tana da kyau sosai. Nace Azima baki zo ?akina ba Ni gashi na zo naki, ko bakya son mu saba ne? Ta?an ta?a baki. "Ni bana da ra'ayin sabawa da kowa sai Hajiya kawai." Nace haka ne. Ni kuma nafi sabawa da Shamaki. Ta kalleni da sauri sai kuma ta sunkuyar da kai ta ci gaba da abinda take yi. Nace bari in tafi,in kin dawo zaki zo ?akina? Tagirgiza kai tare da furta 'a'a.


Na tafi ina mamakin 'yar ?aramar yarinya ta iya kishi haka. ?akinsa na koma na shiga gyarawa har na gama bai zo ba, na fito Juma ta dawo daga kai min abinci nace a kawo turaren gefena tace to, har zan tafi sai nace bari injirata domin inyi amfani da damar in ji wani abu a gurin Juma.
Ta kawo turare, ta ake zata tafi, nace ni ko Baba Juma dan Allah ina da tambaya, sai naga ta juya da sauri tamkar bata jini ba. Na cika da mamaki na kama hanya na yi ?akina. Kaina gaba ?aya ya kulle,sai naji an ?wa?wasa ?ofa, ina bu?ewa sai naga Juma da turaren gefena tace ai 'yannan na jiki ?azu kiyi hankali ba ko ina ake magana a gidan nan ba domin cike yake da kyamarori. Na zaro ido tace zan samu wani dalili da zan shigo ?akin baccin ki a ciki ne ba a saka kyamara. Bata jira jin me zance ba ta wuce.
Na koma na zauna da?as akan kujera, ina tunanin wace irin kyamara, a zuciyarsa nace ?ila irin ta gidan Ya Umar Soja wadda ya sawa Asmy a littafin da na ta?a karantawa na fuska biyu. Ashe dai akwai shi a gaske kenan. To in Yaya Umar Faruk ya saka wa Asmy kyamara domin ya ga abinda take yi in baya nan ko tsoron karya na ?arta kawo masa namiji gida su kuma nan gidan saboda me suka saka? Dole akwai bu?atar in shiga taitayina sosai, tunda shi kanshi da yake i?rarin sona bai sanar da ni cewa in kula akwai kyamara ba.

Laf na yi a cikin ?aki a saman gadona, hatta karin na kasa yi, can naji an bu?e ?ofar falona an shigo. Nasan shine domin naji ?amahinsa. Na tashi zaune yace "Wai har an yaye ni ne?" Nace kamar yaya? Yace baza a za?a min kayan ba? Nace to ai kai nake jira, ga mamakina sai yace "To ba sai a ciro a ajiye min ba tunda an gyara min ?akin." Na mi?e to muje in baka. Ya kamoni zuwa jikinsa, yace "Baby sai inga kamar kina guduna ne, jiya ki ka ?i zuwa ?akin mijin ki." Nace Barci ne ya kwashe ni. Ya ?ago fuskata ya ha?a tsinin hancinmu yace "Ba sai kije can ki yi bacci ba?" Na kumshe ido nace yau zan yi haka.

