Showing 9001 words to 12000 words out of 55418 words

Chapter 4 - HAMSHAƘIYAR-UWA 2

04 Jul 2024

6004

na mi?awa Jamila wayar. Tace "Wai ke duk wannan alkhairi da ya same ki a yau amma har yanzu kina ?unci." Nace dole in yi ?unci baizo ba fa. Jamila tace "Ya zo mana." Cikin sauri nace kun ha?a ido? Tace "A'a amma ga kyauta ya bayar?" Nace zai iya aikowa. Nima zan fara gwada mishi nawa rashin kulawar tunda haka ya za?a. Jamila tace "Kamar zata iya." Nace zaki gani kuwa.
Labari fa ya watsu a unguwa sai murna ake zuwa taya Ummanmu. Da dare ina jin Abba yana cewa Umma kinga dai abin Allah ko? Tace "Wallahi Ubangiji ya share mana hawaye, wannan lamari Allah muna godiya a gare ka." Muka shiga ?akinmu. Jamila tace ki bu?e mana kyautar ango mugani mana. Na tura mata kwalin ke ki bu?e, domin ni ita kanta kyautar haushi take bani. Wani kyakkyawan siririn agogo ne mai kyau ruwan gwal, sai wani zobe kamar na azurfa yana da jan dutse shi mai kyau. Ga ?aramin ?ur'ani mai girma izu sittin, ga kuma wani kyakkyawan carbi mai ruwan gwal. Take na ru?e ina ?aga kayan cikin farin ciki. Jamila ta sa dariya tare da fa?in "Kin daina jin haushin kenan?" Nace ai ba haka bane, ?ur'ani mai girma fa ya bani ya bazanyi murna ba. Haka dai har muka kwanta ban samu wani kira ko sa?o daga mijin da zan aura ba.

Hajiya ta fito daga cikin ?akinta ?arfe uku na rana ta?an matse bacci kafin la'asar. Idanunta suka sauka akan yaranta sun baje a falonta suna ta hira, ga alamu sun gama cin abinci domin Juma tana ta gyaran gurin. Duk suka mi?e suna yi mata sannu da fitowa. Ta amsa musu bayan ta zauna, tace "Ashe kun jima kuna jirana, yau wani bacci na ji tun da nayi azahar na shiga ciki. Maman Nana tace Ai kuna shiga ciki na iso, Juma ke fa?a min sai kuma ga su suma. Hajiya ta ka?a kai cikin isa Tace "Marabanku da zuwa suka amsa. Ta kalli wasu lesuka dake zube kan kujera, tace muga kayan can na waye?" Maman Iman tace nawa ne siya na yi zan baiwa Ango shine aka ce tuni an kai lefen. Shine zan ?inke kayana. Hajiya ta ciro daga leda ta ta?a jikin leshin. "Ina kika samu wannan leshin kayan London ne ko har can ki kayi Oder?" Maman Iman Tace 'a'a akwai DIJANGALA ENTERPRISE sune suke shigo da su, kayan su suna da kyau kuma Hajiya ga ta da farashi Hajiya tace "Mace ce mai kamfanin?" Hajiya ta tambaya tana ?ara ta?a jikin leshin. Maman Umar tace E, mace ce. Hajiya ta gya?a kai tare da fa?in Allah ya dafa mata. Ina son inga mata suna dagewa da kasuwanci, ki duba min lafaya irin wa?anda kika san ina so kamar kala goma sai ki turomin. Maman Umar tace bamu da su a kasuwa ne?" Hajiya tace "Karfafa mata gwiwa zanyi ga kayan suna da kyau." Maman Nana tace Ni dai sar?o?in zaki turomin in duba.
Suka gama tattaunawa tare da yaba kayan DIJANGALA ENTERPRISE. Hajiya tace "Lafiya na ganku kamar kun ha?a baki ku duka?" Maman Umar Wadda tun fitowar Hajiya ta ke sa?a da warwar kan tunanin ta inda zata fara magana saboda Shatima ya kirata ya sanar da ita komai. Tace Hajiya mun zone a tattauna akan bikin nan. Hajiya ta bita da kallo wanda sai da ta sunkuyar da kai haka ya sa kowacce ta shiga taitayin ta. Duk sukayi tsit saboda irin kallon da Hajiyan ta yi wa babbar su. Hajiya ta soma magana cikin isa. "Sanin kanku ne bana son a yimin ?arya ko da kuwa yin haka shine zai ceci rayuwata ko? In ba zaku fa?a min abinda ya kawo ku ba kuna iya tashi ku tafi gidajen mazajenku. Na san komai game da abinda kuka tattauna, haka zalika nasan Shamaki ya sanar da ku cewa na sani. To menene abin wani ?oye ?oye, bakwamin adalci fa, ban yi muku tarbiyya akan rashin gaskiya ba fa."

