Showing 45001 words to 48000 words out of 55418 words
kai alamar 'a 'a. Tace "Ki sa auduga ki ?iba sai ki yi matsai kamar minti biyu sai ki cire." Na.sunkuyar da kai dan kunya nace to.
A ?aki ina shiga ya hau rawar jiki, nace akwai damuwa fa. Ya tsaya yana kallona nace bana salla. Ya ?ara jana jikinsa ya ce "Karki yi min haka bazan jure irin wannan wasan ba." Nace ba wasa bane bari in nuna maka. Yana gani na ga duk yanayin sa ya canza ransa a ?ace. Nace in akwai wani abu da zai sa ka samu nutsuwa zanyi maka. Yace ke da ki ke kyamata." Nace ai na bari. To haka dai ya sa nayi ta yi masa wasu abubuwa har sai da ya samu nutsuwa.
Duk abin da na ke fa?in ina ?yamar dole na yi masa saboda ya bani tausayi.
Bacci ya kwashe mu sai kiran magriba ya tashe mu. Yace "Subhanallah! ba mu yi la'asar ba. Tare muka yi wanka muka yi la'asar sannan ya fita Masallaci.
Haka dai zaman ya ci gaba da tafiya duk wanda ya ganni abin sha'awa amma bani da ko ?arfanfana jiki na ya yi lukui ?amshi ya kama jikina saboda irin turarukan da Hajiya ta ke bani farko na zargi Hajiya ko kishi take yi da matan ?anta har ta ke korar su, amma abin ?aure kai shine, Hajiya bata da wani buri sai in yi abinda zai sa ?anta ya ji da?i. Da kanta take bani maganin mata, kitso da ?unshi kuwa da ya fita zata sa a kuma yi min wani. Sannan kullum in na zo gaishe ta nasiharta shine in farantawa mijina rai kuma in masa biyayya, in jure duk yadda ya zo min domin in kare shi daga matan waje.
Abubuwan da take bani ina sha sun kai matsayin ni da kaina na ke ?osawa mu yi auratayya da shi.
Haka nan zuwa yanzu duk wani abu da ya ke so na gama gogewa da iya su, har ma nakan tambaye shi ya 'akayi ya iya duk wa?annan abubuwan. Sai yace min koya ya yi shima a karance karance.
Kwatsam wata safiyar Lahadi baya fita kasuwa da wuri, yana falon Hajiya ni kuma ina gyaran sasan shi.
Sai naji ?arar shigar sa?o a wayarshi na kalli wayar,, garga?in da aka min ya fa?o min, amma sai na watsar na ?auka na janyo saman inna zan iya ganin sa?on sai naga ta Whatsapp ne, an turo Video ne kuma sunan sai naga an saka NFS.
Bansan dalili ba sai naji gabana ya fa?i, an yi min nasiha sosai akan waya kowa fa?a ya ke yi min in kiyayi wayar mijina. Dan haka sai na aje.
Amma tun daga ranar na tattara hankalina sai da na gano cord ?in wayar. Bayan kwana biyu sai na sake samun dama yana wanka na bu?e kai tsaye na shiga Whatsapp ?in sa. Na yi searching wannan sunan sai ya fito min da chat ?in su, duk da cewa da turanci suke magana kuma gaskiya ni bana fahimtar turanci sosai amma na gane hirar ta batsa ce ya goge Videos amma naga inda ya yi taggin yana fa?a mata cewa hoto ya yi kyau.
Motsin sa ya sa na aje wayar na ci gaba da abinda na ke yi. Na yi ta kallon shi ina mamaki matukar mamaki. Ga wata tafasa da zuciya ta ke yi. Ya kalle ni, "Babyna ya aka yi ne?" Na ?a?aro murmushi kyau na ga ka ?ara wallahi ina kishinka kamar wasu matan suna sonka a waje. Ya yi 'yar dariya "Baby ke dai Allah ya kyauta amma mata yanzu ai ba'a raba su da son maza, suma mazan haka."
Nace Yawwa dan Allah to ina son ka bu?e min Whatsapp ka ga duk 'yan makarantar mu suna yi, ina son muna zumunci. Ya ?an ha?e fuska, yace "Ki bari sai na canza miki waya tukuna." Nace to Allah ya baka iko. Yace Ameen Baby na,ya saki fuska. Na raka shi yadda na saba na dawo na shiga ?akina na soma sabon kuka, ina cewa wai me ya kai ni ne, me yasa na dubo wa kai na damuwa. Amma naji mamaki wai Aliyu Shamaki shine ke neman mata!
Duk da haka ban daddara ba yana bacci na saci wayar na shige ban ?aki na gama duba duk wasu mata da yake soyayya da su. Mata ne masu aji kyawawa sun fini komai, wani abin takaici harda wasu mata 'yan Film.
