Showing 12001 words to 15000 words out of 55418 words
ajiyar zuciya tare da ha?iye wani ?ududu da ya tokare a zuciya ta. Nace Alhamdulillah ashe ka zo, Yayana warke ciwon da ke damuna a zuciya na matsin na ?ara yin ?asa da murya, nifa. lokacin bana cikin hayyacina ni dai kunnena ya ji lokacin da yake sanarwar zai min kayan ?aki, kuma in zaka harbe ni bazan iya fa?a maka kayan da ke jikinsa ba, na san dai akwai ba?in glashi a idonsa. Kuma ko shine ?aruna a ku?i ya yi ka?an bai isa ya raba zuciya ta da sonka ba. Shine ka ?i ?aga kirana tun kafin ranar sauka, shin ko me na yi maka? Yace "Abubuwa ne Baby baza ki gane ba, amma ba da wannan wayar na fita ba ranar sai da na dawo na ga kiran amma kiyi ha?uri. Ya kalli robar gefe na, ki tashi ki karya. Ban musa ba na matsa kusa da robar na bu?e, nace Jamila bani cokali. Ya kalli tuwon shinkafa da miyar ku?ewa ?anya. Ta mi?o ya amsa, nace to kaima kac,i ko baka cin tuwo? Yace "Ni na karya, ke dai ki ci." Na ci ka?an nace nasan baza ka iya cin abincin gidanmu bane. "Saboda me?" Ya jeho min tambaya. Nace to ka ci, in gani. Ya amshi cokalin sannan yace waya girka?" Nace ni mana. Ya sa cokali ya ci dan ?arami sannan ya ?ara. Naji da?i ya ce me kike son cin in aiko maki anjima? Nace babu, yace to zan miki aike zan koma tunda kin samu sau?i. Ya kira Jamila ya bata dubu ?aya yace ta siyo min Maltina. Na rakoshi har soro yace in koma kar in fito zai zo ya kawo min ku?in Party. Jamila ta dawo siyan Maltina tace ?waya biyu na siyo kisha ?aya ni kuma in iragewa su Jafar canjin a baiwa Umma inta tashi. Nace zan rage mata itama ta ?ansha saboda Ummar. Jamila tace ba gashi ya zo ba, amma ke kuka da ?unci kawai ki ka iya sai kiransa ya na ja miki aji. Nace Jamila ai na daina raina wayonki wannan shiri haka, kinga yadda jikinsa ke rawa har tuwon nan ya ci. To haka dai muka ci gaba da tattaunawa har Umma ta farka. Saura kwana biyar biki mutane sai tsegumi ake yi ba aga ina yin wani gyaran jiki ba. Harda muka yi maganar da Jamila tace ko mu yi wa Umma magana. Nace a a mu barta. Umman Amina dai ta kawomin wasu ji?e ji?e ina sha,da wani tsimi. Sai kuma wata kaza nan mara da?i akace in cinye. Saura kwana hu?u biki kuwa aka kira Abba daga Gandu wai yaje zai ?auki kayan da akayi masa al?awari. Da ya kawo kayan sai ma?ocin mu aka ro?a gidansa ya tashi ya yi sabo zai gyara ya zuba haya, aka zuba. Banje kallo ba, amma an ce harda dinning table kaya irin na masu ku?i abin ba a magana. Ranar ya aiko min ta katin ?aurin aure dana Dinner. Muna ta juya katin Dinner wai a ZEENA Event gurin da gwamnoni da manyan masu ku?in Kano suke shagali. Jamila tace "Ni fa na soma zargin Yaya nan kamar yana basaja." Nace ke ba wani basaja kinsan yana musu yaron shago, kuma suna mutunci tsaf zasu iya bashi. Jamila ta ce haka ne kuma. Muka samu Zuhra da Amina muka soma rabon kati. Labari ya zaga lungu da sa?o za a fita perty a bikin Baby kuma ZEENA Event center. Nan fa sai surutun wasu suce ?an karya ne, wasu suce ?ila gadin gurin ya ke har gida wa?anda ba su samu kati ba suke zuwa wai a basu saboda son ?wa??wafi. Ango bai zo ba sai ranar Alhamis. Ya zo bayan magariba wai yana sauri, yace gobe Juma'a in shirya ni da Jamila Yayarshi zata zo ta kai ni gurin wadda take musu lalle. Yace itace zata miki duk wani gyara, kuma sune suka shirya Party. Nace to yace in fa?i me nake bu?ata, nace ba komai dama ai ku?in perty ?in zai bada. Ya fito dubu goma yace duk da haka ga wannan kiyi ha?uri ni baza mu ha?u ba sai a gurin Dinner ranar asabar. Nace to za a zo a ?auke mu ne? Yace e za a kawo motoci ya yi wa abokansa magana insha Allahu. Na ce to na gode. Yace in shiga gida. Na shiga soro na tsaya ya wuce, na dawo na le?ashi ya tafi da sauri, farin ciki ya mamaye zuciya ta. Sai naga su maman Fati suna le?ensa suma dama Fatin ta wuce muna tsaye. Nace kai mutane akwai su da son saka kai cikin damuwar wani.
