Showing 21001 words to 24000 words out of 84387 words

Chapter 8 - ABRAHAM complete Hausa novel

09 Dec 2024

28133

har yanzu mai gurguwa take shafawa amma skin color dinta ya fito tarr yana shining sak'amak'on Air conditioner da take kwana tana wuni da shi.



Albashin ta da madam Gloria ta bata, ta kurawa ido... hawaye suka zubo a kuncin ta, a lokacin da madam Gloria ta bata kudin to tsorata, domin bata taba ganin kudi masu yawa haka ba balle ta rike, Wai yau ita ce ke da wanna tarin kudin...

"Alhamdulilahil-lazee tatimus solihat" ta fada a hankali hadi da mikewa, kudin ta mayar cikin farin envelope din da aka rubuta sunan ta da biro b'aro,-b'aro a kai, hijab dinta ta sanya kana ta sauka kasa, babu kowa a falo sai plasma dake ta yi shi kadai, waje ta fita inda tun zuwanta gidan bata taba fitowa ba, gaisawa suka yi da mai gadi ta fita da sauri domin so take ta yi ta dawo domin ta dora dinner.



Gidan da bintu take aiki ta nufa, k'wank'wasa Dan karamin kofar tayi, Bayan minti biyu mai gadi ya leko hadi da tambayar ta wa take nema, ta sanar da shi, ya Bude mata ta shigo hadi da nuna mata hanyar da zata bi domin yaga bakuwar fuska ce, bata San kan gidan ba.





Bakin kofa ta tsaya hadi da yin knocking, jim kadan wata yarinya ta bude Wacce aysha ta tabbatar itama yar aiki ce, bakinta dauke da sallama cikin siririyar murya ta shigo inda kamilar dattijuwar mata mai sanye da medicated glass ta amsa hadi da binta da kallo irin ban gane wanna fuskar ba, fahimtar hakan yasa Aysha kara so gabanta, durkusawa tayi ta gaishe ta hadi da sanar mata cewa tazo wajen Adda bintu ne.



Murmushi Matar tayi daya bayyana hakoran makkah ta biyu sliver da golden dake gefe da gefen hakorin ta kana tace "ke kanwar tace ko?"


"Eh" Aysha ta amsa mata kawai tana mayar mata da martanin Murmushi.


"masha Allah, bari na kira ta a waya domin suna can suna kiciniyar hada dinner" ta fada tana latsa tsad'ad'iyyar wayar hannun ta....


Mintuna biyar kacal bintu ta fito, ganin Aysha yasa ta kara fad'ad'a Murmushin ta...


"yau Indon baffa ce ta fito da kanta" bintu ta fada cikin zolaya.



Murmushi Aysha tayi tace "wallahi Addah, an biya Albashi ne, kin ganshi nan" ta dora mata a cinyar bintu kana ta cigaba
"ina so kudin su isa ga Innata basan ya zan yi ba"


Jinjina kaifin tunanin Aysha, bintu tayi a ranta, a fili tace "kinyi tunani mai kyau Indo, hakika kin cika y'a ta gari, abinda za a yi shine zan karbi cash din hannun ki, sai na yi wa jauro (kanin bintu) transfer yaje bankin cikin gari ya cira gobe ya bata tunda ya iya, dama gobe ina son zuwa bankin na ciri kudi, Kinga na huta, yanzu nawa kike so a tura mata? 


"duka Addah"

Dariya bintu tayi tace "A'a? ba za a yi haka ba, kin San fa kin girma yanzu, dole zaki kula da kanki, siyan pad, man shafawa, man gyaran gashi, da Dan kayan sawa haka Kinga duk kina da bukatar su, abinda za a yi shine za a tura wa Innah wuro dubu hamsi, saura dubu ashirin din sai a yi miki siyayyar dashi ko, gobe zanzo na yi wa madam magana kan zamu je kasuwa dake"



"toh Addah, Kema ki cire kudi a ciki kiyi amfani dashi"


"a'a? Allah ya kiyaye indo, tamkar kanwata ta jini na dauke ki, duk abinda na yi miki saboda Allah ne, dan haka ki bar kudin ki Nagode kinji"



"toh Addah Nagode Allah ya biya ki, amma nayi kewar Innah ta sosai da su y'ay'ana"? ta fada hawaye na ciko idanunta.


