Showing 30001 words to 33000 words out of 84387 words

Chapter 11 - ABRAHAM complete Hausa novel

09 Dec 2024

28132

ji a tare da ita ba, amma tabbas yanayin bazai misaltu ko ya fadu ba.





Aysha kuwa tun tana duniyar tunani har jikinta ya fara saki sak'amak'on baccin daya fara dibar ta, gyangyadi ta fara yi gwanin burgewa da dariya wanda hakan ya kara bayyana yarintar ta, babu? jimawa ta sulale kasan tiles din, wani bacci mai dadin gaske yayi awon gaba da ita ba tare da ta shirya ba.




ABRAHAM
Kallon ta yake tamk'ar ya samu hoto, domin ko kyafta idanunsa baya yi, kyawawan labban ta da ta tsuk'e yafi komai Jan hankalin sa musaman da ta dan turo shi gaba kad'an, cigaba yayi da Kallon ta har ya dauke idanunsa a kanta, ya Lumshe su hadi da yamutsa fuska domin ya gaji da zaman wheelchair din.




_1:22am_

Sanyin tiles ne ya shiga ratsa ko wani sassa na jikina sosai, wanda hakan yasa ta motsa hadi da ware idanunta, cikin sauri ta Mike domin Sam bata San cewa baccin ya dauke ta ba, a hankali ta kai idanunta kan shi, inda taji wani mugun tausayin sa, ace mutum tun safe yana zaune waje daya bai motsa ba.



Mikewa tayi kusa dashi taga idanunsa a rufe yana bacci, tunanin taimaka masa wurin kwanciya tayi, sai dai ta rasa yanda zata fara, domin shi din ingarman namiji ne, duk da cewa yayi jinya amma bai yi loosing weight ba sai idanunsa kadai da suka fada ciki....




Hak'ik'a ko wani bawa da zaka gani yace abu kaza yafi karfin shi, ko ya dinga tunanin anya zai iya? Toh sai dai idan mutum bai sa kansa ba, amma matukar kasa kanka Allah zai taimaka maka, domin ubangiji baya taba dora wa bawa Abin da yafi karfin sa...

Misali Kamar Aysha Kenan ta kara matso da wheelchair din kusa da gadon sosai ya zamana babu wani sauran space tsakanin gadon da kujeran, sannan tayi kamar zata kife kujerar da dukanin karfin ta, sai ya fada kan gadon, kasancewar gadon bai da mugun tudu sai fadi hakan ya sa ta samu saukin kwantar dashi, sai dai yayi ruf da ciki, tsaye tayi tana sauke numfashin gajiya kamar wacce tayi tseren gudu, zaman wheelchair din ta gyara kana ta rufe shi da duvet bedsheets, a hankali ta shiga takawa cikin sanda domin barin dakin gudun kada ya farka....




*ABRAHAM*

Sai da daya daina jin motsin ta kana ya bud'e idanun sa, da suka bata hours a Lumshe ba kuma dan bacci yake ba, duk abinda tayi yana jin ta, daga kwantar dashi data yi har zuwa fitar ta daga dakin, dan cije labb'ansa yayi saboda wani zafi da yake ji daga cikinsa, ba kuma komai ya janyo hakan ba sai irin yanda Aysha ta kwantar da shi, wanda kuma ya jinjina k'ok'ari da jarumtar ta, haka ya cigaba da jurewa har bacci ya dauke shi...




Manage pls, kaina ya dauki chaji, ban da time wallahi, ina wajen aiki, gashi yau ina Azumi, may be kuga typing errors... >??






Share fisabilillah

Comment



NoorEemaan
07082281566



I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial *131*4# or
*460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.

*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call 0806626851
[10/11, 7:47 PM] =ؖ?NoorEemaan=ؖ?: ABRAHAM

*First edition*



*WATTPAD*
@NoorEemaan



https://facebook.com/groups/943534712916776/
Masu amfani da Facebook sai kuyi join wan nan link din.