Da na shiga na sanar da Ummar na bata ku?in, tace to ai sai kuje da Jamila ko? Na ce shima haka ya ce,nace to kuma wa zai taya ki aiki? Tace ba komai ai 'yan Kurna tun yau zasu zo kin ha?a kayan naki kin cire wanda zaki baiwa Jamilan da su Amina? Nace e nawa ai suna cikin bako Jamila ta kai kusa da akwatuna. Tace to in kunje dai ku kama kanku kar a sake ayi wata rashin kunya." ?arfe sha ?aya ya kira ni yace gashi nan ta turo direba yanzu zai yi sallama da ni.
Muna aje waya ?an sako na shigowa muka yi sallama da umma muka fita.
?????????
*HAMSHA?IYAR UWA????*
*NA*
*HALIMA ABDULLAHI K/ MASHI*
_PAID BOOK_
_Ku?in karatu ?600_
_Account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank a turo shaidar biya ta wannan number 08140004302 ko katin Mtn_
_Phone 08140004302_
*DOKA*
_Ban amince wani ya ?ora littafin nan a wani Social media ba,ko a maida mini shi Audio ba tare da iznina ba yin haka daidai yake da fuskantar fushin hukuma. A kiyaye_
*Masu son a Tallata masu hajarsu suyi magana ta wannan number 09068032427*
*Page 16*
Rantsastsiyar mota ce mai numfashi muka shiga. Na dai san mun wuce gidan gwamna daga nan ban kuma gane ko ina muke ba, sai wani damfareren gida na ga mun shige. Muka bi bayansu zuwa wani falon. yace mu zauna tana zuwa ya fita.
Wata mai kama da Aliyu ta fito, cikin fara'a ta yi mana sannu da zuwa muka sakko muka dur?usa muka gaisheta.
Tace "Ku zauna kan kujera ai ke Antyna ce ta nuna Jamila. Jamila tace gata nan fa. Ta?an zaro ido cikin mamaki tace na zata kece. Jamila tace ni ?anwarta ce. Na sunkuyar da kai ina mamaki yadda kowa ke ?auka Jamila ce Yaya ta ko dan ta fini cika ido da 'yar ?iba. Wata yarinya ta kawo mana kayan marmari da Lemon roba. Ni dai ruwan na sha. Ta kira ni cikin wani ?aki tace kiyi ha?uri bana raina ki bane ?auki waccan rigar ki saka ki yafa mayafinta ga shi can. Sai ki fito da takalmin can ki saka in zamu fita. Cikin mamaki nace to. Ta fita na saka doguwar ba?ar riga tana ta ?amshi, na yafa mayafin na ri?o takalman. Jamila ta zaro ido tana fa?in "Kinga yadda ki ka yi kyau kuwa?" Ta fito da makulin mota tace ku muje. A gaba tace na zauna muna tafe tana min 'yan tambayoyi har mukaje wani gida. ?amshi tun daga waje. Matar ta amshe mu sai naga ta y i mamaki da tace nice amaryar. Tace wai Maman Iman me yasa baku bata maganin gyara na murmurewar jiki ba? Tace "Nima ban ganta ba sai yau, kuma mun zo a makare, nan zan tafi in barta, ki yi mata komai duk abinda ya kama har ?unshi dan Allah ki fito mana da ita saboda surutun mutane.
Matar tace baki da matsala sai dai kuma su kwana. Tace "To ba damuwa ko Antyna?" Ta kalle ni. Nace bari dai mu kira Ummanki sai ki fa?a mata. Tace to ku kira ta ?in. Suka yi magana da Umma sannan ta bani wayar Umma tace a kula da kai sosai in kunga wani abu ba daidai ba ko baku gane ba ku min magana a waya." Nace "To" Na kalli Maman Iman na ce ?anwata za ayi mata ?unshinne? Tace "A yi mata mana itama duk abinda take so, amma karfa ta kai amaryarmu kyau. Cikin tsokana ta yi maganar mu kasa dariya.
Nasha azaba a gyaran jiki amma dana kalli fuskata sai da nace nice kuwa. Aka zuba min ?unshi ?amshi kuwa sai tashi yake duk inda na motsa. Jamila ma an mata ?unshi, sai wasu abubuwa da take bani da madara ina sha. Washe gari ta kuma min hayar jiki. Sha biyu sai ga Maman Iman ta rungume ni tana fa?in amarya ta fito, yanzu sai tafiya gurin wankin kai. Tasha mamaki da ta ga gashin kai na da aka gyara har gadon baya.
