Showing 1 words to 3000 words out of 84782 words

Chapter 1 - FARAR WUTA 1 Complete Hausa novel

01 Apr 2025

10712

??ࡱ?>?? ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????

 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?Root Entry???????? ?F?WordDocument????1?0Table????????@
Data
???????????????????? P??8KSKS?1?p???????rr???????;D??








$ ?1 *r??

????
[ ??[ 
?
[ ?

?? SHIMFIDA.
A lokacin da abinda kake tsoro yake tare da kai...!
Me zai faru a lokacin da abinda kake tsoro yake tare da kai? A lokacin da ka shiga shiga cikin wata duniya da zaka ji baka son barinta? ka bi ahalin cikinta kuna nutsewa cikin ramin da baku san dashi ba? ka shagala da kallon FARAR WUTAR da ta juye tunaninsu, ta wanke kwakwalwar su har kowa a duniyarsu ya manta cewar wuta, WUTA ce! Duk kuwa irin FARINTA.
#Aysha Shafi'ee.
#FikraWriters
#FararWuta.

BABI NA ?AYA.
~~~~~
Wajen karfe goma sha biyu na rana, matar dake cikin kitchen Win da aka zagaye da langa-langa daga Wan madaidaicin tsakar gidan ta kwance wani Waurin itace dake gefe ta ?ara a cikin murhun gabanta sannan ta shiga firfita wutar da wani karyayyen mafici dake gefe. Dattijuwa ce mai kyawun jikin da idan ba fuskarta ka kalla ba zaka zabge shekarunta ?iyasi.
Kayan jikinta riga da zani ne masu kyau da har karin guga zaka hango a jiki, gashin kanta mai laushi ya sirka da kananun furfura da ta fara yiwa kan nata rumfa.
Sai da ta tabbatar wutar ta kama sannan ta mike ta fito, a tsakar gidan ta tarad da babbar ?arta mai suna Amina zaune tana tsintar wake a wani katon farantin silver, shekaru ne kawai suka banbanta kamannin fuskokinsu amma kammaninsu daya sak! Har yanayin jikinsu da komai.
?ar siririya ce mai yalwar gashi irin na mahaifiyar tata, komai a fuskarta maidaidaci ne mai sanyin kwatance, idanunta ne kadai abinda mai Waukar hankali don duk da ba girma ne dasu ba, amma suna da wani kyalli kamar an Wiga wani abu a cikinsu.
"Yi sauri ki gama Amina, sha biyu tayi gwara muyi sauri a Wora don yanzu zaki ji su sun dawo."
Amina ta buWa labule Wakin dake bayanta, ta kalli agogon dake kafe a cikin dakin sannan tace.
"Ashe lokaci ya tafi har haka, ban kula ba sam wallahi."
"Garin ne ba zafi ai shi yasa kika kwanta kika yi ta baccinki."
Da murmushi tace.
"Ni ai na gaji da tashi da wurin ne wallahi, da sun tafi makaranta sai inga gwara kawai na kwanta."
Mahaifiyar tasu da suke kira da Amma ta dauki wata tukunya dake gefe, ta nufi wajen ruwa da ita tana fadin.
"Ki cigaba da addu'a kawai, idan da rabon ki a cigaba da karatun nan zaki yi insha Allah."
Amina bata ce komai ba, don Allah ya sani ta fara karaya, shekararta guda kenan da kammala karatun sakandire dinta, kuma sakamokonta yayi kyau duk da cewar an taimaka musu wajen yin jarabawar, amma duk da haka ta san tana da kokarinta daidai gwargwado, shi yasa ko kadan ?ulafucin son cigaba da karatun bai bar ranta ba.
Kuma ba dole sai wani babban karatu ba, don ta daWe da soke Jami'a a lissafinta, ta sani cewa mahaifinta bashi da halin wannan wajen, yana iya bakin kokarin sa wajen kula dasu da Wan abinda yake dashi kuma duk da haka kullum cikin damuwa yake yana ganin kamar baya basu abinda ya kamata, don yasha fadin cewa yayi burin cewar ?a?an sa zasu huta da duk wani gata na duniya.
Don haka tunanin ta a kullum na ta samu makaranta ne ?arama inda zata dan koyi aikin lafiya... Don mahaifiyarta tasha faWa mata cewa ko allura ta iya yiwa mutane, idan tayi aure hakan zai taimake ta sosai fiye da ace ta zauna bata yin komai.
