Showing 33001 words to 36000 words out of 55418 words
kamar ango." Cikin mamakin irin zuba zance da Yaya ke yi nace naji da?i sosai da na saka a farin ciki, insha Allahu bazan ta?a canzawa ba, yin hakan fa dai-dai ya ke da juyawa aljanna baya. Yace me ki ke yi yanzu? Nace wanka zanyi inyi salla sai na shirya fita filin taron. Sai kawai naji subba ta ratsa kunne na ta cikin waya,ta bi sassan jikina wanda haka ya tilasta min sulalewa na zauna a kan gadon tare da kumshe ido. Na ?ago waya na kalla baya sautin ya katse layin .
Cikin sanyin jiki na shiga wanka. Bayan nayi salla yau ma dai kwalliya ce aka ca?a min na ci leshi ina ta ?amshi su Jamila sunzo da su Umman Amina har da ma?otanmu da yawa abu mamaki,dangin Abba ma sunzo. Wani ?aton fili ne a gidan an shirya shi kamar tantin larabawa. An zuba kujeru a gaban kujerun na alfarma Hajiya tare da wasu manyan Hajiyoyi ?awayenta suna zaune a kai kusan su goma dukkan su kowa tana ji da kanta.
Sai layi na biyu 'yayansu ne. Sannan sauran mutane da abokan arzi?i a sauran kujerun wanda teburi ke tsakiya. Kamar yadda Maman Umar ta shigo ?akina muna zaune, tace matar waliyina Umma su Zuhra ita ce ta ri?o ni har gaban su Hajiya. Haka aka yi, ina dur?usa na gaishe su, suka amsa cinkin isa da ?asaita. Sannan Na du?usa na gaida yayun mijina, aka kaini wata kujera da aka tanadar min. Wata malam ta tashi ta fara gabatar da nasiha game da zaman aure, biyayya ga miji, bin uwar miji, bin dangin miji tsafta iya girki da sauran su. Sai dai banji inda ta fa?i yadda ya kamata uwar miji ta mutunta matar ?anta ba,dangin miji su girmama matar ?an uwansu ba,haka banji ta yi magana game da hakkin mace akan miji ba,amma tayi magana sosai akan ha??in miji akan matarsa. A zuciya ta nace ko ina dai yanzu mutane suna kare abincin su ne suna yin abinda suka san shine fitar su.
Bayan an gama MC ta sanar cewa yanzu lokacin cin abinci ne wanda amarya ta dafa kuma zata fara gabatarwa a gaban Hajiya, amma kafin haka sai ta ?an ?ana dukkan abincin da ta dafa, sannan za a kai ga Hajiya da Aminanta. Yin hakan ba wai ana zargi ba ne al'adace.
Gabana ya fa?i na tashi na nufi gurin da aka jere kayan abincin kowa ya kallona, na zaci su Juma zasu zo su taimaka min amma sai na ga kawai kowa kallona yake yi. Na ?auki tire na jera plate hu?u suka cika shi na zuba shinkafa nasa tuwo a ?aya na saka dambu a ?aya sai kuma na sa Alala a ?aya, na kuma jera hu?u ?aya mai zurfi sa matsami na tsamo ?anwake na zuba a mai zurfin. Sai na zuba kaji da kifi da naman rago. Colsow kuwa shima madubi daban sai na zuma a karamin plate na sa cokali na ?iba na sa a baki ina ci, sai naji an kwashi tafi. Duk a ru?e nake, na ?auki tiren na soma kaiwa ina jerewa a teburin gaban su Hajiya. Sai da na cika teburin komai na zuba musu, lemuka dai dama na ga anjere su da ruwa a kan kowane tebur.
Na koma na ci gaba da zubawa, anan ne Juma suka zo suna mi?awa teburin su Maman Umar zuwa na sauran jama'a. 'Yan unguwarmu da yake a ko ina sai an nuna halin, nan suka fara zuwa suna cewa Baby a bamu. Juma ce ta kore su, ta ce kowa ya koma mazaunin shi zai samu. Bayan an gama da manya sai Mc Ta sanar cewa Amarya ta koma nata mazaunin yanzu masu rabon za su zo su raba. Wata mata tare da 'yan mata suka shigo suka soma rabon abincin ni kam Idanuna da hankalina suna kan teburin su Hajiya har zuwa lokacin da mutane suka fara cin abinci ta irin su ba'a fara ba, sannan yanayin kallon da wasu aminan ta suke min ya sa jikina yin sanyi, a zuciya ta kuwa addu'a nake Allah ya fiddani.