Duk suka dur?usa a gaban ta suna neman afwarta. Tace "In har maganganun da yazo min da su na al'adar da nake gabatarwa ce to in baku son ranku ya ?aci ku rufe zancan, sannan ku ?ace min a nan, haka nake ra'ayin tsarin gidana ku bari in na mutu sai ku canza ku yi duk irin yadda ku ke bu?ata.
?????????
*HAMSHA?IYAR UWA????*


*NA*


*HALIMA ABDULLAHI K/ MASHI*


_PAID BOOK_
_Ku?in karatu ?600_
_Account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank a turo shaidar biya ta wannan number 08140004302 ko katin Mtn_
_Phone 08140004302_

*DOKA*
_Ban amince wani ya ?ora littafin nan a wani Social media ba,ko a maida mini shi Audio ba tare da iznina ba yin haka daidai yake da fuskantar fushin hukuma. A kiyaye_

*Masu son a Tallata masu hajarsu suyi magana ta wannan number 09068032427*

*Page 15*

Su ka yi ta ba Hajiya ha?uri,
?arshe dai ta ha?ura amma fa ba"a tado da zance ba. Sai dai suka ?ige da tunanin yadda za a gudanar da taron bikin. A'isha ta ce gaskiya ayi Dinner su shirya koma i iyaka su ?akko amarya kawai, Maman Iman tace haka za'ayi dan ya ?oye mata ai kuma ranar wanka ba sauran wani ?oyo cibiya tunda nan gidan za'a kawo ta zai ci gaba da ?oye mata ne? Maman Umar tace kwarai kuwa domin duk abinda ya ke son ya samu ko ya sani nasan dai zuwa yanzu ya sani. Haka dai suka kira manajan ZEENA Event center suka sanar da shi suna da Dinner ranar asabar in sun kar?i ku?in wasu to su mayar masu.

Suna gama shirya komai Hajiya tana jin su. Suka kira Shamaki suka fa?a masa yace "Duk yadda kuka ce haka za ayi, amma da kun bari sai an kawo ta ?akin ta sai a yi Dinner ?in.
Maman Umar tace a a ayi Dinner ranar Asabar ,Lahadi a ?aura aure, Monday taron Hajiya. Yace shike nan sai ku buga mata katin da zata baiwa ?awayenta da na shiga gurin Dinner ?in." Ba matsala wannan ta katse wayar bayan ta fa?a masa hakan. Hajiya tace sai ku ?inka wa amaryar kayan da zata saka a shagalin." Maman Iman tace kubar komai na shirya amarya a hannuna. Suka ce mun bar miki dama kece 'yar gayu. Ta ?aga waya ta kira DIJANGALA ENTERPRISE ta fa?a mata cewa zata turo mata hotuna wasu lessis cikin 'yan Swizaland ?innan ta turo mata su zata saka kudin yanzu.
To haka dai suka yini har kusan magriba sanan suka watse.