Tambaya ta ita ce da wane lokaci ya ke samun ha?uwa da su?
??????
Bani da wanda zan tunkara in sanar da shi halin da nake ciki. Amma abinda ke bani takaici na kasa fa?a masa cewa nasan abinda ya ke aikatawa. Haka son sa a zuciya ta yana nan daram na kasa jin haushin sa, sai ma neman yi masa uzri na ke yi. ?ila ya fara ne lokacin da yake bashi da mata, yanzu aiki na ne in rabashi sa su. Ko ?ila su ke binshi kuma iyakacin su a waya sai turo hoton kawai. Dan haka na ?ara dagewa na daina bacci sai na jira shi ya dawo kuma duk yadda ya ke so haka nake masa, sannan da safe kafin ya fita wajibi ne sai na sauke wani ha?kin amma da an kwana biyu in na duba wayarsa sai inga anyi masa sabon turi na tsiraici. Gashi na kasa daina dubawa, sai na yanke shawarar komawa ga Allah ya bani mafita. Sai mun kwanta yana bacci zan tashi ina fa?awa Allah halin da nake ciki ya taimake ni ya shirya mijina ya rabashi da wannan muguwar ?abi'ar.
Yau ma ina tsaka da addu'a sai kuka ya ?wace min ina kuka ina fa?awa Allah cewa. Ya Ubangiji! Kasan halin da na ke ciki Allah kai ka kawo min wannan bawan naka har ?ofar gidan mu Allah ka sani ban ta?a aikata zina ba, Allah na san cewa akwai wani abu da ka ke nufi da wannan ha?in da ka yi. Bani da wata mafita ko wata dabara Allah ka taikeni ka fidda shi a cikin wannan halin. Kuka ya ti?e ni. Na shafa addu'o'in na ta shi naje gefen shi na kwanta na matsa na shige jikinshi kamar yadda muka saba kwanciya. Sai naji ya matseni tsam ya ce wai "Baby wace damuwa ce da ke wadda duk dare sai kin tashi kin yi wa Allah kuka. Nasani shine wanda ya fi dacewa da ki kai masa kukanki, amma tunda ya baki ni Baby ki fa?a min mana ko zan iya yin wani abu akai in bazan iya yin komai ba sai in taya ki ro?on sa?"
Na sake matse shi nace nace wai dama ba bacci ka ke yi ba? Ba wata damuwa ce da ni ba, ina yi wa Allah godiya ne da ya bani kai a matsayin miji wanda wayo na da dabara ta ba su isa su bani ba.
Ya sake matseni ya ce "Baby ni ne ya kamata inyi wa Allah godiya samu mace irin ki sai mai babban rabo.Dan haka karki damu ki kwantar da hankalin ki ni baku ne har aljanna."
Cikin kwanaki yanayi na ya fara canzawa na rame kuma na rage walwala. Shima ya lura da haka ya matsa min da tambaya na ce ba komai, ya siya min waya Iphone 13 yace in bawa Jamila waccan bu?e min Whatsapp duk wai dan in saki raina, ya min garga?i wai kar in shiga wasu groups irin na Whatsapp ?innan wanda ake zuga mata, wai Maman Mubina ta ta?a shiga wani group wanda suka yi ta samun matsala da shi. " Nace masa zan kiyaye nace wa Hajita ta taya ni yi masa godiya dama a gaban ta ya bani. Yana ta ?o?arin in saki jiki in koma walwala ta amma na kasa. Ina kuma ci gaba da bibiyar shi ta wayarshi ina ganin yadda yake ci gaba da hul?a da mata, abinda na gama lura shine ya kan ha?u da wasu, wasu kuma baya ha?uwa da su,amma yana ba su ku?i.
Cikin haka azumi ya gabato. Da dare yana falon Hajiya da yake tun daga wannan ranar nike zuwa ina zuba masa abincin dare da na safe, wanda da ashe Azima ke zuba masa na daren na safe kuma da kansa. Daga shi har Hajiya ni ce ke zuba musu.
Hajiya tace Baby kin kuwa san Azima bata da lafiya kin duba ta? Nace bansani ba,tace to ya kamata ki yi mata sannu jiya da yau bata je makaranta ba. Nace Subhanallah! Na tashi na nufi duba ta tunda na zuba musu abincin. Tana lull?e na mata sannu ta amsa,har zan fita sai tace "Ki fa?awa Yaya ina jiran shi." Na yi shiru,sai na juyo nace kamar yaya kina kina jiranshi? Tace " Shi ya sani." Sai na ji gaban ya yi wata muguwar fa?uwa tsoro da fargaba sun kamani kar dai har wannan yarinyar...Ta katseni, "Ko kina nufin baki san ni wacece a gurinsa ba?" Bance ?ala ba na fice domin yin sa'insa da yarinyar zai zama zubda ?imata.