"shagwaba ko? Toh Karki damu zan fadawa jauro idan ya kai mata kudin ya kira wayata a wajen sai na hadu ku, ai shikenan ko? "

Da farinciki Indo ta koma gida, jin gobe za ta yi waya da Innar ta, a k'age take goben yayi, cikin kwarin jiki da bata taba irin sa ba tun zuwan ta gidan ta shiga dora musu dinner.



*WASHEGARI*

Kamar yadda bintu ta fada tazo wajen madam Gloria tare da rokon Alfarma kan ta bar Indo su Je kasuwa, bata hana su ba, sai dai cikin isar da ji da kai ta ce Indo ta dawo kan lokaci...



Basu jima da hawa keke-napep ba, sai ga Kiran jauro, danna answer bintu tayi hadi da sallama, amsawa jauro yayi suka gaisa kana yace ga Inna wuron, amsa Inna tayi ta fashe da kuka, kana ta shiga yi wa Allah godiya, sannan ta dora da yi wa bintu godiya sosai hadi da yi mata addu'oi'n fatan alkhairi...




"Bakomai Inna, ai yi wa kaine, ga Indon" abinda bintu tace Kenan tana kara wayar a kunnen Aysha....




Rike wayar gam Aysha tayi a kunnen ta, kana cikin murya mai nuna zallan kewa da son mahaifiyar ta tace "Innata... Nayi kewar ku sosai" ta karasa tana sakin kuka....



Itama Inna, hawaye ne masu Sanyi ne suka zubo mata sak'amak'on jin muryar tilon yarta, "munyi kewar ki sosai Indon baffale, yi shiru Karki tada min hankali, kina lafiya dai ko?"


"eh Innata" ta amsa.

"toh alhamdulillah,na ga abun arziki, Allah ya miki albarka ya tsare min ke, Sannu yar albarka kin ji ko? "


"Ameen Innata kin cancanci fiye da haka, albishirin ki Inna? Aradu na iya kalolin girke? irin na yan birni masu dadi, idan na dawo zan yi mana shi ki ci, ki ji dadi ke da yan biyu na" ta fada cikin sakalci da kuruciya.




Dariya Inna tayi tace "toh Allah ya kowa mana ke lafiya, gashi kin aiko mana da duka albashin ki, dame zaki yi amfani?"


"ai inna da ragowar dubu ashirin, albashina dubu saba'in ne fa"



"saba'in!!!" Inna ta maimaita cikin mamaki hadi da zaro duka idanun ta waje.




"aradu Inna, mun zama masu kudi" tilas Bintu dake gefe tasa dariya, indo ba dai sakalci ba.


Itama Inna Dariya tayi a ranta tana kara godewa Allah, a fili tace "ga y'ayy'an ki nan sun ishe ni da Kiran Ammuh"


"wayyo Ammar da Anwar dina, nayi kewar su Inna ki bani su naji muryoyin su"





Anwar aka fara bawa wayan, banda Kiran Ammuh da gwaracin sa babu abinda yake, Lumshe ido Aysha tayi, kewa hadi da tsananin son yaran ya kara shiga zuciyar ta..


bayan nan aka bawa Ammar shima sai Dariya yake saboda jin muryar Ammuh dinsu, kuma abun mamaki sun gane ita ce, itama Aysha take ta tuno tsananin kaman Abraham da Ammar din ta, ta so bawa Inna labari sai tayi shiru.



Zuciyar Indo fess saboda jin muryar su Inna da ta yi, ba dan ta so ba, bintu ta kashe wayar, Bayan ta cewa jauro zata turo masa kati...



Daga bangaren Inna kuwa Dubu Biyu ta bawa jauro daga cikin kudin inda da kyar ya karba, kana yayi godiya ya tafi, itama innah bashin da ta dan ci ta biya, kana tayi musu siyayyar kayan Abinci masu yawa, sabulun wanki, sabulun wanka, man shafawa, man goge baki, har sabbin kaya ta siya musu masu saukin kudi sosai, ranar har da namomi cikin Abincin da suka ci..... (ni Noor nace talauci Nesa da mu ooo, arziki zo nan ga=?9?=ؔ?)




