Showing 3001 words to 6000 words out of 55418 words
maganar bincike shiyasa ban so aka ?ara sati ?ayan nan ba wallahi. Domin gani nake wani zai iya zuga su Umma su ce sun fasa bashi ni. Jamila ta ja tsaki ta kwanta tare da fa?in ni fatana Allah ya sa yana miki irin son da ki ke masa." Nace yanzu har Kinji haushi kenan? Ta ce "Zakewar taki ce tana yawa, kuma kisan Allah Umma da Abba abin yana basu takaici kyazo kija wa kanki suce sun fasa mugani ko zaki bishi ba aure. Na ?ora kaina a gadon bayanta ina fa?in bazan bishi ba Jamila, amma na tabbatar zan mutu. Dakin yayi tsit Jamila haushi ya hana ta bani amsa. Ni kuma na fa?a tunani wai ace an fasa. Da sauri naga Jamila ta tashi zaune tasa hannu biyu ta tallafi fuskata wai ashe hawayena ne suke sauka a gefen cikinta. Tace Kuka ki ke Yaya Baby, me akayi na kuka?" Na sauke ajiyar zuciya cikin rawar murya nace wallahi ban sani ba Jamila, amma na samu kaina a matsananci son Yaya Aliyu iya tunanin sa in na zurfafa sai na yi wannan kukan. Kuma na kasa gane dalili. Kimin fatan Allah ya sa shima yana sona. Jamila ta shiga lallashina tana share min hawaye tana fa?a min cewa tabbas ya na sona, kuma aure babu fashi kuma za a yi komai cikin rufin asiri. Muka kwanta cikin sa?e sa?en zukata. Sai Muryar Abba muka ji yace "Ke Baby zo nan.'.. Muka tashi da sauri zaune nace Jamila me yafaru? Ta yarfa hannuwa alamun bata sani ba. Jikina ya soma ?ari, na ce kodai ya ji zantukamu ko kuma wasu sun shigo shi akan maganar binciken Aliyu ya fasa aura min shi. "Ina ki ke?" Muryar shi ta ?ara ratsowa. Jamila cikin sauri tace kije mana amma komai zai ce ki yi shiru. Na mi?e na fita yana zaune kan tabarma inda sukan zauna da Umma.
Shamaki ya bu?e flas ?in abinci ya soma zuba farar shinkafa, idanun Hajiya suna kansa har ya gama sannan ya zauna ya fara ci yana son tuno wane labari ne Hajiyar ta fi maida hankali sosai. Kodai labarin mahaifin su,ko kuma dai labarin kasuwancin su daidai lokacin wayar shi ta soma ruri, ya kalla Soyayyata . Ya ?ago ido ya kalli Hajiya ta tsare shi da kallon tuhuma dole ya yi wayar a gabanta domin fidda kansa. Ya yi ?an murmushi bayan ya gama wayar ya tauna abincin da ya zuba a bakinsa zai yi magana,sai ta ?aga masa hannu, gama cin abinci, ka fi kowa sanin cewa bana son ana magana lokacin cin abinci, ka gama sai kamin bayani kamar haka..
Duk saboda son yarinyar ne ka soma munafurta ta har ka shirya zama da 'yan uwanka saboda ni? Sannan ka ciro min fayal ?in da kake ?oyewa da hannunka har kana zubar da su dan kawai in rasa gane wanene ka aje gefe. Sannan ka min bayanin dalilin yin duk wannan alamun na rashin gaskiya da kake yi tun da ka shigo gida, kuma ka fa?a min da wa ka yi waya da ka shiga ?aki! Cokalin da ke hannun Shamaki ya fa?i abincin ya zube masa a riga. Yawun bakinsa ya ?afe sannan ya tsaida idanun sa akan Hajiya cikin tsananin firgici.
????????
