Showing 72001 words to 75000 words out of 84387 words

Chapter 25 - ABRAHAM complete Hausa novel

09 Dec 2024

28143

zata.



Tace zata je duba ?a?an ta sannan ta Wora musu breakfast.

Yaki yarda yace ta kwanta ta huta, zai je yayi duk abinda ya dace ta yi.

Ba dan ta so ba ta amince, ya kwantar da ita ya fita, bayan ya sake kissing dinta... tun idanun ta biyu har bacci ya dauke ta dama akwai sauran gajiya a jikin ta.


Abraham yana sauka ya ga mai aiki na gyara falo, cikin girmamawa ta gaishe shi ya amsa, kana ya shige dakin su Ammar.

A nutse ya tarar suna bacci, Anwar har da Wora wa Ammar kafa a baki amma haka suke manne da juna, dariya yayi mara sauti yana girgiza kansa kana ya karasa a hankali ya gyara musu kwanciya hadi da basu sumbata a goshi sannan ya fita.



Kitchen ya shiga, hannu ya dora a kugu, shi kam idan akwai abinda bai iya ba ko yake bashi wahala toh girki ne.


Dankalin turawa ya fara ferewa, ferewar ma abin dariya domin sai ya haWa dankali da bawo mai yawa ya fere ya zubar, bayan ya gama ko gishiri bai barbada ba ya shiga suya.
Bayan ya gama da dankali, ya fasa kwai goma ya saka albasa, attaruhu, da maggi da sauran kadan ya yi yawa a cikin kwan, kana ya hau suya, bai bari kwan ya soyu ba ya juya shi hakan yasa ya hargitse, dan bata fuska yayi irin ba haka na so ba.



Bayan nan ya kwashe, ya haWa da dankalin a warmer daya ya kai dining ya dawo, sannan ya tafasa ruwa a kettle ya juye a flask ya Kai dining domin shikam bai iya dafa irin shayin ta ba, ya kuwa haWa duban gumi, kamar wanda ya tuka tuwon mutane talatin.



Ya fito daga kitchen kenan yaga mai aiki tana kokarin komawa bangaren su, dama aiki kadai ke shigo dasu Sangaren nan, saboda hatta girki a bangaren su suke yi, domin akwai komai a wajen, Idan sun girka sai su zubawa mai gadi da mai gyara farfajiyar gida, kuma lafiyayyen abinci suke yi.

Yace mata "Wan gyara kitchen dinan please"

Cikin girmamawa ta amsa kana ta nufi kitchen din, a ranta tana jinjina saukin kan shi.



Dakin su Ammar ya leka ya tarar da sun tashi, da gudu suka fada jikin sa wanda ya ji dad'in hakan, suka gaishe shi ya amsa cikin tsananin son su,
Kana ya cire musu kaya suka nufi banWaki domin yi musu wanka.

Ta bangaren Aysha kuwa ita ma a daidai lokacin ta tashi, mikewa tayi ta kalli dakin babu ko datti sai gadon daya hargitse a hankali ta shiga gyarawa, domin Abraham ya sanja bedsheet tun jiyan, bayan ta gama ta cire rigar jikin ta, ta daura towel inda hannun ta ya taba sarkan wuyan ta, dan shiru tayi kana a hankali ta sa hannu ta cire sarkan, ta kuma yi hakan ne domin tasan ganin sarkan zai dinga yawan tuno wa Abraham da rayuwar sa ta baya...



Ruwa mai zafi ta haWa wa kanta tayi wanka kana ta fito ta shirya cikin wata gown ta atamfa mai ruwan ja da dark blue daya yi matukar karban farar fatar ta.



Powder da kwalli kadai ta saka, sannan ta yi simple dauri daya fito da gashinta ta baya.

Flat shoe red color ta saka yayi matu?ar yi mata kyau, musamman da jan kunshi kafar ta da aka mata a lokacin biki mai sellotape ya sake maroon.



Turare ta fesa sama-sama kana ta bude kofar ta fita, hakan yayi daidai da fitowar Abraham daga dakin sa da alama shima wanka yayi sai zuba kamshi yake, ga su Twins da ta hango zaune daga falon kasa a shirye su ma.