Kusan kusan mutum uku suka fara cin abincin sannan lura d Hajiya i ta fara ci, sai dai wani abin ban iya gane ko ya ta ji abincin yadda take komai cikin ?asaita.
Masu hotuna da bidiyo ana ta ?auka gaskiya ni tsarin ya yi min, wata zuciyar tace tunda kin tsallake Hajiya ta ci kyace abin ya birge ki mana. Haka dai aka ci aka sha sannan aka gama. Aka kai wa Hajiya abin magana zata yi jawabin godiya amma kafin haka sai ?awarta Hajiya Zulaiha ta amsa ta isar da sa?on Hajiya game da abincin da amarya ta ciyar da su, tace "Zan yi ?an bayani ka?an kafin Hajiya ta yi godiya, gaskiya amarya girki ba laifi amma a ?ara gyara hannu sosai, ta ?an ta?a baki, ya yi da?i sai dai ?an gyara guda biyu dazan miki, na farko ?anwake mai da yaji ne sai kika bamu da miya. Na biyu kin mana ?an zubi a dambu sai ki ?ara sakin hannu ka?an saboda rowa bata da wani amfani kuma bata cikin sunnar gidan nan. Na sunkuyar da kai, ina mamaki amma duk da haka ni ce da godiya tunda ?orafin ya tsaya a haka,,Hajiya ta ci abinci Allah ya soni ni.
Hajiya ta amshi abin magana tayi godiya ga kowa tare da fatan duk za su koma gidajen su lafiya.Sannan ta sa albarka tare min fatan zama jarumtar mace musamman gurin yi wa miji biyayya. Aka abin maganar wai ince wani abu bani wai nima in yi godiya. Gabana yana fa?uwa na amsa. Nace Mun gode Allah ya maida kowa gida lafiya, kuma insha Allahu zan yi amfani duk shawarwarin da aka bani zan kiyaye. Haka taro ya tashi kowa na san Barka. Ana tashi aka kira la'asar. Hajiya ta kirani inyi sallama da ba?inta. A lokaci ne wannan mai cewa ina da rowar same ta tana cewa "Hajiya Zeena duk matan da ke Kano amma Shamaki ya rasa wadda zai ?auka sai wannan cokokuwar ko cikin 'ya 'yanmu ya kasa zuwa ya duba. Na kalli Hajiya lokacin da takecewa
"Bar ?an yau da abinda ya ke so Hajiya Zaliha. Wani mugun so ya ke yiwa yarinyar nan ba domin na samu tabbacin ba asiri suka yi masa ba da a haka zan kalli abin. Gaggawa fa ya yi aka je aka nemo masa auren ta. Ni kuma kinsan matsala ta, ina son ?ana da yawa kuma ya rayu akan samun duk abinda ya ke so, in ba ?ana abinda ya ke so matsawar yin hakan ba sa?on Allah bane." Nace su sauka gida lafiya na juya raina ba da?i, na soma jin takaicin kushe min halitta da ake yi. Gefena tan?am da 'yan uwa da 'yan unguwa sai kallo na suke suna min murna. Na zauna bakin gado Jamila ta zo ta ce "Abinci ya yi da?i Yaya Baby kuma ke ki ka dafa?" Na ce e mana. Wayata ta soma ringin ta mi?o min. Na amsa Mijina ne Hajiya ta hana ni fa?a masa Yaya To bansan wane suna zan saka masa ba. Na ?aga, yace " Yaya Baby gaske ne ke kika dafa abincin nan?" Cikin shagwa?a na ce wai don Allah nice Yaya? Yace "Ina son yadda su Jamila suke fa?a ne." Abicin bai yi da?i bane ko? Na tambaye shi. Yace "Inji wa, ai in fa?a miki abincin Hajiya ne ka?ai ya fi naki da?i." Na yi murmushi a zuciya ta nace ai ita Hajiya komai nata ya fi na kowa. "Sannu soyayyata ,kin yi ?o?ari sosai.
.....
Yace "Yawwa Baby amma Hajiya ta ci abincin kuwa?" Nace ta ci mana har ?awayenta duk sunci. Ya ce to Alhamdulillah! Allah ya yi miki albarka me ki ke so in zo miki da shi?" Na yi ?asa da murya kai kawai nake son ka dawo lafiya bana son komai.