?*HAMSHA?IYAR UWA????*
*NA*
*HALIMA ABDULLAHI K/ MASHI*
_PAID BOOK_
_Ku?in karatu ?600_
_Account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank a turo shaidar biya ta wannan number 08140004302 ko katin Mtn_
_Phone 08140004302_
*DOKA*
_Ban amince wani ya ?ora littafin nan a wani Social media ba,ko a maida mini shi Audio ba tare da iznina ba yin haka daidai yake da fuskantar fushin hukuma. A kiyaye_
*Masu son a Tallata masu hajarsu suyi magana ta wannan number 09068032427*
*Page 12*
Na isa gaban Abba cikin tsoro na zauna, duk jikina babu inda baya rawa, ina da tabbacin da "Abba zai ce an fasa ba Yaya Aliyu ni, bana ko shakka zan iya fa?uwa a gurin sumammiya. Sai naji ya tausasa murya ya ce "Baby" Cikin rawar murya na ce na'amm Abba. Yace "Kina ganin baki da wata damuwa in har aka ?aura auren nan aka kai ki gidan yaron nan a haka babu kaya ko kuwa kina ga akwai wata damuwa in ro?e shi ya ?an ?ara mana lokaci muga abinda Allah zai yi?" Na sauke wata wawiyar ajiyar zuciya. Sannan nace Abba ba ni da wata damuwa akan haka, ai munyi maganar da shi ya ce ai duk al'ada ce, kuma ya ce min zai siya in ya samu ku?i. Abba ya daka min tsawa "Ke! ni ban tambaye ki dogon labari ba, abin da na tambaye ki kawai shine, zaki zauna da mijinki lafiya ko da ba mu samu munyi miki kayan ?aki ba?" Zan zauna. Na bashi amsa da sauri kamar ina jiran tambayar. Umma ta fito daga ?aki tace Sannu Baban Babu nifa gaskiya bazan iya kai yarinyar nan gidan miji babu kayan ?aki ba, kodai ka je ka ciyo ko bashi, ko kuma ka yarda muje ka saka hannu a wancan na tallafin a kar?o, baka da shi, to menene naka na yin girman kai? Abba ya mi?e "Salamatu" ya nuna Umma da yatsa cikin tsananin fushi wanda ban ta?a gani ba, yace ki shiga hankalin ki da ni, in ba haka ba kuma zan yi matu?ar baki mamaki domin zaki tafi gidanku ki haihu a can , ni kuma in aurar da 'yata cikin kwanciyar hankali. Jamila ta fito da sauri ta nufi gurin Umma ta ri?e mata hannu ta na cewa "Umma kiyi shiru: don Allah. Ni kuma kuka ne ya su?uce min na kasa furta komai, saboda ni iyayena suna sa in sa abinda ban ta?a gani ba tunda na ta so. Kamata ya yi ince su yi ha?uri na fasa auren ma gaba daya, amma yadda nake ji koda tafiya Umman zata yi ba zan iya furta hakan ba, shin dama haka son yake ? Da numfashi yake kamar wani bala'i ko kuwa nawa son ne ya zo a haka? Muryar Umma ta katseni. Lallai Abubakar Allah ya kawo mu lokacin zaka fa?i haka tsakanin ni da kai, to ni kuma da inga aure nan a haka gara ayin bana gidan nan, na yarda da haka. Amma in ka tashi ka bani saki uku ras yadda ba sai na dawo ba.. Da sauri nace Umma kuyi ha?uri saboda ni ba zaku rabu ba. Ni gaba ?aya ma na fasa au! au!! Sai na samu kaina da kokowa da numfashi na matsawar na furta kalmar zan iya mutuwa. Jina nayi na kai ?asa ina wani irin numfashi, ina ta kuma ?o?arain furta na fasa auren kuma ina jin salatin iyayena kamar daga can nesa, sannan ga muryar Jamila tana kiran yaya Baby! Zuwa can kuma sai na daina jin komai.
A dai dai wannan lokacin Hajiya ta kalli Shamaki sosai zarginta game da takardar ya bayyana kuma in har haka ne yarinyar sun zo, neman taimako ne ha?i?a sun fadi babbar jarabawar ta. Wanda hakan zai sa ko da an yi wannan auren to sun za?tarewa yar su wani babban maki. "Ka bani in duba" ta furta cikin isa irin yadda take yi in ?asaitarta ta motsa. Bashi da wani za?in da ya wuce ya bata wa?annan takardun na gaskiya ya saurari Allah wanda yake ta kira sunayen shi ?ari ba ?aya a ?asan zuciyarsa. Sanin kanshi ne in ya bata wa?anda ba su bane zata gano na gaskiya ta hanyar yin magana da Maman Afra. Wanda hakan zai iya haifar da ?atuwar matsalar da zata iya soke auren Baby wanda yake ayyana hakan da mutuwar tsaye a wurinsa. "In har ka bari na tafi daga falon nan karka sake ka tambayi dalilin da ya sa na janye batun auren ka."