Sakin baki Abraham yayi yana kallon Aysha, domin bata taSa yi masa mugun kyau irin wanna ba, cikin sauri ya karaso gabanta ya daga ta cak ya shiga juyi da ita yana fadin
"You re so beautiful ?wammmmmmmmm!"




*AYSHA*
Rike shi tayi da kyau tana dariya, wanda dariyarta ta ja hankalin su Ammar, da gudu suka hau saman suka yi tsaye suna dariya suma, sai da Abraham ya gaji dan kansa kana ya sauke ta, sannan suka sauka kasa gaba-daya.



Bayan duk sun zauna, Aysha ta bude warmer domin serving din su, sai dai yanda taga dankalin yayi wani iri yasa wata dariya da bata shirya zuwan sa ba yazo mata, Abraham kuwa bata rai yayi cikin wasa shi da yake jiran ta yaba masa.



"Sorry" tace tana rufe bakin ta, girgiza kansa yayi irin zan kama ki dinan.

Murmushi tayi kana ta shiga zubawa kowa, sannan ta haWa tea mai kauri wa kowa amma banda Abraham domin shi ya fi son Black tea.
Ta saka masa Lipton mai flavour din mix fruit, sai ta saka masa two cube of sugar.


Kusan a tare ita da Abraham suka kai lomar farko na abincin baki ba tare da sun hadiya ba...


kallon-kallon suka shiga yi a junan su kana suka fashe da dariya a lokaci daya, saboda yanda dandanon abincin yayi wani iri ba dadi, amma su twins basu damu ba ci suke sosai...



Ai kuwa Abraham da Aysha basu iya cin dankalin ba, gwara ma kwan sai shayi da suka kora dashi.



******



Abraham kuwa yau yaki fita office, wai zai kula da AYSHA duk da tace masa lafiyar ta kalau, amma yaki, sun kasance cikin farinciki da annushuwa har dare musamman da su Twins ke nan hakan ya kara wa abin armashi.





*TWO MONTH LATER*

A gidan Abraham kullum cikin farinciki suke, ga wata ingantacciyar dangantaka mai dauke da zallan so da ke kara wanzuwa a tsakanin su. Aysha ta jajirce sosai wurin ganin komai da zai kawo farinciki a gidan tayi shi.


Kamar kullum, a kowacce safiya da bayan sallar asuba sai Aysha ta yi wa Abraham karin Alqur'ani, duk da yana zuwa daukan karatu wurin limamun da ya karbi Musulunci, Amma tana kara masa da kuma wasu littattafai addini.


Kamar yau zaune take da farin hijab yayin da Abraham ke sanye da jallabiya baki suna fuskantar juna, dukkanin su da qur'ani dauke a hannun su.
Bayan ta gama biya masa kusan sau biyar, tana jiran shima ya biya ta ji ko ya rike, ya fara biya mata ayar farko kenan taji muryar sa na rawa kana kuka ya kwace masa...



A matukar rude ta ajiye qur'anin a gefe ta matso sosai ta shige jikin sa, hannun sa daya rufe fuska dashi ta cire, cikin sanyin murya tace


"what's it? Why are you crying"

Shiru bai bata amsa ba, Aysha ta kafe shi da ido kwalla na cika idanun ta, tasan halin mijin ta, ta sani cewa ba ?aramin abu ne zai sa shi kuka haka ba.




Fuskar Aysha ya riko cikin tafin hannun sa, hawaye na zuba a idanun sa yace

"my parent are not Muslims...you no they love me a lot... and i love them too. Everyday before my dad dies he always tells me he loves me, my parents are dead! Where are they today? You could pray for your parents, but i can't pray for my parents.
This is the reality, don't underestimate the blessing Allah subhanahu wata'ala has given you"



(Iyayena ba Muslimai bane, kin San Ina kaunar su sosai, su ma suna kauna ta, a kullum mahaifina kafin ya mutu ya kan ce min yana sona. iyayena sun mutu, a wani makoma suke yanzu?
Ke zaki iya yiwa Iyayen ki addu'a, amma Ni bazan iya mu su ba, domin wanna shine gaskiya, kada bawa ya butulcewa albarka da Allah yayi masa)


Jinjina kai Aysha take tana kuka, domin tabbas dukkanin maganganun sa babu karya, ta kuma tausaya masa ainun, hakika duk wanda yake cikin Musulunci ya godewa ni'imar da Allah ya yi masa.