Zancen auren ya tuno mata da saurayin ta Abdallah, ta san shirye-shiryen komawa makaranta yake yi shi yasa bata ji shi ba kwana biyu, a matakinsa na ?arshe yake a can wata jami'ar Sakkwato. Abdallah mutum ne mai kirki da kuma hankali, har islamiyyar dare yake da ita a bayan layinsu wanda yasa kowa ke ganin mutuncinsa kamar yadda itama take girmama shi a kodayaushe, tana ganinsa kamar yayanta shima kuma yana taimakon ta a komai kamar ?anwarsa.
Mu'amalarsu daban take da yadda take ganin tsakanin ?awarta Fatima da nata saurayin, abubuwa da yawa idan Fatiman ta gaya mata ta kanyi mamakin yadda suke iya kasancewa, don ita ko Waga ido ta kalli Abdallah bata iyawa sosai, sau da yawa ma ta kan manta cewa mu'amalarsu aure zata kai.
"Salamu alaikum, wai a bada gullisuwa."
Sallamar wani yaro ta katse tunaninta sanda ya tsaya daga jikin hanyar soro yana miko naira hamsin.
"Ta nawa?" Ta tambaya.
"Ta naira Ashirin."
Sai ta ajiye farantin waken ta mi?e ta karbi kudin, watanni hudu kenan da fara sana'arta ta saida alawar madara, gullisuwa da kuma albishir, kuma ciniki take yi sosai don a kwana uku kawai take sake yin kowannensu na dubu biyu. Wannan shine babban abinda ke Webe mata kewa da kuma faranta ranta ganin yadda take iya yin wasu bukatunta da kanta har ma ta taimakawa ?annenta da Wan kuWin kashewa, saSanin a watannin baya da bata komai.
Lokaci shine rayuwarka ta duniya da kuma lahira, babu amfani ka barshi yana tafiya haka sakaka... Kalaman Ammansu kenan a kullum idan tana bayanin abubuwan da suka dace da rayuwar mutum.
Ta Webowa yaron gullisuwar hade da canjinsa, ta fito daga falon nasu da babu komai sai shimfidadden carpet daidai lokacin da Fatima tayi sallama ta shigo.
"Amma ina wuni."
Ta gaishe da Ammar dake wanke bayan tukunyar data dauka.
"Lafiya kalau Fatima, Hajiyan ta fita ko tana nan?"
Hajiya mahaifiyar Fatiman ce, kuma tana zuwa jinyar kakar Fatiman ne da aka kwantar a asibiti kullum.
"A'a bata fita ba, girki take yi tukunna."
"To bari in gani nima idan na gama nawa ko zan iya bin ta, tun jiya nake wa?ar ya kamata in koma wallahi."
"Ai jikin nata ma da sauki."
Cewar Fatiman tana nufar hanyar Wakin su Amina rike da ledar hannunta, ganin hakan yasa Amina ta dauko farantin waken da ta gama gyarawa, ta nufi wajen rijiya ta zago ruwa ta wanke shi sannan taje ta zuba a tukunyar dake gab da tafasa.
"Kaya Ahmad ya kawo min jiya da yazo."
Tana bude labulen Wakin Fatiman ta fada, da fara'arta kuwa ta goge ruwan hannunta a jikin doguwar rigar da ta saka sannan ta ?arasa gefen katifarta inda Fatiman ke fito da kayan, atamfa ce har guda biyu da kuma farin mayafi Waya sai kayan kwalliya.
"Gaskiya ne Fati, wallahi ki gode Allah, Ahmad na ji dake."
Fatima ta juya idanunta alamun dadi tana murmushi. Fara ce ita sosai, farin da take alfahari dashi a kodayaushe, tana ganinshine silar samuwar abubuwa da yawa a rayuwarta, don iyayenta masu ?aramin ?arfi ne sosai.
"Ni kaina wallahi na sani Amina, shi yasa nake gode masa kullum."
"Allah kuwa yana da kyauta, Allah ya saka masa da alkhairi... Kai wannan tafi kyau wallahi." Ta fada tana daga wata.
"Kamar kin san nima nafi ganin kyanta, har cewa nayi ko in barta sai Sallah kawai muyi ankonta ni dake."
Amina ta bude kwalin wata hoda sannan tace.
"Sallah fa da nisa, ki Winka abarki kawai. Ma yi wani ankon idan lokacin yazo."
"To shikenan." Fatima ta gyara zama tana kallon yadda take kallon kayan, sai kawai tace.
"Wai yaushe rabon Abdallah da ya miki kyauta ne Amina?"
Amina bata bar kallon kayan kwalliyan ba tace.