Chapter 35-36


*WASHEGARI*
Da safe sai da Aysha ta leko dakin sa taga yana baccin kafin hankalin ta ya kwanta, downstairs ta sauk'a domin d'ora musu breakfast, ta rasa meyasa ta damu dashi har haka, sosai maganar sa da fatan ganin ya samu lafiya ya tsaya mata a rai kwarai.






Tana shiga kitchen din babu bata lokaci ta fara hada breakfast, cikin har da light food da ta San cewa zai yi daidai da condition din Abraham yanzu.



Tana cikin soya potato omelet taji knocking daga bakin kofar, cikin sauri ta kwashe omelet din, domin already ya riga ya soyu, kashe gas din tayi ta wanke hannun ta a sink ta gyara wuyar hijab dinta ta fita izuwa kofar falon da aka kara knocking yanzu.










Tsaye taga wani saurayi mai kimanin shekaru 35 sanye da bak'ak'en suit. Da kallo ta bishi na yan seconds kana ta dauke kanta hadi da cewa "ina kwana" duk da bata taba ganin fuskar sa ba.



Saurayin kuwa cikin girmamawa ya russunar da kan sa, domin a tunanin sa Aysha Matar Abraham ce, duk da yaga alamun cewa ita din Musluma ce, amma ba Abin mamaki bane tunda hakan na faruwa, ma'aurata masu mabambamtan addin, kawar da tunanin yayi yace
"ina kwana Hajiya, suna na Kabeer Usman dama nazo neman sir Abraham ne, tun sanda ya dibi ma'aikata da kwana biyar Bamu sake ganin sa ba, ni ne personal assistant dinsa shine naso na duba ko lafiya domin na kira wayoyinsa basa shiga, yanzu ma ma'aikatan? zan wuce na biyo ta nan"




Shiru Aysha tayi tana tunanin Kiran madam Gloria domin ita kam wanna abun yafi karfin ta, amma kasa da sixty seconds k'wak'walwarta ya bata cewa tun baya da madam Gloria ta dawo da Abraham daga hospital bata kara zuwa duba shi ba, shin ita wace irin uwa ce a gareshi? ta aiyana a ranta.



Zuciyar ta ce ta kara sauya tunani, kamar yadda yayi tunanin ita din Matar Abraham ce, a hakan zata tafiyar dashi, cikin sauri ta dago kanta duk da gabanta na faduwa sannan tana addu'ar kada Allah yasa madam gloria ta tashi daga bacci yanzu...




murmurshi tayi tace "ohh! Mijina ya bani labarin ka, ka shigo daga ciki"
tace tana juyawa izuwa ciki yayin da gabanta ke tsananta fad'uwa domin gani take kamar ba Indon baffa bace ke wannan abun, amma ta kasa sarrafa kanta, kamar Wacce ake bawa umarnin yin komai daga ta ciki.



Bayan ya zauna kan d'aya daga cikin had'add'un kujeran falon, kitchen ta shiga ta kawo masa shayi a kofin tangaran, kabeer Usman ya karba yana godiya hadi da yaba karamcin ta a ransa.


Aysha kuwa crossing legs dinta tayi tace "Am... kuyi hakuri bai sanar muku tafiyar sa ba, domin a gaggauce abubuwa suka zo masa, baya kasar shiyasa kuka ji shi shiru, tunda ya tafi nima jefi-jefi muke waya da lambar kasar domin baya da lokaci sosai, sakamakon Abinda ya kai shi kasar mai muhimmanci ne, sannan idan na samu lokaci zan zo duba kamfanin na ga yanda kuke gudanar da aikin, domin zai dauki watannin kafin ya dawo, duk da dama ya fada min cewa yana da mataimaki wanda zai iya kula da company's sa ko da baya nan wato kai, ina fatan zaki yi aiki tukuru wurin rike ragamar kamfanin da amana kamar yadda Mijina ya fada, ya kuma d'aura maka yarda"

Aysha ta karasa tana dan goge wani gumi daya karyo mata ya biyo ta gefen fuskar ta...



Shi kuwa Kabeer Usman murmurshin jin dadi yayi saboda kalaman ta na karshe, cikin kwarin guiwa yace "in sha Allah zan rike amanar company, har Allah ya dawo dashi, duk wani abu dake faruwa zan dinga tura masa ta gmail din sa".




