Showing 9001 words to 12000 words out of 84387 words

Chapter 4 - ABRAHAM complete Hausa novel

09 Dec 2024

28131

sa ta sanya masa abincin a ciki, duk da dadin d'and'anon da abincin ke da shi amma ji yake kamar madaci yake ci, da kyar yaci loma biyar ya kauda kansa, tayi_tayi ya kara yaki, dole ta hakura hadi da bashi ruwa ya sha, kana ta bar dakin, tana kissama abubuwa da dama a ranta....






*KAUYEN GOMBE STATE*


Haka Rayuwa ta cigaba da juyawa
su Indo da ma mutanen duniya baki daya, daga kwanaki zuwa satittika, daga satittika zuwa Watanin, a yau Anwar da Ammar suka cika Watanin uku da haihuwa, sunyi bulbul gwanin sha'awa kasancewar madaran shanun ya karbe su, ga kamanin Abraham da Nonye dake kara fitowa kullum a tare dasu..




Kamar yau Inna da Indo na zaune a karkashin bishiyar lemon tsamin dake dakin, ga su Anwar na ta bangala dariyar su a dalilin wasan da aysha ke musu, Inna da ta yi tagumi tana kallon su da murmushi hadi da jinjina tarin kaunar su ammar a ran diyar ta aysha Indo, sallamar baffa ce ta katse wa Inna tunani, direct dakinsa ya nufa, da kallo innah ta bishi domin wanna shine karo na farko daya shigo gida babu walwala a fuskar sa...


Mai da kallon ta ga Indo tayi, taga wasa take wa su Ammar bata ma lura da shigowar baffan ba, a sanyaye ta Mike zuwa dakin baffan, sallama dauke a bakin ta, amsawa yayi a hankali, kusa dashi ta zauna, cikin tsantsar ladabi, kulawa, hadi da soyaaya tace "baffan Indo lafiya? Meye same ka? ban taba ganin wanna fuskar a tare da kai ba, duk tsawon shekarun nan da Allah ya hada mu matsayin ma'aurata, Allah ya huci zuciyar ka ko zan iya sanin dalilin wanna sauyin a tare da kai"



Duk da ciwon da cikin baffa ke masa bai hana shi sakin murmushi ba, kana ya kamo hannun Innah yace "ko daya ba abinda kike tunani bane, koda an bata min rai a waje bazan zo ga iyalai na da fushi ko rashin walwala ba, Dan haka ki kwantar da hankalin ki, ciwon ciki nake wallahi tun fita ta da safe, naje kamis(chemist) din cikin gari an bani magunguna" ya fada yana fito da bakar leda mai dauke da magunguna.



Fatan samun sauki Inna tayi masa, sun zauna shiru na tsahon mintuna, idanun baffa suka sauka kan jakar da anty Sarah ta bari a bandaki, "wanna ba jakar da muka gani a bandaki bane?" baffa ya fada domin ya tabbatar.

"Eh itace" Inna ta amsa.

"dauko ta mu gani" baffan ya fada still idanunsa na kan jakar.

Dauko jakar Inna tayi, baffa ya karba ya zazzage jakar a kasa take abubuwan dake ciki suka zubo kasa...




https://chat.whatsapp.com/JwYkGXFKcLH95WSHP9QoUg
(Ga link ku shiga)








_har yanzu bamu shigo cikin labarin ba, kamar yadda na fada a farko salon Abraham daban ne da sauran novels dina, comment kadai nake bukata_


_sannan kuyi hakuri kun jini shiru kwana biyu, busy ne ya min yawa sosai wallahi, ga babu wuta transformer ya lalace, chaji nake kai wa, Dan haka ku kara hakuri, ba kullum zan dinga posting ba, Noor na muku sahihiyar kauna_=؞?






Share fisabilillah

Comment



Mai son nayi adding dinta *a Noor novelist world*
'?=???ta yi min magana ta number'n dake kasa. =?G?
07082281566






Monday, 10 January 2022


I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial *131*4# or
*460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.