A ?akinsa duk da nayi wanka sai da muka sake yi tare domin sai da ya ja dalilin haka, gaskiya na yarda da son da yake min domin ya nuna min zallar hakan sannan ya iya tafiyar da mace cikin sati ?aya na amarci bani da bakin magana. Damuwata shine ?aranci lokacin da muke yi da shi. Duk dare sai nayi bacci yake shigowa, ba bu haduwar asbashi, sai da safe kurum muke soyayyar da bata fi ta minti talaatin ko arba'in ba. Ba hira sam, Lokaci dai da zamu zauna mu yi hira babu shi, ko ya fita kasuwa sai dai in masa text na mi?a gaisuwa amma fa in na jiraci amsa to ni ce zanji haushi, ?an lokacin da ya kan samu ya kira ni ma ba kullum ba.
Ranar da na cika kwana goma sai na tashi da mura da zai fita ya sanar da Hajiya. Tace assha sai an kira likita ne ko kokuwa dai akai mata magani?Yace Ina ganin kawai akai mata magani tunda ta yi aiki ma. Hajiya tace Allah ya sawa?a.
Ina kwance akan gado naji sallamar Juma nace ta shigo ciki, ta kawo min magani muta tace "Hajiya tace ayi miji sannu." Nace ina amsawa. Tace to tace ayi miki sannu in kinji ba wani sau?i sai a kira likita. Nace ba komai.
Tace kwanaki kin ce zaki tambaye ni wani abu." Nace e ta ce "To ga shawara duk wani bayani da za ki so ji in kin kwantar da hankalinki zaki same shi, amma in kin fi son ki tambaye ni to kina iya tambaya amma zance ka iya tasowa in fa?awa Hajiya cewa kin tambaye ni abu kaza, bansanta ba amma hakan ka iya shafar jarabawarki. Ta ?ara matsawa kusa ba a banza ki ka ga na kwashe shekaru a gidannan ba, 'yar amanar gidance dan na yaba da halinki ba shine zai sa in za?e ki in bu?e musu sirri ba. Na ?an ta?aki ne domin ku lura da zaman gidan ba wai domin ni da ke mu zama munafukan Hajiya ba." Tuni na yi mutuwar zaune, amma sai na dake nace, Allah sarki Baba Juma waccan ranar dama zan tambaye ki ne ko zan iya zuwa kicin inke tayaku aiki saboda in koyi wanda ban iya ba, to kuma na riga ma na tambayi Hajiya tace in rubuta abinda zan koya sai ta sa a koya min. Juma ta ce "Allah Sarki to ai Hajiya baza ta yarda ki shiga kicin ba, domin Hajiya bata yarda ?anta ya ci abincin wata matarsa ba. Amfanin ki ?aya ki biya wa ?anta bu?ata ki haifa masa 'ya'ya. Na danne tsoron da ya taso min nace, to ita matar aure ai bata da yadda zata yi sai abinda mijinta yace. Juma ta juya ta ce ashe dai kin gano." Na bi bayanta da kallo a fili nace akwai aiki.
.....
Na koma na kwanta ina tunani, kullum in na kalli sau?i ta nan sai ya zama tsuri, na tabbatar wa kai na Juma tana sanar da ni ne cewar bata da sirri sam. Ga gida cike da na'urorin ?aukar hoto. Yawata ta soma ruri, na duba lambar Umma ce, na ?aga Jamila ce, cikin rawar murya ta ce Yaya Baby Umma ba lafiya gamu zamu tafi asibiti haihuwa ce tun jiya jini ne ya ?alle mata da sauri na diro daga gado ina fa?in wane Asibitin ne gani nan zuwa. Tace Murtala zamuje. Da gudu na ja hijabi na saka na sa takalmi har na fita daga falo sai wata zuciyar ta tambaye ni da cewa,kin tambayi mijinki? Na ciri wayar a jaka na yita kiran wayarsa amma bai ?aga ba. Na nufi gurin Hajiya na tsugunna a gaban ta idanuna sun ciko da hawaye. Tace "Jikin ne?" Nace a a ko maganin ban kai ga sha ba, aka kira Ni daga gida Ummanmu za akai asibiti jini ya ?alle mata. Tace Ya Salam! To yanzu ya akayi? Nace zanje ne. Tace kin fa?awa mijinki? Na dubeta bai ?auki wayata ba. Tace to kiyi ha?uri ki koma har sai kin samu izni daga gare shi. Na sake rusunawa nace Hajiya ko ku zaku kirashi wallahi bata cikin hayyacita. Hajiya tace "Samu nutsuwa mana Rabi'atu, ki koma ?akinki ki jira mijinki ya dawo ko ya ?aga wayarki, ko kinje baki da wani taimako da zaki iya yi mata bayan addu'a ki koma ciki ki yi mata.