"Shi da yake dan makaranta ta yaya zai iya wata dawainiya yanzu, in dai sallah tazo ai yana min kaya kin sani."
Fatima ta tabe baki.
"Wannan fa daban, kyauta kuma daban. Ni wallahi Amina na sha gaya miki ki ?yale Abdallah nan, da tuni kin fara ganin wadanda suka fishi, don naga alama yanzu idanunki basa ganin kowa."
Sai a lokacin Amina ta kalle ta.
"Fatee, ke fa kin san ni duk wannan abin ma ba a gabana yake ba, shi yasa nake son mu'amala ta da Abdallah saboda shima yanzu karatunsa yake son gamawa, baya takura min nima kuma bana takura masa."
"Wai har yanzu kina ganin zaki cigaba da karatun ne?"
Ta daga kanta.
"Wallahi ban fidda rai ba Fatee, duk da? na san Baba ba zai iya ba, kuma babu wanda zai yi min bayan shi din.'
"Shi yasa nake gaya miki ki hakura kawai, ba komai mutum yake samu a rayuwa ba, a yanzu auren kawai ya kamata kiyi, ki ragewa su Baba nauyi sannan kema ki sami wajen da zaki iya Waukar Wawainiyar wasu ma."
Kallonta kawai Amina take tana murmushi don ta riga ta sani cewa ba zata taba fahimtar abinda take ji a zuciyarta bane, sai da ta kai ?arshe sannan ta shiga haWa kayan tanafaWin.
"To shikenan, ki bari sai bayan maulidi, idan mun fara kai ki, sai in fara wannan lissafin.
Jin haka yasa ba shiri itama tayi murmushi tana kara juya idanunta, don kamar yadda aka tsayar da rana, bayan maulidin ne bikinta ita da Ahmad din.
"Baki san wani abu ba ma, wata mata na samu mai sayar da magunguna a can layin..."
Da haka ta shiga bawa Amina labarin da yasa ta bar hada kayan ta zare idanu tana kallonta kafin? ta shiga Waka mata duka alamun bata son zancen, ita kuma tana kyalkyala dariya.
Mahaifin Amina mai suna Alhaji Sulaiman dattijon mutum ne mai sana'ar harkar aikin katako, ya samu wadata a da, don gidan da yake zaune da iyalansa na kansa ne, amma a yanzu abubuwa sun tsaya masa ta yadda ya Wauki hakan ya sanya a ransa har ya zama shine damuwarsa a kodayaushe. ?a?an sa biyar tare da matarsa Halimatus- Sadiya bafulatanar Niger da iyayenta suka dawo Nigeria da zama.
Amina ce ta farko, sai Aminu, Maryam, Adam da kuma autarsu Hafsa. Maryam, Aminu, da Adam suna matakin secondary ne a karatu yayin da Hafsa kadai take Primary, amma da yake makarantar da suke zuwa wata community school ce dake waje Waya, tare suke tafiya dukkaninsu tare suke dawowa.
Babban damuwar Alhaji Sulaiman a yanzu shine ganin ?a?an sa na ?ara tasawa kuma harkar samun sa na ?ara yin baya, karayar arzi?in da ya samu ta taimaka ?warai wajen karya zuciyarsa akan komai, kullum cikin lissafi yake da kuma damuwar da ?arara kowa ke gane ta duk da irin nuni da kuma nasihar da matarsa ke yi masa a kullum.
***
?arfe Biyu da rabi.
"Yaya dan girman Allah zaki bani naira dari? ?unshi zanyi."
Maryam ta fada lokacin da take ?o?arin cire uniform Win ta bayan sun dawo daga makaranta. Amina na zaune tana ninke kayan wankinta tace.
"?unshin me zaki yi?"
"Bikin yayarsu Na'imah fa, kin manta jiya nazo da katin."
Jin tayi shiru yasa ta sake tambaya.
"Zan baki Maryam, Allah ya kaimu gobe."
"Me za'a bayar? Idan ana ?aunar Allah nima a taimaka mun."
Aminu ya fada yana shigowa cikin Wakin.
"Kaima ?unshin zaka yi?"
"Me kyau ma kuwa, don kin san sai yafi fitowa a hannu na ma akan bakar fatarta."
Ya fadi hakan sanin cewar shi fari ne, don ?an mazan biyu su suka yiwo mahaifinsu sak a kammani da kuma hasken fatan, matan kuma Suka yo mahaifiyarsu, har gwara Maryam ma ana cewa idonta irin na babansu ne, amma Amina da Hafsa babu abinda suka bari a kammanin Amman.