Na koma Falo na samu su Hajiya suna zancan Umara, nace da Hajiya zan jira in shafa maki maganin ?afa tunda Azima ba lafiya. Tace "To Allah ya yi miki albarka jiya ma ba'a shafa ba. Na koma gefe ina kallo a talabijin.
Yace "Hajiya kujeru goma ne a wannan karon an ?ara biyu, yanzu sai ki bada sunayen mutane bakwai ni da ke da kuma Baby mune cikon na goma." Kamar a mafarki na ji maganar, zani Umara, amma sai dai ba dani suke magana ba dan haka sai na share na yi kamar banji ba.
Hajiya ta ce ka cire Baby a maganar ta fiya Ummara da aikin Hajji sai wata shekarar. Ban waigo ba kuma ban nuna ina jinsu ba. Ba tare da ya tambayi ba'asi ba ya ce "To an cire ta." Suka ci gaba da lissafin su. Sai kusan goma da rabi tace zo ki shafa min maganin nan. Na zo na fara shafa mata gami da matsa ?afafun, tace "Kai amma na ji da?in yadda ki ka matsa min ?afafun nan, ina ganin ma dai ke zaki koma shafa. min maganin nan domin Azima sai ta koya. Nace to insha Allahu zan ke shafa miki. Shamaki yace, "wai kuwa likita ya duba jikin Azimar ? Hajiya tace ya duba ta,kasan bata rabo da zazza?in cizon sauro, can take zuwa ?an lambu can har magariba. Na dube shi, baka je ka duba ta bane? Yace "Sai na shiga zan kwanta sai in duba ta.'
Daya ke ina son in wanke zargi sai na raya cewa zan bi bayanshi. Haka kuwa nayi mun tafi tare mun sallami Hajiya na ce masa bari inje ?akina in ?ak?o kayan bacci.
Yana shiga falon shi na dawo na shiga falon dai-dai lokacin yana fita ?ofar da zata kai shi gurin su. Na bishi sai da
na ga ya tura ?akin Azimar ya shiga sannan na bishi ciki faduwa gaba tare da fatan kar zargi na ya zama gaskiya. Dai-dai Window bana jin komai na yanke shawarar in afka ?akin kawai tare da sallama ko zan tsinci kalma guda ?aya da zan gamsu. Dan haka sai na afka kawai tare da sallama. Yana tsaye bakin gadon ya maida hannuwan shi duka baya, tana kwance riginnine tana kallon shi yana magana. Kalma ?aya na tsinta a maganar itace.. " Baruwana..." Na kalleshi sai na ga ya yi alamar rashin gaskiya amma sai ya da ke. Na dube ta sannu da jiki Azima fuskarta ba walwala tace Yawwa. Na dube shi, Nace ta ?i tasha magani ne baji kana cewa baruwanka? Da sauri ya ce ba maganar ki ?ace, muje ya dube ta yace "Allah ya ?ara sau?i." Na sake kallon ta ?walla ce a idanunta,gaba na ya fa?i ko dai ya hai?ewa yarinyar nan ne to Allah ya sa ba ciki ne da ita ba. Sai naji na kasa jan ?afafuna na tsaya ina kallon ta. Muryar shi ce ta katse ni. "Muje mana Baby" Na ja ?afa na bishi dai dai window yara ya tsaya yana kallon su. Ni kuma shi nake kallo ina me takaici abinda ya ke aikatawa amma kamannin shi na salihan mutane ba zai ta?a bari a zarge shi ba. Ya yafito ni da hannu na isa gurinsa ya kama kafa?a ta yace Kalli yaranki suna ta bacci 'yan rigim. Na lalle su abin sha'awa kowacce laf a gadon ta. Nace Ina son yaran nan sosai musamman Anisa ?ila domin ta kasance ita ce ?ara. Yace "Ba domin tana ?arama bane, tun ranar da mahaifiyar ta ta haifeta kowa ya ganta sai ta shigar masa rai." Nace Allah sarki, wai kuwa iyayen su suna zuwa su gan su? Yace "Gaskiya dai ba sa zuwa,kuma Hajiya ce ta tsara haka,amma duk hutu ana kai su suyi sati ?aya sai a ?akko su." Na ?aga kai sannan nace Allah sarki amma kana yi wa yara nan addu'a ko Allah ya tsare su daga sharrin zamani. Yace "Baby daga dukkan sharri na ke musu addu'ar tsari." Ya kama hannu na muje muje ?aki ki fa?a min yaushe zaki bani ta wajen ki Baby Zeena ?in? " Na bishi ina fa?in ni bana