"Na gode kwarai Malam kabeer Usman" Aysha ta fada, tana dan mazewa wanda hakan ya kara mata kwarjini, kai kace wata babbar mace ce.



Kabeer Usman kuwa kara sipping tea dinsa yayi, domin yayi masa dadi over, kana ya Mike yana goge bakinsa, sallama yayi wa Aysha ya nufi hanyar fita daga falon, inda Aysha ta take masa baya har izuwa bakin kofar falon kana ta dawo ta zube kan kujera tana sauke numfashi, sosai ta jinjina karfin hali irin nata, tuno cewa madam Gloria zata iya fitowa at any time yasa ta dauki kofin shayin data zuba wa P.A ta nufi kitchen, wanke wa tayi ta mayar muhallin sa kana ta shiga gyara kitchen din, tana kokarin jera warmers a tray taji takun takalmin madam gloria na tunkaro kitchen din...



Cikin sauri hadi da girmamawa ta shiga gaishe da madam Gloria, a yatsine ta amsa kamar yadda ta saba, Bude warmers din ta shiga yi, kana ta juya domin fita, har ta je bakin kofar kitchen din ta juyo cikin gurbataciyyar hausar ta tace "wa ya shigo gidan. nan dazu"



Waro ido Aysha tayi gabanta na fad'uwa,?a hankali ta juyo tace "babu wanda ya shigo..." ta karasa cikin aro jarumta, ita kanta bata San dalilin boye mata ba, amma hakan zuciyar ta ke bata umarni.



"babu wanda ya shigo kika ce ?" madam Gloria ta fada tana bin fuskar Aysha da kallo a kokarin ta na son gano gaskiyar maganar ta.




"eh madam!" Aysha ta kara fada cikin dak'ewa fiye da dazu.

Kallon ta madam Gloria ta sake yi na mintuna biyu kacal kana ta jinjina kai tace "zo kiyi serving dina breakfast, zan fita yanzu"...



"toh" Aysha ta amsa tana cigaba da jera warmers din, a ranta tace

"na shiga uku ni Aysha, Mata da danta amma nafi zak'ewa akan al'amarin da ban San mafari ba" ta fada a hankali.



A sanyaye ta fita, ta serving madam Gloria kana ta haura sama domin yin wanka.


Tana cikin shiryawa taji fitar madam Gloria a mota, karasa shiryawa tayi a nutse kana ta leka dakin Abraham, kokarin mikewa taga yanayi amma ya kasa, instead sai ma zafi da yake ji, a sanyaye ta mayar da kofar ta rufe domin dama kadan ta bude shiyasa bai lura da ita, downstairs ta sauka, daga nan ta fita izuwa farfajiyar gidan, wajen mai gadi tace

"ina kwana"



"ah ah Indo ce, Kin tashi lafiya?"?
mai gadi ya fada yana washe hakoran sa da suka sanja kala zuwa brown.

"lafiya lau, dama yallabai zaka taya ni dorawa kan keken sa" ta fada cikin marairaicewa.





"yanzu kuwa indo do, Allah sarki yallabai mai kirki, gashi waccen uwar tasa ta fita, yaro ba lafiya amma taci wata uwar Kwalliya sai kace yarinya ta fita, babu abinda ta iya sai masifa da iya daga hanci" ya fada yana k'waik'wayon yanda madam Gloria ke daga hanci.



Aysha kuwa duk da kalaman sa na karshe ya bata dariya amma Bata yi ba, sai ma gaba da ta yi, domin tana daya daga cikin Wacce bata so ayi maganar wani, ko aibata wani da ita.

Mai gadi kuwa take mata baya yake, ya ja bakin sa ya tsuke ganin Aysha bata bashi fuskar cigaba da kowa mata wata maganar ba.