Hannu tasa tana share masa hawaye amma hawayen yaki tsayuwa, kamar ba Abraham ba.

Ganin kukan sa na taba zuciyar ta sosai, hakan yasa babu zato bare tsammani ya ji Aysha ta kama lower lips dinsa tana kissing din sa for some minutes kana ta hade bakin su waje daya, cikin aminci suka fada duniyar ma'aurata.


Bayan sun dawo nutsuwar su sun yi wanka, Aysha na kwance a jikin sa, yayinda Abraham ke shafa gashin ta in a circular motion ya tsinci murya ta mai dadi tace

" ina rokon wata alfarma daga gare ka, dan Allah, domin rintsi komai wuya Kada ka bari su Ammar su san cewa ba nice mahaifiyarsu ba, wallahi ranar dana fara ganin su na kamu da son su sosai, bana so su dauka cewa basu da uwa a duniya, bana so suyi kukan maraici ta wajen uwa Please"


A hankali ya ware idanun sa, ya kara shigar da ita jikin sa, murmushi dauke a fuskar sa na farincikin samun life partner kamar Aysha, son ta mai zafin gaske na sake ratsa shi yace

"?wammmm! Har abada kece mahaifiyar su Ammar, i swear wasu lokutan ina manta cewa ba kece uwar su ba, in dai wannan ne, baki da damuwa"



Murmushi mai sauti tayi cikin jin dadi, kana ta lumshe idanun ta, babu jimawa wani bacci mai dadi gasken ya dauke su kusan a tare...





*Laifi dadi karewa=?? one more page left fans*






Share share share fisabilillah

CommentI'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial *131*4# or
*460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.

*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call 0806626851




NoorEemaan('
07082281566
[10/13, 2:50 PM] =ؖ?NoorEemaan=ؖ?: ABRAHAM


*First edition*




*WATTPAD*
@NoorEemaan



https://facebook.com/groups/943534712916776/
Masu amfani da facebook su yi join ta wanna link din.


_@sis Mariam jumare, @Ak saraki, @sdeentm, ina godiya sosai da sosai, hakika kuna taimaka min da posting tun daga farkon fara posting book din nan har harshe ba tare da gajiyawa ba, Allah ya sa muku da alkhairi_.>?
?d'?>?
?



Alhamdulillah
#ending


Chapter 71-72


Baccin awa daya kadai suka yi. Abraham ne ya fara tashi, ya kura wa fuskar Aysha ido, gani yayi ta kara haske sosai kamar ka taba ta jini ya fito, har kumatu ta ajiye kai kace kwai ta boye a ciki, gwanin sha'awa da kyau.

A hankali ta fara buWe idanun ta...karaf idanun su suka sarke dana juna, murmushin ta mai kyau ta sakar masa, ya sumbace goshin ta sannan ya mayar mata da martani yace
"Nwunye mm" (my wife/matata).
Murmushi tayi domin a duk lokacin data ji yayi yare abin burge ta yake, har tana ji dama ta iya ita ma.

"Meye ma'anar abinda ka fada yanzu" Aysha ta tambaye shi cikin turanci.
"It means my wife" ya mayar mata da martani.
Jinjina kai tayi alamun ta gane kana tace

"I love You so much my husband"
Cikin zallan mamaki Abraham ya kafe Aysha da ido, sai yake jin kamar kunnuwan sa ne basu jiye masa daidai ba, Aysha ta fahimci hakan sai ta kara maimaita masa tana kifa kanta a kirjin shi...
Wata wawuyar runguma ya sake mata, duk da tana saman kirjin nasa ya shiga birgima da ita kan gadon kamar wasu kananan yara sai faman dariya suke.

******************

Haka rayuwar su ta cigaba da tafiya, A kullum kaunar da suke wa juna kara yawa take.