son ma in haihu. Bansan a fili na furta kalmar ba sai da naga ya tsaya can. Na kalli fuskar shi launin fuskar shi ta canza gaba ?aya, wannan ce rana ta farko tunda na zo gidan da naga ?acin ransa a kaina, ya tsira min ido take fargaba da tsoro suka tsirga min. Ya fincike ni zuwa ?akin baccin sa ya tura ni kan gado ya jawo kujera ya zauna a gabana ya ce "Maimaita abinda ki ka fa?a." Na girgiza kai cikin tsoro tare da ?ora tafin hannuna a bakina. Yace "Ki maimaita!" Yadda ya yi maganar da ?arfi sai na tsorata hawaye suka soma zubo wa,nace nifa na yi tsammanin a zuciya na yi maganar. Yace "To me yasa zaki fadi hakan ko a zuciyar ki? Kice ke bakya son ki haihu to fa?a min da lilinki kuma kar ki sake ki min ?arya." A zuciyata dalilina saboda neman matan da ya ke yi ne, kuma naji ance duk abinda ka yi wa ?an wani sai anyi wa naka. Amma bani da damar fa?ar hakan dan haka sai nace Ni dama na fa?i haka ne saboda ina jin tsoro kada in haihu ni ma ka sake ni kamar yadda ka saki su Maman Anisa kuma ka kar?i 'yar ka kabar ni ina tunanin ku. Na kai ?arshen maganar da sakin wani kukan. Ya tashi ya dawo bakin gado ya janyo ni jikinsa ya rungume ni tsam. Yace" Baby ni da ke babu abinda zai rabamu sai mutuwa, akan ki na fara soyayya duk auren baya ashe ba soyayya na yi ba sha'awa ce kawai." Na ?ago na dube shi nace dama ana aure saboda sha'awa? Yace "Ni kaina ban gane hakan ba sai bayan auren sai inji duk sun fita a raina." Nace sai kawai ka sake su? Yace 'A'a Baby babu wadda na saka saboda hakan sai bisa wani dalili na Hajiya wanda har yanzu ban san shi ba." Nace Ni ma na fara fita a kan ka ko? Cikin far gaba na yi tambayar. Yace "Baby kullum ?ara son ki nake yi, da kika ce baki son ki haihu kalmar ta min zafi, ya kai hannu ya shafa cikina, na ?osa inga wannan shafafen cikin ya tasa ya ?anyi tudu, ina son inga naki salon laulayin dame zai zo." Na zuba mishi idanu a zuciya ta kuwa tunowa ta ke da kalaman da ya ke rubutawa na batsa da hannun sa yana turawa matan banza,ga waccan yarinyar da nake zargin su da ita.
Ya hura min ?wayar idanu tare da fa?in "Kamar kina min kallon tuhuma Baby." Nace Me zaka yi wanda zai sa in tuhume ka? Kai mijina ne mai gaskiya da ri?on amana,ga ibada kyauta da sadaka gidan ku ya yi fice, gashi ka tsare kanka daga sharholiyar zamani ta bin matan banza da yawancin mazaje ke yi,ko tunanin bayansu basa yi,. Ina matu?ar tausayin ahalin mazinata, domin sai uba ya ja a yi wa 'yarsa a banza ba tare da hakkinta ba .Ko miji ya ja wa matar sa ?a ya jawa uwarsa...Hannu ya sa ya rufe min baki tare da fa?in "Ki taya su addu'a Allah ya shirye su. Ni yaushe ma na samu lokacin matata har bare in tsaya neman wasu matan. Ina da kamar ki wace damuwa gare ni. Baby komai na ke so kina min yadda ki ke sakin jiki da ni a gurin kwanciya ban ta?a samun haka ba. Kina kore duk wata sha'awa tawa. A zuciya ta nace kaji ?arya. Ko a wannan daren na yi bincike a wayarsa, kuma sunyi al?awari da wata za su ha?u ranar Lahadi da ?arfe sha biyu.
....
A Cikin kwanaki kullum ina yin tunani aka yadda ya kamata in da?ile wannan haduwar ta sa da karuwar nan, kwata kwata bana son yasan nasan abinda ya ke aikatawa domin ?oye min ?in ma alfarma ce, in har namiji ya na aikata wani laifi ya ?oye miki alfarma ce kar ki sake ki binciko, sannan in har kin gano to karki nuna masa domin zai yi borin kunya ne ya nuna miki bai damu ba, sannan zaman lafiya ya ?are. Zuciya ta ce ta yi min wannan karatun don haka sai na ?ara