Showing 15001 words to 18000 words out of 84387 words

Chapter 6 - ABRAHAM complete Hausa novel

09 Dec 2024

28130

halin innar na matukar burgeta, Sam Abin duniya bai dame ta, sai da ta rantse wa Innah cewa Wacce zata dauke ta aiki ce ta bayar da kudin kana Inna ta amince, har soro lnna ta rakata tana godiya kana ta dawo cikin gidan tana addu'ar Allah yasa tafiyar Indo alkhairi ce .


************************


Indo kuwa sosai ta fara kewar yan biyu da Innar ta, sai ta shige dakinta tayi kuka sosai, amma bata bari Innah ta gani, domin ta San zata iya cewa ta fasa zuwa kaduna aikatau din.




*BAYAN KWANA UKU*

A gurguje ta fito daga wanka ta shirya domin inna tace ta hazantar su isa tasha da wuri kada motocin safiya su tashi, kayan ta take hadawa cikin sauri inda idanun ta suka sauka kan jakar data ciro sarkar dake wuyanta, shaf ta manta cewa bata mayar da jakar ba kamar yadda ta aiyana a ranar, take ta tuno da baffan ta wanda hakan yasa? wasu hawaye masu dumi suka zubo mata, wanda hakan yayi daidai da kwala mata Kira da Inna tayi, cikin duburbucewa ta saka jakar cikin Ghana most go dinta, zuge zip din tayi ta fito, bayan ta share hawayen ta.



Da su ammar dake tsaye suna mata bangala mata dariya a tunanin su tare zasu tafi ta fara sauke idanun ta, murmushin ta mayar musu yayinda take jin zuciyar na karyewa, kewar su mai tsanani na ratsa ta, rungumosu tayi gabadaya da hannayen ta biyu kana ta sumbace su a goshi.



Maganar da Inna ta yi mata ne ya sanya ta Mike rike da hannun su Anwar, yayinda Inna ta dauki Ghana most go dinta suka fito, machine biyu hau inda ya fito dasu bakin titi, kana suka sake hawa wani daya kai su tasha, saukar su a tasha ke da wuya suka ji wani driver yana fadin "Kaduna! Kaduna!! Kaduna!!!" sauran mutum daya...



Cikin sauri Inna tace "Ayshatu ki kula sosai da tarbiyyar ki, Karki manta duk abinda na fada miki, Allah ya tsare ya kiyaye, ga wannan ki rike a hannunki innah ta fada tana mika mata dubu biyu, sannan ki rike takardan nan da bintu ta baki da kyau" karasawa gaban driver Inna ta, biya wa Indo kudin kujera tayi, amsar jakar ghanan driver yayi ya saka a booth, lokacin ne wani kuka mai ciwo ya kufce wa Indo, tunda aka haifeta yau ne rana ta farko da zata tafi wani gari, ganin haka yasa Inna kama hannun yan biyu suka bar wajen domin zuciyar bazata juri ganin Indo na kuka haka ba, su Ammar ihun kuka suka saka ganin da gaske Ammuh dinsu(Indo) zata tafi ba tare da su ba, haka suke kiranta da Ammuh.



Sosai suke kuka suna tirjewa alamun suna son dawowa wajen Indo, kasa juran kallon su Indo tayi ta shige motar hadi da kifa kanta kan cinyoyinta tana sakin kuka...




2:30 daidai suka sauka a tashar kaduna, kalle? Indo ta shiga yi domin ta rasa wani waje zata nufa, driver daya kawo su ne ya lura da ita yace "yarinya lafiya dai? Ko wani kike jira?" ya tambaya, yana goga aswaki a bakin sa daya dan rine, wanda hakan zai tabbatar wa mutum cewa shi din ma'abocin cin goro ne.


"hmmm uhmmm, wajen na cikin takardan nan" ta fada tana nuna masa takardan, domin ita ba karatun boko ta iya ba.
Sai dai a fagen karatun addini ba baya bace.


Kallon takardan yayi yace "ai can zaki tsallaka sai ki samu a daidai ta sahu ki bashi takardan zai kai ki har wajen domin ba boyayyen waje bane.