Na tashi da zazza?i amma haka na ci gaba da aikin gida domin nasan ciwon na rashi ji daga masoyina ne. Dayake anyl hutun boko hakan islamiyya an bada hutu tunda aka yi saukarmu, dan haka Jamila ma suna gida. Ta same ni kwance ga dumamen tuwao na da kunu na kari a gabana. Tace "Wai don Allah ke haka kike son a kai ki gidan mijin?" Nace Jamila ina ganin Yaya ba wani sona da yake yi, hawaye suka soma zubo min. Ki duba fa Jamila ba zuwa ba kira ko sa?o na kira ya ?i ?agawa. Jamila cikin sanyin jiki tace "Nima dai inata yin waswasi amma kawo wayar ki mu gwada wata dabara." Umma ta le?o tace wai jikin ne kin kuwa sha maganin? Nace Nasha tace harda gajiya ,bari inje gurin Umman Amina inji batun zannuwan gado da labulaye da muka yi magana. Muka ce to. Jamila ta rubuta sa?o kamar haka.. Yaya Aliyu barka da War haka, nice Jamila ?anwar Baby, bada sanin ta na ?auki wayar ,na turo sa?on nan ba. Baby bata da lafiya tun cikin dare, ta suma ta farfa?o amma jikin da sau?i yanzu, nace ta sanar da k¨¤i tace abarka ka fa?a mata. Kana cikin uzrori, amma ta bar sa?on cewa in ajalinta ne ya zo dan Allah ka jagoranci gawarta zuwa kabarinta ,kuma ka yi mata addu'a. Na saki baki lokacin da Jamila ta ke karanta sa?on. Nace ke ina kika samo wannan iya tsara zancen? Tace "Haba Yaya Baby kina mace baki san yadda za ki dagula lissafin namiji ba, in ya dagula miki naki,? Ni nan da kike gani na in har na fara soyayya za a sha fama." Nace duk yadda kike kallon abin ba haka bane. Amma mu jira lokacin sai mugani yanzu dai tura masa wannan sa?on muga ya abin zai zama. Minti kamar biyu da tura sa?o har na soma fargabar ko ya gani ya share, sai ga kira, zan ?aga Jamila ta amshe wayar tare da fa?in dakata tukunna handsfree. Ta yi sallama,, yace "Baby" Tace Jamila ce Yaya Baby ta samu bacci. Yace "wai me ya faru ne Jamila?" Tace To ni dai tun juya bangane mata ba, ta damu wai baka zo gurin sauka ba, kuma baka ?aga mata waya, wannan dai shine mafarin ciwo har tana suma, mukam har mun sare amma yanzu da sau?i, sai dai fa ba cin abinci ga dumamen safe ya nan har kokon bata ci ba. "Innalillahi wa'inna ilaihira'un! To an kaita Asibiti ne?" 'A 'a ko magani ta?i sha sai wasiyya take bari. Yace ina zuwa ya kashe. Muka sa dariya, Jamila ta ce "Yanzu zai zo. Nace in su Umma sukaji fa? Ta ce ke zaki a?a musu? Barshi ya zo." Umma tana ?aki ta kwanta. Muka ci gaba da tattaunawa kamar minti ashirin da gama yawa sai ga kira ya kuma shigowa. "Waye? Na tambayi Jamila da sauri ta nuni min fukar wayar kafin ta ?aga. Tace Yaya. Yace "Kizo gani a waje tace to. Ta kashe wayar. Na mi?e zaraf tace ina zakije? Kwanta kawai ki jira ni. Ta fita wai sai naji kishi Jamila zata gurin masoyina, amma nasani ba wani abu bane. Sai dai duk da haka na ji tsoro na la?e ina jiyo muryata tana maimaita masa. Yace ya zo ne muje asibiti, tace ai da sau?i kuma Umma na bacci Abba baya nan kaga ai badama aje amma ka shigo kaga jikin nata. Da gudu na juya na kwanta kan 'yar tsummar katifar mu na rufa.
Yau ne karo na farko da Yaya ya shigo cikin gidanmu, duk da gidan talakawa ne ko ina siminti ya ?urje amma fes a share ko tsinke ba zaka gani ba. Ta je ?akin Umma ta ?akko sallaya tazo ta shinfi?a masa a gefen katifar inda muke salla. ?amshin turare sa ya cika ?akin kamar na tashi zaune, amma ba dama dole umarnin Jamila zan jira a wannan lokacin. Ya ce haka jikin ya yi shine bata sanar da ni ba. Jamila ta ce Wallahi ta hana, yanzu dai bari in tashe ta. Yace "A'a barta kawai Jamila ta ta?a ?afa ta tare da fa?in Yaya Baby! Na yi mi?a ka?an dama fuskata na kallon bango na juyo a hankali, sai na sauke idanuna kan angona, na tashi zaune da sauri na zuba mishi ido. Jamila ta sulale ta fita ?ofar ?aki. Yace Baby ya jiki? Nace na samu sau?i ya akayi ka sani? "Jamila ta sanar da ni, ki daina damuwa saura kwana nawa mu zama a tare na har abada Baby, kwana biyar kacal." Na lumshe ido na ware su a kan fuskarsa, me yasa baka zo min sauka ba? "Nazo Baby, kun yi karatu ku duka, kin yi ke ?aya kina kuka suratul Muhammad wanda nima sai da na zubda hawaye, ashema kece shugabar ?aliba, kin amshi kyautuka harda na ladabi babban ba?on ku wani Basarake ya ba?i kyautar kayan ?aki yadda ya yi ta jawabi akan ki shine duk kishi ya kama ni, na tafi domin sai naga kamar yana sonki gashi mai hali kar ki juya min baya." Na sauke

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login