Su Aysha kuwa sha biyu saura suka dawo gida, inda bintu ta taya ta zaban man shafawa da ta San zai karbe ta da sabulun man, sai toothbrush da tooth paste, kayan make up, turare, palm shoe guda daya, sai wasu roba? ready made gown guda biyu masu saukin kudi......

Wanna Kenan.




____________________


*1 WEEK LATER*
_5:56 am_


Zaune take kan sallaya, ta tankwashe kafafunta, yayin da take rike da Kur'ani tana rera karatu cikin suratul-tawbah, cikin sanin ya kamata take bawa ko wani harafi Hakkin sa.., kasancewar kuma gari bai waye ba, ko ina yayi shiru yasa amon zazzak'ar muryar ta ke fita....



A kuma daidai lokacin ne Abraham dake gyming room din shi yana daga karfe ya fara jin tashin muryar ta na shiga kunnen sa, cak ya tsaya da abinda yake yi, hakika zai iya rantsewa bai taba Jin dadin wani abu a kunne sa kamar karatun da Aysha'n ke yi ba, duk da bai San menene ba, bai San me take cewa ba, bai kuma fahimci ko harafi daya ba, amma yana matukar son abinda take fada, Lumshe ido yayi, yana jin yanda ko wani mahuda na gargasan jikin sa ke mikewa, yayin da wani Sanyi ya fara shigar shi slowly, duk da gumin daya hada saboda motsa jikin da yake yi....



A hankali ya dire karfen a kasa, kana ya Bude lumsassun idanun sa hadi da bude kofar ya fita, bai San me yake yi ba, kawai dai ya tsinci kan shi da bin hanyar da yake jin sautin muryar ta...., duk taku daya da yayi, yana kara jin sautin muryar ta na kusanto shi, kana bugun zuciyar sa na karuwa....
'?






_kuyi manage da wanna please, wallahi am so so tired today, meye ra'ayinku kan wanna episode din? Mu hade a next page_....





Share fisabillahi'
Comment for more typing.'



Noor>؋?



Wednesday, 2 February 2022


I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial *131*4# or
*460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.

*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call 0806626851
[10/9, 8:12 AM] =ؖ?NoorEemaan=ؖ?: ABRAHAM

*First edition*




*WATTPAD*
@NoorEemaan




https://facebook.com/groups/943534712916776/
Masu amfani da facebook su yi join ta wanna link din.




_Am so sorry for keeping you guys waiting, na San ba dadi, kun jira ni da yawa, amma ba laifi na bane, ban ji dadi bane kwana biyu, ga ba lokaci, amma kuyi hakuri in sha Allah bazan kara jimawa irin wanna ba, har in gama Abraham, ngd sosai da kokarin jirana da kuka yi=?O? much luv masoyan NoorEemaan_=?
?




Chapter 25-26


Cak! ya tsaya a lokacin ya isa bakin k'ofar? dakinta, inda a yanzu amon sautin zazzak'ar muryar ta ya fi tashi, hannu yasa kan handle din kofar a kokarin sa na son bud'e kofar, sai kuma yayi saurin d'auke hannun sa hadi da murza su cikin na juna, a hankali ya jingina bayan sa da kofar dakin ta, sannan ya Lumshe k'yawawan idanun sa yana cigaba da sauraron kira'ar ta mai dadi....


Sosai ko wani mahuda na gashin jikin sa suka kara bude wa, kasancewar yanzu yafi kusanci da ita, wani yanayi mai kama da zubar tsigan jiki, da Sanyi ya shiga ratsa shi...



*40 Minutes later*

Wanda yayi daidai da lok'acin da Aysha ta rufe qur'anin ta, kana ta shiga yin addu'oi'nta...

A kuma lokacin ne Abraham dake tsaye a bakin kofar ya sauk'e wata k'arfaffar ajiyar zuciya, kana a hankali ya bud'e lumsassun idanunsa da suka dan rine sak'amak'on jimawa da suka yi a rufe.