Godiya tayi mishi kana to dora Ghana most go dinta a kai ta tsallaka dayan bangaren...


********

Saukar sa Kenan a airport, Cikin takun kasaita ya bar filin jirgi rike da wani jaka karami irin ta matafiya, tun tafiyar sa dubai bai dawo ba sai yau, ba wai dan bai gama abinda ya kai shi ba, hakan nan yayi zaman sa a wani tsadadden hotel dake can kasar dubai din, burin shi kawai ya isa gida domin ya huta shiyasa ma ya kasa hakurin jiran driver ya zo, ya gwammace ya hau adaidaitasahu....



Isar sa babban titi kuwa sai ya fara Jin wani irin, ta yanda zai tarar mai adaidaitasahu, domin abu ne wanda bai taba yi ba, bai taba hawa motar haya ba, bema San abinda zai ce ba, yana cikin wannan tunanin yaji tsayuwar mai keke a gabansa yana tambayar sa tafiya ne? Ajiyar zuciya ya sauke kana ya fada ciki, juyowa mai keke yayi yace "oga wani area zamu je? " duk da kasancewar Abraham baya jin hausa amma ambatar AREA da Dan sahun yayi ya sashi fahimtar abinda yake nufi, motsa cute lips din sa yayi yace "barnawa" kana ya fito da bakin sunscreen dinsa ya manna a fuskar sa wanda ya kara masa kyau ainun.


*****

Tun daga nesa Indo da ta gaji da tsayuwa, fuskar ta har wani jaa yayi kamar na tumatir gwanin tausayi saboda rana da ta jima tsaye a ciki, abinka da farar mace, ta hango wani keken da alaman mutum daya ne a ciki ya sanya ta fara tsayar dashi tun kafin ya karaso, domin yawanci masu wucewa a cike take...


Mai Dan sahu kuwa hango yarinya daga nesa ya Sanyi shi yin slow kadan da kadan , kana ya juyo ga Abraham yace "oga drop ne ko a dau passenger?



Shiru Abraham yayi, ba tare da yace uffan ba, kara maimaitawa mai keke yayi still ba amsa sai kawai yayi wa Indo alaman ta taho, cikin sauri ta taho tana me mika masa takardan, karba yayi ya karanta yace "kudin ki dari biyar hau muje"


Cikin sauri ta hau tana sauke numfashi, yayin da taji bugun zuciyar ta ya karu, runtse idanun ta tayi da karfi tana kara k'amk'ame Ghana most go dinta.


Ta bangaren Abraham kuwa fiye da abinda indo taji yake ji, amma kasancewar shi namijin gaske yasa mutum zai yi tunanin bai San da zaman ta kusa dashi ba, Abin ya bashi mamaki kwarai, ta yanda yake jin kirjin sa na bugawa da sauri? daga zaman yarinyar da ko fuskar ta bai kalla ba cikin keken.




Indo kuwa ta jima idanunta a runtse kana ta ware su a hankali ta saci kallon fuskar sa, inda lafiyayyen beard din shi kadai tayi nasarar hangowa, domin ya dan juya kan sa ne, gabanta ne ya sake fad'uwa tayi sauri dauke kanta, jakar ta ta ajiye a kasa domin ta gaji, da kuma alama wajen da nisa domin sai tafiya ta ga suna yi...




Masu bada hannu ne suka tsayar dasu, wanda hakan yasa tilas duka ababben hawa dake bangaren suka tsaya, domin bawa yan dayan barin damar wuce wa...


Karan takun dokuna dake ratsa motoci suna wucewa ta fara ji, inda take ta rasa nutsuwar ta, domin tana matukar Tsoron su, daidai ta jikin adaidaitasahun su ta ga wani ya taho, saboda tsananin Tsoron da take ji ya sa ta ga kamar ita dokin ke kallo, a zabure ta manne jikinta Dana Abraham hadi da kamkame shi sosai ta boye fuskar ta a kirjin sa tace "wayyo Inna ta doki! bawan Allah kayi hakuri wallahi tsoron doki nake"




Duk da Abraham yaji wasu bakin al'amura a jikinsa amma ko gezau bai yi ba, "wacece wanna yarinyar da nake jin komai nata daban?" Ya tambayi kansa, kasancewar kuma bashi da mai bashi amsa ya sa shi kara lumshe idon sa yana jin yanda take goga masa fuskar ta a jikin sa, mai Dan sahu dake kallon su ta cikin mirror dariya ma yarinyar ta bashi...