Sabanin dazu da yake kokarin mik'ewa, yanzu kawai ya kwanta ne ya Lumshe ido cikin kunar rai, yaji shigowar mutane amma bai Bude idanun sa ba bare ya ga ko su waye , karasa jikin gadon mai gadi yayi yana cewa "sorry sir, how Body? your body go soon better you hear, sorry oga na" mai gadi ya fada cikin pidgin English daya koya a nan kaduna, duk da tune din hausa ya fito sosai a harshen sa wanda hakan zai sa mutum ya fahimci cewa shi din bahaushe ne.



Abraham kuwa shiru yayi still bai Bude idanun sa ba, da k'yar mai gadi ya fara kokarin daga shi, jajayen?idanun sa sun firfito waje, kasa hakuri yayi yace "jar uba! Wallahi Indo oga ya shiga gasar dambe dole ya kad'a maza, karfi ne dashi sosai Al-k'uranin ubangiji"



Kasa d'aurewa Aysha tayi har sai da ta fashe da dariya cikin siririyar muryar ta da amon sautinsa ya fito, wanda hakan yasa Abraham Bude sexy eyes dinsa ya watsa mata su, saurin gimtse dariyar ta tayi, tana mai yin kasa da kanta.


Mai gadi kuwa bayan ya dora Abraham a keken sa da k'yar yace "Allah ya kara lafiya oga, Indo sai anjima" ya fada yana fita daga dakin cikin tafiyar sa ta sauri.




Shiru dakin ya dauka, can ta Kara sa wajen shi ta tura shi izuwa toilet, maclean ta matsa masa a brush, sabulu da soso ta ajiye masa a inda hannun sa zai kai, kana ta bar bandakin tana rufe masa kofa, gyara masa dakin ta shiga yi, ta goge masa komai, Airfreshna ta fesa a ko wani kusurwa na dakin, sannan ta shiga kitchen da gymimg room din sa ta goge hadi da gyara masa, domin babu wani datti sai kura kawai suka yi....



Bayan ta gama taji shiru bai fito ba, hakan yasa ta kara sauka ta dauka masa breakfast ta dawo, sai a lokacin ta fara jin alamun an Bude kofa, idanun ta takai wajen kofar inda yake fitowa, tozalin da ta yi dashi Yasa ta juya da sauri tace "Innalillahi wa innah ilaihi raju'un" sak'amak'on ganin shi data yi da short nicker kadai, domin ya cire rigar da dogon wandon jikin sa, domin sun ishe shi.



Da fari ya zata wani abu ta gani, sai daga baya ya fahimci abinda take nufi, sai ma ta bashi dariya, murmushi da iyakar sa labb'a yayi kana ya dawo da fuskar sa yanda take a had'e har girar sa na tattarewa...



Aysha kuwa ba tare da kara juyowa ba ta nufi wardrobe din shi, wani riga ta gani hadi da 3 quarter wando ta miko masa idanun ta a gefe, bai kalle ta ba ya karba hadi da sanya rigar, sai wandon daya sa da k'yar shi ma bai zauna da kyau a waist din shi ba, kasancewar a zaune yake wanda kuma bashi da ikon tashi domin hakan na daga cikin kaddarar sa a yanzu....




Sai da ta daina jin motsin saka kayan, ta shiga bude idanun ta a hankali ta kalleshi, take idanun ta suka fada cikin nashi, saurin dauke idanun ta tayi kunyar sa mai yawa na ratsa ta, hakan nan take ji a ranta cewa tana huce gona da iri wurin bashi kulawa, domin da bata yawan zuwa dakin sa bazata ganshi a haka ba, duk da cewa wanna ba shine karon farko ba, amma akwai bambamci da ganin data fara masa ba riga, sai dai bata da zabi daya huce kula dashi din, tunda babu mai kula dashi din baya ga ita, domin ko kafar mahaifiyar sa bata gani a dakin sa, wanda hakan ke daure mata kai sosai, kawar da tunanin tayi ta fara serving din shi Abinci, ta dora masa a cinya, Bayan ta caka fork kan Irish potato omelet din, sai tea data zuba masa a cup, dakin ya gauraya da kamashin mai shiga zuciya...

Idanun sa ta ga ya rufe ya dora hannun sa saman abincin ya fara addu'a irin na chiristian a lokacin da zasu ci abincin...