*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call 0806626851
[10/6, 7:50 AM] =ؖ?NoorEemaan=ؖ?: ABRAHAM





ELEGANT ONLINE WRITER'S =???
'?





*WATTPAD*
@NoorEemaan






Chapter 13-14


(Not edited)


Wani had'add'en album ne ya fado, sai wani sarka na zallan diamond har wani kyalli yake mai dauke sunan NONYE da manyan harrufa, an kawata rubutun sunan da wani irin salo mai matuk'ar kyau hadi da Jan hankali duk wanda? yayi tozali dashi, hannu baffa ya saka ya dauki album din, shafin farko ya bud'e hoton Abraham ne yana da? shekaru goma hadi da iyayen sa da katon cake a gaban su, an yi decoration a wajen daya fi kama da hall da balloon masu kyau, wanda hakan ya yi nuni da birthday part din cikar Abraham shekaru goma aka yi.




Haka baffa ya cigaba da bud'e ko wani shafi na album din yana ganin hotuna kala?, wani ya ga Abraham shi kadai, wani ya gan su da iyayen sa da kuma madam gloria, wani ya gansu tare da dangin su, gasu nan dai kala-kala...



shafi na gaba ya bude wanda hakan ya sanya shi zaro ido cikin zallan mamaki a sak'amak'on tozali da ya yi da hoton Abraham hadi da Nonye a ranar auren su inda Nonye ke sanye da white wedding gown ta rike flower irin na bride yayinda Abraham ke sanye da suit black daya yi matukar yi masa kyau ya kuma fito da halittar sa na karfaffa kuma lafiyayyen namiji, duk da babu murmushi a fuskar sa hakan bai hana hoton yin kyau ba, sannan hoton ya fito da fuskar su tarr.



Abinda ya bawa baffa mamaki shine hango tsantsar kamanin yan biyu a tare dasu Abraham, take zuciyar sa ta raya masa cewa wadannan sune iyayen ammar da Anwar, amma meya dalilin raba su da akayi? Sannan a wani hali suke ciki a dalilin rasa gudan jininsu? Meye kuma dalilin daukar su da anty Sarah tayi zuwa nan ta ajiyesu? Tabbas yana bukatar sanin wadannan amsoshin...




Kasa cigaba da kallon hotunan yayi, domin album din babba ne, hoton masu yawan gaskiya ne, ga kuma jikin sa daya mutu "baffan Indo da alama iyayen Ammar ba Muslimai bane daga yanayin su" Innah ta fada cikin tabbaci.



Jinjina kai baffa yayi kana yace "tabbas ba karya, abinda ke raina Kenan, na kuma kara tabbatar da hakan ta dalilin matar da ta ajiye su ta gudu yanayin shigar ta kadai ya isa ya sanar da hakan, dama haka Allah yake ikon sa, ya fitar da mummuna daga cikin kyakyawa, haka Zalika zai iya fitar da kyakyawa daga cikin mummuna, banda ikon Allah 'yayy'an da iyayen su ba Muslumai, amma gashi sun shigo cikin Rayuwar Muslimai"


Jinjina kai Inna tayi cikin tabbaci, numfashi baffa ya sauke yace "ina ganin wannan album din zai taimaka mana kwarai wurin nemo iyayen su, in sha Allah zuwa gobe idan naji dama-dama zan fita cikin gari domin nemo gidan talabijin(television) ko redio domin mu bada cigiyar su, har ga raina banason rabuwa da yan biyu, domin ina so su taso cikin hasken musulunci amma hakan bazai hana mu nemo iyayen su ba saboda bamu San a wani halin damuwa suke ciki ba, kuma in sha Allah idan suna da rabo?zasu samu shiga muslunci...."



"Assalama alaykum Innah ki........ laa baffana yaushe ka shigo" Aysha da ta shigo yanzu ta katsewa baffa maganar sa.


Murmushi baffan yayi kana yace "indon baffa Kenan, ai yanzu kin daina ji da baffan ki sai su Ammar" dariya tayi cikin jin kunya.