Sai da ta daina jin takun tafiyar su kana ta dago kanta, wanda yayi daidai da bada hannu da akayi domin su wuce...




A hankali ta kalli yanda ta yamutsa masa farar Rigar sa, har kwallin ta ya bata Rigar, kunya ce ta kamata, kallon gefen fuskar sa dashi kadai tayi nasarar gani har yanzu, mamaki take ta yanda ko motsi bai yi ba, kana bai yi magana ba, ko dai kurma ne? Ta tambayi kanta, kasa tayi ta kanta a sanyaye tace "bawan Allah kayi hakuri kaji, wallahi tsoro nake ji"


Shiru babu amsa, dauke kanta tayi tana tunanin dai kurma ne, mayar da idanun ta tayi ga titi tana kallon jama'ar dake ta hada- hadar su, ga gidaje masu kyau da suke ta wujewa...

Mai adaidaitasahu yana jiran yaji Abraham yace zai sauka ya ji shiru gashi sun zo unguwar barnawa, ya kuma San idan ya tambaya ba lallai ya bashi amsa ba, kawai ya shiga cikin Layin domin sauke Indo, yana jinjina miskilanci irin na Abraham.




Daidai kofar gidan da bintu ke aiki mai keke ya tsaya, yace "yarinya mun iso, ga gidan Alhaji Umaru Kwangila nan"



Sauka Indo tayi tace "Nagode sosai ga kudin ka, amma dan Allah ka kira min lambar nan"
Amsar takardan yayi yayinda Indo ta shiga kallon gidajen Alfarman dake unguwar....


Bude gajiyayun idanun sa yayi, ganin har an zo gate din kusa da gidan su ya bashi mamaki, domin bai sanar da mai keke hakan ba, domin duk a tunanin sa a titi mai keken zai sauke shi, sauka yayi ya zaro kudi da bai San nawa bane ya mikawa mai Dan sahu ya tafi, galala mai keke yayi ganin uban kudin daya bashi, "wani irin passenger na dauko yau ni zubairu" ya fada a hankali yana kara kallon kudin, sosai kuma yaji dadi, ya kuma sa a ransa cewa daga nan gida zai wuce domin ya tashi daga aiki yau...


Indo da ta gama kallon ta ta dawo da idanun ta cikin keken taga wayam babu bawan Allah nan, yaushe ya sauka ta fada a ranta tana mamaki...


"gashi ta daga" mai keken ya mika mata wayar sa kirar vivo, fuskar sa fess kamar gonar auduga, amsa tayi tace "Adda bintu gani a kofar gidan, Indo ce."


Tana gama fadin haka ta mikawa mai keken waya, bata ma jira taji abinda bintu zata ce....


Mai keke kuwa yaja Dan sahun shi yayi gaba cikin nishadi, mintuna biyar kacal bintu ta fito da fara'a kan fuskar ta, rungume indo tayi kana ta dauki jakar Indon suka nufi gidan su Abraham, tana yaba mata da kokarin kawo kanta da ta yi....




WASAN YA SOMA GUYS>?)?



Not edited >??




Share fisabilillah

Comment for more typing




If you re interested in my group just chat me up with this number =?G?and I will add you.
07082281566


8:06am
Sunday 23, January 2022.



NoorEemaan>؋?





I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial *131*4# or
*460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.

*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call 0806626851
[10/7, 7:50 PM] =ؖ?NoorEemaan=ؖ?: ABRAHAM



WATTPAD
@NoorEemaan




ELEGANT ONLINE WRITER'S=???
'?