"Wallahi ni ba ba?a bace kaima ka sani, irin wannan kalar fatar sai ka zagaye garin nan kaf baka samu irinta ba."
"To idan ma an samu me za'ayi da ita? Da dai irin ta Amina kika ce sai in yarda, amma ke duk gidan nan ma akwai mummuna kamar ki."
Maryam ta kara haWe ranta tana saka hijabin data Wauko. Amina ta jefo masa wata riga dake hannunta tana murmushi.
"HaWa mu kayi kawai kake zagi Aminu, dani da ita Win me ya banbanta damu, ka takurawa Maryam wallahi."
"Haba ya zaki hada kalar ki data wannan fingilar? itama ta hakura ta karSi kanta yadda take ne ta?i, sai faman iyayi fal ciki."
Da ?un?uni Maryam ta faWi wani abun kafin ta tayar da sallarta. Hakan yasa shi dariya don shi kansa ya sani girman dake tsakaninsu ne kawai yasa take raga masa a azababbiyar magana da kuma rashin kunyar dake cikinta.
"Sai yaushe zaka fita yau?"
Amina ta tambaya sanin cewar da ya dawo baya dadewa a gidan yake tafiya can inda yake koyon gyaran mota a can hanyar gidan zoo, har? ma ya fara kwarewa don kusan shekara biyu kenan da Baba ya kai shi wajen.
"Sai na ?arbowa Baba, kayansa daga wajen guga..." Ya shafo kansa.
"... Tun dazu ma fa ya kamata in je, sun ce sun gama."
Kafin Amina tayi magana, Hafsa ?aramar ?anwarsu ta shigo gidan hannunta ri?e da ?ullin farar ledar atturuhun data siyo na girkin dare da kuma takardar yashin madina tana zubawa a Waya hannunta tana lashewa. Amina ta Waga murya ta kirata ganin bata da alamun shigowa.
"Ki shigo ki cire kayan nan ki saka na islamiyya, ga uku nan har ta kusa, Adam har ya tafi kina nan."
Tana jin hakan Idanunta irin na Amina suka kaWa a take sannan muryarta ta koma ta kuka, ta shigo Wakin da sauri tana faWin.
"Dan Allah kice Ya Maryam ta raka ni, wallahi zane ni za'ayi..."
Kafin Aminan ta amsa, Aminu yace.
"Saka kayan muje in raja ki daga nan sai in wuce.
Ai kuwa da murnarta ta ruga da gudu zuwa dakin Amma inda kayanta suke, ta sani ba wanda ya isa ya dake ta makarantar tunda Aminu ne zai raka ta.
Aminu ya ciro Naira dari biyu daga aljihunsa ya cilla kan sallayar da Maryam ke sallah yana faWin.
"Gashi nan kije a zana miki abinda ba ganinsa za'ayi ba."
Amina tayi murmushi tana godewa Allah a zuciyarta, tana son yadda suke tallafar junansu akan irin ?ananun bu?atun nan.
Hafsa bata dawo ba suka tsinci sallamar mahaifinsu, dukkaninsu suka kalli juna a lokaci guda sanin cewa lokacin ba lokacin dawowarsa bane, ?a'ida ne sai bayan sallar magriba kullum yake dawowa don har Aminu yana yawan riga shi isowa ma.
"Allah yasa kar ya tambayi kayan nan..."
Aminu ya faWa yana dafa kansa.
Ta tsakanin raga-raga labulen Amina ta hango yadda mahaifin nasu ya dafa kan Hafsa da ta taho ta rungume shi, sannan kai tsaye ya nufi hanyar Wakinsa.
Taga Amma ta fito daga falo sanye da hijabi alamun salla tayi ta bin bayansa tana fadin sannu da dawowa.
"Ke maza ki dauko takalminki mu fita."
Cewar Aminun, sannan ya juyo ya kalli Amina.
"Kice masa tun dazu na tafi karSi kayan."
Ai kuwa yana sanya kafarsa waje suka ji Baban yace.
"Fita ce ta kama ni Halima, ina kayan da nace a karbo min?"
Basu ji amsar da Amman ta bayar ba sai muryarsa da ta sake dagawo wajen kiran Aminu.
"Aminu! Yana gidan nan?"
"Na shiga uku.."
Cewar Aminun, kuma Amina na kallon sanda Maryam ta murmusa a sallarta don daWi.
"Baba sannu da zuwa, wani abu ne ya faru ka dawo yanzu?"
Ta tsinci muryarsa da yayi sauri ya tsugunna yana shafa kai ganin ya fito.
"Ni da gidana don na dawo sai ka tambaye ni me nazo yi? Ina kayan da nace ka karbo min?"
"To, to, bari aje a karbo."