Sai kurum na ji sumba a kunne na tare da fa?in ina sonki da yawa zan fa?a miki wani abu amma don Allah kar hakan ya sa ki canza min." Nace ka fa?a min Allah bazan ta?a canzawa ba. Yace "Baby idan yadda nake ji a game da ke shine soyayya, to a baya ba soyayya na yi ba, duk bugun numfashi sai na tuno ki,na samu kaina da hirar ki da kowa harma da wa?anda ba su kamata inyi hirar da su ba. Don Allah Baby kina jin makamancin abinda nake ji?"
Na sauke ajiyar zuciya, zanfi son in fa?a maka idona yana kallon na ka, in ka dawo wannan hirar za muyi. Ya kuma sumbatar wayar ba tare da ya kuma cewa komai ba ya katse wayar.
Na zurawa wayar ido ina farin ciki.
Zuwa biyar duk aka watse sai su Jamila suka ?ara gyara min ko ina fes ita da Amina na ?auki ku?in da abokansa suka bani na ba Jamila nace ta kaiwa Umma duka dubu Ashirin ne. Tace "Ki aje goma a hannun ki a kai mata goma saboda ko za kiyi ba?i zaki iya ba su ku?in mota." Nace to haka ne. Na basu turare da janbaki daga cikin kayan lefena ita da Amina, su Jafar ma. turare na basu suka min sallama suka tafi.
Na yi wanka nayi sallar magariba na saka wani farin leshi mai ratsin gwal na sha turaruka ina jiran mijina. Sai dai har nayi sallar Isha'i aka kawo min abincin dare amma babu labarin angona na ?an dai ci farfesun kajin da farar shinkafa ka?an domin naji yunwa, da rana ban iya cin abinci ba. Na sake gyara fuskata na zuba ?aurin ?an kwali na zauna ina kallon TV, na aje turare a gefe na da zummar in ya ?wan?wasa ?ofa infeshe jikina da shi kafin in bu?e.
Can cikin bacci naji bugun ?ofa Lokacin ina mafarki ina gida gamu tare da su Umma. Na tashi firgigit ?ankwalina ya fa?i na ganni a ?aki na naje na bu?e ?ofa shine tsaye ga jakarsa a rataye. Na zuga hamma sannan nace masa sai yanzu ka dawo sannu da zuwa, Na mi?a hannu zan amshi jakar hannunsa Yace a a barta zomuje ?akina." Nace bari in yi shirin kwanciya. Yace 'a 'a muje haka." Na juya na ?akko ?ankwalina ya kulle ?ofar da makulli. Da ?yar na ke tafiya na gaji li?is saboda aikin da muka sha ?azu kuma ni ina da wata ?abi'a in na fara bacci aka tashe ni raina ?aci ya ke ga ciwon kai. A ?akin nashi na kalli agogon bango ?aya da minti biyu. Na zauna bakin gado ya shiga ban?aki, a zuciya ta nace haka zai ta zama a gurin Hajiya Kullum har irin wannan lokacin? Ta? da sake na furta a zuciyata. Na kwanta a kan gadon inajin futowarsa ya yi wanka ya gama feshe feshen turaren sa, na yi laf ni a dole bacci ya kwashe ni.Ya zo ya shafa gefen kumatuna ya na fa?in "Baby." Na sake jan bargo . Ya min magana a kunne wai Baby ki tashi ki saka kayan bacci. Sai na yi kamar zan tashi sai in kuma ?ingirewa, ina jin sa yace Baby kinsha gajiyar aiki ne bari dai in ha?ura nima yau. Ya jani jikinsa,. hardai , baccin gaske ya ?auke ni.
Yauma kamar jiya zai tafi masallaci ya tashe ni, haka nan shiru bai shigo ba bisa dukkan alamu yauma sai zai tafi kasuwa, to kenan bani da wani lokaci da zamu zauna da mijina muyi hira wannan babban ?alubale ne a tare da ni ya zama dole in nemo wa kaina mafita, sannan ya kamata in kula sosai gurin nemo mafita kar in nemo wadda zata fiddani daga gida. Yau ya kamata in fara bugar cikin Juma domin insan ina nasa gaba a gidan.