Cikin yanayi mai kama da rashin jin dadin ya yamutsa fuska tamk'ar yaro dake son wani abu daga mahaifiyar sa, haka nan yaji ba dadi a dalilin daina jin amon sautin muryar ta dake rera karatun qur'ani.
A karo na biyu ya kara sauk'e numfashi kana cikin tafiyar sa ta ingarman na miji mai ji da lafiya da kuruciya ya bar wajen...



Aysha kuwa bayan ta iddar da addu'o'in ta ta Mike, a gaggauce ta shirya kana ta sauko kasa ta fara shirya musu had'add'en breakfast mai rai da motsi tamkar ba Indon baffa ba.



*********



9:00am.

ABRAHAM tare da madam Gloria ke zaune a had'add'en dinning area suna jiran Aysha tayi serving din su, a hankali cikin takun nutsuwa Ayshan ta fito daga kitchen hannun ta dauke da plates na tangaran da zata yi serving dinsu dashi...




Jin kamar ana kallon ta yasa ta a hankali ta dago kanta idanunta suka fad'a cikin nashi, gaban ta ne ya bada dam! Domin tun lokacin da ta fara serving madam Gloria abinci yau ne karon farko data ganshi a dinning table, gabadaya ji tayi idanun sa na yawo a jikin ta wanda hakan yasa jikin t???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?a fara rawa domin sosai yake ladabtar da ita da sexy eyes d'insa masu masakaicin girma, hannunta ne ya fara rawa, ba tare da zato ko tsammani ba plates din suka kufce daga hannunta suka tarwatse kan tiles din...


A zabure madam Gloria ta mike, hadi da daga lukutan hannunta da niyyar marin Aysha da ta k'amk'ame jikin ta sannan ta runtse idaunta...



Ganin yasa Abraham mikewa, taku biyu kacal yayi ya kamo hannun madam Gloria ya sauke, kana ya kalle ta, ba tare da yace komai ba ya koma kan kujerar sa ya zauna, yana k'ark'ad'e hannun sa saman dinning table din...




Da kallo ta bishi kana tace "why son? Meyasa zaka hana ni? Daka barni na nunawa wanna Bush Village girl din hankali"

Juyawa tayi ta ga Aysha tace "ke! Baki da hankali ko? what's your problem? Hannun ki ciwo yake? Kina abu kamar zararriya, bari in gaya miki, this should be the last time da zaki kara fasa min plate, kin San nawa each one?... 




" mummy plssssssssss" Abraham ya fada a dake, yana rike da kansa, haka nan yaji fad'an da take wa Aysha na bata masa rai, be San mai dalili ba, baya ga haka shi mutum ne mara son hayaniya...




Shiru madam Gloria tayi, ta zauna tana sauke hucin bacin rai, amma ba halin magana, domin ta San Abraham kaifi daya ne, sannan ta yi Controlling kanta ne domin kada tsanar da take wa Aysha ya fito b'aro-b'aro, saboda har ita kanta Ayshar bata so ta San cewa ta tsane ta, ta kuma tsara hakan ne domin plan din ta ya tafi daidai yanda ta tsara...





Indo kuwa runtse idanunta tayi tana jiran sauk'ar mari, jin shiru ne yasa ta Bud'e idanunta cikin mamakin rashin marin da madam Gloria bata mata ba, cikin sheshek'ar kuka ta dauko Abin shara da Abin kwashewa ta shiga tattare fasashen plates din, cikin rashin sani ta taka wani fasashen plate...

Kara ta saki, inda a tare ita da Abraham suka runtse idanun su, wanda shi kanshi bai San yayi hakan ba.....



Saboda d'auriya irin na Aysha, ta kuwa Mike ta karasa tattara wajen ba tare da ta damu da cire broken plate dake tafin kafar ta ba.



Cikin k'ok'arin shanye zafin da take ji ta koma kitchen din ta dauko wasu plates din, wanna karon Sam bata yarda sun hada ido ba, duk da yanda take jin idanun sa na yawo a kanta, a nutse ta fara serving dinsu, amma tayi kokari matuka wurin controlling kanta domin sosai hannun ta ke rawa....