Tace mu Fulani ne nace a a, amma an ce asalin Kakarmu ta gurin Uba Buzaye ne.
Daga can sai shagon kwalliya acan mukayi salla ta kawo mana abinci muka ci, sannan aka soma kwalliya, ban san cewa yamma ta yi ba, sai da Umma ta kira ni wai ina muke ga mutane sun soma cika gida 'yan zuwa party. Na bawa Maman Iman wayar nace kiji wai masu zuwa gun party sun zo sun cika gidanmu. Maman Iman tace bari in fa?awa Ango ya aiko da mota ita amarya daga nan gurin kwalliya zamu wuce. Umma tace shike nan. Ta kira Shamaki ina jin muryar shi yana cewa '"yar uwa wai ina yarinyar nan ne ko muryar ta kin ce bazan ji ba a tausaya min.
Tace "Ba za kaji ba sai kun ha?u anjima, ka aika motoci gidan su a kai mutane gurin party yanzu.
Yace "To" suka yi sallama. Ta dube tace "Ni na hana angon ki ya kira ki."
Azuciyata nace na gode Allah da yasa nima ban kira shi ba. Na sunkuyar da kai ina murmushi. Tace nafi son lokacin da zai ganki sai yaga kin canza gaba ?aya har muryarki ko bata baki wani ha?i ba ne? Jamila Itama aka mata kwalliya ta kawo mana kaya Jamila ma wani leshin Maman Iman ta bata tace kici albarkacin amarya ko za su yi miki kayan cikin nata ne gashi kin fita ?iba. Azuciyata nace ko da yaushe tasa akayi min ?inkin ko gwada ni tela baiyi ba. Kamar ta san na sa?a hakan a zuciya tace da kayan ki da kika cire akayi gwaji.
Nace Allah ya saka da alkhairi. Jamila ta saka cif.
Suka shirya ni cikin wata doguwar riga bayanta yana jan ?asa gashi ta ?ame ni da suka gama komai aka kaini gaban madubi. Maman Iman ta kaini ta ce "Kalle ki." Cikin mamaki nace ni ce haka! Suka sa dariya. Nace ko Umma uwar da ta haifeni baza ta gane ni ba. Suka yi ta ?aukana a hoto. Nan dai muka nufi mota don ana ta matsawa da kira. Ina bayan mota Jamila a gaba Maman Iman ita ke tu?i. A harabar gurin motoci na alfarma iya .ganin mutum ta ce da Jamila ta fita ta duba mutanan unguwarmu ko sun samu shiga. In taga wa?an da ba su da pass ta yi mata magana zata sa abarsu su shiga.
Ta dube ni "Amarya ki zauna bari naje mu fara shirya shigarku. Na kuma tsakiyar kujerun bayan tafiyar su ina sake kallon kaina a madubi gaskiya ni kyakkyawar ce a she ko dai don an canza min kamanni ne. Naji a ?wan?wasa gilashi Jamila ce ta bu?e tace kinga kuwa 'yan unguwa maza da mata a wajen gate wasu. ma ni dai ina ganinsu ko magana bata ta?a ha?a mu da su ba. Nace kije ki fa?awa Anty Maman Iman in sun shigo arziki ne.
Tana tafiya Yaya na zuwa ya ci wata shadda kalar sararin samaniya, ya yi mugun kyau a zuciya ta nace ashe dai akwai mijin Nobel da gaske. Ya shigo ya zauna kallona ya ke ya kasa magana. Nayi ?an murmushi, Yaya ka yi kyau sosai. Yace "Baby baki lura na kasa magana ba, gaskiya ne ina son gayu sosai zaki na gyara min jikin ki haka ko?" Na ?aga kai alamun e. Ya ciro waya ?an matso muyi hoto. Gabana ya fadi Allah ya sa ba ta?ani zai yi ba. Na ayyana a zuciyata. Hularsa da ?ankwalina ne kawai suka ha?u ina jin sautin numfashin sa. Na lumshe ido domin wani yanayi na samu kai na. Cikin murya ?asa ?asa yace "Bu?e ido Amaryata ki kalli camara. Na kalleni a cikin wayar munyi mugun kyau. ?wankwasa motar ya tsaida ?aukar hotunan da ya ke yi. Abokansa ne da su Anty. Maman Iman tace "Wai waya ce kazo ne? " Yace Na ga shigowar ki fa, nasan amaryata ta na wurin ki. Nan dai muka fito aka nufi shiga Hall. Yaransu ne aka jera a gaba sun sha wata farar riga bulawus su kuma mazan sun sha shadda mai kalar ?asa. Sai su Antys da Jamila da Zuhra da Amina suma dai an sako su saboda Maman Iman tace ina ?awaye na tace gasu nan. Leshi dai suka sa daidai ?arfinsu amma fa kowacce da kalar nata. Sai abokan Yaya ni yau nata?a ganinsu.
Hawaye naji