Kalaman Hajiya suka ratsa kunnuwansa. Cikin sauri ya mi?a mata tare da fa?in afwan afwan ina duba shi ne. Ta amsa tare da fa?in "Ai guda ?ari ne a gurin dole ka kasa tantancewa. Ta ?auki gilashinta ta saka ta soma bin shafi shafi tana dubawa, bata ga wani abu da zai sashi yin irin wannan rashin natsuwar da har ta jefa shi a zarginta ba, amma dai ta yi imani dole akwai wani abu. Don haka ta maida hankali ga Number daya ?auka, yana kallon ta har ya soma murna, sai kuma ya zaro idanu ganin tana ?aukar lamba. Ta danna kira ya tafi, har ya katse ba a ?aga ba.Ya ha?iye yawun bakin sa da ya ?auke, sai kuma ya ga ta ?ara dannawa. Sai aka ?auka, ta danna handsfree ta yi sallama, cikin yanayin damuwa aka amsa. Tace "Daga Zeena Foundation ne inda kuka zo neman taimako, ance ku kawo mahaifin yarinyar amma ba ku zo ba?" Cikin girmamawa aka bata amsa, "Kiyi Ha?uri Hajiya Mahaifinta ya ce shi ba zai zo ba." Kafin ta ?ara magana sai taji muryar namiji ya amshi wayar. yana magana cikin fushi, Hajiya yarinyar nan tawa ce dan ina talaka bani da rashin godiyar Allahn da har sai naje maular kayan ?aki. Batare da izinina taje ba. Kuma ban aike ta ba, bana bu?ata kiyi ha?uri. Hajiya zan mata iya yi na, ku ba wa?anda suka fini bu?ata." Ya kashe wayar ba tare da jiran amsar ta ba. Falon ya yi tsit in bada ?aran AC da kuma TV da ke yi can ?asa. Kusan da?u?a tamanin, sannan Hajiya numfasa ta ce, "To kaji sirikin ka irin amsar da ya bayar." Shamaki yace Sirikina kuma Hajiya? Tace "Ka dai na yi kamar wani baka gane komai ba, tun daga sunan yarinyar na fuskanci surukan ka ne, kana son ka ?oye min domin kar in gani, dama baka ?oye kana nuna rashin nutsuwa ba, babu lallai in gane abinda ka ke ciki. Ta gyara zama ta ?anyi ?asa da murya, tace, In tambaye ka mana Shamaki." Ya sunkuyar da kai tare da fa?in ina jinku Hajiya. Tace "Wai inada wani mugun hali ne? Da sauri yace Subhanallah! Mai ya kawo wannan furucin! Baki da mugun hali Hajiya, baki kusanci, mugunta ba. Tace "To me yasa ka ?oye min cewa surukan ka sun zo neman taimako?" Ya numfasa Wallahi Hajiya zaman da nayi a nan gurin shine ya kawo har na na kula. Sannan na ?auki lambar ne na bincika na gano. "To daka gano da wane irin hukunci zaka ?auka?" Dama dai zan maida ne su bi ?a'ida da ake bi, domin abu bai min da?i ba, yadda nasan mahaifin yarinyar nan da ha?uri wadatar zuci da ?o?arin nema kuma ace sun zo neman taimako. Wallahi da kika kira shi naji da?i sosai da naji cewa babu sa hannunsa, ita ma Umman ta su ?ila wasu ne suka zugata. Hajiya ta sauke ajiya zuciya tace "Ni kaina da ace Uban ya zo ha?i?a sun kayar da 'yar su babbar jarabawa. Amma me zaka ce game da ita uwar da take aikata abu ba tare da sanin mijinta ba, wane tunani zaka yi game da 'yarta mai kwaikwayo daga gareta? Kasan dai uwa ce makarantar farko a gurin kowane yaro." A ?asan zuciyarsa yace ta ?ir?iro wata damuwar Allah ka fidda ni. Ya ?anyi gyaran murya yace Hajiya ba wannan ne abin dubawa ba, abin dubawa shine, da Abba ya ji abinda Umma ta yi kuma ya daka tsawa, ya hana kuma akaji ba a bijire ba. Shine abinda za ku duba Hajiya saboda wancan kuskuren ne da kowa zai iya aikatawa. Ko Allah da ya halicce mu muna yi masa kuskure amma da mun amshi kuskurenmu mun tuba shike nan. Hajiya ta saki maganar da fa?in "To ko ba komai sai ka godewa sirikin ka domin yadda ya yi jarumtar ?in amsar kayan nan, ya kwace ka daga ?aryar da kamin ta farko, sai dai kuma bayan tiya akwai wata caca." Shamaki ya zaro ido. Wacce fa? Hajiya tace "Wannan zan jira sai lokacin da ka ke jin cewa ni mahaifiyar ka ce, kuma wadda ta ke yi maka so da ?auna zalla babu sirki, wadda ko mutum ka kashe zata iya rufa maka asirin da har duniya ta tashi ba wanda zai ji. Kai wadda zata iya bada ranta domin fansar naka. Lokacin da duk ka fahimci hakan sai mu yi ?aya magana."
?????????
*HAMSHA?IYAR UWA????*
*NA*
*HALIMA ABDULLAHI K/ MASHI*
_PAID BOOK_
_Ku?in karatu ?600_
_Account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank a turo shaidar biya ta wannan number 08140004302 ko katin Mtn_
_Phone 08140004302_
*DOKA*
_Ban amince wani ya ?ora littafin nan a wani Social media ba,ko a maida mini shi Audio ba tare da iznina ba yin haka daidai yake da fuskantar fushin hukuma. A kiyaye_
*Masu son a Tallata masu hajarsu suyi magana ta wannan number 09068032427*
*Page 13*
Cikin sanyin jiki Shamaki ya sunkuyar da kai, tabbas ya sani Hajiya tana yi masa so tsantsan na tsakanin ?a da mahaifiya. Kuma tabbas 'yan uwansa suna son sa sai dai fa ba kamar Hajiya ba.
Kuma su suna iya tattauna damuwar shi da mazajensu saboda so da kuma yarda da juna. Amma Hajiya bazata iya tauna kowace matsala tasa ko ?arama ko babba da su 'yan uwansa ba. Hajiya ce keda maganin damuwar sa kuma ita yafi dacewa ya kai ma wa kuka, kamar haka ta ke nufi.
Ya ?ago ya kalleta ta zubawa TV ido, kamar tana kallo, amma ko shi ya san tunani kawai take yi. Ya ?an ?ara matsawa kusa.