Ya fada kamar sai a lokacin yace 'je ka karbo din,' kuma bai jira ya sake cewa komai ba ya kama hannun Hafsa da ta gama shiryawa suka yi waje.
Alhaji Sulaiman?ya girgiza kansa kawai saboda takaici sannan ya kalli Amma dake tsaye a gefensa.
"Hajiya Kilishi ce yanzun nan ta kira ni tace tana son ganina."
Daga cikin Wakin Amina zata rantse daga ita har Amman a lokaci guda suka yi murmushi.
Hajiya Kilishi ?aruwar Baba ce, mace ce mai kirki da son kyautatawa, ta taka muhimmiyar rawa a rayuwarsu ta kowanne fanni, tun kafin Mahaifinsu ya rasa arzi?insa har bayan komai ya cakuWe musu, don hatta kuWin rubuta jarabawarta ta fita daga secondary ita ta tallafa aka biya, babban taimakon da tayi musu na kwanan nan shine lokacin da Maryam ta kamu da rashin lafiyar ciwon ciki, wanda daga ita har su kowa ya wahala kafin a gano cewar wani ?ari ne ke fito mata a gefen cikin kuma yayi girman da har sai an cire shi.
A wannan lokacin komai nasu ya riga ya ?are wajen jinya, don hatta abinci sai daga gidan wan Baban ake kawo musu kullum ko tukunya basa dorawa, Wan abinda Baba ya samu da kuma na wajen Amman daga ?an sana'o'in da take yi duk a asibitin suke karewa.
Don haka a dole Baban ya shiga neman bashi ?ofa-?ofa, ?anuwansa suka hada masa iya abinda zasu iya amma ko kwata ba'a shafe na lissafin ba, Hajiya Kilishi ita taji labari a danginsu, ta kira Baban har gida ta bashi tallafin naira dubu Wari uku, kuWin aikin har da Woriya akai, tun daga wannan lokacin zuciyoyinsu suka kara girman darajarta a wajensu.
Mijin ta wani babban mai kuWi ne kuma sanannen mutum ne, itace matarsa ta biyu kuma ?a?an ta biyar dukkaninsu mata, amma ance saboda zaman amanar da suke yi da uwargidanta babban Wanta ma a wajen Hajiya Kilishin ya tashi tun yana yaro ta yadda ba kowa ne ya san cewa ba itace ta haife shi ba, Baba yasha gaya musu cewar ko gidan yaje baya iya banbance ?a?an ta dana uwargidan.
"Shinkafa da wake kuka yi? A zubo min dan Allah kafin yaron nan ya dawo."
Muryan Baban ta katse tunanin Amina daidai lokacin da Maryam a gefenta ta idar daga sallah, ta sake kallonsa ta cikin labulen sanda da yake cewa.
"Allah yasa Amina ta daka yajin nan nata mai daWi."
A lokaci guda murmushi ya suSuce a fuskarta, sai kawai ta mike tana faWin.
"Akwai Baba, Bari in kawo maka."
***
Royal Brompton Hospital.
Sydney St, London SW3 6NP, United Kingdom.
...So I took your hand, back through lamp-lit streets,
I knew,
Everything led back to you
So can you see the stars over Amsterdam?
You're the song my heart is beating to...
Wa?ar a hankali take fitowa daga cikin labtop Win dake ajiye a wani Wan ?aramin tebur da kujerarsa dake can jikin dogon windon Wakin, Wakin asibiti ne da banda gadon mara lafiyar da kuma tarin computers Win gefe dake auna lafiyar wanda ke kwance, babu komai sai wata drawer daga can gefe wadda aka yi mata ado har da wasu ?an fulawoyi, Wakin a gyare yake tas yana kuma ?amshi mai daWi, ga room heater dake fitar da wani Wumi mai daWi sakamokon sanyin ?an?arar snow Win dake zuba daga waje.
A hankali idanun mara lafiyar dake kwance akan gadon suka buWe, kuma duk da lumshewar su girman su ya fito a lokaci guda, matashi ne mai siririyar fuska, yana da yalwar gashin kai da kuma na gira kamar yadda na idanunsa suke dogwaye ta yadda idan ka kalle shi zaka ga kamar baya iya buWe idanun nasa ne sosai.
Ya Wago da hannunsa dake ma?ale da allurar ruwan drip Win gefe, ya kalli hannun tsawon wasu sakanni kafin yasa Waya hannun nasa ya murza goshinsa alamun takaici,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login