Bayan ta gama, ta jaa kafar ta zuwa sama tana zub da hawayen da bata San koma menene ba, domin indai fada da zagin madam Gloria ne ta fara sabawa, har hakan bai fiye damun ta ba...



Kan mad'aid'aicin bed dinta ta zauna tana sauke nishi, kafar ta daya ta d'ora kan dayan da niyyar cire k'walban, amma ta kasa saboda zafin daya ziyarci k'wak'walwarta....



Kwanciya tayi a gadon ta cigaba kuka, har wani wahalallen bacci da bata shirya zuwan sa ba ya dauke ta....



Ta bangaren Abraham kuwa, hakan nan yaji ransa ba dadi a dalilin abinda ya faru, duk da dadin dandanon da abincin ke dashi akan bai sa yaci da yawa ba, ruwan black tea yayi sipping kana ya goge bakinsa da tissue, sannan ya mike...



"wait! Son don't tell me you re full?" ta fada cikin rashin jin dadi da kulawa kamar gaske.



"yes mum! Am going out"

ya amsa a takaice kana ya haura sama cikin abinda bai fi 7seconds ba...
da kallo mai tattare da zallan tsana hadi da muradin cika mugun nufin ta a kanshi ta bishi, kana ta dawo da kallon ta ga plate dinta mai shake da chips with fried eggs, a hankali tace "shege mai taurin rai, dama kayi accident a hanya ka mutu idan ka fita, kaga ka sauk'ak'e min aiki, na rasa me yasa har yanzu na kasa cika burina akan ka, tabbas nayi kuskuren barin Dan zaki ya girma" ta fada cikin yaren igbo hadi da cizon yatsan ta mai dauke da artificial nails...


*ABRAHAM*
Har ya murda handle da niyyar shiga part dinsa, sai kuma ya tsaya cak! Sak'amak'on brain din sa daya tariyo masa lokacin da fasashen plate din nan ya caki kafar ta da karan da ta saki, Lumshe ido yayi a hankali ya furta "is it still in her leg?  (ko har yanzu yana tafin kafar ta).


Tamkar wanda ake ja, haka ya nufi hanyar dakin ta, a hankali ya tura kofar ciki...

Kwance ya hangota, jin bata motsa ba yasa shi fahimtar bacci take, wanda hakan ya bashi kwarin guiwan zuwa gareta duk da bugawar da kirjin sa ke yi...




Tafin kafar ta da yayi jaa ya kurawa ido, a hankali ya dire guiwar sa kasa, kasancewar rub da ciki tayi ya bashi daman ganin kafar da kyau, a hankali yasa karfaffan hannun sa mai laushi ya kamo kafar ta, sannan ya a hankali ya fara zare fasashen plate din...
motsa kafar tayi wanda yasa shi dakatawa, hadi da fatan kad'a ta farka har ya gama...



Sai daya bari baccin ta ya kara nisa kana ya cigaba, inda yayi nasaran cirewa, ajiyar zuciya amma boyayye ya saki, kana ya cilla fasashen plate din cikin wani karamin dust bin dake dakin, da haka ya Mike ya bar dakin zuwa nasa, inda cikin mintuna arba'in ya shirya cikin wani Turkish suit ya bar gida zuwa ginin company dinsa daya kammala, inda a cikin satin nan za a yi bikin bude shi....




*AYSHA*
Awa biyu ta d'auka cikin baccin da bata jin dadin sa ba Sam, kana ta farka...

mikewa tayi zaune tana marairaice fuska saboda zogin da ta ji daga kafar ta, a hankali ta kamo kafar, yayin da kwalla ta cika idanun ta, sai dai rashin ganin alamun fasashen plate din ya bata mamaki kwarai, a hankali ta kai hannu ta shafi daidai wajen ciwon, taji wayam babu alamun plate din a tafin kafar ta, sosai hakan ya tsaya a ranta domin iya tunanin ta bata cire da kanta ba, toh waye? ganin kanta ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login