EDITING IS NOT ALLOWEDL'


_assalma alaikum my lovely fans, musamman wadanda basu karanta Abraham ba sanda nake typing din shi, zan kara maimaita wa Abraham ba sabon novel bane reposting nake, ban kuma buWe masa specific group ba kasancewar ba sabon typing bane, masu min magana private kan nayi adding din su a group din Abraham wasu na basu amsa Wasu kuma ban samu basu amsa ba domin abubuwan sun min yawa, to cut it short, Ban bude wa Abraham group ba, waccan maganar dana yi cewa duk mai so tayi magana ayi addinig din ta a group nayi shi ne lokacin da nake rubuta littafin, yanzu dai kara reposting nake, fatan kun gane, sai dai normal group Dina nan novels, idan kina so kya iya shiga, Ngd sosai da kaunar da kuke nunawa littafai na, jazakallahu khair_>???>?p?




Chapter 19-20

(Not edited)


K'wank'wasa karamar kofar Bintu tayi mai gadi ya leko da kansa, ganin bintu ce ya sa shi washe hakoran sa, bude musu kofar yayi suka shigo, a mutunce suka gaisa yana tsokanar Indo kasancewar shi mutum mai faram-faram da jama'a.




Sunyi dan tafiya kafin su kara so kofar da zai sada mutum da general falo, kallon gidan Indo take amma ba ta sigar kauyan ci ba, domin duk da cewa bata taba ganin gidaje masu kyau haka ba a kafatanin rayuwar ta amma still tayi behaving kanta, a kasan ranta kuwa jinjina tarin dukiyar da aka narka wurin gina wanna had'add'en gidan take...



Wani alarm dake manne a bango bintu ta danna yayi kara.

Madam Gloria dake zaune a daya daga cikin kujerun falo ta kwala Kiran daya daga cikin masu aikin ta da gurbataciyyar hausar ta , da ta dan koya a zaman ta a kaduna tace "Hajiyayye! Hajiyayye!! Zo ki Bude kofar falon nan"


Da gudu Wacce aka kira da Hajiyayye ta fito ta nufi kofar hadi da Bude wa, bintu ce ta fara shigowa kana Aysha ta biyo bayan ta cikin Sanyi da yanayin bakunta,
"ke hajiyayye! Komai ya zama neat ko? Domin banason son ya daga ko digon datti daga zuwan shi"


Cikin ladabi hajiyayye da har ta soma tafiya tace "eh madam mun gama gyara komai"


"go??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????od"

madam Gloria ta fada cikin Izza kana tayi wa hajiyayye alamar ta tafi....


Cikin isa da takama ta dago kanta, fess ta sauke su kan Indo dake manne da bintu, Wani irin mahaukacin bugu kirjin ta yayi wanda hakan har ya nuna a saman fuskar ta, take taji? tsanar Indo a ranta wanda bata taba yiwa wani mahaluki shi ba baya ga Abraham, kamar tace bata son yarinya amma ta kasa, domin ta hada duk qualities din da take so ga housemaid, amma me yasa taji wani irin yanayi a kallon farkon da ta yi wa yarinyar?

"madam ina ta gaisuwa" bintu ta katse mata tunanin ta.


Dan sakin fuska tayi kana tace "yawwa lafiya, wanna ce yarinyar?"


"eh itace madam, sunan ta Aysha"


"Ok! Ku zauna mana" ta fada a gadarance, tana kokarin controlling fad'uwar gaban da ya riske ta.


Zama suka yi yayin da Indo ke shigewa bintu domin wani mugun Tsoron matar ne ya shigeta at once, yayinda take jin gaban ta na tsananta fad'uwa....

"ya ya kike ce sunan ta?"


"Aysha"

"OK, Aysha kin iya gyaran gida, komai ya zama neat?"


"eh ta iya....."


"ki bari tayi magana ko? Or is she deaf?"


Madam Gloria ta fada tana tauna chewing gum hadi da yamutsa fuskar ta.


Shiru bintu tayi kana ta zunguri Indo alamun tayi magana, "e.... eh... eh... na iya" ta fada cikin cracking voice.