Mika masa Anwar dake ta tsalle yana kallon baffa tayi, kana ta zauna kusa dashi rike da ammar, take idaunta suka sauka kan sarkan Nonye, hannu tasa ta dauka kana cikin murna tace "wayyo baffa siyomin kayi, kalli kaga sai daukar ido take" ta fada cikin murna da yarinta.



"ke! ajiye" innah ta fada a dan kausashe

rau rau tayi da ido kana ta mai da dubanta ga baffa tace
"baffana"
a shagwab'e...

"ki bi maganar Innar ki kin ji ko ? Baya ga haka gobe nakeso In sha Allah naje na bada cigiyar iyayen su Ammar da taimako sarkan nan hadi da photo album dinnan, dan haka ki ajiye kinji idan naje cikin birni zan siyo miki mai kyau"



Ihu Indo ta fara yi hadi da shure? ita fa ba za a raba ta da su yan biyu ba, cikin fada Innah tace " ke rufemin baki a wajen kafin na make ki, ke kin san dadin su bakya son rabuwa dasu, mahaifan su fa? kin San a wani hali suke ciki? Kin San wani radadi suke ji a halin yanzu? mu kan mu bamu so rabuwa dasu ba, amma tunda mun samu shaida dole mu sada y'ayy'an ga iyayen su"



*1 hour later*

Ganin da gaske kukan yaki karewa ya sanya baffa yiwa inna sigina kana yace "yi shiru Indon ta baffalle, mun ji mun hakura bazamu raba ku ba, maza share hawayen ki"


Shiru tayi tana k'amk'ame Ammar hadi da sauke ajiyar zuciya, daga nan su Innah suka shiga Jan ta da hira domin ta manta da komai, ai kuwa ta saki jikin ta ta cigaba da wasan ta da su Ammar, fita tayi waje da ammar a hannun ta, still sarkan nan na zaune daram a ranta...



ganin fitar Indo ya sanya baffa kallon Inna yace "dole cikin dabara zamu fitar da yaran ta yanda Ayshatu ba zata gane ba, idan Allah ya bayyana iyayen su yaran nan"




Dariya Inna tayi tace "gaskiya dai, in ba haka ba rigimar Indo yafi karfina"




Murmushi baffan yayi yana kara jin kaunar tilon 'yarsa na shiga zuciyar sa.





Da magriba baffa ya lallaba ya tafi masallaci domin yana jin ciwon cikin na lafawa, anjima ya fara, Inna kuma ta shige bandaki? domin kama ruwa, sadaf-sadaf lndo ta shige dakin baffa ta dauki jakar nan kana ta koma dakin ta, bude jakar tayi ta dauki sakar kana ta mayar da zip din ta rufe bata damu da ko kallon album din ba, zata fita ta mayar da jakar kenan, taji motsin Inna ta fito hakan yasa cikin sauri ta cusa jakar kasan kayan ta sannan ta raya a ranta cewa anjima zata mayar idan Inna ta shige bandakin, sarkar? ta saka a wuyanta hadi da mayar da hijab dinta jikin ta, dama tunda ta yi Wayo bata fiye zama ba hijab ba....


WASHEGARI
6:00am

Bayan baffa ya dawo daga sallar asuba yaji ciwon cikin nasa ya matsa masa gadan-gadan ya kuma kara shan maganin yaji ciwon bai lafa ba, hankalin su innah ya tashi sosai, ga yan biyu dake ta kuka sosai wanda ya kara dagawa su Innah lissafi...

*kullun nafsin za'ikatul maut* da misalin 9:00am na safiyar juma'ar baffa ya amsa Kiran ubangiji, mutuwar data girgiza dubban jama'a, inda kowa ke masa fatan ya dace domin yayi mutuwar shahada, Inna tayi namijin kokari wurin danne zuciyar ta matuk'a, domin ko kuka bata yi ba, sai na zuci daya fi na fili ciwo, yayin da Indon baffa ta sha kuka har da suman ta, domin kowa yasan tarin kaunar dake tsakanin su, haka suka hakura suka fawwalawa Allah lamarin su, sannan suka bi baffa da addu'a domin abinda ya fi bukata Kenan....