*ANTY SARAH*
Bayan ta koma kauyen su, a ranar tayi kuka sosai kamar ranta zai fita, tayi nadamar mugayen halayen ta na baya ya fi cikin kwando.
Kudin da ABRAHAM ya bata da shi ta fara sana'a inda anan take samu tana rufawa kanta asiri, amma bata jin dadin komai a rayuwa, sakamakon mugayen halayen ta na baya, domin hakkin rai ba wasa bane, duk da ba ita tayi kissan ba, kullum cikin kuka da nadama take, a haka ta cigaba da rayuwar ta...

Bayan kwana biyu Abraham yayi musu booking flight suka je har wajen dangin iyayen sa, abin mamaki sun karbi shi hannun biyu-biyu, duk da ya sanar da su ya zama muslumi sannan ya auri Hausa Fulani
Ya basu labarin Madam Gloria, sun kuma yi mamaki da Allah wadai da mugayen halayen Madam Gloria.
sannan sun karbi Aysha a matsayin suruka a gare su, sosai Abraham yaji dadi dama tsoron sa kenan kada a samu matsala, kuma gashi alhamdulillah an samu akasin haka. Hak'ik'a addu'a bata taSa faduwa kasa a banza...



*****&**********&******


*SOME MONTHS LATER*

A parking lot ya daidaita parking din motar sa kirar Mercedes Benz white color, kana ya fito rike da brife case a hannun sa, ya kara kyau hadi da dan jiki kadan wanda yayi matu?ar amsar sa, rufe motar yayi kana ya nufi cikin gidan.

Sallama dauke a bakin sa ya shige falon, inda ya tarar da Ammar da Anwar sun baza littafan su da alama home-work suke, da gudu suka ruga jin muryar mahaifin su suka dane shi, cikin kaunar ya'yan sa ya rungume su yace
"Uma aka mm how are you doing?" (Y'ay'ana ya kuke)

"We are Fine Daddy" suka amsa a tare, domin yana dan koya musu Igbo, kuma yaran na da kunnen ji, domin suna saurin rike wa.

Sauke su yayi ya shafa kan su... rarraba idanun sa ya shiga yi amma bai ga abinda yake nema ba.
Kallon su Ammar yayi yace "where is Ammuh?"

Suka ce "tana bacci".

Jinjina kai yayi cikin tausayin ta kana ya nufi saman, a ko ina zai fada cewa matar sa jaruma ce, domin duk da cikin ta ya tsufa amma haka take ?o?arin kula da su daga shi har su Ammar, wani zubin sai ya bata rai take barin aikin, domin shi kam tausaya mata yake amma ita kam ce masa take tana jin dadin aikin, wai motsa jiki take.

A hankali ya sanya kafar sa cikin dakin sanyi Ac da dadaddan k'amshin dakin ya bugi hancin sa, lumshe ido yayi kana ya ware su kan Aysha dake bacci da tulelen cikin ta haihuwa ko yau ko gobe.

Gaban gadon ya karasa ya zauna a kasan tiles ya tankwashe kafafunsa, kafar ta daya kumbura ya sumbata kana ya shiga yi mata tausa tsawon Mintuna goma, sannan ta motsa, cikin sauri ya matso gab da ita, yace "You re awake"

Jinjina masa Kai tayi tana Murmushi, dan kara kan sa yayi kan cikin ta dake ta motsi yace "how are my babies doing?"

Cikin shagwaba tace "babies? "

Dariya yayi yace "yes nah"

Dan ture kanshi tayi kana tace "i'm carrying baby, not babies" ta fada cikin iyakar gaskiyar ta, domin idan yace babies dinnan tsoro yake bata.

Dan girgiza kan sa yayi da murmushi kan fuskar sa, ya lura ta koyi rigima kwanan nan. Hannunta ya manna wa sumbata yace "A h?r? m g? na ?ny? ?wammm, i mara mma"
(I love you my life, you re beautiful)

Dan far da ido tayi cikin jin dadi, a duk lokacin daya ci mata yana son ta, tana da kyau wani girma kanta keyi, duk da cikin ya sata dan muni amma bai fasa gaya mata haka ba, kullum a sallar ta sai tayi godiya ga Allah daya bata miji kamar Abraham, ko a aljanna tana fata da addu'a ya zama miji a gare ta.