Na gyara ko ina a sashen sa sannan na dawo na gyara nawa, na karya na yi wanka sannan naje gaida Hajiya. tace "Ya ba?unta?" Nace Hajiya ai na zama 'yar gida. Ta "'A 'a har yanzu ke ba?uwa ce tunda baki gano lokacin da ya kamata ki gaisa da mutanen gida ba sai rana ta hudo ki ke iya fitowa Ina fatan dai ba sai yanzu shima Ubangiji aka gaida shi ba?" Na matsa kusa da ita na sunkuyar da kai ina ?an murmushi, ba yanzun bane, tunda zai fita ya tashe ni, nan ?inne dai Allah bai sa na zo akan lokaci ba, ina neman afuwa akan hakan. Ta ?an ta?a baki tace "Ko kusa ba kiyi laifi ba gidan aurenki ne nan dole ki huta in sautin ki ka za?a." Na sunkuyar da kai Nace, akwai abinda za ayi muku ne? Tace a a babu komai,.kije ki sallami mijinki mana." Na sunkuyar da kai ina zaton yana shirya wa ne domin tafiya kasuwa. Tace "In ya gama ai dole zaku yi sallama ko?'" Na mi?e tare da fa?in To Hajiya.
Ina sane na yi musu haka sai da ya shiga na zo gaisheta dole nima in nemi mafita ta akan wannan lamarin, amma ina da bu?atar sanin wasu abubuwa.
Zan tashi sai ga su Meema cikin shirin makaranta. Suka dur?usa har 'yar Anisa suka gaida Hajiya. Nace kun gama shirya wa. Suka kalle ni sai suka ce Hajiya ina Dady?.Tace "Yana ciki kuje da sauri ku gaida shi karfa ku jima ku dawo yanzu ku tafi."
Azima ta shigo itama cikin kayan makaranta ta gaida Hajiya sannan ta nufi ciki kenan zata gaida mijina. Na mi?e tare da fa?in to bari inje. Hajiya ta ce Allah ya yi albarka. Ina shiga falonsa na samu yaran suna ta wasa Azima ta ?wan?wasa ?ofar ?akinsa. Na dube ta sai naji wani kishin ta ya kamani, nace Ke ?an jira mana ta tsaya. Nace zauna bari ya fito. Tace "Za muyi latti." Yadda ta yi maganar ya nuna itama akwai alamun kishin. Nace bari ya fito yanzu.
Ya gama shiri tsaf cikin farar shadda, ya ce "Yau ba a zo an bani kaya ba." Nace naje gaida Hajiya ne. Ya janyo ni jikin sa, "Jiya kinyi bacci kin barni nasan gajiya ce." Nace na gaji sosai, kuma inna yi bacci aka tashe ni dama ciwon kai nake yi ,jiya Allah ya taimake ni kaina baiyi ciwo ba da ka tashe ni, ko da yake na koma baccin da wuri. Yace "To saboda me?" Nace ban sani ba, amma ?ila domin bana yin baccin rana ne. Yace "To kinci bashin na jiya yau za'a maida min. Na zaro ido bashin me? yace "Zan fa?a miki inna dawo," Nace yara fa na jiranka a falo. Da sauri ya fito yana fa?in "Za su lattti." Azima ta gaida shi ya amsa tare da tambayar ya yaga fuskarta haka ba walwala. Tace ba komai. Ya ?auki yaran duk ya sunbace su ya musu addu'a suka rugo gurina "Momy ina kwana?" Na amsa na yi musu addu'a nima. Azima ta gaishe ni na amsa sannan suka fita. Ya kalle ni "Momy yara." Nace na am Dadyn yara. Muka koma ciki muna dariya. Ya zauna bakin gado yana min wani kallo, "Zan tafi kasuwa ina ?ishirwa." Na yi kamar ban gane ba sai nace, Bari a ?ebo maka ruwa mana. Ya ?auki jakarshi na amsa. Yana fa?in "Ba wannan ba, nace To wanne? Ya lakuci kumatuna "Zaki sanshi inna dawo." Muka fito har ?ofar falon Hajiya na mi?a masa ya ?i amsa ya shige falon Hajiya ya rusuna ya cire hula ta dafa kanshi tana yi masa addu'a. Ya mi?e na saci kallon Hajiya cikin ?ari ?ari na ce mishi ga jakar. Ita ma ni take kallo, yace "Kin fasa rakani motar ne?"
Na kalli Hajiya da sauri, ta ?aga kai alamun inje,sai na bishi. A falon kusa da waje ya tsaya yace "Da bazaki rako ni ba tsoron me ki ke ji?" Nace inajin nauyin Hajiya ne. Yace Hajiya zataji da?i taga kina kula da ni yana cikin abinda take dubawa a cikin jarabawarta." Na sunkuyar da kai. Dama kaima kasan Hajiya tana jarabawa? Ya sunkuya ya sunbaci le?unana, yace "Ki koma daga nan bana son masu aiki su lalle ki, ki