*************************



BAYAN KWANA ARBA'IN

A yau baffa ya cika kwana arba'in da rasuwa, zuwa yanzu su Inna sun hakura har su fara sabawa da rashin 6affa, amma yana nan daram a ransu, domin manta baffa ba abu bane mai sauki, zai kasance a ransu har abada, Bayan an gama addu'o'i, an raba abin sadaka mutane duk sun tafi, amma banda yan'uwan baffa da suka rage, dakin Inna suka shige, inda wan baffa mai suna sule ne a gaba, kallon Inna da ta rame sosai yayi, cikin gadara yace "baya ga wanna shanayen guda biyar da rago biyun nan ina sauran kadaran Mijin ki"



A sanyaye Inna tace "yaya babu komai, baya ga abinda ka lissafo sai gidanan babu wani kadara da ta yi saura"



"toh ai shikenan, shanayen zamu tafi dasu, eh zamu tafi da su, domin mu ma dole mu ci gadon dan'uwan mu, ke da yarki Kuma ku rike rago biyun nan" yana fadin haka ya fita, sauran suka mara masa baya, wasu hawaye masu zafi inna taji sun zubo mata, meyasa mutanen yanzu suka shagalta da son duniya suka manta da lahira, yaushe baffan ya rasu da har zasu hau kan gadon sa? Hakika mutuwa tayi musu yankan kauna, da yan biyu basu yi wayo ba, dame zasu dinga shayar dasu tunda sun kwashe shanayen? Inda taji dadi sun dan fara cin abinci kadan? Indo dake kallon inna ta share mata hawaye, domin duk da kananun shekarun ta amma ta fahimci wasu abubuwan dake faruwa...



*************


A haka suka cigaba da Rayuwar su cikin rufin asirin Allah, da tafiya tayi tafiya kudin hannun Inna ya kare, dole basu da zabi daya fi su siyar da ragunan biyun nan kacal, kayan abinci Inna ta siyo, wanda ta San zai dade musu kafin ya Kare...




*IMO STATE*

Sanye yake da wando 3quarter blue-black, da riga body hug fara daya yi matuk'ar yi masa kyau, zaune yake kan daga daya cikin had'add'un kujeran daya kara k'awata falon, idanunsa a lumshe tamkar mai yin bacci, madam Gloria dake gefensa a zaune ta kurawa plasma screen din ido wanda ba wani kallo take ba, lokaci zuwa lokaci tana juyowa ta jefa Abraham da wani irin kallo mai dauke da ma'anoni masu tarin yawa...



Bata zata ba, bare tsammani ta tsinci muryar sa kamar kullum cikin turanci domin bai fiye magana da igbo ba yace "mummy cikin satin nan zamu bar imo zuwa? kaduna state , bazan juri cigaba da zama a nan ba kuma, I think zan fi samun peace of mind idan nayi nesa da Imo, I want to start a new life, already na siyi gida da duk wani abun bukata a can" ya karasa ko motsi bai yi ba, kai ka rantse bashi yayi magana yanzu ba.



Gaban madam Gloria ya fadi ras! Cikin tashin hankali tace "why son? You can still live a better life here, just forget about the the past and face the future, you re too young for all this, and why did you even prefer Northern state, if you don't want to stay here in Imo, then we can move to delta state or other Eastern state, but why kaduna uhmm son?"



Boyayyen ajiyar zuciya ya sauke, shi ma bai San meye zo kan shi ba, hakan nan shi ma yaji yana son zama a arewacin Nigeria, abinda bai taba bashi sha'awa ba Kenan, amma yanzu yaji zaman imo ya fita a ransa gabadaya, dama baya da???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? company ko daya a garin, baya ga gidan nan, wanda shi ma ya riga ya siyar dashi ga wani attajiri.




Mikewa yayi tsaye yana gyara zaman rigar sa kana ya bar wajen cikin takun sa na lafiyayyen namiji mai ji da kuruciya...