**********************



_*INNAH*_

Ta bangaren ta kuwa Abraham ya siya mata gida a nan Kaduna domin ta dawo kusa da su, amma tace ita kam bata so ta fi zama a tushen ta, Abraham ya bawa Anty Bintu gidan halak malak saboda hallacin data yiwa rayuwarsa (Aysha).

ANTY Bintu tayi godiya ba iyaka, tana kuma taya Aysha murnan samun miji Waya tamkar da dubu.

Abraham bai kyale Inna ba sai daya sa aka fasa gidan ta na Gombe aka dawo mata da komai ginin zamani, sannan ya bata kudade masu yawan gaske ta fara business. Inna fa ta dawo yar business ta yi sharrrr ta ita ainayin skin color dinta ya fito saboda jindadin rayuwa da kwanciyar hankali da ta samu .

Yan'uwan su baffa da suka ji Inna tayi arziki suka kwaso kansu suka zo suna bata hakuri cikin borin kunya, Inna abu Waya ta duba ta yafe masu darajar mijin ta baffa duk da baya raye, amma har gobe kaunar mijin ta na manne a ranta.

Wanna kenan.


____&________& __


_*2:00pm*_

malam bahaushe yace dare mahutan bawa, ko ina yayi tsit sakamakon baccin da mafi yawan mutane ke yi, hakan take ga su Abraham, domin kwance Aysha take ta Wora kanta kan kirjin sa suna baccin su cike da nutsuwa, can cikin bacci Aysha taji kamar wani abu ya karce ta, a dan zabure ta mike zaune, nan ta kara ji mararta ta kulle sosai, yarfa hannun tayi tana cije labb'an ta, domin zafin ya fara zama unbearable, hakan yasa ta saki kuka, ta shiga girgiza Abraham...

A rude ya tashi ganin tana kuka ya tada hankalin sa, take ya fahimci nakuda ce ta zo, cikin sauri ya mike ya buWe sif dinta ya dauko mata daya daga cikin maternity gown dinta ya sanya mata, sannan shima ya saka riga da wando, mukullin mota ya dauko da jakar da suka hada kayan haihuwa kana ya dauke ta kamar yar jaririya suka sauka kasa...
Gaban Mota ya buWe ya saka ta a ciki bayan ya kwantar da kujerar, sannan shima ya shiga ya danna horn wa mai gadi dake gyangyadi, a 360 mai gadi ya buWe kofar Abraham ya cilla hancin motar sa waje, yama manta da su Ammar dake bacci a dakin su, Burin sa a yanzu shine matar sa ta rabu da wanna zafin da take ji.

Had'add'en private hospital ya kawo ta, inda cikin sauri da sanin makamin aiki suka karbe ta, kana suka yi *maternity ward* da ita ba tare da sun yarda ya shiga ba.

Safa da marwa ya shiga yi fuskar sa na bayyana tsananin damuwar da yake ciki, fata da muradin sa Aysha ta dawo gareshi, domin bazai iya juran rasa ta ba.

Daga karshe ma famfo dake cikin asibiti ya nufa yayi alwala kana yaje mota ya dauko sallaya ya dawo ya fara nafilfili...

Bayan ya gama ya zauna kan sallayar yana addu'o'in sa, ya ga wata nurse ta zo wajen shi murmushi dauke kan fuskar ta, boyayyen ajiyar zuciya ya sauke kana ya mike cikin sauri yana tambayar ta ina matar sa, nurse ta sake Murmushi tace
"congratulations sir, please come with me"

Nan Abraham ya bita zuwa dakin hutun da aka mayar da Aysha kamar zai tashi sama... Bakin kofar nurse din ta tsaya ta nuna masa ya shiga dakin yayinda ita kuma ta koma domin kula da wata patient da aka kawo Sakamakon barin cikin da ta yi, dama haka rayuwa take, wani yana farinciki at the same time wani yana kuka.

BuWe

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login