Na mi?e a hankali hawaye suna tsiyaya daga idanuna, na nufi ciki a hankali kamar kazar da ?wai ya fashe mata na nufi sashe na.
Ina shiga na cire hijabi kaina nayi jifa dashi na na zube nan a ?asa ina rera sabon kuka tare da kiran dukkan layukan Shamaki amma babu wanda ya ?aga. Na kira wayar Umma itama Jamilan bata ?aga ba. Na kira ta Abba shima sai a kira na uku ya ?auka, cikin kuka nace Abba ta haihu? Yace "Kash waya fa?a miki ba na hana kowa ya sanar da ke ba!" Nace Abba saboda me? Yazun ma saboda baya nan ne shiyasa ban taho ba,amma ya jikin nata? Yace "To a ci gaba da addu'a sun dai shiga da ita ciki har yanzu ba su fito sun ce mana komai ba, sai fa?a suke wai anbarta a gida ta galabaita. Su kuma kowa yasan cewa in ba ku?i baza su ta?a ta?a mara lafiya ina ta buga bugar neman ku?inne bansamu na kirki ba gara a gurinta an samu dubu tara."
Nace Abba ka turo Jamila ina da dubu goma ta kawo maka su. Yace "Ina ki ka samu karfa kice zaki ta?a ku?in mijinki." Nace nawa ne abokan sa suka bani Jamilan ma tasan ina da ku?in tunda agaban su ne aka bani.
Yace "To zan turo ta yanzu daga nan Asibitin Murtala sannan karki sake ki fito ba tare da sanin mijinki ba." na. Cikin kuka nace to Abba.
Muna aje waya na ?ora sabon kuka ina addu'a. Kamar minti arba'in sai wata wayar tarho da ke ma?ale jiki bangon ?akina kusa da gado ta shiga tsuwa, ni har na tsorata zan fita da gudu na jiyo tsuwa a ?akin bacci tunda ban ta?a ji ba. Na le?a na kalli inda nake jin ?arar sai naga ashe gurin wayar ne, naje na ciro na saka a kunne, muryar Hajiya naji tana cewa "Kece ki ke da ba?uwa a gate? Nace e ni ce ?anwata ce Jamila. Tace koma waye ba ?anwarki ba, kamata ya yi ki sanar a fa?awa mutanen da ke gate in ba haka ba baza su barta ta shigo ba.
Cikin dasashiyar muryar da na sha kuka nace zan kiyaye gaba insha Allahu Hajiya tace shike nan. Jamila tana shigowa muka rungume juna muka ?ora sabon kuka,kunsan minti uku sannan na lallasheta na ?akko ku?in na bata, nace su da waye a asibitin tace Umman Amina ce da Umman su Zuhra, sai Abba.

Na rakota zuwa falon Hajiya ta yi wa Hajiya sallama Hajiya tace "Har zata wuce to kin bata ruwa ta sha kuwa?" Nace na shafa'a sauri take daga asibiti ta ke. Jamila na fita zan juya Hajiya tace "To me tazo yi kenan haka?" Nace sa?o na bata. Tace "Amma banga komai a hannun ta ba?" Har zan ?oye sai na tuna da maganar Juma da ta Shamaki, game da fa?an gaskiya, sai nace ku?i ne na bata zata kai wa .Abbanmu asibiti. "Ina kika same su?" Ta jeho min tambaya da sauri. Nace abokan shi suka bani ranar da aka kawo ni. Tace "Kin ce abokan shi, shi wa?" Na fara gajiya da tambayoyin ga halin da nake ciki sai na soma hawaye cikin rawar murya nace Shamaki. ?a gya?a kai tare da fa?in "To na gane, shi kuma kukan na menene?" Na share hawaye tare da girgiza kai nace ba komai. Ta maida kallon ta ga TV na wuce ciki zuciyata fal da takaici.

Haka azahar da la'asar suka riske ni a gurin ba wani

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login