"what about cooking? ta kara tambaya tana kallon Indo, rudewa Indo tayi ta mayar ta kallon ta ga bintu, "Addah me ta ce?" indo ta fada cikin rada.


"Cewa tayi kin iya girki" kasancewar bintu na Dan fahimtar turanci duk da cewa gidan bahaushe take aiki amma yaran gidan na son Rayuwar turawa daga nan take fahimtar wasu abubuwa.


"eh.. Na iya irin namu na kauye" ta fada gwanin tausayi.


Yamutsa fuska madam gloria tayi tace "wa zai ci na kauye? Kenan baki iya ba, anyway zan kira k'warariyyar mai girki domin ta koya miki"



"toh an gode kwarai madam, zan iya tafiya ko?" Bintu ta tambaya, yayin da a ranta tana fatan Indo ta iya zama da ita domin ta lura matar ba sauki, kuma yanzu ta fahimci hakan.



"eh! Zata fara aiki gobe, aikin ta shine gyara dakin na, da na yarona, girki da gyaran kitchen that's all, sannan salary dinta 70 thousand ne duk Wata"


Jinjina kai bintu tayi cikin jin dadi domin ko ita albashin ta bai kai haka ba, ta kuma yi wa Indo murna har ranta.




"toh Indo ni zan tafi, zan dinga shigowa duba ki bayan kwana biyu-biyu ki rike halayen ki na kirki, kar naji ance kin yi wani Abu mara kyau kinji ko?"


Jinjina kai Indo tayi tana kokarin hadiye kukan ta, da haka bintu ta fita, daya daga cikin masu aikin gidan mai suna lubabatu madam gloria ta sake kira domin ta nuna Indon dakin ta.


yarinyar mai shekaru ashirin da uku ce, har da taya Indo daukar ghanan most go suka bar falon, wani huci mai zafi? madam gloria ta saki, domin tun ganin da ta yiwa indo gaban ta ke ta fad'uwa, wanda ta rasa dalilin haka.
?


Ta bangaren su Indo kuwa saman bene suka hau, inda dak'unan? Abraham ne kawai a saman , sai wani daki can karshe Inda ba kowa, inda nan madam gloria ta sa aka gyara domin indo ta zauna, saboda a amatsayin ta na mai yi musu girki da gyara dakuna boys quarter yayi nisa, a cewar ta gwara tana kusa da su ta yanda ko wani Abu ake bukata ta dafa za a fi saurin sanar mata...


Daki daya ne babba inda aka yi masa paint da pitch color wanda ya fito da kyan dakin ainun, sai toilet dake cikin dakin, babu wasu tarkace a dakin daga dan madaidaicin gado sai wardrobe, hadi da dressing mirror da babu komai a kai, sai centre carpet dake shumfud'e saman tiles din kasa, ba laifi dakin ya hadu.


"yawwa ga sif dinki nan ki jera kayan ki a ciki, amma kafin nan bari na kawo miki abinci"

lubabatu na gama fadin haka ta bar dakin....
?
Kallon komai indo ke yi daki_daki, duk da cewa dakin yayi kyau sosai, sannan ko a mafarki bata taba shiga irin wanna had'add'en daki ba, kana bata taba sanin cewa zata mallaki irin wanna dakin ba, amma bai burgeta ba, kasancewar babu Innar da yan biyun ta a kusa, take hawaye ya biyo kucin ta sak'amak'on tuno su da ta yi, tun ba a je ko ina ba har ta fara shiga wani hali na tsananin kewa, jin alamun mutum ya taho wanda take da tabbacin lubabatu ce yasa ta share hawayen ta da sauri...


Ajiye Abincin lubabatu tayi tace "ga abinci nan ki ci"

"Nagode sosai"? Indo ta fada kanta a kasa, murmurshi lubabatu tayi domin hakan nan taji lndo ta shiga ranta duk da cewa ta girme mata.
Shiru dakin ya dauka, ganin cewa indon bata ci abincin ba ya sanya ta Mikewa hadi da cewa "bari na tafi domin ki samu ki ci abincin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login