Kura masa ido Aysha tayi ganin abinda yake yi, domin ita kam bata da ilimi kan abinda yake yi, garin kallon nasa ne idanunta suka sauka kan cross(+) din wuyar sa dake rito, a ranta tace "Dama maza na sa sarka, oh ni Aysha Indo" ta fada a ranta tana cigaba da kallon sa, sai da ta ga yana k'ok'arin d'agowa tayi saurin dauke kanta zuwa wani bangare daban...





Da yamma Lubabatu ta samu Aysha a kitchen tana girkin dare, gaisawa sukayi, kana ta mikawa Aysha kudin albashin ta, inda Lubabatu ke sanar mata cewa tun jiya madam Gloria ta mata transfer na albashin su, amma iya su mata masu aikin gidan, domin yau tafiya zata yi ba kuma zata dawo yau ba, duk da Aysha tayi mamakin jin cewa madam tayi tafiya, amma ta 6oye mamakin ta hadi da yiwa Lubabatu godiya ta fita, domin bata taba bari hira mai tsayi ya hada ta da ma'aikatan gidan ba, domin daga nan kananun maganganun ke fara tashi har ta kai ga gulma, hakan yasa take tsaye kan Lane(iyaka)dinta.



Allah yaso ruwa kadai ta dora a gas din, sai kawai ta tafasa musu spaghetti, Bayan ta gama tayi musu egg sauce daya hadu sosai sai tashi k'amshi yake, daga nan tayi mango juice da zallan fresh mango sai flavour data saka, hadi da sugar kadan, sai da ta tabbatar komai yayi daidai, ta dauki warmers biyun da jug din mango juice din ta nufi up stairs dasu....


Dakinsa ta ajiye warmers din, kana ta nufi dakin ta tayi wanka, domin ya zame mata sabo matukar tayi girki sai tayi wanka take jin dadin jikinta, tana cikin wanka taji Kiran magriba hakan yasa ta d'aura alwala kana ta fito daure da towel a jikinta, mai ta shafa a jikinta sama-sama sannan ta saka inners hadi da riga da skirt na atamfar ta mai saukin kudi, dama ita ba gwanar Kwalliya bace, hakan yasa ta saka hijab dinta ta tayar da sallah...



*8:01pm*
Tana iddar da sallah'n isha ta fito domin zuwa dakin sa, ko ina shiru ba motsin kowa, a hankali ta nufi dakinsa, ta kama handle din ta shiga,
hango shi tayi a zaune idaunsa a Lumshe, girgiza kai tayi irin na tausayin nan ta shiga serving dinsa, sannan ta mika masa, karba yayi kamar dazu yayi addu'a sannan ya fara ci, lomar farko ya Lumshe idaunsa, saboda wani mugun dadi daya ratsa kwanyar sa, sosai yaci fiye da rabi kana ya ajiye, mango juice din ta siyaya ta bashi ya shanye, yana tand'e baki daya sa Aysha murmusawa a 6oye, Abraham kuwa a ransa yana yaba iya girkin ta, domin tun daga lokacin daya fara dandana girkin ta yaji cewa bana biyun ta a iya girki.



Aysha kuwa sai daya gama ta dauki plate mai dauke da ragowar abincin sa ta cinye ta kora da juice, a ranta tana jinjina karfin halin ta na yau, domin ko giyar wake ta sha bata isa cin Abinci a waje daya da Abraham ba, bare daga kwanon daya ci, matuk'ar madam gloria na nan, tana zaune a dakin shiru, sai goman dare ta koma dakinta ta kwanta...









Washegari da misalin karfe goma anty Bintu ta zo gidan, inda take sanar wa Aysha cewa gobe zata je gombe, amma kwana biyu zata yi ta dawo, tafiyar gaggawa ce ta taso mata, idan
Aysha nada sako ta kawo a kai wa Inna, domin yanzu haka kasuwa ta nufa...




Ai magiya Aysha ta fara yi cewa zata bi ta, dama tayi kewar su Inna, Anty bintu tace Sam bazata bi ta ba...

"waye zai dinga yiwa su madam girki? Indo

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login