Da wani mugun kallo madam Gloria ta bi bayan sa har ya bacewa ganinta, ta San cewa shi din kaifi daya ne, baya magana biyu, Kwafa taja kana tace "da Sannu kai ma zaka bi bayan Nonye na more duniyata Dan taurin rai kawai, kaje ka siyi gida a wani gari ban sani ba sai yanzu, babu abinda ya bari a halin shegiyar uwar sa"






*I WEEK LATER*
Kaduna state unguwar barnawa



Yau kwanan su Abraham uku da dawowa kaduna, duplex house ne da ginin ya tsaru sosai, yayinda aka zuba abubuwan k'awa a ko wani lungu da sako na gidan, fadin kyau da haduwar gidan bata time ne, just mai karatu ya yi imagine din gidan masu hannu da shuni.


Zaune madam Gloria take a had'add'en kuma yalwataccen falon kan daya daga cikin kujerun, ta harde kafa daya kan daya tana shan wine, ta chaba ado sosai tamkar zata je gidan biki yayinda take latsa tsad'ad'iyyar wayar hannunta kirar iPhone 13promax.



ABRAHAM ne ya fito daga saman bene inda nan ne bangaren sa, sanye yake da kananun kaya ga key din mota a hannun sa da alama fita yakeson yi, dagowa madam Gloria tayi cikin fara'a tace "my handsome son, ina zaka je? Gashi ina son mu yi magana, na fadawa musa mai gadi ya nemo yan aiki, yace min akwai Wata mai aiki a gidan dake jikin namu, ya fadamaka, ta ma zo mun yi magana tace a bata nan da 1 week zata nemo su



"zan fita shopping ne mummy, idan na dawo zamu yi magana" ya amsa mata a takaice kana ya bata side hug ya fita cikin sauri, mota ya fada, sabon mai gadin su musa ya wangale masa gate din ya fita, duk da bai San ko ina a garin ba, amma ya San bazai bata ba, tunda yanzu duniya ta cigaba, kuma in dai mutum ya iya karatu an gama, goggle ya shiga yayi browsering nearest supermarket, take kuwa goggle ta fito masa da ita, wuta ya bawa motar ya harba kan kwalta....


WANENE ABRAHAM?.....






*Note*

(karfa ku manta da yaren igbo hadi da turanci madam Gloria da Abraham suke duk Wata magana, ina yawan amfanin da hausa ne domin mai karatu ya gane, sannan ya fahimci inda labarin ya dosa)




Share fisabilillah


Comment for more typing...




Noor>؋?
07082281566




I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial *131*4# or
*460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.

*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call 0806626851



d'
=?%?d'
=?%?d'
=?%?d'
=?%?d'
=?%?d'
=?%?
_Kamar yadda na fada, Abraham ba sabon Novel bane, hakan ne yasa ban bude masa group na musamman ba, ma'ana group iya posting Abraham din, amma saboda massages na min yawa kan ana son na bude group, amma ban bazan iya bude wa ba gaskiya, domin bana son tarkarcen groups da yawa, Ina da dai group Waya na novel wanda ga link nan zaku iya joining, Ngd sosai jazakallahu Khair, ina godiya da soyayyar da kuke nuna wa books dina_.


Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JwYkGXFKcLH95WSHP9QoUg
[10/6, 7:51 PM] =ؖ?NoorEemaan=ؖ?: #NoorEemaan


ABRAHAM

*First edition*



https://facebook.com/groups/943534712916776/

Masu amfani da Facebook sai kuyi join wan nan link din




ELEGANT ONLINE WRITER'S =???
'?





*WATTPAD*
@NoorEemaan



Banyi editing ba>??



Chapter 15-16

Asalin Abraham dan kabilar igbo ne na jihar imo state, haka zalika iyayen sa, mahaifin sa (Patrick Samuel) shahararren dan kasuwa ne, wanda duniya ta San da shi, inda ya hadu da mahaifiyar Abraham (Victoria) a wani bussiness trip daya je Canada, inda ita kuma Victoria tana hada master's dinta ne a lokaci, inda ita ma yar mai kudi ce domin mahaifinta babban

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login